Showing 1 words to 3000 words out of 49582 words

Chapter 1 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt









Compiled By Umar Dalha Funtua.




🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻

WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


0⃣1⃣

Ma dai daichin gida ne wanda ya tsaru iya tsaruwa, masu hidimar gidan sai kaiwa da komowa suke.
Gabaki dayansu suna zaune a dinning table suna breakfast ba wanda ke cewa komai har suka kammala
Ammii ce ta kwashe kwanukan takai kitchen tahau wanke wa.


30mints later
Daddy ne ya fito cikin shirin sa na zuwa daurin auren dan kaninsa wanda xa ayi a garin Karaye
"To Ammii zan wuce to daddy Allah ya kiyaye hanya "
" Ameen ameen sai na dawo.

Tafe yake akan hanyar sa ta zuwa Karaye gudu yake ta tsulawa kamar dan shi akayi titin kasan cewar titin ba cunkoson abin hawa.
Sai da yaxo dai dai inda ze shiga garin gwarzo ya taka kusa aiko tayar sa ta fashe.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU UN shine abinda daddy yake maimai tawa, waye zai tai makeshi da sanyin safiyar nn gashi bashida spare tier balle ya canja.
Daddy yana tsaye jikin motarsa yana neman mafita tunani yake kodai ya bar motar ne yatafi gurin daurin auren? To in ya tafi wa zai bar wa motar sa, yasan komai zai iya faruwa idan ya tafi.
"To ynx ya zanyi yace afili.


Sauri yake tayi kasan cewar yau daurin auren amininsa ya zama dole ya halarchi wnn daurin auren.
Tundaga nesa ya hango shi kuma tabbas yaga alamar yana cikin yanayi na neman taimako kasa ya farayi da motarsa yayi parking dan gaba da daddy sannan ya fito.

Sannu Alhaji
Yawwa sannu yaro
"wani abu yasami motar ne?
" Ehhh taya ce ta fashe gashi banida spare.
"subahanallahi" Aikuwa inada spare a bayan motata nn ya xagaya ya dauko masa tayar.
Bari naje nn gaba kadan akwai masu gyara sai suzo su saka maka
To madallah inji daddy yana mai fadada fara 'arsa. Daga nn safeer yy gaba shikuma daddy ya tsaya.
Befi 20mints sai gashi da Mutum biyu sun dawo nn suka shiga daura taya suka gama.

Nagode sosai yaro
"Bakomai wlh ae yiwa kaine "
Ina kanufa daddy ya tambaya.
Karaye zani daurin auren abokina, Ae nima nn na nufa
Daga nn kowannen su ya shiga motarsa suka kama hanya wanda cikin lokaci kadan suka isa kuma aka daura auren dasu.

Sai bayan da aka daura auren ne Alh. Al 'ameen sarakee Ya samu kebewa da safeer inda ya bashi complementary card dinsa
"Ga wnn card dina ne don Allah gobe ka sameni a office"
To nagode kuma insha Allah xaka ganni....


ASSALAMU ALAIKUM wa alaikumussalam sannu da zuwa Alhaji
"yawwa Ammii ya gidan? "
" lafiya kalau Ammii tace tana binka bayan Alhaji zuwa daki.


3 hours later
Shukra kixo inji daddyn ki yana son magana dake
To Ammii shukra tace tana mikewa daga kwancen da take

Da sallama ta shigo cikin dakin cike da biyayya ta gaida mahaifinta ya answer da fara 'arsa.
Zuwa chan daddy yayi gyaran murya ya fara magana kamar hk
"shukra inaso ki bude kunnenki ki saurare da kyau kuma ki dauka cewa maganar da xan fada miki umarnine ba shawara ba.
Gaban shukra ne yashiga bugawa da sauri sauri to me daddy xe gaya mata ne wae
" Kina jina ya katse mata tunanin da take "
" Ehhh Kawai ta iya cewa tana sauraronshi
Nayi miki miji kuma nn ba da dade waba sai zo ku fahimci juna
" miji kuma shukra tace tana xaro idonta

Alhaji miji fa kace
"Ehhh miji mana menene "?
Ae naji ka fadi abinda baxe yiwu bane

Ae kuwa dae sai ya yiwu kuma ki zuwa ido ki gani yana gama fadar hk yafice daga gidan ma gaba daya.




KO WANENE MIJIN DA ALH SARAKEE YA XABA WA YARSA?
SHIN XASU AMINCE DA AUREN KO KUWA A A?




SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/22, 9:24 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA

0⃣2⃣


Knocking yake a kofar office din Alh sarakee
" yes come in inji sarakee,
Kai tsaye safeer ya shiga cikin office din har kasa ya durkusa yana gaida Alh sarakee
Abun ba karamin dadi yama sarakee ya answer fuskarsa a sake
" Have a sit
"Thank you sir
Safeer nasan xakayi mamakin abinda yasa na nemeka kuma ni anawa ganin ba abun mamaki bane, Alfarma nake so kayimin dan Allah
" Alh wace Alfarma kakeso nayi maka
Inaso dan Allah duk abinda nace kayi min kayi
"indai be sabawa addiniba me zai hana nayi maka
" be saba bama cewar Alh sarakee cikin sauri

" gyara xama yayi yafara dacewa
A gaskiya na yaba da hnklin ka shine nakeso na hada ka da yata dan Allah ka aure ta
Maganar ta xowa safeer a BAZATA baxe iya cewa a a ba amma shi har ga Allah bashida burin Aure a wnn lokacin
" Dan Allah karka ce a a inaso kasani yata batada wani aibu ba kuma dan tarasa mijin aure ne na bakaba a a kawai dai dan na yaba da hankalin kane nakuma ji dadi da ka temaka min a lokacin da nake tsananin bukatar temako
" To Alhj madallah nagode
" nine da godiya safeer ynx sai ka bani number wayar ka kuma in kuma in ka samu lokaci sai kazo ku sasanta kanku ko
To insha Allah xanxo.

Yawwa baka gayamin suwaye iyayenka ba da kuma karatunka da inda kake aiki
"sunana safeer muhammad mai lafiya babana shahararren dan kasuwane, nayi makarantar primary da secondry a garin Abj kasancewar kasuwanchi yakai mahaifina can garin Abj bayan na kammala secondry ne muka dawo garin kano inda na samu Admission a B U K na karanci "Architectural technology" ynx hk ina aikin gwamnati sannan kuma ina aiki on my own nakanje gari gari indai ai nemeni ina zuwa nayi Aiki.

To masha Allah, Allah ya taimaka
" Ameen ameen Alhj nagode
" Nine da godiya sai najika

Daga hk sukayi sallama.



WASHE GARI
shukra wai me yake damunki ne ace tunda aka miki maganar auren nn shikenan bakida wani aiki sai kuka
"Ammii ya xanyi da raina wae ni xa ayi wa auren dole
To shukra ya xakiyi ae sai hkr kawai
" yanzu Ammii ba abinda xakiyi akai?
To me xanyi shukra ae a gabanki yace na zuba ido ko? sbd haka rungumar kaddara ne kawae ya dace dake a halin ynx
"Bazan iya ba wlh Ammii banason koma wane ne kawai a kyaleni
To ae sai ki bari inya dawo kije ki gaya masa (zuwa wannan lokacin Ran Ammii ya soma baci da kalaman shukra) tana kaiwa nn tafice mata a dakin.

Wayar shukra ce ta fara ringing kamar BAZATA dauka Ba sai kuma da dauka "Aneesa ce class mate dinta tun a secondry har zuwa ynx da suke karantar" Optometry " a B U K.
" Hello Aneesa Y kk
"lfy shukra are you coming today?
"i don't think so
Buh why?
Am not feeling better
"wishing u quick recovery shukra luv
Thanks
Aneesa dan Allah inkin gama lectures ki biyo gida kafin ki tafi
"to insha Allah zaki ganni

Da sallama Aneesa tashigo cikin gidan Ammii ta samu a falo suka gaisa ann ne ta tambayeka shukra..

Tana ciki tana aikin kuka.
" kuka kuma Ammii bari nashiga ciki na sameta to.....




SHUKRA YARA GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/24, 3:58 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻



WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA



0⃣3⃣


Shukra wae me yake damunki ne Ammiii tace min kina kuka
Hmmmm Aneesa ba dole inyi kuka ba wae ni xa ayi wa auren dole..
What...come again shukra i didn't get u aure fa kika ce
"Ehhh aure wae daddy xemin da wani banza wnd ban sanshi ba
To ynx shukra zuba ido xakiyi ayi auren bawani mataki da zaki dauka.

Hmmmm banida wani zabi Aneesa abinda dae na sani shine" Wallahi tallahi daga ranar da aka daura auren nn daga ranar koma wane mijin yayi sallama da kwanciyar hankali da xaman lafiya.... Tunda dae ya zabi aure na tokwa ya xabar wa kansa masifa ne wae ni shukra zai Aura.... Hmmmm!!!


Hmmmm to nidai ba abinda xance sai dai
Ince Allah ya kyauta
"Ameen inji shukra"
Nidai Kinga tafiya ta cewar Aneesa tana mikewa
"ki gaida mamah"
Zataji insha Allah tafada tana ficewa daga dakin.




@Safeer's house

Dukansu na gani zaune a palourn mamah suka kallo
Safeer ne ya ke ta satar kallon Abba, Abban ne ya lurada shi
"Safeer ya akayi ne

" Abba wata magana nake so nayi daku sai dai ban san yanda zaku dauki maganar ba,
Juyowa Dukansu sukayi suna fuskantar shi suna jiran suji me zai ce
"muna jinka Safeer fadi me kake so kace kaji

Nan Safeer ya gyara zama ya fara basu labarin tun haduwar sa da Alhj sarakee har zuwa bashi yar shi da yayi
" Alhamdulillahi "shine abinda daddy yace yana me kara fadada murmushin kan fuskar sa
" ynx yaushe ne bikin to inji Mamah ta fada da murnar ta.

Yace baxe dau lokaci ba
To Allah ya nuna mana
Ameen Dukansu suka hada baki gurin fada


Yeyyyyyy!! Miemie ce tasa ihu ynx xan fara kiran kawaye in fada musu bikin yaya na yazo
Kae ranar akwai buduri wlh xamusha rawa da one leg yeeeeyyyyy ta cigaba da ihu....

Dukansu dariya suke banda Safeer daya hade ransa dama shi ba shiga harkarsu yake ba shi baya son rainin hnkl
"zan koya miki hnkl wlh meye hk mtwsssssss ya fada yana ficewa daga palourn.

Allah ya shirye ki miemie inji Aysher (yayar miemie ita take bin Safeer).



Alh sarakee ya yanke auren Safeer da shukra nn da sati biyu xa a daura aure inyaso ta tare koma yaushe ne.


Yau ta kama ranar da Safeer xexo Ammiii ce ke shirye shiryen ta banda shukra dake kwance a daki kamar kullum tana aikin kuka..............


Safeer ne ke saukowa daga upstairs cikin shirin sa na zuwa gidan su shukra sanye yake da shadda light brown gezna hannunsa sanye da agogo kirar rolex kansa da hula
Kai tsaye falon Mamah ya nufa ya shiga ya durkusa kusa da Abba ya shiga gaida iyayensa cike da ladabi
Da fara arsu suke answer wa
"za a tafi neman auren ne miemie ta fada tana buya a bayan mama

Ai kuwa a xuciye ya taso kamar wanda xe doke ta "yi hkr inji mamah kaifa babba ne
" Mamah yarinyar nn ta raina ni wlh inaji fa dana gaisheku sai da answer
Dariya daddy yayi yace ayi hkr kaji "tashi ka tafi kar ka makara
To kawae yace ya fice ransa a bace.....





DEDICATED TO MIEMIE BIE


SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/26, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA

Dedicated to miemie bie 😘.


0⃣4⃣


"kai tsaye safeer gidansu shukra ya nufa wanda cikin lokaci kadan ya karasa, parking yayi a inda aka tanada domin parking motochi sannan ya fito
"kai tsaye cikin gidan yanufa xuciyarsa tana harbawa da sauri da sauri ai kuwa sai yaci karo da kaninta
"yana ganinsa ya taso da fara arsa
" Good afternoon uncle
"Afternoon! How are you
"Not bad
" good "
Shukra fa? Ya tambaya
" tana ciki tana kuka
"toooooo to ynx xaka iya karamin ita
"Ehhh ammii tace in kazo ka shigo daga hk yayi gaba shikuma yabishi har guest room ya zauna shi kuma ya fita

Ammii! Ammii! Ammii
" Na am meye ne kake ta kirana ta fada tana fitowa daga kitchen
"Ammii mijin Aunty shukra ne yazo
" ohhh har yazo ince dai ka kaishi guest room ko
"Ehhh Ammii yana chan yace in kirata
" to jeka abinka zan turo ta
"To kawae yace ya koma gurin safeer inda suka cigaba da hirar su kamar dama chan sunsan junansu ne.

"sanda Afeer ya fita Ammii kai tsaye dakin shukra ta shiga 'shukra tashi ki shirya ga safeer chan yaxo yana jiranki' tana gama fadar hk tafice ba tare da ta jira me Zata ceba"

Koda Ammii ta fita shukra xamanta tayi batada niyyar tashi har sai da takai 40mints a zaune
"Ammii ce ta leko 'ynx shukra har ynx kina nn a zaune kinbar yaro yanata jiranki shima fa yana da abinyi amma ya vari yatawo gurinki amma kika barshi a zaune ko?
" A a Ammii ynx xan tafi fa.
"karma ki tafin mana ynx in kira Daddy in fada masa
" Dan Allah kiyi hkr Ammii wlh ynx xani ta fada tana mikewa
Ammii ce ta fara fita sannan itama ta fita

"kai tsaye guest room ta shiga Amma koda ta shiga sai tayi tsaye abinta ta kuma sunkuyar da kanta dan ko kallo ma be isheta ba"


"Tsahon lokacin suka dauka ba wanda yace da dan uwansa komai
" safeer ne ya katse shirun ta hanyar mikewa yana cewa toni xan wuce
"sai na dawo ko
" komai bata ce ba illa matsa masa da tayi ya huce
Yana fita ita ma ta fice kai kai tsaye dakinta ta shige ta rufe.


"koda safeer ya koma gida be nuna wa iyayensa hk ne ya faru ba kuma koda Alhj sarakee ya kirashi cemasa yayi to karbe shi hannu biyu - biyu.



" To biki fa ya gaba to kamar yadda Alhj sarakee yace xa a daura aure inyaso ta tare daga baya hk kuwa akayi
" Yau ta kama saturday wanda yaune za a daura AUREN iyayen sai farin ciki suke banda yayan da suke a cikin tsananin bakin ciki musamman shukra da ba son auren take ba
'Har gwara na safeer wanda shi daman tunda yaga shukra yaji sonta ya shige shi sai dai yayi wa kansa ALKAWARIN baze taba nuna mataba har sai ya koya mata sonshi

(🤔🤔 uhmm su safeer manya)
"To abokan safeer duk sun hallara a gurin daurin auren don taya shi murna".

Sanye yake da farar shadda tasha aiki wanda aka yimusu shida Abbansa iri daya, bakin takalmi da bakar hula yasa sai kuma farin agogo da yasa sai kyalli yake yana ta fara a wadda shi kansa besan na menene ba kawae dai ya tsinchi kansa cikin farinciki ne a yau din ( Niko nace luv ne).


To Daurin auren ya samu halartar manya manyan mutane daga ko ina a fadin Nigeria wanda yawanchinsu abokan Abba da daddy ne
"An daura AUREN akan sadaki naira dubu dari.
Haka dai daurin aure ya watse kowa na farin ciki ana kuma ta sa albarka.
To kamar yadda daddy yace shukra BAZATA tare ba hk kuwa akayi bata tare dinba tunda ynx ma final exam dinta xata fara ta kammala university.
To shukra fa sun fara exams gadan gadan wanda ynx ma sun kusa gamawa shikuma safeer ya cigaba da zuwa Aikin sa kamar da.


Shukra ta kammala exams dinta kuma ansa ranar tare war ta nanda sati uku.

"Duka banga rorin biyu shirye shiryen su suke tunda xa ayi mothers night kafin akai amarya dakinta.

" yau ta kama saturday wanda yaune xa ayi mothers night shukra taci kwalliya kamar ba gobe "Fancy Makeover" itace ta mata kwalliya kuma tayi shirinta cikin wani material me tsadar gaske kalar peach tasa head orange (hmmmm abin dai ba a cewa komai readers zanso kuga shukra yau din nn ba karya) takalmi da jaka duka orange tasaka.....
"Daga nn dai aka dunguma zuwa" Shukra event centre "inda ann ne za ayi mothers night din.

To anchi ansha Alhamdulillahi guri ya kayatu daga nn ne aka kwashi shoki sannan aka rufe taro da addu a aka dauki amarya aka wuce da ita gidan ta dake nn Nassarawa G R A.................................

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login