Showing 42001 words to 45000 words out of 49582 words

Chapter 15 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt

da bucket na karfe, Mamah tasa Kaskon cikin bucket din tazuba angurya(wanda ake samu a jikin audiga) tazuba bawon (kwanson) citta Shukrah ta zauna akai, Bayan an gama wannan Mamah ta kara zuba wani turare da wata kawar ta ta kawo mata daga Senegal "

" T haka dae rayuwa ta cigaba da tafiya kuma yau Shukrah tayi sati biyun da Mamah ta kara mata, Mamah tasan halin Safeer sarai shiyasa ma bata kirasa ta tuna masa ba, Amma ga mamakin ta har bayan magrib Bai shigoba, abin ya damu Shukrah sosai shiyasa ta faki idon Mamah ta shige dakin ta fara kiran wayarsa, bugu biyu tayi yayi picking "

" Hello *Papan Twins*


"Yap *Mamin Twins* ya kuke?

"Lafiya kalau muke, kai muketa jira dae"

"Murmushi Safeer yayi wanda har Shukrah na iya jiyo sautinsa yace ke bakin biyewa Mamah ba kin share ni, nifa da har na fara tunanin dama akwai wata yarinya teemerh luv tana masifar sona to da har nayi niyyar zuwa gurin Dad nata in nemi AUREN ta nanda two weeks in za ayi bikin Haiydar a hada namu kawai "


" Shukrah ta saki kukan shagwaba tana bubbuga kafa Ni wallahi bazan yarda ba, Ni wallahi kawai kazo mu tafi ko in tawo da kai na "


" Kukan da Shukrah take ne yasa Mamah ta shigo dakin, jin abinda Shukran ke cewa yasa Mamah ta fahimci da wanda suke wayar, saboda haka ta ta koma ta ta samu Miemie aparlour

"Miemie je ki kiramin Aysher tazo ku kai Shukrah gidanta, to Miemie tace sannan taje ta kira ta, Mamah da kanta tayi wa Shukrah bayanin Su Aysher zasu rakata, Bayan kamar minti goma sha biyar Shukrah ta shirya tsaf haka ta shirya twins, Aysher da Miemie suka tayata sa kaya a booth, Mamah dae tana tsaye sai da taga fitar su ta koma ciki... . .





*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞
[5/17, 4:49 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected marriage*)




*WRITTEN BY*
*ZAINAB YAKASAI*
*SHUKRAH*



*DEDICATED TO MIEMIE BIE*😘





4⃣0⃣


"Cikin Mota *SHUKRAH* tayi wa *SAFEER* Text tace masa tana hanya, zo kuga murna gun sa don beyi tunanin *Mamah* zata yarda ta barta ta tawo ba, saboda tsabar zumudi zaman cikin gidan gagarar sa yayi saboda haka ya sa jallabiyya ya fito ya zauna gurin gate man, jefi jefi suke hira, Zaman kamar minti goma sha biyar yayi yajiyo horn a, ko ba a fada ba yasan su *SHUKRAH* ne shiyasa ma yayi Saurin mikewa yaje get din da sauri da nufin bude musu, get man yayi Saurin karaso wa "

" Ranka ya dade, kabari za a bude yace yana kara sawa jikin get din"

"Yi sauri ka bude dae, ba surutu nace kayi min ba *Safeer* yace cikeda kaguwa"

"Nan get man ya bude musu, Aysher ta shigo da motar, yayi Saurin ban bayan motar, Tun kafin Aysher ta gama Parking *SHUKRAH* ta bude ta ziro kafarta, kadan ya rage *labeeba* ta fadi a hannunta, Da sauri *Safeer* ya karaso ya hada ta da *labeeba* ya rungume su cikeda so da kaina, sam ya manta ma dasu *Miemie*(Baki abun magana) suna tsaye "


" Aysher tayi Saurin dauke kanta, *Miemie* ta tabo Aysher, Aunty Kinga ya *safeer* din nn ko kunyar mu ma beji ba, lallai ", Aysher ta buge mata baki tace kin cika surutu wallahi, bazaki iya dauke idonki ba"

"Duk wannan maganar a kunnen *SHUKRAH*sukeyinta shiyasa tayi Saurin ture *Safeer* din tace su *miemie* na kallon muda, dariya kawae yayi sannan ya daga kafada irin ko a jikin sa din nn, *SHUKRAH* ta kallo *Aysher*, *Aysher* tayi Saurin dauke kai, ita Shukrah dariya ma aysher ta bata tace Bazaku shiga bane kuka tsaya wae, Aysher tayi Saurin kallon ta ta girgiza kai tace baxamu shiga ba Aunty dare ya fara yi kuma ban iya driving din dare ba"


"To Kawai *SHUKRAH* Tace sannan *MIEMIE* ta mikawa *Safeer* *Labeeb* dake hannun ta, *SAFEER* Tsabar mugunta sanda ya karbe shi sai da ya murde hannun *MIEMIE* yace fitsararriya kawai, Allah ya sa dae kina karatu don naga har ynx kanki yana rawa "

" Yar kara *Miemie*ta saki sannan ta kallo shi da fuskar tausayi tace Eyya ya *Safeer* akwai zafi fa, cika mata hannun yayi yace wuce ki bani guri ni, harda dan gudun ta ta wuce ta shiga mota *Aysher* tayi musu sai da safe sannan ta shiga motar tayi reversed T fice a gidan"



10:15 *Safeer* ya samu *SHUKRAH* a dakinta tana shirin kwanciya, ya karaso ya rungume ta ta baya yace mata a kunnen ta kinsan fa yau ke amarya ce, hope you are ready "


*SHUKRAH*ta danyi murmushi tace twins dae suna jinka ni ba ruwa na, Dariya shima yayi ya juya ya kallon su, bacci suke hankali kwance, ya dawo da kallo shi gurinta yace Bawani nn wayo kike son min, ae sun riga sunyi bacci, Dan ture sa *SHUKRAH* tayi sannan ta ja hannunsa suka kwanta suna fuskantar junansu "



" *safeer* ya kara matsowa jikinta yace mata *i luv u Babe beyond your expectation* "Murmushi *SHUKRAH* tayi tace kayi shiru bacci zamuyi, Matseta *Safeer* ya kuma yi sannan yace tunda nake da ke ban taba jin kince min i luv u ba, kodai har ynx bakya sona ne"


" *SHUKRAH* tayi Saurin matse hannunsa dake cikin nata haka kuma ta runtse idonta don tana masifar jin nauyin kalmar nan, dakyar ta iya bude baki tace

*My feelings for you are so strong and deep that i cant convey them in words, because i found no word strong enough to tell you how much i luv u, You are more than amazing, my heart is all yours*~i luv u~"



"tana kaiwa nn ta kifa kanta jikin pillow tana dariya kasa kasa, *Safeer* fa be taba tunanin jin wannan maganar a bakin taba though he's quit sure tana sonsa, tunda dae alamu sun nuna hkn, Saurin dago kanta yayi ya zira harshen sa cikin bakinta ya fara tsotsa cikeda so da kauna da kuma kewarta, kara shigewa jikinsa tayi don tayi missing dinsa sosai 54 days basa tare fa, haka dae suka raya wannan daren"



~~~~~~~~~~~~~~~~~~~




"yau saura kwana biyar bikin *Haiydar* amma bemasan me ake ciki ba, don *hajiya* kobi ta kansa batayi ba, duk wani abu da yakamata da *Safeer*take hatta kayan da zesa suna gidan *safeer* haka ma invitation cards suna gurin sa "


03:25 pm *safeer* ya shigo office din *Haiydar* da sallamarsa ya ajiye envelop kan desk sannan ya zauna yana fuskantar sa, ko kallo *Safeer* be ishi *haiydar*don yana kula da take~takensa, kuma sam zuciyar sa bata aminta da yawan zuwan da *safeer* din yake gidan su "



" *Haiydar* ga wannan invitation cards din ka ne ko zaka bawa abokanka na gida, don na office na gama basu *Safeer*yace yana nuna masa envelop din daya kawo "



" Murmushin takaichi *haiydar*yayi yana bin *Safeer*da mugun kallo tsawon lokaci sannan ya dauki envelop din ya mika masa yace cikeda takaichi karbi ka fitar min a office kafin ranka ya baci, kuma wallahi ka cire hannunka a maganar nan don gudun bacin rai"

"Dariya Safeer yayi sannan ya mike yace ni bazan karba ba don bana bukatar su, kuma ni bana gudun bacin rai indae akan wannan maganar ne "


" Fita Dalla malam kafin rai na ya gama baci don wallahi komai yana iya faruwa " *Haiydar* yace yana nuna masa kofa, Dariya *Safeer*
Yayi sannan ya fice yana cewa ba lefin ka bane wallahi nanda wani dan lokaci zaka dawo dai dai ae *Auren Bazata Alheri ne*


" Kwanaki sunja kuma gobe za a daura Auren *haydar*amma *Miemie* bata samu labari sai yau din da taji Aysher da Mamah suna maganar, ta zaro ido sannan tazo da sauri ta durkusa kusa da Mamah tace ki kace wae bikin ya Haiydar za ayi da wata banida ta fashe da kuka tace wallahi ina sonsa ina kaunar sa Mamah ku rufa min asiri zan mutu wallahi"



"Aysher ta harare ta tace Dalla can rufe mana baki wae, ina sonsa ina kaunar sa, ke har kinsan wani so "

" Mamah ta janyo miemee jikinta tace yi hakuri kinji Kinga ynx makaranta kike kuma wadda zai aura yar uwar sa ce, kema inkin gama school zai aure ki ae"

"Miemie ta turo baki tace ni wallahi bana son kishiya sai dae ya sake ta ya aure ni, Mamah tace yawwa hk za ayi ke dai ki kwantar da hnkl 'nki kawae, ynx kitashi kije daki ki dauki ankon ki kan bed ki gwada"


"Mikewa tayi ta nufi dakin tana bubbuga kafa' ni wallahi bazan je bikin kishiya ba... .






*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞💞
[5/23, 11:43 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected marriage*)



*WRITTEN BY*
*ZAINAB YAKASAI*
*SHUKRAH*




*DEDICATED TO MIEMIEBEE*



4⃣1⃣


"Friday 26 october 2015 da karfe hudu na rana daukacin al'ummar musulmai suka shaida daurin auren *ALIYU KABEER DAN KASA* ( *HAYDAR*) Da amaryar sa *KHADEEJA ABDALLAH MAI KANO*( *ZAFEERA*) Kan sadaki naira dubu dari da hamsin, daurin auren da ya samu halartar manya manyan mutane daga fadin Nigeria kai harma da mak'otan Nigeria, "





Da daddare akayi kayatacciyar dinner ta gani ta fada, abokan haiydar duk sun halarchi dinner din haka ma kawayen zafeera guri ya cika har ba masaka tsinke kasan cewar harda yan gayyar sodi ma sun je, haka akaci aka sha aka tashi mutane sai sawa auren albarka suke "
" Washe gari akayi yini da daddare kuma Aka kai amarya dakinta, misalin karfe goma sha daya na dare haiydar yana mike a dakinsa na gidan Hajiya bama shida niyyar fita, a bangaren amarya Zafeera kuwa har ta gaji da jiran ango ta kwanta ta fara bacci kuma generator ya mutu saboda zafi ya dameta, mikewa tayi ta leko palour amma duhu ya gauraye gurin da kyar ta lallaba ta leka dakin dake kusa da nata, wanda take kyautata zaton na Haiydar ne amma ga mamakin sai taga baya ciki, parlour ta dawo ta zauna amma tsoro ya hana mata sukuni sai take ganin kamar Mutum ne ke giftawa ta gefen ta hakan yasa ta mike jikinta na rawa ta shige bedroom dinta ta dau wayar ta, number Safeer ta nemo tayi dialing, Allah ya taimaka mata kuwa ringing biyu tayi yayi picking


"Hello Safeer "Zafeera tace murya na rawa, ba tare da ta jira yace wani abu ba ta cigaba
" Safeer dan Allah kazo ka kunna min generator wallahi tsoro nakeji "

" Shi Haiydar din yana ina? Safeer ya tamvayeta cike da mamaki"


"Nina wallahi ban Sani ba, dan Allah kazo, Zafeera ta Bashi answer tana fashewa da kuka, dan har ga Allah tsoro takeji tunda a gidansu bata saba zama cikin duhu ba "


" To shknn gani nan zuwa ki dena kuka, tare ma zamu tawo da haiydar din kinji safeer yace sanda ya mike ya dau car key dinsa, dakin Shukrah ya wuce ya mata bayanin komai, ta mishi Allah ya kiyaye hanya sannan ya fice da sauri "

" Gidan Hajiyar Haiydar ya wuce direct don ya tabbatar Haiydar yana can, Sanda ya karaso gidan dakin Haiydar ya tura, ae ko ya ganshi kwance yana ta bacci abinshi, Safeer yaja tsaki sannan ya karasa ya fara buga mishi pillow 'nda yake kai da karfi, don iya haushi yau haiydar ya bashi "


" Bude ido Haiydar yayi waze gani in ba Safeer, ya hade rai yace lafiya zaka tashe ni ina bacci "

" Ba lafiya ba Haiydar kai kazo nan hankalinka a kwance kana bacci kabar yarinyar mutane a cikin duhu ko, to wallahi ko ka taso mu tafi ko kuma inje in kira hajiya Safeer yace yana hararar Haiydar "


" Haiydar wanda yasan in aka kiramai hajiya tasa ta kare yayi Saurin mikewa yana hararar safeer sannan yace muje cike da kulewa, tabe baki Safeer yayi sannan yayi gaba, shima Haiydar din takalmi kawae Yasa ya bi bayansa, "


" Cikin mota ba wanda yace da dan uwansa ci kanka kowa sai cika yake yana batsewa, Sanda suka karaso gidan ne Safeer ya kalli Haiydar yace
"Haiydar Zafeera amana ce a gurinka duk wani nauyi nata da hakkin ta a wuyanka ya rataya, kada ka manta zamu mutu zamu koma ga Allah kuma za a tuhume mu kan duk wani aiki namu, kuma kasan Allah baya yafe hakkin wani akan wani, iya abinda kai masa ne kawae in ka rokeshi gafara zai gafarta maka, Wallahi indae k zalunci yarinyar nan sai Allah ya kamaka karka manta yanzu tun a duniya dan adam yake girbar abinda ya shuka, kuma a hakanma sai Allah yasoka da rahma, kaje kayi tunani Haiydar, kada ka yarda ranka ya baci hankalinka ya gushe, nasan anmaka wannan auren ne ba a son ranka ba wannan aurene na baxata, Amma inaso kayi tunani sosai nanda dan wani lokaci zakaji dadi, yana kaiwa nan ya fice ya koma motar sa ba tare da ya jira answer ba, don ya nada tavbacin nasihar sa ta samu shiga tunda yaga jikin Haiydar din yayi sanyi sosai "



" Generator Haiydar ya kunna sannan Y shiga cikin gidan, Sanda ya shiga ya ganta a takure idon ta harya kumbura don kukan da tashi, take yaji wani tausayin ta ya shige shi nasihar safeer ta dawo mishi ya tuna Zafeera fa yar uwarsa ce Kuma yana daya daga cikin wanda zasuji bakin ciki in wani ne ya aure ta ya wulakanta ta, sannan ya tuna *RAYUWAR SAFEER DA SHUKRAH* Ta da data yanzu, yasan hakuri da juriya shine jigon farin cikin su yaji a ransa yana son dan dana rayuwar kwanciyar hankali da zaman lafiya, shiyasa ma yaji duk tsanarta ta goge a cikin zuciyarsa haka wani sonta da tausayin ta suka mamaye zuciyarsa, saboda haka ya karasa gaban ta ya durkusa gab D ita ya riko hannaye ta duka biyun yana mata wani kallo, tsawon wani lokaci kafin ya bude bakinsa dakyar yace

"Zafeera ki dago ki kalleni, Haiydar ne a gaban ki yake magana, nasan zakiji zafin wannan auren haka kuma zakiyi bakin cikin auren wanda bakya so kuma baya sonki, Ni dan uwanki ne bazan ki kiba, matukar dae zaki cire kowa a ranki ki rungumi kaddara, to insha Allah bazaki samu matsala daga bangarena ba"


"Daga mishi kai kawae tayi alamar gamsuwa daga nan dae yaja hannunta suka shiga daki, sunyi alwala a tare suka gabatarda sallar godiya ga ubangiji haka suka kwanta kowa yana sake saken sa, kai a takaice dae a wannan Daren Haiydar ya zama cikakken namiji don ya dan dani zumar da bai taba dan danar taba ya kuma jinjinawa kanwar sa haka kuma ya samata Albarkar rike mutunci ta da tayi"






"kwanaki sun ja sosai Haiydar ya shiga sabuwar rayuwa ya yarda zagin iyaye yafi zabinka ya tabbatar wa kansa wannan itace Kyakykayawar kaddara haka kuma yayi amman na da cewar safeer a kullum wato( *AUREN BAZATA ALKHAIRI NE*) "



~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Yau watan twins shida a duniya sun girma sunyi wayo sosai haka kuma kyansu ya dada fito kamar ka sace su, kuma yau Shukrah zata fara aiki a *MARYAM CLINIC* Hakan ne yasata tunda ta tashi tayi sallar a suba bata koma B tanata kiciniyar hada breakfast ga twins sai rigima suke ta rasa inda zata sa kanta ta dauki wannan ta goya wannan sukayi shiru abinsu zuwa can ta ajiye su ae tana juyawa suka kuma fasa kuka, zuciya ta cita ta kwada wa *Labeeba* duka a bayanta ae ko akan idon safeer wannan abun ya faru ya kara so ransa a hade kamar be taba dariya ba ita kanta Shukrah ta tsorata, ya daga *labeeba* yana jijjagata saida tayi shiru sannan ya juya yana kallon Shukrah da fuskarshi datayi ja saboda bacin rai ya nuna da yatsa yace

"wannan ya zama na farko kuma na karshe dazaki sake dukarmin yara in bakya sonsu ni ina son su, wannan ma ae mugunta ne zaki kama yarinya kina duka me ta Sani? Kuma ki hada min kayan su zan kaisu gidan Mamah kafin in auro wadda zata kularmin dasu, yana kaiwa nn yayi ficewarsa ya barta, ae Shukrah bata san sanda ta zube ba a gurin tana kuka kamar ranta zai fita, tayi data sanin dukan labeeba datayi sau ba a dadi, ganin datayi lokaci yana kure mata yasata mikewa taje tayi wanka a gurguje ta shirya tadau labeeb ta fice a gidan, Gidan Ammii ta kaisa sannan ta fice, Sanda ta karasa asibiti office din *DR. MARYAM ANAS* Ta wuce kai tsaye"


"Shukrah bata wani yi mamakin ganin karamci da mutunci da kuma girmamawar da *Maryam Anas* tayi mata ba don tasan labarinta gurin Ammii, Mamah da Safeer ta babbatar zatayi abinda yafi haka"


" *DR. MARYAM* Da kanta takai *SHUKRAH* office dinta, kuma a gaban ta tafara attending patients, sosai ta ya bawa Shukrah kuma bata boye a cikin ta ba saida ta fito ta fadamata"

"Shukrah nayi mamaki sosai yadda kika iya aiki haka "

" Dariya Shukrah tayi sannan tace ai ban manta ba saboda nasa abun a raina kuma ina karanta littattafai sosai dasuka shafi bangaren ido"


"ae haka ake so Shukrah Allah yayi miki Albarka kinji DR. MARYAM Tace sannan ta fice"

1:35pm *SHUKRAH* ta gama komai saboda hk sai da ta jira 2:00tayi sannan taje tayi wa Dr Maryam sallama, gidan Ammii ta fara zuwa tayi sallah taci abinci sannan ta dauki labeeb suka wuce gidan Mamah, basu wani dade ba tadau labeeba suka wuce gidansu"


"4:35 pm safeer ya shigo gidansa yana wani cin magani wae shi a dole fushi yake da Shukrah, Shukrah wadda take cikin kitchen da gudun ta ta rungume shi tana mishi oyoyo, ya tabbatar baze iya yin fushi da Shukrah ba don ta zame mishi jigo a rayuwar sa, matseta yayi sosai a jikin sa yana kissing wuyanka, zuwa can yadago yana kallon ta, Shukrah ya office da Aunty Maryam hope every thing is moving fine "



" Lafiya kalau Shukrah ta bashi answer sannan taja hannunsa zuwa dakinsa, da kanta ta mishi wanka ta tayashi shirya wa sannan suka dawo parlour tadau labeeb ya dauki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login