Showing 9001 words to 12000 words out of 48659 words
Chapter 4 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
a falon
tana jiran futowarsa megidan
Ba ta jima ba sosai ya fito cikin shiga ta wani
danyen boyal baki sai sheki yake yi, hular kansa
baka mai gashi, takalminsa baki sai agogon
hannunsa na Daimond. Duk sun yi kyau kamar wadanda za su zaben
sarauniyar kyau. Ya yi waje ba tare da ya kalle ta
ba, ta mike ta rurrufe ko ina ta fito tana takawa
sannu a hankali yana kallon ta ta mudubin motar,
duk sha awarta ta motsa shi, amma saboda iya jan
ajinsa ba zai taba nuna mata ba, ko ya bari ta gane ba.
Ta kama murfin mota ta bude ta shiga baya ta
zauna, be kalle ta ba kuma be yi mata magana ba
be kuma ja motar ba. Ya yagi takarda ya yi rubutu
ya cilla mata baya ta dauka ta duba, "Ba ki kai
matsayin da zan zama direbanki ba, "Tana gama karantawa ta bude ta fito ta dawo gaban motar ta
rufe.
Ya kuwa figi motar a guje kamar me shirin tashi
sama. Babu wanda ya yi wa kowa magana haka
suke tafe sai da suka zo wani super market ya fita
ya yo musu tsaraba suka ci gaba da tafiya. Gidansu ya fara kai ta, yana tsayawa ya mika mata
takarda ta duba ta karanta a wa daya na baki ki yi
ki fito mu tafi. Ba ta ce komai ba ta bude ta fita ta yi
sallama falon ta shiga.
Aunty tana ganinta ta mike ta taro ta da murna tana
jawahir 'yata barka da zuwa 'yata ta kaina." Ta rungumeta ta a jikinta, "Zo mu hau sama Alhaji
ya ganki tukunna, "Suka hau ta durkusa har kasa
ta gaida Abba cikin fara'a da murna yake amsawa,
"Jawahir ke ce haka? lallai yau zan huta da mitar
Auntynki."
Aunty ta ce, "Wa ya kawo ki ne? ko kun dauki direba ne?
Cikin jin kunya ta ce, "Ai yaya ne ya kawo ni.
Tana rufe baki ya yi sallama ya shigo kai tsaye ya
wuce gaban Abbansu ya zauna ya gaishe su. Abba
ya dafa kan Haidar ya ce, "Yau na ga jawahir na
gode muku da yanda kuka rike kanku ba ku mu kunya ba.
Haidar ya ce, Yanzu ma cewa ta yi na kawo ta za ta
dauki Sayyid ga shi ban gan shi ba. Aunty ta ce,
jawahir ta Sayyid ai yanzu ba irin da ba
ce da kike zuwa ki dauke shi ya yi kwana da
kwanaki a gidanku yanzu ai sai ya takuraki. Cikin jin kunya ta ce, "Lah Aunty wallahi ba komai
ai ba zai takura ni ba.
To shikenan gobe za a kawo miki shi ya yi kwana
biyu kawai.
Ta ce, to Aunty na gode. Aunty da kanta ta kawo
musu abubuwan ci da sha suka sauko kasa da Aunty. Duk yanda Aunty ta yi
don ta ji ko da wani abu a tsakaninsu amma
jawahir ta ce kalau suke. Haidar ya shigo ya yi wa
Aunty sallama ya fita
jawahir ta kalli agogon hannunta ta ga awa dayan
da ya ba ta saura minti uku ta mike ta ce Aunty zamu tafi.
"Haba jawahir tun yanzu?
Ta ce, Ai za mu bi ta gidanmu da gidan inna. "To
jawahir na gode Allah ya yi muku albarka.
Manya ledoji biyu Aunty ta ciko mata da kayayyaki.
Abba kuma ya ba ta dubu ishirin. Daman Haidar ya sa maigadi ya shigo musu da tsarabarsu. Ta bude
motar ta shiga awa dayan ta cika dai-dai shi ma ya
shigo suka tafi. Gidan Inna ya kai ta shi ma sai da ya
ba ta takarda
ta karanta kar ki wuce awa daya. Ta shiga gidan
inna murnarta da tsallenta ta cukuikuye inna. Inna ma murna take yi ta zaunar da ita "Daga ina haka?
ke me Haidar din yake baki kika sake zama
baturiya haka sai dai rashin kiba amma kin kara
kyau ko dai ciki ne dake?
Daidai shigowar Haidar a zuciyarsa ya ce, "Ciki yaya
za ayi ayi ciki yanzu ai ta yi kankanta. Ya yi sallama falon ya shiga inna ta tare shi da
murna duk bakinta yaki rufuwa ganin jikokinta
shar dasu babu wata alamar damuwa a tare da su.
Inna jikinta sai rawa yake yi ta rasa inda za ta sa
kanta don murna, ta kawo musu wancan ta kawo
musu wannan tana ta hira. "Dan ka'ida bature ya duba agogo saura minti biyu
awa daya ta cika Haidar ya yi wa Inna salllam ta
rinka yi masa godiyar wannan uwar tsarabar da
suka kawo mata.
Ya fita ya koma mota yana jiranta. Sai hira kuma ta
dawo sabuwa tsakanin inna da jawahir har ta manta da dan ka'ida lokacin da ya ba ta, to tana ta
shan labarai da abubuwan ban dariya daga inna.
Ba ta yi aune ba ta ga kara minti arba'in da biye a
kan awa dayan da ya ba ta zumbur ta yi ta mike
inna za mu tafi sai kin zo. Inna ta ce, Au ba sai
magariba za ku tafi ba? "Ta ce, "Uhm yana mota yana jira na.
"To shi ke nan na gode ku gaida gida. Allah ya yi
muku albarka. A cikin mota ta same shi ya kwantar
da kujera ya
na shan A.C da sautin rediyo ya lumshe ido kamar
mai bacci. Ta bude mota ta shiga ta zauna. Ta fi minti goma ba
shi da niyyar ta shi bare ya tuka motar su tafi. Ta
gaji da jira ta ce, "Yaya na fito. Ya bude ido daya ya
ce, Awa nawa na baki.?
Ta ce, "Awa daya." "Sai yanxu awa dayan ta cika.?
"A'a Inna ce ta tsayar da ni da hira." "To kin cinye lokacin da za ki yi a gidanku, yanzu
gida za mu tafi sai wani lokacin kuma."
Gabanta ya fadi, duk da dokin da take yi na zuwa
gidansu ga shi ta fito din amma ba damar zuwa
gidan nasu.
Ita girman kanta ba zai bar ta ta ba shi hakuri ba bare ya hakura yakai ta. Kawai sai ta ji hawaye
yana zubo mata.
Haidar na kula da ita amma sai ya dauke kansa ya ci
gaba da tukinsa kamar be san tana yi ba. Tana
kukanta har da shassheka amma sai ya karo
rediyon ma don kada yaji kukan. Ba wanda ya sake cewa da kowa komai har suka je
gida
Yana tsayar da motar ta bude ta fito tana goge ido
ta bubbude ta shiga dakinta ta fada gado ta yi rub
da ciki ta ci kukanta ta koshi.
Ta shiga ban daki tayi alwalla ta yi sallar la'asar zuciyarta tana ta zuga ta da kada ta yi masa girki
don ya dan dani bacin ran da ta ji, to kuma sai ta yi
wani tunani ai ita ta fara bata masa kuma girman
kai ya hana ta neman afuwarsa to idan ba ta yi
masa girki ba ai ta dada shiga hakkinsa kuma ita ba
iya cewa za ta yi ya yi hakuri ba, kuma zai yi bacin ran da ya fi nata, ita kuma ba burinta ke nan ba.
Duk da irin zaman da suke yi na rashin yiwa juna
magana to amma ba ta so ko kadan ta ga ta bata
masa rai. shi yasa kullum take yin abin da ta san zai
ji dadi.
Ta mike ta fito falo takarda ta gani a ninke, "Na fita unguwa sai magariba zan dawo," Ta yaga takardar
ta fada kicin ta dora girki .
Yau tuwon samovita ta yi miyar danyan kubewa da
ta burge kaza a ciki. Sai ta gasa masa dan shila ta
soya masa kifi ta hada
masa lemon abarba ta jere komai a tebir. Yau Dela ta bawa wanke wanken don zuciyarta a
bace take.
Kafin ya dawo ta gama abin da take yi ta gyara
wajen ta shige dakinta ta kulle kofa. Sai da ya yi
sallar magariba sannan ya shig, ga
mamakinsa sai ya ga tayi abinci a zatonsa yanda ya bata mata ba za ta yi girkin ba, har yana shirin fita
Hotel ya siyo musu.
Duk kuma sai ya ji tausayinta ya dame shi a ransa
sai ya yi da yasanin bai ki kai ta gidan nasu ba. Ya
zauna ya ci abincinsa ya koshi yau har da senti
ya mike ya je ya sake alwalla ya yi sallar isha'i. Haka ya yi zaman falon har goma na dare amma bai ga
fitowar ta ba, abun ya dame shi dan be ji dadin
yanda ta takura kanta ba. Haka tai ya hakura ya je
ya kwanta zuciyarsa ta na
ta tunane tunane.
"Washegari da safe da ta gama komai da ya shafe ta ta daddasa kwalliyarta yadda ta saba ta fito yana
tebir yana break ta durkusa ta ce, "Ina kwana.?"
Ya amsa, "Lafiya lau jawahir kin kwana kalau.?"
"Lafiya kalu." Ta ce ta mike tana koma daki tana
mamakin canjin
yau da ta samu na sakin fuskar Haidar. Har ya fadi sunanta ba tare da ya ce mata kwaila ko
tatsitsiya ba.
******* ******** ****** ******** Haidar bai
dade ta fita ba direba ya kawo Sayyid,
jawahir ta yi murna da farin cikin ganin sayyid don
ta samu abokin debe kewa. Sai magariba Haidar ya dawo sayyid yana jin karar
motarsa ya fito a guje ya tarye shi, Haidar ya dauke
shi ya rungume shi, "Auta wa ya kawo ka? ina ka
baro Auntyn taka?
"Tana gida Abba ya ce kada na dade kwana biyu
zan yi." Haidar duk ya gama wani abu da zai yi na game da
cin abinci, wanka ya sa kananan kaya na shan iska
ya haye saman gado yana shan surutun Sayyid da
yake ba shi dariya. Wayarsa ta fara ruri alamar ana
kiransa. Haidar ya duba ya ga bai san lambarba ya
share ya ki dauka, ta katse dan kanta, can aka sake bugowa be dauka ba ta kuma katsewa. Sai da aka
yi sau biyar a na shi dan Haidar ya gaji ya dauka,
"HELLO. Ya amsa a kasan makogaronsa. Cikin doki
Kausar ta amsa, "Ranka ya dade saraki
har yazu mulkin yana nan ne ba a sauke ba?"
Ya ce, "Wake magana ne? ko sai na ajiye kan wayar ne.?
Ta ce, "A'A ayi hakuri Saraki kausar ce.
Yac, "Wa cece kuma me wannan sunan.? "Ranka ya
dade Saraki Kausar dinka da kuka yi
karatu America tare ka gudo ka bar ta.
"Oh. Kausar kenan kin cika na ci, yanzu sai da kika lalubo ni."
"To ya zan yi Haidar wallahi tun ranar da ka taho
ban kuma nutsuwa a zuciyata ba sai yau da na ji
muryarka. Haidar ciwon son ka ya zamo gyambo a
cikin zuciyata. Haidar ni musulma ce ka tallafi
rayuwata Haidar ka zo gare ni ka aure ni. "Haba Haidar ka san darajar 'ya mace da kimarta
amma duk na watsar na tunkare ka na ba da kai na
ke rokonka da ka aure ni. Haidar wace irin zuciya
ce da kai? Ka tuna fa kana
da kanne mata kuma nan gaba in Allah ya ba ka
haihuwa kila ka samu 'ya 'ya mata, to ya za ka ji yayin da 'yarka ko kanwarka ta fada irin wannan
halin da na fa da akan kan wani? Ka san kaddarar
ubangiji babu inda ba ta fadawa mutum." Haidar ya
ce, Ki yi hakuri ba burina na yi miki
wulakanci ba, ai duk inda masoyinka yake ya fi
makiyinka sau dubu, to amma kin ga yau shekara daya ke nan iyayena sun hada ni aure da wata 'yar
karamar kanwata, wadda har a yanzu da nan gaba
rainonta nake yi." Kausar ta ce, Haidar don Allah
don Annabi ka
amincewa bukatata wallahi ni ba ruwana da wata
matarka don ba a kanta zan zauna ba. Ya ce, "To shi kenan Kausar ki ba ni lokaci zan yi
shawara.
Ta ce, "Haba Haidar. Ya ce, "Uhm no kada ki damu
ba matsala insha
Allahu komai zai zo da sauki.
Suka yi sallama kowa ya dire wayar. Haidar ya fada tunani ko na amince da bukatar Kausar na aure ta,
ko ni ma na ji yanda auren yake? To ya zan yi da
Aunty da Abba? ko da yake in sha Allahu ba za su
zamo matsala ba. Haba dai ya kwanta yana sake-
saken abinyi.
Washegari yana office wajen azahar jawahir ta yi baki kawayenta ne suka zo. An sha hira kuwa inda
jawahir take cewa, "Bilki ai kun yi min rashin
mutunci wai duk yanda muke da ku aure shekara
daya amma kuka kasa leko ni."
"To ai kin san abun ne sannan ba kwa shiri da shi
mu zo wani abun ya faru sai ya zamo matsala, some kin ga yanzu ai komai normal don yanda kike
wannan kyallin goshin na san an samu rabo ma
( Hahaha kunji gulma. Hmmm Ni dai Bomboy ba
ruwa na idan Haidar yaji ku).
Ta yi dariya, "Uhm kwa ji da shakiyancinku ku zo
mu ci abinci." Wajen karfe hudu suka gama shirinsu suka fito za
su tafi ta yo musu rakiya har bakin get, megadi
yana dan dakinsa yana lazimi, Hira suke yi suna
tafawa tare da shewa da dariya. Sai ga motar Haidar
ya.
[8:35PM, 12/6/2016] : shigo ya danna hon megadi ya taso da sauri ya bude masa get. Haidar ya hango
jawahir ba mayafi a jikinta ta yi
kwalliya tana ta faman dariya duk sai ya ji kishi da
bakin ciki ya dame shi.
Yaya za ayi ma ta fito nan a haka? Ga megadi da
'yan aikin gida suna nan du su gano ta. Lallai ma yarinyar nan. Ya yi parking ya fito gunsu ya nufa
kawayenta suka gaishe shi ya kalli jawahir ke me
ya fito dake nan? Wa ya ba ki izinin zuwa kofar
gida.?
Kanta a kasa ta ce, "Kawayena ne suka zo shi ne na
rako su. Rakiya ba ta isa ba iya kofar cikin gida har sai kin
fito bakin get.? Ya shige ciki ya bar ta a nan.
Kawayenta suka ce, "Lallai Haidar yanzu har wani
kishinki yake? "To Allah ya sa dai mu jawo miki
wata matsalar ba.?"
Ta ce, "Haba dai ba komai ai yana da saukin kai shi ke nan kuma fadan ya wuce. "To mu dai mun tafi
sai wata rana."
Suka fita ta juyo ta shigo cikin gidan. Yana zaune a
falo ta tafi za ta shige daki ya ce, "Ke
zo nan.
Ta dawo ta durkusa nesa da shi. "Daman in ba na nan bain da kike yi ke nan ko? Kalle ki yanda kika
fita ga megadi da yaran gida duk suna ganin ki ko
kin manta cewar ke matar aure ce? To bari ki ji duk
da an aura min ke ba tare da ina son ki ba, to
hakan ba zai hana ni yin kishinki ba, kuma dole ne
na sa miki ido don ganin yanda kike tafiyar da rayuwarki, kada na kara ganin wata kawa ta zo
miki kin ba ta fuska bare su zo su bata miki tarbiya
ko su rinka zuwa tsegumi su samu damar bugun
cikinki kina gaya musu sirrinki ko?
Ita dai ba ta ce koami ba ya karaci fadansa ta tashi
ta yi shigewarta daki. Tana barin wajen wayar Kausar ta shigo, "Hello Kausar kina lafiya.? "Lafiya
lau Haidar shiru banji ka ba.
Ya ce, "Kai kausar kin fiya gaggawa, amma ki ba ni
adres din gidanku insha Allahu jibi zan zo, ta saki
wani ihun murna yayin da take gaya masa adres
din gidansu dake Abuja. Suka yi sallama ya ajiye wayar. Washegari yana zaune a office ya kifa kansa
da
tebir tunanin yanda zai bulluwa da iyayensa
maganar Kausar yake yi.
Abokinsa ne ya shigo ya sa me shi a haka. Duk
sallamar da yayi bai ji shi ba bare ya amsa masa. Faruk ya kwankwasa masa tebir din gabansa.
Haidar ya yi firgigit ya dago kansa ya kalli Faruk din
ya saki ajiyar zuciya. Ya ce, "Yaushe ka shigo ban ji
shigowarka ba.?
Faruk ya ce, "Yaushe dama za ka ji ka tafi cikin
wannan zurfaffan tunani haka, wai don Allah me yake damunka ne? jiya da yau duk wani sukoko
nake ganin ka.
Ya ce, "Ga ni nan dai abubuwan ne suka tarar min
"Ba dai matsalar jawahir ba, ca nake mun gama
wannan maganar da kai.
Haidar ya ce, "Ai ni ba zan taba iya abun da ka ce na yi ba. Ciknin zaro ido ya ce, "Ba dai kana nufin har
yanzu
babu abun da ya hada ku ba?. Aure shekara daya.
"To kai me kake tunanin zai faru? kanwata ce fa.
yarinya ce, ko hannunta na kama ai raina ni za ta
yi." Faruk ya ce, "Amma wallahi kana daukan
alhakinku. Gaskiya ba ka kyauta ba, yaya za ka
rinka wahalar da yarinya, kana zaton dutse ce ita
ko waliya ce da ba za ta ji sha awa ba?
Haidar ya ce, "Ko dai take wahalar da ni tana gasa
ni, ka ga dai ni nake gaba da ita ya kamata ta fara neman sulhu da ni, to amma yarinyar nan gaisuwa
ce kawai da safe take hada mu. Ga yarinyar ta iya
tsara kwalliya komai ta sa sai yayi mata kyau ya yi
das a jikinta kamar Aljana.
Duk dare yanzu bacci gagarata yake yi, na dinga
murkususu ke nan ina juyi sai ka ce dole, ai ba waliyyi ne ni ba, don haka na yanke shawarar aure
zan kara a kwanan nan.
Faruk ya dafe kirji ya ce, "Aure Haidar! kai kuwa me
yayi maka zafi? Ba gwanda ka nemi sulhu da
matarka ku dai daita ba. :
(Hmmm barshi da kanshi zai sauke wannan jiji-da- kan. Mu dai yan kallo ne kuma yan rahoto. Da fatan
dai idan anzo kamen dan leken asiri ba zaku nuna
ni ba).
((((((((((SALON SO)))))))
(((((PART 16 TO 18)))))
:
BY SULAIMAN BOMBOY.
.
Haba Faruk yaya za a yi na kwantarwa da wannan karamar yarinyar kai. shi kenan na ba da kaina
girma kuma ya fadi, ni dai kawai aure zan yi na
rabu da ita ta karaci tsiyarta ita kadai.
Faruk ya daure fuska alamar ba wasa ya ce, "To kai
duk abun da ake gaya maka ba za ka ji ba ko, to
shi kenan ka je ka aika ta abun daka ga dama, in kuma abu ya kwabe maka kada ka sake ka nemeni
tun da ban isa na ba ka shawara ka dauka ba,
"Faruk ya juya ya fice tare da bugo kofar.
Haidar ya yi ajiyar zuciya tare da tallefe kansa da
hannu biyu, "Gaskiya ba na jin zan iya fasa auren
nan, ni kawai zan yi auren nan ne don debewa kaina kewa da sha awa saboda kullum ni na san
yanda nake kwana ina cutuwa.
To me yayi zafi ni dai ba zan kai kaina ga halaka ba
bare na nemi matan banza Allah ya kiyaye mu da
aikata zina gwara kawai na yi auren, "Haka dai
ranar ya wuni babu wata walwala. Alhaji Sa'adu mashi, babban ma'aikacin gwamnati
ne wanda aiki yake yawo da shi ko ina a Nigeria. A
haka ne ya zo Kano inda ya yi gida ya tare da
iyalansa. Da yake makotaka suke da gidansu
Haidar to sai shakuwa da aminci suka shiga
tsakaninsu. Kasancewar Alhaji Sa'adu ba shi da wani dan uwa a
garin kano to da ya samu Abbansu Haidar sai ya
rike shi ya zama dan uwanshi na kut da kut.
Faruk da Haidar sa'o'in juna ne tare suka ta so
iyayensu suka sa su primary tare, secondary ma
tare Faruk da Haidar sun shaku da junansu. Abun ya wuce abotaka ya koma 'yan uwantaka. Bayan
gama secondary dinsu ne aiki ya kuma mayar da
Alhaji sa'adu gida wato katsina ya tatara iyalinsa
suka koma can gida. Hakan kuwa bai yi wa su
Haidar dadi ba sai dai don
basu da yanda za su yi ne, to daga nan ne Haidar da yaya