Showing 3001 words to 6000 words out of 49582 words

Chapter 2 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt











SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/27, 9:52 AM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA

Beauty, intelligent, respecting peoples are what makes you swthrt #MIEMIE BIE i Dedicated this page to you.



0⃣5⃣


ASALIN SU

Alhj AL 'ameen sarakee haifaffen garin adamawa yola ne yayi karatun primary & secondry dinsa a garin Adamawa wanda daga nn yayi exam jinsa wato Jamb ya kuma samu point me kyau
Ya nemi admission a usman danfodio university sokoto wanda cikin yardar Allah ya samu ya fara karanta 'Geology'.
To bayan ya kammala karatun sa ne be dade ba yasamu Aiki a wani company a garin kano inda ya tattaro gaba daya ya dawo kano da xama


"Alhj sarakee ya hadu da matar sa fateema ne (Mahaifiyar shukra) a saudiyya inda yaje aikin hajji
" itama fateema gabaki daya yan gidan su suka je Aikin hajjin kasancewar mahaifinta me Arzikin gaske shine senator na kano central a wnn lokacin
"To kasan cewar A lokacin Aikin hajji suka hadu yasa basu wani fahimci junansu ba sundai yi exchanging numbers na niyyar in sun dawo gida sarakee zaije ya sameta.

" to bayanda suka dawo gida ne Alhj sarakee yaje gidansu fateema kuma ta hada shi da iyayenta..
Baban fateema ya yaba da hnklin sarakee kwarai shiyasa ma bayan dayayi bincike a kanshi sosai ya nemeshi ya kuma shaida masa ya turo iyayensa.

" Iyayen Alhj sarakee sun zo sun kuma yi duk abinda ya kamata akasa ranar biki wanda ba a wani dau lokaci ba aka daura auren aka kuma kai fateema gidanta dake unguwar 'Farm center'.

To zaman fateema da sarakee xama ne abin sha awa domin akwai girmamawa da mutunta juna.

'Haka zaman su ya cigaba har na tsawon shekara biyar wanda a wnn shekara biyar din fateema ko bari bata taba yiba balle haihuwa abinda yayi matukar daga mata hnkl kenan
"A bangaren sarakee kuwa sam abin be dameshi ba shine ma kullum yake kwantar mata da hankali yana cewa haihuwa ta Allah ce Kuma lokaci ne beyiba in yayi xa ta haihu
" To da wannan kalami na sarakee fateema tayi amfani wajen kwantar da hankalin ta.
Ana cikin haka ne fateema ta sami ciki, zo kaga murna wajen sarakee da fateema kai har ma da iyayansu wanda daman suma rashin haihuwar ya damesu shiru dai kawae sukayi.

"Ciki dai yana samun kulawa yadda ya kamata
Haka suka cigaba da kulawa da cikunsu har watan haihuwa yayi wanda Alhj sarakee takanas ya tafi 'Egypt' danyin siyayyar kayan baby

" To ana gobe fateema xata haihu sarakee ya dawo wanda washe gari da asuba fateema ta tashi da ciwon mara da ciwon baya wanda sarakee be bata lokaci ba ya dauki fateema sai asibiti.

" Cikin lokacin da be wuce awa daya ba fateema ta haifo kyakykyawar yarta me kama da Alhj sarakee sak daga nn akayi discharging dinsu kasan cewar fateema da babyn lafiya kalau suke.

" Ranar suna yarinya tachi suna 'ZAINAB' wato mahaifiyar Alhj sarakee hakan nema yasa suke kiranta da suna 'SHUKRA'



" Sai da shukra ta kai shekara 7 sannan fateema ta kara samun wani cikin. To wnn cikin ma anyi farin ciki da samun shi kasancewar sun cire rai ma da kara samun wani cikin.


," Haka dai take ta rainoncikin har lokacin haihuwar yaxo inda ta haifi yaron ta namiji.
"shikuma sunan mahaifin fateema yaci wato Mukhtar suke kiransa da 'AREEF.


" Tundaga kuma wannan lokacin har zuwa ynx fateema bata kara haihuwa ba.
"Haka yaran suka taso cikin soyayya da kuma kulawar iyaye sosai yaran suke da tarbiyya ga girma ma manya ga kuma kunya da tsoron Allah.






CIGABAN LABARI

" TO koda safeer ya taso daga office gidan mahaifin shi ya wuce kai tsaye inda iyayen nashi suka hadu suna mai nasiha kan ya kula da matar sa domin amana ce a gurin.
" Godiya safeer yayi musu sannan kuma ya kama hanyar gidansa xuciyar sa cike da sake sake tunani kawae yake wace irin tarba shukra xatayi masa?
" zata karbi kaddara ne ta zauna dashi a hk ko kuma BAZATA karba ba?
"To da wnn tunanin ne safeer ya karasa gurin wani suya spot ya siyi kaji da kuma fresh milk xe kaiwa amaryar sa...........

" Bayan yagama da suya spot kai tsaye gidansa dake nassarawa G R A ya nufa koda ya isa yayi worn a gate, gate man ne Y taso da fara arsa ya bude mishi yana gaida shi da fara arsa.
" To safeer dinma da fara arsa yake answer wa kafin ya wuce gurin da aka tanada don parking yayi parking motarsa sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye..........................





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/29, 4:33 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻



WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


I don't care weather people will like it or not, ☹if they like it "cool ' if not it left for them (Hmmmm such is lyp). I only know that i luv u #MIEMIE BIE
Dedicated to you 👆🏻




0⃣6⃣



Ko da SAFEER ya shiga cikin gidan kai tsaye dinning area ya huce ya ajiye kayanda ya shigo dasu sannan ya shige dakinsa.
"kayan jikin sa ya rage ya fada bathroom don yin wanka.



" A bangaren shukra kuwa yan kawo amarya na fita ta mike ta rufe kofar ta sannan ta koma tayi wanka tasa sleeping dress nata ta kwanta.

"Bayan kamar 30 mints da shigar SAFEER toilet ya fito daure da towel a waist nasa da kuma wani a hannun sa yana goge kansa dashi.
" kai tsaye gaban dressing mirror sa ya wuce ya shafe jikinsa da lotion sannan yasa turare ya wuce kan gabon sa dan sa kaya wanda already dama ya fito dasu.

Bayan da ya gama shirya ne ya fito ya nufi dinning area ya dauko ledar da yashigo da ita sannan ya wuce dakin shukra.

"Yana karasawa ya murda handle din kofar amma ga mamakinsa sai yaji kofar a rufe gam.

Cikin bacci shukra taji ana taba handle tsaki kawae taja tana hararar kofar kamar yana kallonta.
" A zuciyar ta take cewa munafiki da ajinka xan bar kofar a bude ne" mtwsssssss ta dada jan tsaki sannan ta juya baya ta cigaba da baccin ta.



"Shiko SAFEER juyawa yayi ya nufi dakinsa jin kofar shukra a rufe.



" Washe gari misalin karfe 12:00 na Rana ko wannen su na dakin sa.
"knocking din da ake a kofar falo ne yasa SAFEER fitowa ya karasa ya bude kofar.

"kokarin tureshi take yi xata shiga ciki da basket a hannunta
" ke bakida hankali ne wae kike ture mutane ya fada a tsawace yana binta da mugun kallo...... Wallahi ki kiyaye miemie inba hk ba hmmmm ya fada yana wuce wa cikin falo.

"Dan nazo gidan ka shine kake min hk ta fada tana tura baki gaba kamar xatayi kuka.
" Ammiki din ya fada yana hararar ta (shi sam be so wannan yarinyar tazo ba don surutun ta yafi aikinta yawa).

"Wae ke me kika zo mn gida da sassafe.

" Baki ta saka tana kallon shi da mamaki 'ynx ne safiya ya SAFEER?...


"To ynx ma ba wannan ba ina Aunty na.

Tana ciki ya fada a takaice.
"Au ita bata rashi ba 🤔 ikon Allah koda yake ae da gajiya gwara ta huta.
" Gajiyar me ya fada yana mikewa wane zai daketa.

"Tana ganin haka ta mike gajiyar biki fa nake nufi.
God save you ya fada yana koma kan kujera.
" To ynx yaya haka xan tafi ban ganta ba.
"Ehhh yace yana nuna mata kofa 'fita Dalla kinzo kin Sani a gaba da surutu
Fita tayi tana waigensa tana zuwa bakin kofa ta labe shikuma ganin ta fita yasashi komawa daki tunda bashi da abinda xeyi.

" Aiko miemie na ganin ya shige daki tashigo cikin gidan da saurinta tana waige- waige.
Kai tsaye dakin shukra ta huce aiko sai ta ganta tsaye jikin dressing mirror tana makeup.

" Aunty shukra ta fada tana yi mata murmushi.


"Murmushi itama shukra take mata haka kawai taji tana son yarinyar.
" ya sunanki ta fada tana kamo hannunta.
Sunana miemie.
"Miemie ya gida ya mamah?
" lafiya kalau muke.
Aunty wae me yasa yaya ya hanani inzo gurinki ta tambaye ta tana karewa dakin kallo.

"Bakomai miemie inaji saboda sanda ya fita ina bacci shiyasa yayi tunanin ban tashiba (Tayi mata karya).


Ok na dauka sbd yaga kin gajine bayaso in tashe ki.

" Gajiyar me miemie? Ni ban gaji ba ae.
Uhmm kawae tace tana hayewa gadon.

" Dariya shukra tayi ta koma ta cigaba da makeup dinta.

"A takaice dai miemie a gidan ta yini sunata hira da shukra kamar dama sun saba da juna.
" Sanda miemie xata tafi sai da shukra ta cika katuwar leda da kayan makeup ta bata.
Godiya sosai tayi mata sannan SAFEER ya dauketa suka tafi.



" Yau ma da safeer ya dawo dakin shukra ya wuce amma yasame shi a rufe juyawa kawai yayi ya koma dakinsa kasan cewar a gajiye ya dawo (shi dama ba wani abu xe mata ba kawai dai zai duba lafiyar tane kamar yadda mahaifinsa yace amana ce a gurin sa).




" Yau sati biyu da bikin safeer & shukra amma cikin sati biyun nn safeer be taba sa shukra a idonsa ba.


Dawowar sa daga masallaci knn amma ga mamakinsa sai yaga kofar shukra a bude ae kuwa sai Y xarce dakin.

" Shigarsa yy dai dai da fitowar shukra daga toilet daure da towel dinda be karasa rufe mata cinya ba..
Kallon kallo suka shiga yi kafin shukra ta bude baki ta fara zaggaga mishi masifa.





SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/29, 5:00 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻


WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA



Dedicated to miemie bie ❣



0⃣7⃣




Wnn wani irin hauka ne xaka shigo dakin Mutum ba excuse ta fada tana hararar sa..

Hauka ya nanata kalmar a zuciyar sa

"Allah ya baki hakuri ya fada yana juyawa zai fita.
" Yana zuwa bakin kofar ya rufe da key sannan ya xare key din ya sa a aljihun wandonsa.
"Takowa yayi gabanta fuskar sa a daure ba alamar dariya.

" Iya tsorata shukra ta tsorata nn ta shiga yin baya - baya shi kuma yana binta.

"Hannu yasa ya jawota yana kokarin kunce towel din jikin ta" Bari ba miki cikin mahaukachi yanda ko waje kika fita kika ga mahaukachi vazakiyi masa goriba tunda kina dashi.

"Kuka tashiga yi tana turashi yayinda take rike towel dinta da dayan hannun, Amma dake karfin ba daya ba sai da ya kunce towel din sannan ya turata zuwa gadon shima ya hau.

" Ganin batada wata mafita yasata fara rokonsa 'Dan Allah ya safeer ka bari wlh tsoro nakeji, na tuba bazan sake ba.


" Gani kawai shukra tayi safeer ya mike ya nufi kofar fita sannan yasa key ya bude ya fece. (shi dama beyi niyar mata komai ba kawae dae barazana ya mata).


" Tun daga wannan rana shukra take masifar tsoron safeer bakuma ta sakachin kin rufe kofar ta.


" Yau ta kama monday kuma yau safeer zai koma aiki sbd hk ya tashi da wuri ya gama shirin sa na zuwa office ya fito palour rike da briefcase dinsa. Ko dinning be kalla ba tunda yasan shukra ba zatayi masa girki ba.

" Yasa kai xe fice kawae tasha gabansa hade rai yayi yana kallon ta shi sam be ma kula da ita a palour'n ba,

," ya safeer dan Allah xan bika ka kaini gida
To jeki dauko hijabi mu tafi..

Ihu murna tasa ta shige daki da gudu



SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[3/31, 2:28 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻




WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA


Wishes to congratulates you as you finished your novel that always makes people happy, because it composed a lots of lessons.
May God bless your entire life #MIEMIE BIE
Dedicated to you 👆🏻



0⃣8⃣


"koda shukra tashiga cikin dakin bata wani dade ba kasan cewar dama a shirye take mayafi kawae ta dauko ta fito ta samu safeer zaune cikin motarsa yana jiranta.

"Bude motar tayi ta shiga bata cemasa ba shima bece mata ba haka suka kama hanyar gidan su shukra kowa na sake sakensa cikin ranka.


"cikin lokacin da be wuce 40 mints ba suka karasa gidan su shukra, kasancewar safeer nada aiki sosai a office yasa ko da shukra ta fita be bita cikin gidan ba.


" Ango kasha kamshi abokinsa yace masa yana dariya irinta tsokana.

"Koma bece ba yakaro yana mika masa hannu suka gaisa sama - sama kasan cewar sun kusan makara.


" sanda shukra tashigo cikin gidan bata samu kowa a palour ba hakan nema yasa ta shigewa dakin Ammii kai tsaye.

"zaune ta samesu ita da Areef suna kallon wani serious.
" Da mamaki suke kallon ta kafin Ammii tayi karfin halin mata magana

"ke kuma lafiya kika xomana gida da sassafe, ina safeer din yake ta fada taba kallon kofa kamar me neman shi.

" Ya wuce office in ya tashi zai shigo ae ta fada tana wucewa kan gadon Ammii.

"Aunty shukra yaushe ya safeer xe dawo inji Areef.


" Ban Saniba ta fada tana juya masa baya.

"To Aunty ki kirasa ki tambaye sa mn.

" Karka dameni Dalla malam.

" Bekara cewa komai ba illa ma fitan da yayi daga dakin.

" Duk abinda suke Ammii na jinsu sai da Areef ya fita ne ta juyo tana kallon shukra

"shukra anya ko kuna zaman lafiya da yaron nn

" Ammii wace irin magana kikeyi ne wae, waya gaya miki bama zaman lafiya.

"Halinka nasani ae shukra.
" To Ammii ki kirasa mn ki tambayesa.

"Bazan kirasa ba sai dai in bari shawara kan kiji tsoron Allah kada ki tauye wa yaron nn hakkin sa karki ganshi shiru - shiru ki zaluncesa, idan mu bama ganinki Allah na ganin ki.

" Kai Ammii dan Allah wae waya fada miki bama zaman lafiya me ma ya kawo maganar xalunta da wani tauye hakki.

" kedai kika Sani inji Ammii tana ficewa daga dakin.



"shiru shukra tayi tana tunanin mgnr da Ammii ta gaya mata, tanason daukar maganar Ammii amma shedan yana mata huduba.






4:00 pm


" Daddy ne ya shigo cikin gidan daga office shukra yasamu a palour, da mamaki yake binta da kallo.

"Daddy sannu da zuwa ta fada kafin Ta durkusa har kasa ta gaida shi.

" Ba yabo ba fallasa ya answer sannan ya shige dakinsa, Ammii ma ta fito daga kitchen tabi bayan daddy.

4:40 daddy ya fito palour yace Ammii ta kira masa shukra.

"Bayan Ammii sun fito tare da shukra dukansu suka zauna a kasa suna jiran me xance.


"shukra lafiya na ganki a gida kuma.


Ita abinma mamaki ya bata exactly tambayan da Ammii tamata irinta daddy ya mata.
" Lafiya kalau daddy kasan yau ya koma office shine yace bari ya kawoni gida inya dawo xexo mu tafi.


"Ajiyar zuciya daddy ya sauke yace to madallah Allah ya dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login