Showing 36001 words to 39000 words out of 49582 words
Chapter 13 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt
ba IPhone 6s+ ta bude idon ta sosai tanaso ta gasgata abin da idon nata ke fada mata, iPhone din dae ta gani, ta fasa ihun murna, Aysher ta juyo da Sauri tana binta da harara don ita har ga Allah tayi tunanin wani abu ya same ta Amma ta ganta a zaune kuma har a lokacin ihun take "
" Meye hk Dalla malama ina bacci zaki dinga min ihu, inji Aysher ta fadi ranta a bace "
" Aunty Aysher ki tashi Uncle Ahmad abokin ya Safeer ne ya sai mun IPhone 6s+, Miemie tace tana janyo Hannun Aysher zata tayar da ita "
" Da sauri Aysher ta tashi tana zare ido ganin da gaske IPhone din ce a gaban ta, kin nuna wa Mamah ne,? Aysher ta tambayi miemie "
" Nima fa ban saniba kawae dae ya bani polythene ne Dazan tawo so ban bude ba sai ynx nake gani Miemie ta bata Answer sanda take saukowa akan bed ta fice ta shiga dakin Mamah, Abbah zaune a gefen bed yana duba wasu papers yayinda Mamah take kwance akan bed din da Alama ta fara bacci"
"Ihun Miemie ne ya sa suka dago dukansu da sauri suna kallon ta, ta karaso cikin dakin da gudun ta tana mikawa Abbah Wayar hannunta "
" Abbah kagani Uncle Ahmad ne ya bani ita "
" Murmushi Abban yayi sanda ya karbi wayar yana kallonta kafin ya dago yace
"Miemie ae wannan wayar ta miki girma kinsan ma fa ni banason rike waya da wuri saboda batawa yaro brain yake, haka kuma yana bata tarbiyya"
"Wallahi kam, ae kawae karike mata wannan sai tayi graduation (Candy) sai ka bata, in wayar take so sai ka siya mata baby nokia ta dinga communicating da friends nata, Mamah dake kwance har a lokacin ta fada ba tare da ta dago kanta ta kalli Miemie ba "
" Miemie ta bata rai kamar zatayi kuka tana kallon Abbah daya maida kansa jikin papers dinsa yana cigaba da dubawa, Abbah Please karka ji Mamah ka bani wayana kaji "
" Ae kinji me na fada miki bazan bayar ba, zan siya miki karama wannan sai kin gama skul zan baki Abbah yace sanda ya mike ya shige toilet "
" Kuka kawae Miemie tasa ta juya ta shiga dakinsu inda ta tarar Har Aysher tayi bacci, nan ta kwanta tana kuka a hk har bacci ya dauke ta "
" To Rayuwa ta cigaba da tafiya, ynx Aysher ta kai level three (3)a B. U. K inda take karantar nursing, so ynx haka madai anyi posting su Aysher hospitals daban daban don yin practicals inda Aka kai aysher Malam Aminu kano teaching hospital, so Aysher bata wani shan wahala kasancewar ta mai kokarin gaske, sosai Doctors din keji da ita kasan dae itace over roller, "
" Aysher da kawayenta Maryam da Nuriyya tsaye a var render 'n S. O P. D da wani handout a hannunsu suna duba wa, gabaki daya hankalin su nakan abinda suke, Sallamar da sukaji anyi musu ne yasasu Saurin juyo wa suna kallonsa "
" Black jeans ne ajikinsa da white t~shirt yayinda ya dora white lab ~coat akai yayi un buttoning lab coat din, kafarsa sanye da wani black shoe hannunsa daure da white watch, Answer sallamar sukayi cikeda ladabi don shine doctor'n da aka hada su da yanada sakin fuska sosai shiyasa suka saba dashi sosai "
" Cikeda fara a ya answer gaisuwan su sannan ya kalli Aysher wadda gaba daya hankalin ta nakan handout, Aysher in kin gama ki sameni a office yace kafin ya juya ya koma office dinsa "
" Mikawa Nuriyya handout din tayi sannan tabi bayansa, Be dade da zuwa office dinba ta shiga itama, kara gaisawa sukayi kafin kuma sukayi shiru tsawon minti goma, zuwa can yace
"Aysher wata magana zamuyi dake to amma kuma naga kamar Karatu kike so kibani number ki inyaso sai muyi magana a waya ko zuwa anjima ne"
"Badan Aysher taso ba sai dan kawae ganin girman sa da take ne yasa ta karbi wayansa da yake miko mata ta sa masa number ta ta mika masa, Hannu ya miko mata alamar ta basa wayarta aiko ba musu ta miko masa nan dae yayi mata saving number sa as Mahmoud sannan ya bata, ta masa sallama ta fice "
" Bayan kamar kwana 2 da faruwar Hakan Mahmoud ya kira Aysher suka gaisa, Aysher batayi wani mamakin jin cewa Mahmoud yana sonta ba don dama ta dade da ganin alama, Mahmoud dae be kyale Aysher ba har sai da ya tabbatar ya samu shiga "
*San Francisco*
" Shukrah da Azeeza zaune a parlour suna hirar haihuwar Shukrah don yanzu cikin nata nada wata takwas kenan, inda Azeeza ke cewa ita tafi son a haifi Namiji ita kuma Shukrah wae tafi son Mace suna cikin wannan musun ne Ahmad da Safeer suka shigo da kaya masu uban yawa daga gani dae daga kasuwa suke, Azeeza ta mike ta karbi kayan ta shige dasu wani dan karamin daki inda anan ne suka ware don tara kayan Baby, Shukrah dae daga zaunen da take ta musu welcome don baxata iya tashiba saboda swelling da legs nata sukayi, Safeer ne ya karaso inda take ya durkusa gaban ta ya fara massaging mata legs din har sai da ya tabbatar swelling din ya ragu sosai sannan ya taimaka mata ta mike suka shige dakinsu, a tare sukayi wanka bayan sun shirya suka dawo parlour inda Safeer da Ahmad suka fice Azeeza kuma ta shige kitchen "
" White spaghetti ta musu bayan ta gama ta daura soup kan gas, bata wani dau lokaci ba ta gama ta dauko flask set din ta jera a dining sannan ta dawo parlour tayi joining Shukrah suka cigaba da hirar su har lokacin magrib yayi suka tashi sukayi "
" Ba *Ahmad* da *Safeer* suka dawo ba sai ba'adi salatul Isha, abinci sukaci a tare suka danyi kallo sannan sukayi wa junansu sallama Suka shige dakinsu, *Shukrah* ce kawae ta sake wanka don cikin nn yana sa mata jin zafi sosai,Sanda ta fito har Safeer yayi bacci saboda haka itama ta kwanta gefen shi sai bacci "
" To rayuwa tanata tafiya don ynx cikin *Shukrah* ya shiga watan haihuwa saboda haka *safeer* da *Ahmad* sukayi handling company 'n su gurin wani yaron Ahmad *Ammar* don Ammar yanada Amana da hankali sosai, zaman gida kawae su *Safeer* suke, Da zarar *Shukrah* tayi wani motsi na nuna alamar jin ciwo zasuyo kanta suna jero mata sannu "
" To ana cikin haka har E D D' n Shukrah ya cika, tun safe Azeeza ta shirya musu trolley, Shukrah dae ta dage bazata hospital ba wae ita batajin ciwo saboda hk a gida zata haihu "
" Haka suka yini lafiya cikin gidan, sai zuwa yamma sannan Mara da bayan Shukrah suka fara mata ciwo nan fa hankalin kowa ya tashi ba kamar Safeer da hankalin ya gama tashi, wani karfi yaji yazo mishi bemasan sanda ya daga Shukrah ba sai mota, nan Ahmad ya biyo shi, nan Azeeza ma ta fito da trolley sai hospital.........
SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE 💕
[5/8, 1:47 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA* 👮🏻
WRITTEN BY
*ZAINAB* *YAKASAI*
*SHUKRAH*
DEDICATED TO *MIEMIEBEE*
3⃣5⃣
"Sun isa asibitin cikin sa a aka karbi *Shukrah* aka wuce labour room da ita, Shukrah tafi karfin awa daya acikin labour room amma ta kasa haihuwa hakan ne ya bawa likitocin damar bata inducing drug tasha amma ta kasa haihuwar, Anan kuma suka fara tunanin yimata C. S ".
" *Safeer* ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kewaye yake ya rasa inda zaisa kansa, duk da Air condition din dake gurin amma gumi sai zuba yake a jikinsa kafafunsa sai rawa suke jiyake kamar ya cire ciwon ya dawo kansa, *Azeeza* da *Ahmad* sai kokarin bashi baki suke amma sam yaki jinsu, ya zauna ma yaki zama *Shukrah* kam sai ihun ta take tana kiran *Ammii, Mamah, Aysher, Miemie kai har meela ma sai da Shukrah ta kira, yana cikin wannan halin daya daga cikin Doctors din da suka karbi *Shukrah* ya fito Sukayi Saurin mikewa suka nufeshi, *Safeer* bakinsa sai rawa yake ya kasa ma yimasa magana, doctor ne ya dafa kafadar *Safeer* yana bashi baki kafin ya miki masa wani paper wa yayi signing ayiwa *Shukrah* C. S "
" Duk jarumta irin ta *Safeer* besan sanda ya fashe da kuka ba, da kyar ya karbi pen a hannun Doctor din ya dora kan paper, maganar da Wata Nurse ta fito tana yiwa doctor be kan yazo *Shukrah* ta haihu ta samu baby Boy ne yasa *Safeer* wulli da pen & paper hannunsa ya bi bayan Doctor cikin dakin, nan *Azeeza* da *Ahmad* ma suka rufa musu baya sai dakin, Sanda suka shiga dakin har Nurse ta dauki Babyn ta fice dashi"
" *safeer* ya kara da gudu da niyyar rungume *Shukrah* Amma sai yayi Saurin dakatar da kansa don ganin tayi wani mugun nushin sai ga baby Girl ta fito, Zaro ido sukayi cike da mamaki da kuma farin ciki, *Safeer* ya rungume *Shukrah* tsam a jikinsa yasa kukan farinciki, besan da bakin da zeyiwa *Shukrah* godiya ba don ta bashi farin cikin sa Twins, *Shukrah* tayi karfin hali tasa hannunta tana goge wa *safeer* hawayen idonsa, Don tafi kowa sanin irin son da *safeer* yakewa yara, Doctor ne yayi gyaran murya *Safeer* yayi Saurin daga *Shukrah* yana goge hawayen daya gangaro masa "
" Nan dae Nurses su 2 suka shigo da babies *Safeer* yayi Saurin karasawa ya karbi Baby girl din shikuma *Ahmad* ya karbi boy din, anan kuma Nurse ta shiga da *Shukrah* toilet don ta gyara jikinta "
" Nan safeer ya shiga snapping babies yayi marking duk contact nasa na WhatsApp yayi musu sending, nan fa aka fara kiransa ana masa murna, Aysher ma ta kirasa sanda yace takai wa *Mamah* wayar kin karba tayi, tadai ce Allah ya raya *Twins* "
" washe gari akayi discharging nasu, Abokan aikin su *Ahmad* sai zuwa suke, kayan Babies kuwa kamar zasuyi magana don yawa, sai zuwa dare sannan *safeer* ya samu damar kebewa da *Shukrah* ya zuba mata ido tana rike da Baby girl dinta, tsawon minti Arba 'in suna hk, Har sai da *Shukrah* ta gaji da da kallon nasa tayi magana"
"Your look is so intense, it makes me nervous, what do you want? *Shukrah* ta tambayi *Safeer* sanda ta dauke kanta "
" *safeer* ma dauke kansa yayi sannan yace ALL what i want is your love, can you do me a favour and give me that much? I promise to live with you for ever, Indeed you are a blessing, kinbani farin ciki a rayuwa ta, i have never expected dis, being a Daddy of twins at this very tym"
"Why not? I will give you my luv for the joy you brought into my life, for understanding my needs, for allowing me to be part of you at the same time for turning back to the face of all my mistakes *Shukrah* tace harda dan hawayenta "
" Rungume *Shukrah* , *safeer* yayi itada Babies dinsu ya musu selfie.......
SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[5/11, 9:17 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA*
👮🏻
*WRITTEN* *BY* *ZAINAB* *YAKASAI*
*SHUKRAH*
Dedicated to *MIEMIEBEE*
3⃣6⃣
" *SAFEER* ya kurawa twins dinsa ido fuskarsa dauke da murmushi, yanaji a ransa yanzu bashida wata matsala tunda Allah ya masa babbar kyauta wadda ba kowa yake waba, a fili yace 'Alhamdulillahi'
" *SHUKRAH* ta juyo ta kalleshi ya mata murmushi yace
'Baki tambayeni wani suna nayi wa yara khudubah (Huduba) dashi ba'
" tayi murmushi sannan tace abinda nake taso in tambaya kenan wallahi, wani suna aka sa musu?
"Murmushi Ya fadada sannan ya dauki Baby boy dinsa ya rungume yace
'Saboda karamci, da mutunci, da Alfarma da kuma babbar kyauta da *ALHAJI* *SARAKEE* Yamin yasa nayiwa dana huduba da suna *AMEENULLAH* Alkunyar sa kuma shine *LABEEB* Inaso a ringa kiransa haka don suna ne me kyau sosai, Ya ajiye shi gefe sannan ya dauki Baby girl din, itadai *SHUKRAH* sakin baki tayi bawae batayi sammanin haka ba, a a kawae dae abin yazo mata a *BAZATA* ne, Ta zame daga kan bed din ta durkusa akan kafafunta zatayi magana *SAFEER* Shima ya zame yayi Saurin sa hannunsa daya ya rufe mata baki sannan yace, ita kuma nasa mata sunan Mamana wato Khadeeja za a dinga kiranta da suna *LABEEBA* "
" Hawayen farin ciki ne yazubo mata tayi Saurin goge wa tana murmushi tana kara jin son *SAFEER* Na ratsa jinin jikinta don ya mata komai a rayuwa yayi wa *DADDY* ' *NTA*Takwara, tasa hannu ta zame nasa hannun sannan tace
' Hakika banida bakin yimaka godiya don kayiwa mahaifi na abinda ba a taba yimasa, yayi Saurin dakatar da ita ta hanyar cewa
'Nima Yamin abinda ba a taba min ba a rayuwa ta inajinsa kamar *ABBANA* , banajin a kawae abinda zan masa nabiya sa abinda yamin saboda hk karki ce zaki min godiya kinji "
" Wayarsa ce ta fara ringing yayi Saurin mikewa ya dauko akan bed *MAMAH* Yagani ajikin screen din yayi Saurin dagawa yamata sallama "
" Idan kai bazaka dawo ba to ka kawo min *SHUKRAH* kaji ko bakaji ba tace rai a bace "
" Dakyar ya iya bude baki yace *MAMAH* naji kuma insha Allah cikin satin nan zamu dawo "
" Gobe nake so ku dawo na fada maka... Tana gama fadar haka ta kashe wayarta "
" *SAFEER* YA juyo ya kalleta yace *MAMAH* Tace gobe take so mukoma so ynx zan fita nayi mana Booking flight, Da sauri *SHUKRAH* tace to don itama zaman garin ya isheta musamman ma ynx data haihu tana bukatar ganinta kusada *AMMI*' *NTA*
, tare suka fito *AZEEZA* Kadai ce a a parlour don *AHMAD* Bayanan, *SHUKRAH* ta mika mata babyn hannunta sannan ta karbi na hannun *SAFEER* , "
" shiko yana fita ya nemi commercial car yace driver ya kaishi ' *AL* *HARAMAIN* *TRAVEL* *AND* *TOURS* *LIMITED* , be dauki wani lokaciba ya gama komai, sai da ya shiga wani shopping complex yayi shopping sosai sannan ya wuce gidan, Sanda ya isa ana kiraye~kirayen sallar magrib nan yayi alwalla suka fice mosque tare da *AHMAD*, sai da su kayi sallah isha sannan suka kamo hanyar gida, a hanyar dawowar sune *SAFEER* Yakewa *AHMAD* Bayanin tafiyar su gobe, sosai *AHMAD* Yanuna rashin jin dadin tafiyar su koba komai sun saba, kuma yana jin tausayin *Azeeza* sosai don tasa *LABEEB*& *LABEEBA* Sosai azuciyarta, besan yadda zasuyi goben ba, Saurin goge Hawayen dasuka taru a idon sa yayi dai dai sanda suke shigowa parlourn gidan, a tare *Ahmad* & *Safeer* sukaci abinci don tuni su *SHUKRAH* sukaci nasu "
" Sanda suka gama cin abincin sukayi sallama, lokacin da *Safeer* yashiga dakin tararwa yayi *SHUKRAH* na hada musu trolley yakarasa kan bed ya dauko *LABEEBA* Yamata kiss a kanta yace Babyna ki tashi ga *PAPA* YA dawo, Baby kice you are welcome *Papa*"
" *SHUKRAH*tasa dariya tace kai *ya* *safeer* karfa son baby yamaka illa, yarinyar da kwanan ta 3 kawae a duniya kake expecting tayi welcoming naka "
" Hade rai *safeer* yayi yana hararar ta toke ina ruwan ki, Ni banason irin hk ehe, Dariyar ta cigaba da yi har sai da ta k'ularda Safeer yaja tsaki sannan ya kwantarda *Labeeba* ya musu addu a sannan ya kwanta"
"Sanda *SHUKRAH* ta gama hada trolley toilet ta shige tayi wanka, koda ta fito kitchen ta wuce tahada tea tasha sannan ta dawo dakin tasaka wata doguwar sleeping dress ta kwanta a bayan *Safeer* "
" Ya Safeer kayi hakuri dani naga kamar kayi fushi, Shiru yayi mata alhalin yana jinta, nan ta cigaba da masa magiya amma yaki kulawa, zuwa can dabara ta fado mata tasa harshen ta a fuskarsa tafara yawo dashi, nan *safeer* ya juyo ya rungume ta....
*washe* *gari*
"Dukansu a airport, *Azeeza* rungume da *labeeba* tanata kuka kamar shi aka aikota, ita tunaninta daya yadda zatayi rayuwa bau tare da Shukrah ba gakuma twins da tasa su a zuciyarta,j *Ahmad* ganin kukan *Azeeza* bame karewabane yasashi mata alkawarin kaita Nigeria before or after naming ceremony, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka koma gida
~~~~~~~~~~~~~~~
*HAIYDAR* zaune gaban Hajiyarsa da alama fada take masa
"Haiydar wai kai yaushe zaka nutsu kayi Aure ne, akan idonka Safeer yayi Aure gashi har matar ta haihu amma kai kaki kafitarda matar ko"
"Ba hk bane Hajiya yarinyar da nakeso yanzu tayi junior waec dinta, so jira nake tayi grads sai a fara maganar auren "
" Kana hauka ne Haiydar, nace hauka kake Haiydar, ajinka zan cigaba da zama da kai har nanda shekara 3 to inma bacci kake ka farka, Nabaka two weeks kakawo min mata ko in zabo maka da kaina hajiya ta fada rai bace daga hk tafice ta barshi yana tunanin wae shi za a samowa mata yarasa me zai kira wannan auren da Hajiya take shirin yimasa (Niko nace *AUREN* *BAZATA* Xatayi maka), Ringing din dawayarsa yake ne yasa shi daukan car key dinsa ya fice daga gidan, tafiyar minti talatin ce ta kai shi Airport, nan ya kwashe su sai gidan Mamah, A hanya ne yake fadawa Safeer Hajiya zatamai AUREN BAZATA, me Safeer zeyi inba dariya ba. . . Dakyar ya tsayar da dariyar sa yace karka damu Haiydar *AUREN* *BAZATA* *ALHERI* *NE*. . .
*SHUKRAH* *YAR* *GATAN* *MIEMIEBEE*💞
[5/12, 1:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN* *BAZATA*👮🏻
WRITTEN BY
*ZAINAB* *YAKASAI*