Showing 42001 words to 45000 words out of 48659 words
Chapter 15 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
ta shiga ta feraye doya ta dora a wuta ta debo
manyan busashen tarwada ta farke cikinta ta kan kare ta kwara masa ruwan
zafi.
Ta hade markade iya ta yi mata abu landa doyar ta dahu ta tsame ta mika wa
iya ta daka mata sakwara, ta hade miyar busashen kifin nan da ta ji onga, kori,
reko, mai da sauren kayan da su ke sa girki armashi, sannan ta cuko zallar
tsokar nama a firinji ta tafasa shi da albasa gishiri da dan magi.
Bayan ya tafasa ta kwankwatsa attaruhu albasa ta dakko tafasashen naman
nan ta hada a turmi ta daka.
Ta ciro shi ta rinka dunkulawa ta fasa kwai ta zuba gishiri onga reko ta dora
manta a wuta ya dau zafi ta rinka daukan dunkulan naman nan tana tsoma sha
a rwan kwan tana sa wa a manta na soyawa, ta gama wannan ta zo ta yanka
salak ta yi masa wanki sosai ta zuba a filet, ta yanyanka tumatur da albasa ta
gewayesu a saman salak da albasar ta kawo dafaffiyar hantarta da ta yi mata
kananan yanka ta zuba a kai.
Bayan ta yada salak, cream ta zuba heinze beans a tsakiya duk wanda ya kalli
hadin salak din dole yawunka ya tsinke, ta debo kayatattun fulas dinta ta zuba
komai taje ta jere su a santara tebir.
Ta debo fararen gobarta manya ta markada ta tace dusar ta markada kankana
da gwanda da ayaba a duk ta tace dusar ta hada akan ruwan gwaibar, ta
daddara rake ta matse ruwan ta hada akai, ta zuba ruwan kwakwa da ruwan
markadaddiyar aya ta zuba madarar ruwa gwangwani biyu ta kawo zumarta me
kyau ta zuba a ciki ta juya ta saka a firinji.
❤❤❤SALON SO❤❤❤
.
❤❤❤ PART 39 ❤❤❤.
..
By Sulaiman Bomboy.
.
"Subhanallahi! Lallai jawahir kin hada kyakkywan
lemo mai saurin saukar da ni'ima a jikin ta bar wa
iya rama ita kuma ta kara gyara falon da dakin megida ko ina ta turare shi da daddadan turaren
wuta na kamshi kowacce kusurwa ta feshe ta da
Air freeshner.
Ko ina ta sa ka AC sai sanyin dadi ne yake fita ta
gyara toilet ma shima ta turare shi da daddadan
kamshi, ta rufe sashinsa ta fito ta sakko ta shiga nata sashen ta sake gyarawa ta saki kamshi ta fada
toilet don yin wanka, ta dade tana murzar jikinta da
daddadan sabulu ga ruwan wankan nata ya sha
turaren wanka sai turarin kamshi ne yake tashi
Uku da rabi ta fito daga wanka ta dauro alwala ta
zo gaban mudubi ta fara tsara kwalliya shafa nan goge nan ko ina ya yi das, ta fara gabatar da sallar
la'asar, ta tsara kwalliya da wani pink din les mara
nauyi sai dai anyi masa shafi a ciki, duk da rigar fitet
ce ta dan fara kamata ko don cikin jikinta de da ya
fara bayyana, duk wata gaba ta jikinta ta mulke ta
da turaren kamshi, ta fesa na fesawa ta daura dan kwalin les din ya lafe kan gyaran gashin da ta yi.
Gaskiya ta yi kyau wannan da gasar sarauniyar
kyau zata je babu abin da zai hanata lashe gasar. Ta
dakko turare tana sake fesawa, daidai lokacin da
Haidar ya shigo da kyar yake daga kafa don
tsananin gajiya da yunwa tun break dan safe. Ya zube a kujerar falo yana mai nishi, "Bebina."
"My love." Jawahir ta fito daga cikin daki ta zagayo
gabansa idonsa yana limshe kamshin turarenta da
ya ji ne ya sa shi bude ido.
Subhanallahi, duk kyan jawahir sai yaga yau tafi
kullum kyau kamar wata fure aka dasa don kyau tuni gajiyar da ya kwaso ta ware, ya jawo ta
cinyarsa yana yi mata wani fitinannen kallo mai
tada sha'awa da raunannar zuciyar mai bege.
Ta sa hannunta ta rufe masa idon ya ciji hannun
nata ta yi saurin janyewa ta langabe kai cikin
shagwaba tana 'yar kara tare da yarfe hannun nata.
Shikuwa Haidar tuni ya samu damar zira harshensa
a kyakkyawan bakinta, ya dade yana sumbarta ta
cikin shaukin so da igiyar bege da kyar ta zare
jikinta sakamakon wani nishi da ta ji yana yi gudun
ka da ta jawowa kanta jan gwam ta yi saurin haye wa samanta ta fada toilet dinsa ta hada masa ruwan
wanka, tana fitowa daga toilet din taga ya shigo
idon sa duk ya yi ja saboda fitina, ya sake jawo ta
ya mannata a jikinsa ya sake rungume ta ta
langabe cikin shagwaba take cewa, "My love ka je
ka y wankan kai muke jira fa Bebinka be ci abinci ba. Ya yi saurin cika ta ya dago kai yana shafa cikin
"Haba don Allah me yasa za ki bar min beby da
yunwa kina so ya galabaita ne, taho muje na fara
baki abincin tukuna, in kin koshi nayi wankan. Ta
make kafada ta ce um um ni dai ka shirya muje mu
ci tare. Ya jata ya zaunar da ita a gefen gado, to zauna nan yanzun nan zan fito ba zan dade ba.
Ya shige toilet din da sauri ita kuma ta tashi ta
dakko masa kayan da zai saka farar shirt ce da
bakin wando, ta feshe su da turare bai jima ba ya
fito daure da tawul sai wani akansa, ta yi saurin
tashi ta ciri tawul din kan nasa ta fara goge masa jikinsa, ta jashi gaban madubi ta shafe masa jikinsa,
da lafiyayyan cream me taushi da dadin kamshi, har
da shafa masa farar, hoda ta feshe shi da turare ta
ware masa kyansa ya karba ya saka.
"Au my love na manta ban sa maka man lebe ba"
ya sunkuyo da kansa ta shafa masa. "Inye! Nawan ba, ka kara kyau. Ya yi murmushi
tare da manna mata kiss a lebe ya riko ta suka taho
falo.kasa
suka sauko da kayan abincin ya hau kan kafet aka
baje don jawahir tafi sakewa.
Ta je firji ta tsiyayo hadadden lemon ta a je ya dau sanyi kuwa, ta zo ta ajiye ta dauki babban filet ta
bude fulas din ta sako musu sakwarar ta bude
miyar yayin da kamshinta ya bugi hancin Haidar ya
limshe ido yunwarsa ta dawo sabuwa, ta bude
daya filas din shima ta zubo musu hadin curaram
naman da ta soya da kwai, ta bude farantin hadin salak ta kalli Haidar ta ce, "My love bismillah.
Ya kalle ta yana murmushi sannu bebyna na gode
miki Allah ya saka miki da alheri Ubangiji ya yi miki
albarka, burinki kullum ki faranta min ki yi min abin
da zai sani farin ciki.
"To my love in ban yi maka ba wa zan yi wa, ina alfahari, ina matukar farin ciki da baiwar da Allah ya
yi min ta haduwa da gwarzon masoyi
Suka fara cin abinci dole jawahir ta rinka kyalkyala
dariya saboda yanda Haidar ya ta karkare yana ta
ziri tare da suba santi.
Komai sai da suka ci su ka koshi suka yi kat da su. Jawahir ta rinka tsiyaya wa Haidar hadin lemon
yana sha yana zuba santi shi dai ba don ya ji cikinsa
yana barazanar fashewa ba da ba zai bar sha haka
ba.
Jawahir ta kwashe kayan ta mayar kicin Haidar ya
jingina da kujera ya mimmike kafa ya dauki romote din tibi yana danne dannan tashoshi.
Jawahir ta dawo ta zauna ya juyo ya kalle ta cike da
kulawa yana murmushi ya ce, "Ya aka yi ne
bebyna? Ta jawo jikinta ta kwanta a cinyarsa cike
da sangarta, ya sa hannunsa kasan mararta yana
shafawa ya cire dankwalinta yana yaba kyan gashinta ya koma shafa kumatunta yana yaba
santsin fatarta da taushin jikinta kamar auduga.
Ya dora hannunsa kan kirjinta yana shafawa tare
da limshe ido jawahir ta ture hannunsa tare da
cewar "Meye haka kake yi a jikin ta tsitsiyar
kwaila.?" Ya yi saurin rufe mata baki da nasa ya dinga sumbatarta yana ruda mata jiki da wasanni
har sai da ya tabbatar ta manta da maganar
tukunna ya cikata.
Ikon Allah kenan duk yanda jawahir ta tsani
halayyar Haidar ba sa shiri da juna ba sa son
junansu, yau ga shi sun fi kowa kaunar junansu. Halayyar Haidar da jawahir ta tsana ta muskilanci da
kasaita da jan aji tare da rashin hayaniya ko
kwarniya yau tafi kowa murna da alfahari da
muskilancin Haidar da daukan kansa hade da
isarsa da kasaitarsa.
Tun da babu wata budurwa da ta isheshi kallo bare a kai gabatun magana har ya furta mata so, bata isa
ba kowacce.
So, kauna, aminci, yarda, shakuwa, duk ya tara su
ga tauraruwarsa jawahir. Bangaren Haidar kuwa
kullum sai ya yi wa iyayensa addu'a da fatan
gamawarsu da duniya lafiya saboda yanda suka hada shi aure da jawahir yanda da ya tsani
halayyarta ta miskilanci yau ga iyayi shagwaba.
Yanzu ga shi sun zamo abin alfaharinsa don suna
dada hura wutar kaunar jawahir a zuciyarsa.
Hakika ya yi sa'a da ace da samun kammalalliyar
mace ga kyau ga tsafta ga addini, ga usuli me kyau. Allah ya yi mata baiwa kala-kala na iya furta kalami
wanda lokaci daya zata siye zuciyar mai sauraronta.
Abu na biyu ta iya sahirtaccen kallo wanda zai jawo
afkawar mutum kogin begenta. Abu na uku ta iya
kissa da mutum ya so ta ko da baya ksunarta. Abu
na hudu yarinya ce me nutsuwa ga ta da ladabi da biyayya ga hakuri da tawakkali duk ta tara su.
Abu na biyar ta iya nau'ika na girki da abubuwan
sha ga ta da zakin hannu don duk wanda ya ci
girkin ta yai ta zuba santi da ya bawa kenan.
Abu na shida ta iya kwalliya gwanace wajen amfani
da hadaddun turaruka masu dadin kamshi, da san sutturar da ta dace ta saka kowanne yanayi da
kowanne lokaci.
Abu na
bakwai gwana ce wajen iya tsafta da gyaran gida
tun daga dakunnansu falukansu zuwa kicin
bandaki harabar gida ko'ina da launin turaren da take kamshinsa da yake yi
Abu na takwas ta riga ta gano makamar kama
Haidar domin ta fuskanci abin da ya fi so a jikinta
wata kirjinta, don haka koda yaushe ta kasance
cikin gyara kirjinta tare da sake kaya masu fito
mata da surar kirjinta. Abu na tara ta iya tarairayarsa tana ba shi
kyakkyawar kulawa ta siye zuciyarsa da
kyawawan halayenta, abu na goma na karshe
kuma, ta san sirrinkan kwanciya yanda duk yanda
ya juyata haka take binsa kowanne kokaci kuma
akwai sabon samfarin da zata gudanar masa a makwancinsa.
Ba ta gajiya da shi tana dauriya da jure bukatarsa
har sai ya gamsu don kanshi ba ta da korafi bare ta
nuna gajiyarta, ko ta ce ya fiye fitina
Wa'yannan halaye su ne suka ingiza kaunar
jawahir take dada ruruwa a zuciyar Haidar. Kwance tashi wajen Ubangiji babu wuya, ga shi
cikin jawahir ya shiga wata tara komai na haihuwa
sun tanada sai jiran haihuwar kawai suke yi.
Wata sabuwar sangarta jawahir take yiwa Haidar
saboda ganin yanda take bata tsantsar kulawa.
Cikin nata ya yi nauyi duk da haka ba ta yi sakaci da girkin megidan nata ba, bata sakaci duk yanda
Haidar ya kai da lallaminta da lallabata baya son
yaga tana wani aikin wahala don haka duk safiya
yake shiga kicin ya hada musu break.
Ya taimaka ma ta ta yi wanka shi yake yi mata
kwalliya, ya sa mata kayan da ya san baza su yi mata nauyi a jiki ba, ya rungumo ta zuwa falo kan
kafet ya zauna tana rungume a jikinsa yana bata
break a baki, sai daki ya kwantar da ita a gado
kamar wata jaririy yana yi mata tausa da matsa
sannu a hankali sai ya ga ta yi bacci sannan zai
shirya ya tafi office. Sha biyu na rana jawahir ta tashi daga bacci sannu
a hankali ta mike ta nufi kicin ta fara hada
abubuwan da zata dora girki, duk wani yanke
yanke da dake dake ko markade a bulanda me
take yi mata.
Ita kuma tana kula da girkinta da kuma hada lemummukan da ta san mijinta yafi so da sha'awar
shi.
Karfe biyu taje ta yi salan wayar Haidar ta sake
shigowa bugowarsa ta hudu kenan bayan tashinta
daga bacci.
Ta dauko "Hello Honey, na baka gajiya da yo waya ko"?
❤❤❤SALON SO❤❤❤
❤❤❤ PART 40 ❤❤❤
.
BY SULAIMAN BOMBOY
.
Bebyna ya za ayi na gaji da jin muryarki hasken
zuciyarta tare da jin lafiyarsu ita da bebyna.
Ta yi shashshekar dariya cikin kissa da jan hankali ta makale murya tare da lankwasar da murya ta yi
masa magana cikin yanga da marairaita.
"Honey na ka kwantar da hankalinka kalau muke
ni da bebynka, sai dai muna kewar dumin jikinka
na dan lokaci."
"Okey, beby na kada ki damu karfe hudu zan dawo gida mu kasance tare zuwa wayewar gari ko beby
na?"
Ta ce "Um hum thank you Honey na, sai ka dawo
muna jiranka.
Ya sumbaci wayar ya huro mata isa ta cikin wayar,
ta shashshekar dariya da ta saukar wa da Haidar matsananciyar kasala yayi saurin ajiye wayar tare
da jan diguwar ajiyar zuciya.
Jawahir ta mike ta koma kicin ta debo fulas fulas
dinta ta malmala tuwon farar shinkafarta da ya
tuku ya yi luku luku da shi, kowanne ta malmala sai
ta sa alaida sannan ta jera acikin fulas din. Ta juyo hadaddiyar miyar wake da ganye wadda ta
dahu da hanta da koda da manja sai dan man kuli
kadan lallai jawahir kin iya hada abin da zai kara
muku jini da lafiya. Ta juye farfesun kifi irin ragon
ruwan nan ta zai zuba kamshi yake yi, ta bude
oben ta zaro gasashen naman ta da ya ji tumatir da albasa gashi yayi ruwa ruwa sai zuba kamshin
kayan kamshi yake yi. Ta hada lemon kwakwa da
madara sannan ta hada lemon abarba.
Kowanne ta zuba a jug ta cilla kankara ta rufe ta
kwashe kayan taje ta jere su a kasa yanda suke yi
yanzu saboda girman cikinta. Iya ce ta gyara mata kicin din da duk wajen da ya baci.
Jawahir ta shiga toilet ta tsalo wanka tare da tsala
kwalliya ta shafe shafe da hadaddun kamshi na
tururuka daban daban, simpil doguwar riga ta saka
me rubi biyu sai walwalin dutsunan jiki ne suke ta
zuba sheki. Ta dora sirrin mayafin akanta, ta futo falo ta zauna akan kafet ta mimmike kafafuwanta ta
wara su yayin da ta jawo rumote ta latsa TV ta
kama, ita kuma ta jingina da kujera tana kallo.
Haidar ya turo kofar tare da sallamar tasa, ya yi
saurin karasowa in da take ya zube a gabanta, ya
tarairayo ta jikinsa "beby na" ya shafa mararta ya ku ke ya beby na yana dawo na same ku beby na
komai lafiya ko?"
Cikin murmushi take daga kai tana amsa masa tare
da shafar sumarsa ta kansa.
"Sannu beby na zauna anan kada ki tashi na hau
sama na watso ruwa na zo mu fita muje mu ci abinci ko, ta daga kai.
Ya mike ya yi sama da sauri ya fada toilet be jima ba
ya fito ya shirya cikin kananan kayansa ya sakko,
ta mike ta taro shi ya rungume ta a barin damansa
"Muje restaurant mu ci abinci ko.?"
Ta langabe a jikinsa "Haba my love da raina da lafiyata na kasa yi maka girki har sai ka fita waje ka
ci? Honey na na yi mana girki." Ya rike baki
"Bebyna bana hana ki wahalar da kanki ba? Daidai
sanda suka zauna gaban kayan abincin yana
bubbudawa, ta ce "Wallahi Honey na ba na son
naga ka ci girkin waje ko na wani wajen, shi yasa nake daurewa na yi maka da kaina."
"San kyau bebyna, na gode Allah ya yi miki
albarka, ya raba ku da cikin nan lafiya"
Amin Honey na gode."
Suna cin abinci Haidar yana zuba santi, jawahir tana
kyalkyala masa dariya. Da haka suka gama Haidar ne ya kwashe kayan, ya dawo ya same ta ta
kwanta kan kafet ya durkusa kanta yana yi mata
tausa sannu sannu yake matsa mata jikinta tare da
mulmula mata bayanta a hankali ta ke fadin "wash,
wash, tana limshe ido na son yin bacci.
Karar wayarsa ce ta sa ta bude ido, ya dauka "Hello Inna kina lafiya kwana biyu?"
Inna ta ce, "Lafiya lau nake ina jawahir din?"
"Ga ta kusa da ni."
"Yauwa
daman dai kan maganar da nafara yi maka ne, zan
zo na taho da jawahir don ta yi wankan gida". "Haidar ya katse ta da "Haba Inna saunawa zan
gaya miki ne ni matata babu inda zata duk girman
gidan nan bai ishe ta wanka ba sai kun dauke min
ita, wanne hali kuke son saka ni?'
Ta daka masa tsawa "Kai marar kunya bana son
shashanci, haihuwar farin zaka yi wa wauta yaushe zamu barta ko mu ma wayaye ne irin ka.? Ta kife
wayar tana mita.
Jawahir ta dora kanta akan cinyar Haidar tana
shafa fuskarsa. "Honey na me yake faruwa ne, don
Allah ka daina damun kanka."
"Bebyna ba dole na damu kaina ba, suna kokarin raba ni da ke, bebyna wai za ki iya tafiya wankan
gida ki bar ni a nan har tsawon kwana arba'in da
'yan kai?
Ta girgiza kai cikin yanayi na tausayi da son ta yi
kuka "Honeyna ba zan barka ba bazan yarda su
raba ni da kai ba, babu in da zan bi su." Daidai lokacin da ta dafe cikinta tana wash, wash!,
yayi saurin rungumarta cikin rikita yana cewa,
"Bebyna menene, me ya faru da cikin nawa.?
My love bayana, cikina, kuguna, duk ciwo suke yi."
Da sauri ya buga wa direbansa waya ya ce ya fito
da mota zasu asibiti. Ya dakko jawahir direban ya bude musu bayan mota suka shiga, ya rife ya ja
suka nufi asibitin, abinka da lafiyayyen asibiti tuni
suka shigar da ita dakinta daban ita kadai a ciki
Haidar ya furgice ganin yanda jawahir take wahala,
gani yake kamar ciro cikin ya dawo da shi jikinsa
shi ya yi nakudar ya haihu. "My love" ta kirawo shi maganarta kasa-kasa ya
durkusa kanta yana jinta "My love kayi waya su
Mama su zo kada na mutu basu ganni ba.
Ya sake rungume ta yana ta mulmula mata bayanta,
"Ki yi hakuri bebyna, ba za ki mutu ba kin kusan
haihuwa. Idan ki ka haihu sai na yi musu waya su taho da
kwarin gwiwarsu yanzu kuwa idan na gaya musu
hankalinsu tashi zai yi su zo su cika asibitin ai ta
damunki.
"Wayyo Honey." Ta kankame shi tana nishi likitocin
da suke kanta suna gaya mata ta yo nishi suna danna mata cikin a hankali tana yo nishi jariri ya
fado tare da tsala kuka. Haidar ya yi saurin
daukansa a cikin jinin ya na ta murna.
Likitar ta yanke masa cibiya ta karbe shi ta mika wa
nas don su gyarashi
Wata sabuwar nakudar jawahir ta kama ba jumawa ta sunkuto 'ya mace ba da jimawa ba wani da
namijin ya kuma futowa.
Ikon Allah, Allah mai baiwa, Allah mai kyauta, har
da kari jawahir ta haifi 'yan uku maza biyu mace
daya, 'ya'yan kyawawa kamar 'ya'yan indiyawa
don kyau da ja, Haidar duk ya rikice don murna waya yake ta bugawa kawai baya tsayawa
gaisuwa sai dai ya basu labarin jawahir ta haifa
masa kyawawan 'ya'ya har guda uku.
Kafin ki ce meye wannan, tuni asibitin ya cika ya
zama filin barka barka tare da murnar samun
wannan kyawawan karuwar da aka yi. Kwanansu daya a asibiti aka sallame su don ba sa
mun hutun suke ba saboda jama'a da suke ta
tuttudowa ganin wannan kyauta da Allah ya yi
musu da ba kowa ake ba wa ba.
Nan kuma gaddama ta kaccame in da Inna ta daga
gida za a yo da jawahir da jarirai shi kuma Haidar ya ce babu in da za 'a kai masa mata da 'ya 'ya, sai