Showing 3001 words to 6000 words out of 48659 words
Chapter 2 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
daga Allah, kin ji,ki share
hawayenki kar ya gane har yanxu kuka kike yi.
Ta ce,,To momy ta mike ta nufi dakinta.
******************************
A gidan Haidar kuwa Alhaji ya gama gayawa Aunty yanda suka yi da yayanta. Aunty ta ce Nina san
yaya zai amince ni dai tsorona yaron nan ka san
jin kansa kar a yi auren ya zo yana wulakanta min
'ya."
Alhaji ya ce, Kirawo min shi mu ji ta bakinsa, ta
daga waya ta danna lambobinsa ta yi ringin ya fi sau nawa kafin a daga sai can ya daga.
Hello wallahi ban san ke ba ce sai da na kalli
wayar sai na ga lambarki lafiya Aunty.?"
Lafiya kalau ka zo falo Abbanka yana son magana
da kai yanxu"
To Aunty ga ni nan zuwa Suka ajiye kan wayar. ya yi sallama tare da tura kofar ya shiga bayan sun
amsa masa, Ya zauna gaban Abbanshi a kan kafet,
Abba ga ni.
Ya ce, Yauwa Haidar na kirawo ka ne daman don
na ji ko ka tsayar da matar da zaka aura?
Haidar ya ce, Wallahi Abba ni ba ni da lokacin kallon matan ma bare na ga wacce ta yi min.
Alhaji ya ce, Ni kuwa ka ga ina da lokacin kallon
su, don har na samo maka matar da za ka aura,
don nasan za ta yi maka yar uwarka ce Jawahir."
A firgice ya daga kai ya kalli Aunty ya ga karatunta
ma take yi ya juya ya kalli Abbansa ya ce, Abba jawahir fa ka ce, Haba Abba me zan yi da wannan
kwailar yarinyar, yarinyar karama zan aura? Haba
'yar da ko kilewa ba ta yi ba, kwanan nan fa ta
gama secondary.
Alhaji ya daga masa tsawa, Kai ba ma son zancen
banza, ni ita na zaba maka kuma ita nake so ka aura ta zamo uwar 'ya 'yanka.
Haidar ya marairaice kamar zai yi kuka, Wallahi
Abba jinina bai hadu da yarinyar ba ta da kunya
shi ya sa na tsane ta.
Aunty ta zaburo ta rufe shi da fada, Yar tawa kake
cewa marar kunya ka tsane ta? To bari ka ji na gaya maka ko kana so ko baka so aure bsbu fashi,
munyi niyyar hada ku kuma sai mun yi, in ya so
ranar da aka kai ta dakinka ka yanka ta gunduwa
gunduwa ka kawo mana namanta, wannan shi ne
maganin kiyayya marar kunya wanda bai san
mutunci ba. Abba ya dakatar da ita, To fadan ya isa haka, na
san bai yi dai dai ba amma ki yi hakuri. Ya kalli
Haidar, Ka tashi ka tafi amma ka sani jawahir ita ce
zabinmu ba gudu ba ja da baya, sai ka je ka yi
tuananin abin daka ya fi dacewa da rayuwarka.
Haidar ya taso cikin bakin ciki, zuciyarsa tana kuna ya yo dakinsa yana magana a zuciyarsa yana
zagaye falon nasa maganar har ta fito fili.
Haka kawai a rasa yarinyar da za a ce na aura sai
wannan figaggiyar yarinyar 'yar karama, yarinyar
da
muka yi rainonta? me zan ji a jikin wannan kwailar, yarinyar da kyar ma in ta fara kirgar dangi? Haba ai
an cuce ni, yanda nake ji da kaina nake so na auri
katuwar mace wadda ta gama jami'a me hankali
wadda za ta fuskanci halina ta bi ni yanda nake so
mu zauna lafiya yaushe za a hada ni da wannan
faratun? Yarinyar da ba ta fi ta tsaya min iya ciki ba, gaskiya a canja shawara, don in har yarinyar ta
yarda ta aure ni sai ta gane kurenta.
,
To ya mu ci gaba ko
11 décembre 2016, 19:48 · Public
*******SALON SO*****
****PART 7 TO 10****
:
BY SULAIMAN BOMBOY.
.
Da Alhaji ibrahim ya gayawa inna shawarar da suka yanke na hada Haidar da jawahir aure, Inna ta
yi murna ta yi godiya ga Allah ta sa wa abin
albarka burinta zai cika ke nan na hade kan
zuri'arta. Bayan Alhaji ya dawo yana cikin iyalinsa
suna hira
ya kalli jawahir ya ce mata, Jawahir dan uwanki fa na zaba miki wanda za ki aura, wato Haidar
Cikin fargaba da tashin hankali ta wuntsilo daga
kan kujerar da take zaune ta dirkushe a gaban
Uban tana kuka ta rike kafafuwansa tana rokonshi,
Don Allah Dady ka yi min rai kayi hakuri kada ka
aura min yaya Haidar, wallahi ba ya so na ba ya kaunata, ba ma shiri da shi. Dady kada ya je ya
shake ni namutu Dady ku yi asarata.
Ba abin da zai faru jawahir yana son ki ba zai yi
miki komai ba, ki yi biyayya a gare mu insha Allahu
za ki ga kyan abin kin ji.?"
Ta daga kai ta mike ta yi dakinta tana kuka mai ban tausayi ga mai sauraro.
Momy ta kalle shi ta ce, Dan Allah ka hakura da
auren nan tun da yarinyar ba ta so kuma yanzu an
daina yayin auren dole." Ya yi saurin daga mata
hannu, Dakata don Allah ba
na so ki ari halin da ba naki ba ki sawa kanki. komai da kika sani mukaddari ne daga Allah,
yanda nake son jawahir ba zan taba cutar da ita
ba, ko na kai ta inda za ta cutu ba.
Ki sani duk wani Uba an fi so ya zabarwa 'yarsa miji
na gari, ki yi la'akari da shekarun jawahir sha
bakwai fa, to a ina ta ga hankalin da tunanin da za ta iya zabawa kanta miji na gari?
Ki yi hakuri ki barwa Allah zabinsa
Momy ta ce, Shi ke nan Alhaji Allah ya zaba mana
abin da ya fi alheri Cikin lokaci kankani an kawo
kudi har an sa ranar
aure wata biyu kacal. Hankalin jawahir ya kara tashi duk ta fige ta rame
ba ta da aikin komai da ya wuce kuka kullum.
Ita ta kasa zuwa ta gayawa Dadynta a fasa auren
nan do ita ba yanda za a yi Dadynta ya gaya mata
magana ta tsaya ja in ja da shi, don haka yamma
tana yi a surare ta yi gidan Inna A gigice ta shiga kowa ya kalle ta ya san tana cikin tashin hankali.
Inna ta tare ta cikin tsoro da tashin hankali tare da
cewa, Ke kuwa yarinyar nan me ya same ki haka
kika yi irin wannan ramar haka? Jawahir ta saki
wani tsumammen kuka, hankalin
Inna ya kara jagulewa tana tunanin ko wani ne ba shi da lafiya ko mutuwa aka yi musu. Ganin yanda
Inna ta rude ne ya sa ta yin shiru amma
idanuwanta be daina zubar da hawayen ba, Inna ta
ce, Jawahir me yake faruwa ne? Ki gaya min waye
ya mutu?"
Jawahir ta ce, Don Allah Inna ki hana Dady ya hada aurenmu da yaya Haidar wallahi inna ba ma
son junanmu ko kadan ni da shi halinmu be zo
daya ba, irin rayuwar kowanne daban. ko an yi
auren ba dadin zama da juna za mu ji ba. Inna da a
zo a na bata zumunci ai gwanda ma kada a yi
ko ba gaskiya ba? Inna ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba,
jawahir ta suka daga kujerar ta rirrike kafar Inna
tana gunjin kuka, Ki taimakamin inna kada
rayuwata ta salwanta. Inna ki yi wa Dady magana
ya janye maganar aurenmu.
Innata kamo jawahir ta rungume ta tana rarashinta ki yi hakuri jawahir, komai nufin Allah ne, ba na
son yin shisshigi a lamarin aure, don ba mu san
abin da Allah ya boye ba, amma zan yi kiran
Alhajin na yi masa maga.......sallamar Haidar ce ta
katse mata zancenta. Ya shigo wujiga wujiga kamar
wanda aka jefo har ya furgitar da Inna. Inna ta ce, Lafiya Haidar me ya same ka haka duk ka
yankwane kamar marar lafiya.?"
Ya ce, inna. Abba da Aunty sun takura min wai sai
na auri waccan kwailar yarinyar. Inna ki dube ni
yanda nake a rasa wanda za a ce na aura sai
wannan tatsitsiyar, haba inna gaskiya ba a yi min adalci ba." inna ta daga masa hannu ta ce, "To ya
isa haka ka
je gida ka kirawo min Auntyn taka. Ka biya gidan
kawun naka ka kirawo min shi, ina son ganin sa.
ya ce, "To ya yi waje cikin fushi.
Jawahir ta sake fashewa da kuka ta ce Inna kin ji irin wulakancin da yake yi min ko, wai ba zai iya
fadar sunana ba sai dai ya ce min kwaila ko
tatsitsiya amma ake kokarin lika min shi haba inna
ai ba ayi min adalci ba.
Inna ta ce, "Ki yi hakuri bari su zo sai a san abin yi.
Bayan sllar magariba Aunty ta iso shi kuwa Dady sai da aka yi sallar insha'i amasallacin gidan inna
sannan ya shigo cikin gidan tuni daman jawahir ta
koma gida haidar kuwa daman bai dawo ba. Bayan
gaishe-gaishe da wasa da dariya na uwa da ya ya,
Inna ta yi gyaran murya ta ce, " Daman abin da ya
sa na tara ku game da maganar auren yaran nan ne. Inna ga a hakura da hadin nan kada zumuncin
da ake ta ikirarin ya zo yana lalacewa.
Dady ya ce, " Inna duk ki rabu da yaran nan insha
Allahu hadin auren nan nasu babu abin da zai jawo
mana sai alheri saboda bayan ranmu zumuncinsu
ba zai lalace ba. Amma yanzu ba kwa ganin yanda ba su damu da
junansu ba, nan gaba abin ya zame musu gaba me
karfi.
Inna tace, "Gaskiya haka ne.
Aunty ta ce, "To yaran nan fa mu muka haifesu ba
su suka haife mu ba, to don me za mu bi son rainsu bayan mun san gaskiyar magana inda take Inna ta
ce, to shi kenan Allah ya yi mana zabi na
alheri suka yi addua suka shafa kowa ya nufi
gidansa.
Yau da gobe taki wasa kwance ta shi babu wuya a
wajen Allah cikin ikon Allah lokacin biki ya zo ana ta shirye shiryen biki. Biki ne da yaye da 'yan uwa
suke ta yi masa shiri na
musamman wanda za mu ce su kadai suke yin
abinsu, don Ango da Amarya na cikin mummunan
bakin ciki da bacin zuciya.
Ba yanda ba a yi d a jawahir ta je ta rabawa kawayenta katin biki ba amma taki da ta ga ma za a
matsa mata sai ta gudu gidan inna. Da inna ta yi
mata maganar rabon katin bikin sai ta sa mata
kuka dole sai aminiyarta ce da manyan kawayenta
suke ta shige da fice na bin kawayen duk inda
suke suna kai musu katin biki na gayyata. ******** ******* ******** ********* *********
Bangaren Angon kuwa Haidar abun duniya duk ya
dame shi, ganin da gaske suke lamarin nan ba za
su fasa aura masa wannan kwailar yarinyar ba.
idan ya zauna shi kadai yana yawan tambayar
kansa cewa, "Wai su abba me suka gani ajikin jawahir har suke kokarin aura masa ita? wayarsa
ce ta yi kara yana dubawa ya ga Abbansa
ne da sauri ya amsa, "HELLO ABBANA.
Abban ya ce, "Ka zo yanzu ina son ganin ka a falon
sama."
"To abba ga ni nan zuwa. "Ya mike cikin hanzari ya nufi bangaren babanshi ya hau samansa.
"Assalamun alaikum."
"Alaikas salamu, shigo Haidar. Aka amsa masa tare
da ba shi umarnin ya shiga .
Haidar ya shigo ya durkusa a gaban Abban nashi
ya ce, "Abba gani. Abban ya ce haidar me kake so ka nuna min ne?
kana so ka tozarta ni a idon duniya su san ban isa
da kai ba?.
Ya dago a firgice ya ce Abba me ya faru kuma?
haidar na nema maka auren yarinya ka ki kula da
lamarin ga shi yau saura kwana biyu daurin aure, babu wani shiri da kake yi. Yanzu da ba dan na
bawa abokinka katunan
daurin auren ya rabawa abokananka ba da haka
za a daura maka auren ba abokin ango ko daya,
kuma ko wajen jawahir din baka je ba bare ka san
me take bukata da za ka ba ta ko? Haidar ya ce, ka yi hakuri Abba ganin dana yi kuna
tsaye akan komai duk kun gama wani shiri da zan
yi shi ya sa ban mayar da kai ba, amma don Allah
Abba ka yi hakuri in an jima zan je gidansu jawahir
din don na ji abin ta take bukata.
"Yauwa Haidar ko kai fa Allah ya yi muku albarka . Ya dauko kudi dubu dari ya ba shi to Haidar ga
wadannan sai ka ba wa jawahir din.
"Abba da ka bar shi ga kudi can da na ware zan kai
mata na shagalin 'yan mata kawayenta.
Ba komai hada ka kai mata gaba daya ai
abubuwan shagalin da yawa. "To Abba an gode, Allah ya saka da alheri.
Amin dana Allah yayi maka albarka.
Da yamma Haidar ya gama shirinsa ya hau motarsa
ya nufi gidansu jawahir. Ya tura maigadi ya yo
kiranta .
maigadi ya daga waya ya buga cikin gidan mummy ce ta dauka. maigadi ya rissana ya gaisheta kamar
tana kalonsa sannan ya fadi sakon Haidar na son
ganin jawahir. momy ta ce Ai ba ta nan tan gidan
inna maigadi ya
gayawa Haidar to sai Haidar din ya shiga ya gaisa
da momy ya fito ya nufi gidan Inna. Yayi sallama falon ya shiga ya ga jawahir kwance
kan cinyar Inna ya kalle ta ya doka tsaki. A
zuciyarsa ya ce, "Sangartacciyar yarinya in an yi
auren na ga jikin uban wanda za ki hau.
Inna ta ce, "Lafiya daga shigowarka kake tsaki?"
yace, "Bakomai inna suka gaisa suna hira tare ya dan taba wasan jika da kaka ya ce, "Inna tursasani
fa aka yi na zo wajen waccan.
Inna ta ce, "Ai ga ta bari na bagu waje. yace a a
inna ki yi zamanki ba sai kin tashi ba, ji zan
yi dame da me take bukata.
Inna ta ce bari na fita kwafi jin dadin sakewa." Sunfi tsawon rabin awa ba wanda ya ce da kowa
komai, Haidar ya kalli ta ya ya mutsa fuska tare da
tabe baki ya yi tsaki, "Ke in banda kinci albarkacin
iyayenmu da sai kin raina kanki, don ni banga abin
so a jikinki ba.
Domin baki da cikakkiyar surar dazaki ja hankalina. Don haka ma in kin shigo gidan sai kiyi hakuri da
irin zaman da za kiyi don ba wai wani abu ne zai
shiga tsakaninmu ba. Ya debo kudin da Abban ya
bashi dubu dari ya jefe
tada su. "Ga shinan ba don halinki ba kuma wai a
aljihuna na baki ba Abba ne ya bayar a kawo miki tatsitsiyar kawai."
Yayi daya falon da inna tashiga yayi mata sallama,
"Inna mun gama zan tafi don akwai ragowar shirin
da ban kammala ba.
Inna ta ce, "To Haidar a sauka lafiya, ya fito da kudi
dubu hamsin ya ba ta ga wannan inna ke ma kya yi hidimar bikin.
"To duk ni kadai Haidar ? to na gode Allah ya saka
da alheri, ubangiji ya albarkaci wannan auren
naku. Shi dai ya yi ficewarsa .
INNA ta shigo gurin jawahir ta kula da halin datake
ciki don saboda tsananin bakin ciki da takaicin da haidar ya haifar mata sai ya hadu ya dunkule mata
a kirji ga hawaye ya ki fitowa bare in ya zuba ta ji sa
'ida. Kan ka ce meye wannan kirjinta ya hau zafi ga
ba
daya jikinta sai ya hau kakkarwa yana bari. inna ta
rikice tana cewa, "Lafiya jawahir, yanxu fa na barki kalau dake me ya same ki.?
Ta nunawa inna kirjinta ta ce inna kirjina ne yake
ciwo, "Da kyar take iya maganar. sai numfashinta
yakoma fita sama sama, ba jimawa
abu ya ci tura idan ta ja numfashin sai ya dade be
dawo ba. Hankalin inna ya yi masifar tashi ta kidime da kyar
ta iya kiran direbanta a waya ta kira shi ya zo da
sauri suka hadu suka kinkimi jawahir suka sa ta a
mota inna ta shiga ya ja suka tafi asibiti
Inna asibitin da Daddy yake zuwa za muje?" inji
direban. "EH can za mu je mana"
suna isa asibitn aka dora ta abin tura marasa lafiya
a ka shigar da ita wani daki. likitoci biyu suna tsaye
akanta. Can suka fito inna ta mike da sauri ta tare
su "Yaya likita?
Yace, inna ki kwantar da hankalinki, damuwa ce ta yi mata yawa da bakin ciki, amma za ta samu sauki
idan an ankiyaye dokokin da likita zai kafa mata.
Yanzu mun ba ta gado an kwantar da ita.: A ka
nunawa inna dakin da take ta shiga ta zauna a
gefen gadon sannan ta zaro waya ta bawa me
aikinta ta ce ta buga gidan Dady da gidan Aunty ta gaya musu. Cikin mintuna kadan 'yan gidansu
duka sun zo har Dady da momy can gidan Aunty
ma ta sako Haidar a gaba dole ya tuko motar suka
zo.
Gaba daya sun gewaye gadon da take kwance,
kowa ya sa mata ido. Likita ya shigo ya zare ledar karin ruwan da ta ya sa mata wata. likita ya gaisa
da Dady ya ce, dady sai an rinka kula da lafiyarta
dole ne a rinka barin zuciyarta tana hutawa don a
samu nutsuwa a rinka kiyaye duk wasu abubuwa
ko maganganu da za su rinka bata mata rai a rinka
yawan lallabata da rarrashinta har ta warke, idan ba haka ba tana gab da kamuwa da ciwon zuciya."
Dady ya ce, "Ba komai likita insha Allahu za a kula
kuma Allah ma zai kiyaye. Shin kuwa Haidar ya yi
zukulu yana tunani a
zuciyarsa ya ce, "Anya kuwa ba shi ya haddasawa
jawahir wannan matsalar ba? shi fa musulmi ne ya kamata ya yarda da kaddara ko ba komai jawahir
yar uwarsa ce yana da imani don haka ya tausaya
mata halin da ya ganta a ciki. dazun nan ya gama
gaya mata maganganu ga shi
yanzu halin da take ciki. Dayan biyu ko rai ko
mutuwa. Washegarin jikin jawahir ya yi sauki don tana iya
komai da kanta wajen magariba Dady ya
matsantawa likita sai ya sallami jawahidr sabo da
gobe daurin aurenta
Likita ya rubuta mata takardar sallama da
magunguna Washegari aka daura auran Haidar da Jawahir,
daurin auren da ya samu halattar manyan mutane
da 'yan boko abokanansu haidar da yaya Abba da
Nasir.
Anyi taro lafiya an gama lafiya mata kuma sun
shiga hadaniyar biki. Haka kawayen amarya suke ta shiga da fice na gudanar da hidimomin bikin
kawarsu, amarya kuwa ba ta um bare um-um
kowa kallon sa take yi. kakarta ta wajen uwa Hajiya
Rabi ta zaunar da ita
tana yi mata nasiha ki yi hakuri jawahir ki zauna a
gidan mijinki lafiya ba ki da wani gata da ya wuce dakin mijinki.
Ki rinka taka tsantsan da harshenki, kada ki gaya
masa bakar magana ko wace za ta sa shi yayi fushi
saboda lahirarki."
kowa dai ya ta mata nasiha zai ce ta ji tsoron Allah
ta yi biyayya ga mijinta. An gama biki amarya ta tare a tsantsareren gidan
angonta da yake nasara G.R.A.
Kowa ya fashe 'yan kawo amarya sun watse sai ita
kadai kwal a cikin gidan sai maigadi da yake bakin
get.
Tana zaune tana tunanin irin zaman da za su yi da HAIDAR har bacci ya fara daukan ta a zaune ta ji an
turo kofa anyi sallama an shigo.
Ta yi saurin gyara zamanta . Ya shigo dakin ya nemi
waje ya zauna
******SALON SO*****
:
****PART 11 TO 15*****
.
BY SULAIMAN BOMBOY.
. Ba ce mata komai ba ita ma ba ta kalli gun da yake ba. Can ya ce mata kinci abinci?
"EH na ce. Ya janyo ledojin da ya shigo da su da
karamar akwati ta siyen baki ya tura mata gabanta
ya tashi ya fita. Jawahir ta yi tagumi a ranta ta ce, "O
ni 'yansu, ga me so na can an kawo ni gidan wanda
ba ya kauna ta ko da