Advertisement
Showing 6001 words to 9000 words out of 48659 words

Chapter 3 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt

yake ni ma zan zauna ne darajar
iyayenmu. "A nan ta tuno nasihar da mommynta ta
yi mata.
Jawahir ni dai babu abin da zan ce miki sai fatan
Allah yayi miki albarka yanda kike binmu kike
mana biyayya ubangiji ke ma ya baki 'ya 'yan da za su biki haka.
Jawahir ta dauki duk abin daya same ki a rayuwa
matsayin kaddara. ki kasance me biyayya ga
mijinki ki boye sirrinku kada ki buda shi ga wani
don Allah ya tsinewa matar da take bayyanar da
sirrin mijinta. Duk abin da ya yi miki yi hakuri kada ki kai kararsa wajen kowa. Ki dage ki yi ta yi muku
addu'a don Allah ne zai warware muku matsalarku.
Ka bacin rai ya sa ki bin boka ko malam babu abin
da za su yi miki face ki barnatar da kudadenki a
banza kuma ki jawowa kanki tsinuwar Allah ki rike
alkur'ani dan zancen Allah ne shi ne waraka ga komai.
Jawahir ta saki ajiyar zuciya ta ce, "In Allah ya yarda
zan rike nasihar mommyna.
Haka ta kwanta ita kadai ga tsoro da yunwa tana
jin amma ba ta bude ledojin da Haidar ya ajiye mata
ba. Da asuba ta yi sallah ta dauki kur'ani ta karanta
abin daya sauwaka ta yi addu'a ta ta sha fa ta cire
hijabinta ta ajiye. Ta yi takumi, "Ni kuwa na je na
hada break ko kuma na kyalle shi? Kai gwanda na
yi ko ya ci ko ba ya ci Allah ya gani dai na fita falon
tsarin falon ya yi mutukar burge ta da ba ta sha awa, lallai daddynta ya kashe mata kudi.
Ta bude kicin din shiga haduwarsa ya yi mugun
gigita ta, sak irin wanda a ke nuno tallolinsu ne
kasashen waje, duk wata na ura ta amfanin dan
Adam don hada abu a saukake an tanadar mata a
kicin din nan, sannan duk wani kayan girki da za su bukata an tanade shi ta bude disk freezer cike
yake da kaji, zabi xuwa naman kasuwa duka
danyu, sai daya firizar kayan miya ne irinsu attarihu
tattasai, tumatir, albasa, koren, wake, karas, kabeji
da sauransu. Firinjin tsaye kuwa lemummuka ne
kala kala na kwali da na gwangwani da robobin ruwan sha,
kamar su swan water, Highland water, da dai
sauransu. Ta ga wata kofa daban a kicin din ta
bude ta ta shiga ashe sito ne kalolin abinci iri iri
buhunan shinkafa, katon dinsu taliya, makaroni,
kuskus, buhun sikari da na fulawa, garwar manja da na jan kuli da kuma man shanu, busasshen kifi,
daddawa, kanwa busasshiyar kubewa, magi kama
daga Reko, onga, kori, Ajino-moto da dai sauransu,
babu abin da za ta nema na amfani komai an dire
mata.: Ta debo dankali ta fere ta soya ta jona ruwan
zafi ta sa citta da kanun fari, ta zuba ganyen shayi me kamshin Nescafe ta koma daki ta dauko ledar
jiya gasassun kaji ne manya guda uku ta zuba su a
oben ta dumama su. Ta fasa kwai ta soya ta debo
filas-filas masu kyau 'yan dubai ta zuba komai a ciki
ta rufe ta juye ruwan shayin a fulas din shayi
wanda yake duk saiti ne da fulas din da ta zuba ragowar kayan a ciki. Ta jere komai a tebir ta debo
kofuna da filet da cokula duk ta zube kan tebir din
ta sa wani farin kyalle me ban sha awa ta rufe
kayan kan tebir din. Ta dauki nata break din ta yi
dakinta da shi. Ta rufe kofarta ta shiga toilet ta yi
brush sannan ta ci ta koshi ta koma gado ta kwanta.
Mintina kadan bacci ya yi awon gaba da ita.
Shikuwa Haidar da ya tashi da asuba ya yi sallah ya
yi karatu ya shafa addu'a gado ya koma ya kwanta
saboda baccin gajiya da yake ta dawainiya da shi.
Karfe tara ya tashi na safe ya yi mika tare da salati ya duro daga gadon ya nufi toilet. Ya salla wanka
ya zo ya gama goge gogensa da shafe shafensa ya
yi tsantsararriyar shiga, shiga ta alfarma ya feshe
jikinsa da turaruka. A zuciyarsa yake cewa ya
kamata na je na gano yanda yarinyar nan ta tashi
ko don nasihar da Abbansa ya yi masa kamar haka.......
"To Haidar yau Allah ya nufa an daura auernka da
jawahir to duk wani nauyi da hakkinta ya koma
kanka, amana ce a gare ka, idan ka zalince ta ko ka
cutar da ita kai da Allah, idan ta yi maka abin da be
yi maka dadi ba ka zaunar da ita ka nusar da ita cikin nasiha da tattausar murya. Kar ganin yanzu ta
zama ikonka tana zaune a karkashinka wallahi
idan ka zalince ta ubangiji ba zai taba kyale ka ba,
sai ya fitar mata da hakkinta don haka ka kiyaye."
Ajiyar zuciya Haidar yayi, "Haka kawai a daure ka
da jijiyar jikinka, bari na je na gani ko ta karya. Ya sauka kasa da yake benen nasa a cikin falonta
yake.
Ya kula da tebir din da ya sha kwalliya da kayan
alatu. Ya karasa wajen ya yaye farin kyallen ya
bude komai.
Kamshi ya daki hancinsa nan da nan sha awar abincin ta kamashi. Ya zauna ya hada ruwan tea me
kauri ya debi soyayyen dankali da kwai da kaza
daya. Haidar ya rinka ci yana lodawa cikinsa don
jiya da daddare bai ci komai ba ya kwanta, yanzu
kuwa ai
ya yi lodi, ya yi gyatsa tare da yiwa Allah godiya. Ya mike ya nufi kofar dakin jawahir ya ji ta a rufe.
Ya samu takarda da biro ya rubuta mata sako
kamar haka: "idan kin tashi ki yi break ni mun fita
gaisuwar surukai sai yamma zan dawo."
Haidar
Ya ninke ya dora kan tebir din. Ya fice. Ya samu abokanansa suna jiransa suka tafi gaisuwar
surukai. jawahir sai sha biyu na rana ta farka, tana
mikewa ta fada toilet ta yi wanka ta kammala
shirinta
sannan ta fito falo, ga mamakinta ta ga Haidar ya ci
break din da ta shirya masa. Ta hango takarda ta dauka ta bude ta karanta ta
tabe baki, "Kada ma ya dawo ni ko kwana zai yi me
ya dame ni?" Ta dauko yogougt ta zauna tana
yagar kazar tana korawa da nonon har ta koshi.
Wajen sha biyu da rabi direba ya kawo Inna da
kannanta Auwal da sani da su Hassana da Usaina kannan Haidar. Jawahir ta cukuikuye inna tana
tsallen murna.
Inna ta dube ta tana dariya ta ce, "Ke cika ni kada ki
karasa ni, ni ina can zuciyata ta kasa sukuni sabo
da tunanin yaya kwana ke kuma kina kokarin
karasa ni. jawahir ta yi dariya, "Amma dai inna a nan za ku
kwana ko?"
Inna ta tabe fuska ta ce, "Ke ba na son hauka
yanzun nan ma za mu juya. Hassana ta ce, "Allah
Aunty ni dai gidanki ya ba ni
sha awa zan kwana. Usaina ta ce, "Lallai kina so Yaya haidar ya yi
tamaula dake kenan.?
Jawahir ta ce, ba wani abu da zai yi mata kin ji
Usainar nan wai don kar ta kwana, ba abin zai yi
miki Hassana."
Inna ta ce, "Babu wanda zan bari, kafata kafarsu. Auwal ya ce, "Su Aunty jawahir 'yan gayu. "Gaba
daya sukai yi dariya.
Sani dauko muku ragowar break din Yaya ku ci. Ta
tashi ta shiga kicin ta kwaso musu yogouht da
lemummuka da ruwan sanyi ta zube musu. Da
ragowar gasassun kajin amarcinta. Inna ta gyara zama da jikokinta suka ci suka koshi. Inna ta kara
yi mata fada da nasiha.
Karfe hudu suka tafi. Jawahir ta mike ta yi sallah
bayan ta idar ta shiga
kicin ta dauki kaza daya ta yayyanka ta yanka
albasa ta sa gishiri da citta da magi ta dora kan wuta.
Ta debi kayanmiya yanda zai wadace ta ta markada
ta dora ruwan kuskus. Ta gama hada soyayyiyar
miyarta ta dafa kuskus
dinta da ya sha karas da koren wake ya yi wara
wara da shi gwanin kyau. Ta gasa kifi irin manyan nan ta yi farfesun kayan ciki, ta markade kwa kwa
a ciki blinder ta tace ta sa madara, filebo, sukari ta
hada lemo me dan karen dadi. Ta samu wasu
kayatattun fulas ba irin na safe ba ta
kuma jere komai a kai.
Ta hau saman dakin nasa, ga mamakinta sai ta gan shi a bude ta gyara masa gadon da ya kwanta ta
kade komai ta share masa dakin. Ta wanke
bandaki ta goge ta kunna turarukan wuta ta fesa
Air freeshner a kowacce kusurwa, ta sakar masa
A.C Nan da nan sanyin dadi ya soma tashi.
Ta rufo masa dakin ta sauko ta gyara falon kasa da nata dakin ko ina ta feshe shi da Air freshner da
turaren wuta dan maiduguri ta saki labulayen ta
kunna A.C ta rufe kofar falon ta shige dakinta ta
rufe ta fada toilet don yin wanka Sai karfe biyar da
rabi Haidar ya dawo gidan a
gajiye ga yunwa da take azalzalassa don tun break din da ya yi bai sake cinn wani abun ba.
Don shi Allah ya yi shi mutum ne mai kyankyami ba
ko ina yake iya cin abinci ba. Megadi ya wangame
masa get din ya shigo ya
rissina ya yi masa barka da zuwa.
Ya murda kofar falon ya shiga tare da yin sallama shiru kamar ba kowa a gidan.
Daddadan kamshi ya bugi hancinsa, ko ina tsaf a
share a goge ya ji gyara, ya yi sha awar yanda take
da tsafta take kula da komai. Ya haye samansa
yana tura kofar dakin, nan ma
sanyin da kamshin dadi suka yi masa sallama. Ya sheka ya limshe ido ya yi godiya ga Allah, shi
kansa falon saman nasa ta canja masa tsarin gyara
wanda kuma hakan ya fi kyau yana shiga cikin
dakin nasa sai kansa ya kwance, wani hadadden
zanin gado ta shimfida masa , ai yanda ta dame
gadon ya burge shi ya cire kayansa ya fada toitel ya fara wanka.Ya gama shirinsa ya sa kananan kaya.
Sun karbe shi kuwa sun yi masa kyau.
[07069210827: Ya feshe jikinsa da turaruka ya
sauko kasa ya hau tebir ya bude komai, kamshin
girkin ya buge shi sha awa da jin dadi suka bige
shi. Ya zauna ya rinka dibar garar girki, yana ci komai
na kan tebir din sai da ya ci da ya wa ya ci ya koshi
ya yi hamdala ga ubangiji. Ya rinka tsiyayar lemon
kwa kwar nan yana sha,
don Allah daman hausawanmu sun iya hadadden
lemo haka, amma muke bugewa kullum yawon siyen juice.
Ya cika kofin tangaran da shi ya tashi ya koma kan
kushin can gefe daya ya dauki jarida yana
karantawa yana kurbar lemon kwakwar. Ita kuwa
jawahir tana daki ba ta ma san ya dawo
ba ta gama shirya kwalliyarta cikin riga da siket na atamfa kwali wax, rigar fitet ce 'yar firit,siket din ya
yi tsantsan a jikinta.
Ta dora daurin dan kwali wuyanta da kunnanta
wani rantsattse fashion ne mai kyau. Ta feshe
ilahirin jikinta da daddadan turaruka masu kamshi.
Ta bude kofar dakinta ta fito kamshin da ya ji ne ya sa shi dago kai ya kalle ta, a ransa ya fada,
"Yarinyar tana da kyau sai ka ce Aljana, ga shi ta iya
gyran jikinta. Yanda siket din ya matse ta dole ta
rinka takawa
sannu a hankali gudun kada ta harde. Ta shiga
kicin ta debo abinci a filet dan kadan sai ka ce wadda za tabawa dan yaye sai robar nono
yogougt dake daya hannun nata.
Ta zo ta nutse a cikin kujera ta dauki remote ta
kunna T V. tashar CNN ta kunno, sannan ta fara cin
abincin,
yanda take diban abincin kamar ba ta son ci a yangance.
Duk abin da take yi idon Haidar yana kanta, ita
kuwa ba ta san ma ya dawo ba bare ta san yana
falon. A zuciyarsa ya ce, "Yaushe dama za ta girma
tana cin wannan dan mitsitsin abincin kamar na
'yar yaye. Can wayarta ta yi kara ta dauka, tana dubawa da
murnarta ta dora a kunnanta, "Hello Dadyna. sai ta
kunna (Handsfree) Daddy ya ce, "Jawahir yaya
kike? Ya megidan naki? "Wallahi lafiya lau Dady
muna zaune kalau.
"Kina son masu aiki ne a kawo miki? Cikin shagwaba ta ce, "Lah Dady mai aiki, ni wallahi
ba na son kowa su zo su yi batawa mutane waje.
don iya girkinmu mu biyu da gyaran dakunanmu
Dady ai duk zan iya. "To jawahir wanke-wanke fa,
ga sharar harbar
gidanku.? Dady ka san ba na son kazanta da gama girki nake
wanke kayan na goge su na mayar inda suke.
Harabar gidan kuma dakin saukar baki yana da
yaro da yake gyara masa me bawa fulawowiyin
gidan ruwa.
"To jawahir wa zai rinka ba su abinci ko har da su za ki yi rinka yin girkin?
Ta kara shagwabewa, "Uhm Dady wallahi ba zan yi
musu girki ba, abincina daga ni sai Yaya kawai. "To
shi ke nan jawahir za a samu haidar din na yi
mishi magana na ji yanda za a rinka yi da su wajen
ba su abinci." Cikin shagwaba ta ce, "Don Allah Dady kada ka yi
masa magana ya zo ya ce sai na rinka girkin da su
ka ga wahala zan sha. "To jawahir ai a karkashinku
suke, dole ku rinka
kula da hakkinsu ko to kwace kuma za ku bar su
da yunwa. Cikin shagwaba ta ce, "Haba Dad. to Dady na yarda
a kawo tsohuwa amma ba za ta rinka shigo min
sashena ba, sai dai ta tsaya can bangaren masu aiki
ta rinka da fa musu abincin, ai ya yi ko Daddy.?"
"Yauwa ko ke fa jawahir gobe za a kawo ta, Ki kara
hakuri jawahir ki dinga biyayya ga mijinki. Allah ya yi muku albarka .
To Dad na gode, "good day Dad."
Tayi ajiye wayar ta mike ta dau filet din ta shiga
kicin. Haidar ya mike ya haura samansa ya yi dai dai
a
gadonsa yana tunanin hirar jawahir da Daddynta. A ransa yake cewa, "Ko dai don muna 'yan uwa ne
halayyarmu da ra'ayinmu suke neman zama daya?
Gaskiya ta burgeni da za ta rinka yi min komai da
kanta, don ni na tsani gidan da me aiki take yi wa
matar gidan da mijinta girki, amma jawahir tana da
dadin murya ga dadin saurare, ban so suka gama hirar ta su ba.
To haka da i zaman ya ci gaba tsakanin miskilan
guda biyu. kowanne yana ji da girman kai da
miskilanci babu wanda zai wa dan uwansa magana
idan har sun hadu da safe za ta ce masa ina kwana.
Yayin da shi kuma yake daukan lokaci kafin ya amsa da lafiya lau.
To sai ta yi shigewarta daki ba ta fitowa har sai ya
tafi. sannan ta zo ta gyara musu dakunansu ta
turare da
turaren wuta ta feshe ko ina da Air freshner ta
zauna ta shirya musu hadadden girki me gamsarwa.
Ta hada masa lemo da kanta kullum da sabon
samfir din girki da lemon da take yi masa. Ba ta taba
barin waje da datti ko kura ko ina fes a
gyare dai dai da wanke kwanikanta ita take yin
abinta. Ta gyara kicin dinta fes kamar ba a yi komai a ciki
ba. Tukwane ne kawai da kaskon suya saboda
maiko take bawa Dela me aikinta ta wanke mata
Tun da akawo Dela take zaune a bangaren masu
aiki za ta yi girkinsu su uku da maigadi da ita sai
yaron gidan da ta yi gama za ta wanke komai ta share ta goge da yake ita ma me tsafta ce shi ya sa
suke shiri da jawahir din. Haidar kuwa yana jin
dadin yanda jawahir take da tsafta komai take
kulawa da shi yanda ya kamata,
don haka duk san da ya taso daga office burinsa ya
yi sauri ya dawo gida don ya narki special din girki da jawahir za ta yi masa.
Ya zauna a kayataccen falonsu yana shakar
daddadan kamshin falon. Idan ya tashi daga office
yana biyawa ta gidansu a gurguje yake yin komai
don yana sauri ya koma gida.
Idan Aunty ta ce masa ga abinci ya kan ce um Aunty sai na je gida zan ci. Duk da ba magana suke
yi wa junansu ba, to amma hakan bai hana su
kyautatawa junansu ba Ana yawan kawo mata
kannanta Auwal da Sani da
kannan Haidar Hassana da Usaina idan yamma ta yi
direba ya mayar da su gida Yaya Abba ma da yaya Nasir suna yawan zuwar
mata. Inna ma ta na kan zo amma ba sosai ba
iyayensu ne dai har yau ba su zo ba. HAIDAR ya
samu kwanciyar hankali don ba a bin
da ya ke damunsa don haka jikinsa ya kara
murjewa kyansa ya kara daduwa kowa ya kalli fatarsa ya san ta goge da jin dadin duniya ita kuwa
jawahir da yake abincin be da meta ba to yanda
take haka take babu wata 'yar kiba da ta yi.
Shekara daya ke nan da yin auren har yau jawahir
ba ta taba lekawa kofar gida ba.
Yau asabar da jawahir ta kammala da hada break dinta ta diba ta ci ta gama gyara wajen ta sa turaren
wuta ta feshe da gidan ta shige toilet ta yi wanka.
Yau shigar turawa tayi 'yar bingilar shimi ta saka iya
cibiya me siririn hannu sai dogon wando da ya
dame mata cinyoyi da kafar wandon an bude shi ta
hade gashinta a tsakiyar kai ta sa tafkeken ribon ta daure shi.
Cikinta a dame kamar ba ta zuba masa abinci ba,
fuskar nan tata sai fitar da sheki da wa ni asirtaccen
kyau ta ke yi, ta gama feshe jikinta da tuararuka ta
fito falon inda Haidar ya ke break ta durkusa ta ce,
"Ina kwana?" bai juyo ya kalleta ba ya ce, "Lafiya lau.
Ta mike ta isa bakinTV ta dauki takarda da biro ta
koma ckin kujera zaman mutu daya ta kwanta tana
rubutu.
Tun da ta mike Haidar yake bin ta da kallo sai
hadiyar yawu kawai yake yi ta yi mugun ba shi sha awa, hankalinsa ya tashi sosai.
Ta gama rubutu a takardar ta ninke ta taso cikin
nutsuwa ta zo gaban Haidar ta ajiye masa a kan
tebir dinta ta juya ta koma daki, shi kuma ya bi ta
da kallo.
Sai da tashige daki sannan ya ware takardar ya fara karantawa .
Yaya Don Allah yaya ina so zan je gidanmu da
gidan inna da wajen Aunty. Ina so na taho da
sayyid Autan
Aunty idan ka yarda.
Jawahir Yana gama karantawa ya ajiye ya ci gaba da yin
break dinsa sai da ya gama sannan ya mike ya
dauko takarda da biro shima ya rubuta mata kamar
haka.
"In kin shirya ki jira ni na kai ki da kaina, Sayyid
kuma in kin ga ba zai takura miki ba kya iya daukoshi
Haidar Jawahir duk ta matsu da ta ga amsar da zai
ba ta. don ita dai tana so yau ta je gidajen nan ko
dan
dadewar da ta yi rabonta da fita .
Ita jin kanta da miskilancinta ya hana ta ta fito bare ta ga amsar da ya rubuta mata , shi kuma girman
kansa da isarsa ba za su bar shi ya kai mata ba. Sai
da ya gama kallon sa da hutawarsa sannan ya
koma sama. Sai
da ta ji tafiyarsa ta fito ta dauki takardar ta karanta,
aikuwa sai ta hau tsalle tana murna kamar yarinya. Nan da nan ta shiga shiri a kakale nan a kakale can
ko ina ta yi fes kamar wacce aka karawa kyau.
Wani dandasheshen less ta saka me dan banzan
kyau da shegiyar tsada. Ta yi kyau kamar ka sace
ta ka gudu don haduwar da ta yi. Ta kalminta da
mayafinta da jakarta duk ruwan less din ne. Takalmin me tsinin dunduniya. ta hakimce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login