Showing 45001 words to 48000 words out of 49582 words

Chapter 16 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt

labeeba, sunacin abinci suna basu haka kuma suna dan taba hirar su, cikin hirar ne Safeer yake fadawa Shukrah iyayen DR. MAHMOUD Sun kawo kudin auren Aysher kuma ansa ranar biki nanda wata goma "


" To Allah ya sanya alheri ya kuma sa ayi damu Shukrah tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi "



" Ameen ameen likitan ido me bawa mutane glasses, nima idona namin ciwo har bana iya gani sosai yaushe zaki min glass Safeer Yace yana dariya sosai"




"Dariya itama Shukrah tayi tace duk sanda ka shirya ka sameni a office zanmaka daga hk tadau plate din da suka ci abinci tawuce kitchen don wankewa........







*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💘
[5/24, 10:20 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected marriage*)


*Written by*
*Zainab Yakasai*
*Shukrah*




*Dedicated to Miemie bie*



4⃣2⃣


"sosai shukrah take jin dadin aikin ta don batada wata matsala da mijinta tunda yana so, HK batada matsala da *Maryam Anas* don ba laifi shukrah ta iya aikin ta kuma batada kyashi"


"kasan cewar mutane masu matsalar ido basuda yawa yasa SHUKRA kullum take tashi a office da wuri hakan yayiwa kowa dadi musamman ma Safeer a cewar sa gwara Shukrah tayi tarbiyyar yaranta da kanta, bawae don bae yarda da da tarbiyyar su Mamah bane a a shudae kawae yafi ganewa hakan ne"



°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*Bayan wata takwas*


Abubuwa da yawa sun faru a rayuwar ma'auratan nn guda biyu,twins sun girma sunyi wayo sosai don yanzu har suna iya tafiya,magana ma suna tilastawa Kansu suna dan gwadawa"


"Yau ta kama Saturday kuma kamar yadda suka saba basa fita week ends saboda haka yau duk suna gida, Safeer na kan one sitter ya daura Labeeba kan jikinshi yana mata wasa yayinda labeeb ke wasan sa daga kasa kusada Shukrah ,ita kuwa Shukrah tana zaune ta maida hankalinta kan wani littafi da take karantawa"


"Safeer ya kalli Shukrah sannan ya kalli labeeb yace 'Sweetheart ' kirawo min Shukrah"


"Labeeb ya dago Kansa ya kalli Daddy'nsa sannan ya kalli Shukrah wadda batama San me sukeyi ba ya Kara kallon Safeer,Safeer ya daga
Masa kai,sannan ya Mike yana tafiyarsa irin ta 'yan koyo yazo gaban SHUKRA ya riko hannunta yana Mata murmushi yace"

"Chuklah Jo Daddy". Yana nuna mata Safeer Wanda ya dage sai Dariya yake mata, ta turo baki gava ta bata fuska wane zatayi kuka ta kalleshi"

" Ynx sabida Allah other half Shukrah zaka koya was yaran nn fada ko,? Dariyar ya tsagaita sannan yace yi hkr yan matana ni bance yacemiki Shukrah ba shi ya fada"

"Murmushi kawae Shukrah tayi ta mayar da hankalinta kan book din hannunta don tasan in ta biye masa haushi da takaici zaita tura mata"


"shirye shiryen bikin Aysher ya kankama tunda next month za ayi bikin hakan nema yasa Mamah da Hajiyar Haidar suka shirya tsab suka tafi Cairo donyin siyayyar bikin ,sati biyu kawae sukayi a can suka dawo inda aka shiga cikin bikin gadan gadan"


"Mutanen Mamah duk sun halarchi bikin kuma sunyi bajinta ba kadan ba, ciki kuwa harda *Aunty Maryam Ana's* ,sosai Mamah keji da ita don a duniya batada kamarta duk da kasan cewarta kawace a gurinta amma tamata abinda yan uwanta da yawa basuyi mata ba,hakan ne yasa ta Kara mata matsayi sosai kuma take alfahari da ita"


Sunday 23 December 2016 aka daura AUREN *Mahmoud Mustapha da Aysher Muhammad mai lafiya* Kan sadaki naira dubu hamsin, musalin sha biyu na rana, sosai Auren ya samu albarkar manya manyan mutanen da suka halarta"


"Karfe takwas da rabi na dare aka kai amarya dakin ta"



"Rayuwar Safeer da Shukrah rayuwa CE da aka gina ta cikeda so da kauna,yarda ,amana, karamci dakuma mutunta juna, sosai suke son junansu sika kuma yarda da Kansu"

"Shukrah a kitchen tana wanke wanke yayinda labeeb da labeeba suke tayata da barna, Safeer ne ya shigo cikin kitchen din yana Yar wakar sa da alama dae yana cikin nishadi,karasowa yayi kusada Shukrah ya nannade hannun rigarsa ya sunkuya yana tayata daurayewa"


"Other half yaushe za ayiwa twins kani ne sunyi girma fa yace yana kallon ta cikin ido"


"Dau ke idonta tayi daga kallonsa tana murmushi kasa kasa sannan tace 'ynx idan nacema inada ciki ae saika rufeni da duka yara wata goma sha biyu amma ace za a musu k'ani"


"Ware idanunsa yayi sosai a kansa don ta bashi mamaki sosai be taba tunanin zatace HK ba shi a ganin sa Shukrah tanada hankalin da ko ciki ta samu bayan ta haihu da wata biyar bazata yi korafi ba, amma sai yaji Sabanin hk, shiyasa ma yace' Haba Shukrah da girman ki da hankalinki zakice HK,"


"Dariya tayi don taga kamar abinda tace ya bata ransa tace' yi hkr Ya Safeer ni ko ynx ma a shirye nake kazo kamin ciki shknn"

"Haka kikace Shukrah?

"Haka nace, meye to ae mu munci dubu sai ceto ya safeer Shukrah tace tana dariya sosai,daga nn ta kwashe plates din da cups duk ta jerasu a muhallin su sannan ta dawo ta wanke sink din"


"Shammatar ta Safeer yayi ya dagata cak ya nufi bedroom da ita yana cewa bakince kinci dubu sai ceto ba,kuma a shirye kike nayi miki ciki ko,ae ko ynx zan baki triplets
Ma, kan gado ya ajiyeta, itadae Shukrah batada bakin magana tunda ita ta janyo wa kanta,shafa ta ya fara yi tunda kanta har zuwa kirjinta duk ya wani susuce dan dan kwana biyun da beyi ba, haka dae yayita romancing dinta har ya cimma burinsa ae nan ya Kara susucewa donji yayi Shukrah ta zamar masa sabuwa fill don Shukrah bata wasa da gyara sam nan ya fara Mata surutai ,Shukrah na baki gidana na zoo road, na baki duk wani dukiya Dana mallaka na baki kaina Shukrah na baki raina gaba daya gani kiyi yanda kikeso dani Shukrah ki juya ni yadda kike so kinji......

"Da yamma bayan sunyi wanka suna zaune suna hira Shukrah ta kalleshi ta kyalkyale da dariya ,ya hade rai yana hararar ta don yasan mugunta ta shirya masa, a kufule yace' meya faru kuma'


"Dariya Shukrah ta cigaba dayi harda rike ciki tana kallonsa HK kuma tana nunasa da daya hannunta ,haushine ya cika shi ya mike yazo kusa da ita, Kafin tace zata tashi ta gudu harya riketa ya matseta sosai har saida tayi Yar Kara ,yace fadamin me yasaki dariya kafin in bata miki rai"

"Sai da takara darawa sannan tace""Shukrah na baki dukiya ta ,nabaki gidana na baki kaina kiyi yadda kikeso dani ta karashe tana sake yin dariyar sosai"

"Sake matseta yayi ya hade rai don ya gano abinda take nufi yace to waye ya fadi hakan?


"Dariya ta kuma yi sannan tace waye to inba Ya Safeer ba"

."Murmushi ya kuma yi sannan yace nidae sharri kika min amma zan hkunta ki da daddare,"



Bayan kamar sati uku Shukrah ta Fara ganin canji a jikin ta don ynx wata kasala CE ke addabar ta ga yawan zazzabi da ciwon kai ga kuma wani saurin bacci da take data dan jingina sai bacci wani lokacin ma ko girki take data dan zauna sai bacci,"



"Shukrah CE a kitchen tana dafawa twins indomie don basa son cin abinci sosai, da zarar sun faracin wani abun da sunci sau uku zuwa hudu zasu dena ci, ga kuma rigima dasuke damunta dashi Sam basa barinta ta huta in bacci ma take haka zasuje su hau kanta suna tsalle suna'chuklah ci taci cijo Daddy ,wani lokacin sai ta hada da duka suke nutsuwa su kyaleta shiyasa ma ta yanke shawarar yaye su tunda sunyi wayo sosai"


"Tana zuba indomie din ta dawo ta kwanta a kasa Dan danan kuwa bacci ya kwashe ta zuwa can indomie ta fara kamawa ,Safeer dake bacci a parlour yaji kauri na Neman halaka shi ga twins sai tari suke suna kuka, da sauri ya karaso kitchen din kai tsaye gurin gas ya nufa ya kashe sannan ya dawo gun twins ya daga su yana jijjiga su,duk wannan abinda ake Shukrah bata sani ba, Haushi ne yasa Safeer fara bubbuga Shukrah yace meye HK wae yake damunki Shukrah ko ina kika samu sai bacci kin barmin girki yana konewa yarana sai tari sukeyi amma ke sai baccin ki kike hankali kwance ,kije kiga doctor mana in cuta kike ya baki magani"


"Taikaici ne ya rufe Shukrah don tasan ko a mafarki bazata iya mayar masa da magana ba shiyasa ma ta mike ta dau wayarta ta koma parlour tayi kwanciyar ta sai bacci, sanda Safeer ya futo yaga har ta koma bacci tsaki kawae yaja ya rike hannun yaransa suka bar Gidan...........





*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIEBIE*💞
[5/26, 1:14 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected Marriage*)




*Written By*
*Zainab Yakasai*
*SHUKRA*






*Dedicated to MIEMIEBEE*





4⃣3⃣


"misalin sha biyu da rabi *Shukrah* ta gama attending patients NATA,tana zaune shiru kasan cewar bazata tafi gidaba sai 2:00pm bacci ta fara ji tun tana kokarin hana kanta yi har ta saduda ta kifa kanta a jikin desk dan danan ko ta fara baccin"


*Aunty Maryam Ana's* taji shukrah shuru don ta saba in dae ta gama attending patients gurin ta take zuwa suyi hira,hakan ne yasata mikewa da niyyar dubo Shukrah, sai da ta fara duba Dr.Nuriyya taga tana nn sannan ta wuce office din Shukrah"


"Da sallamar ta ta karasa office din amma ga mamakin ta sai taji shiru, tura kofar tayi ta shiga taga Shukrah kwance tanata bacci abinta, ta karasa jikin desk din tana bugawa, kamar daga sama shukrah taji bugun ta dago da sauri don ta tsorata sosai,Ganin Aunty *Maryam Ana's* yasata turo dan bakinta tana shirin yin kuka"

"Sleeping on duty ko? Good ki sameni a office, zaki answer query Aunty Maryam Ana's tace tana dariya sannan tayi gaba, Dariyar itama Shukrah tayi sannan ta dau handkerchief ta goge fuskar ta ta fita ta rufe office din ta wuce office din Doctor Maryam, a zaune ta sameta tana duba wani file ta karaso ta zauna a side chair din office din tana kallonta"



"Lazy Doctor daga duba patients basufi 30 ba amma har kin fara bacci ko,meye matsalar kine wae kwana biyun nn ?Inji Dr.Maryam Ana's"


"Murnushi Shukrah tayi ta kauda kai don tana gudun abinda zai je ya dawo, kamar bazatayi magana ba sai can tace' Nima Aunty bansan meke damuna ba gaba daya banajin dadi, yawan bacci, jiri wani lokacin ma har da zazzabi nake ta fama dasu a yan kwanakin nn"ta fada cikeda damuwa


"Kin harbo jirgi Shukrah, Allah ya raba lafiya da kaina zan miki test don INA son sanin watansa nawa Dr.Maryam tace sanda ta taso ta dawo kusa da Shukrah"


" Result na Test din da akayiwa Shukrah ya nuna tanada ciki har na tsawon wata biyu da kwana uku, Dr.Maryam Ana's ta kalli Shukrah da fara'Arta tace sannu Shukrah Allah yasa twins ne ko nasamu amin takwara, Shukrah ta bata fuska kamar zatayi kuka'Aunty nifa banason cikin nn watan twins fa Tara, yazanyi dasu fisabilillahi"


"Murmushi Dr Maryam tayi tana kallon Shukrah, tace koda wasa karna kara jin kince bakyason k'aruwa Shukrah,ko kinsan wani son haihuwa yake kamar zaiyi hauka amma Allah bai bashi ba,ita haihuwa babbar kyauta ce bakowa Allah ke bawa ba amma ke kinsamu kice bakya so Shukrah, Allah da kansa yace yanajin kunyar idon duk Wanda bai azurta da haihuwa ba, haba Shukrah ina hankalinki ya tafi? Yaranki sunyi girman da ko yanzu zaki iya yaye su, me kike tunani Shukrah"



"Hakikanin gaskiya maganar Aunty Maryam ta shiga Shukrah, kuma itama ta sani amma ta share tayi rau -rau da ido kamar zatayi kuka tace insha Allah koda wasa bazan kuma fadar hakan ba kuma Alhamdulillahi Allah yana sona shiyasa ya bani haihuwa Allah ka bani ikon tarbiyyantar dasu kan hanya madai~daiciya"


"Ameen Yar gata na cewar Dr.Maryam sanda take hada kayanta, atare suka fito da Shukrah Inda take rokon Shukrah tazo da twins gidanta ran Saturday, Shukrah kuma ta tabbatar mata zasuzo harda Safeer ma ,nan sukayi sallama kowa ta shiga motar ta suka fice *MARYAM CLINIC*"



" yau ta kama saturday kuma Kamar yadda Shukrah tayiwa Dr.Maryam Alkawarin kawo mata ziyara ran Saturday haka suka shirya tsaf gurin 12:00 bayan Shukrah ta gama duk ayyukan ta suka kama hanyar Gidan Doctor Maryam Ana's, cikin mota Labeeb ya tabo Shukrah yace 'Chuklah jidan Aunty mayyam jamu ae ko' ,Shukrah ta doke bakinsa tace wace'''Shukrah'''? ,ae kamar jira yake ya fasa ihu harda fadowa daga kan sit ya buga kansa kuwa a jikin driver sit ya dinga birgima wane Shukrah Zane mishi jikinsa tayi,Safeer yayi saurin gangarawa gefen titi yayi parking ya juyo yanawa Shukrah mugun kallo sannan yace'Wae Shukrah sau nawa zan hanaki dukarmin yara,ko saboda ban isaba ne yasa bazaki jiba, meyayi miki ma da har ya cancanci duka daga gareki, sai kace bake kika haife suba komai duka, me zakiji ajikin yaron nn in kin dakeshi"


"Labeeb ko tunda Daddy'nsa ya Fara magana yayi shuru kamar yasan me yake cewa sai ya kalli Shukrah ya juyo ya kalli Safeer,...Shukrah bata iya mayarwa da safeer magana koda kuwa rashin mayar da maganar zai zamo mata matsala, amma tanajin tausayin Safeer bataso son da yake yiwa yaransa yasa shi rufe idanunsa ya kuma toshe kunnensa haka kuma ya juyawa gaskiya baya shiyasa ma yau ta daure tace

"Haba ya Safeer Dan Allah me yasa wae kai kullum in yaran nn sukayi laifi saika rufe idonka ka nuna kai bakason ayi musu hukunci,bayan ice tun yana danye ake tan kwara shi.. Kuma naga ae ba wani Abu nayi masa bige masa baki kawae nayi sabida ya kirani da sunana ko saboda Ina son su sai ya barsu suyi yadda suke so ?karka manta fa yaranmu amana ce Allah ya bamu kuma zai tambayemu, me zamu ceda Allah in ya kasance mun koma gareshi ba tare da mun sasu akan hanya madai daiciya ba,nasan kafini sani kuma ba fada maka nayiba dan baka sani a a na tuna tarda mune, Amma dan Allah in na bata maka rai ka yafe min ban Dada da niyyar bata ran kaba kaji.. Tana kaiwa nan ta Kifa kanta jikin window wasu zafafan hawaye suka fito Mata a kokaci days kuma tana da tasanin saukin bakin da tayi ita a rayuwar ta batason wani ma ya bata ran safeer bare ma ita da kanta ta bata"



"Shiru Safeer yayi yana nazarain maganar ta ya tabbatar da cewa gaskiya ta fada, take yaji ya kara mata matsayi ya kuma Dada tabbatar wa yayi dacen mace ta gari kuma yaransa sun yi dacen nahaifiya ta gari.. Sonta yaji yana ratsa duk wata gaba ta jikin sa,ya juyo yana kallon ta har a lokacin bata dago ba yace cikin zuciyar sa'Ya Allah ga salihar baiwarka nan kayi mata gafara ka buda mata ka kuma kareta daga sharrin duk wani mai sharri, Karasowar da sukayi Gidan Doctor Mariam Ana's yasa Shukrah dagowa suka hada ido da Safeer suka sakarwa juna murmushi ,Safeer ya fito ya bude mata kofar motar ta fito bayan ta dauko labeeb daga kasa nan inda ya gama rigimarsa yayi bacci"

"Safeer ya rike Mata hannunta yace Other half bacci?

"Murmushi tayi tace wallahi nima bansan inayiba saida motar nn ta tsaya sannan na farka, Murmushin shima yai sannan suka shigo parlour"

"Da murnar ta tafito ta taresu tana musu ya hanya bayan sun zauna ne kuma ta tashi ta fara kawo musu drinks, hira sosai sukeyi Dr.Maryam sai yaba halayen SHUKRA take Safeer yana tayata, yinin ranar a Gidan sukayi harda Safeer Wanda sallah ce kadai ke fitar dashi a Gidan, don dama can shi jinin su yafi a haduwa Dana Dr.Maryam duk cikin kawayen Mamah tanaji dashi kamar danta"


"Sai bayan sallar isha suka bar Gidan,Labeeb
Dan rigima wae anan zai kwana suna tafiya ko barin layin basuyiba ya dasa kuka wae Sai ta kaishi Chuklah,ae kuwa ba shiri ta Kira su suka juyo sukadau Dan rigimar su suka wuce gida"



*Bayan wata takwas*


"Cikin *SHUKRAH*ya girma sosai kusan ma yafi na twins girma abinda ya tashi hankalin Shukrah Knn musamman ma in ta tuna kalar wahalar da tasha da haihuwar twins har kuka take duk ta Hana kanta sukuni gani take kamar zata mutu sai ta zauna tayi shiru tana tunani don yanzu ta dena zuwa aiki tunda cikin ta yakai wata takwas"


"Yau ta kama Saturday amma Shukrah ce kadai a gida sai Labeeba dake kwance jikin Shukrah shi Safeer yaje Gidan Haiydar shida Labeeb sun tafi kai Zafeera asibita zata haihu, Kasan cewar Zafeera mai juriya yasa ba a wani sha fama da ita ba ta haihu cikin kankanin lokaci, ta haifi da namiji murnaa a gurin Haydar da Safeer kamar me dan danan suka kira Hajiya a waya suka sanar da ita ,nan itama ta Fara kiran yan uwa a waya cikin kankanin lokaci asibiti ya cika da jama'a ,a ranar da yamma kuma aka yi discharging dinta tunda lafiyarsu kalau "


"Washe gari a can Shukrah ta yini yan uwa sai zuwa Duke,ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Zafeera wato Abdullahi za a dinga kiransa da little "



Bayan wata biyu ranar wata Friday Shukrah ta tashi da matsanan cin ciwon Mara har bata iya motsi ko kuka ta kasayi sai hawayene kawae yake zuba a idanunta ,ga wayarta tana gani takasa dauka ta Kira Safeer kasancewar bayanan yanacan wajen Gina company dinsa tun safe



*Shukrah Yar gatan Miemie bie💞
[5/26, 7:37 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected marriage*)





*Written by*
*Zainab Yakasai*
*Shukrah*



*DEDICATED TO MIEMIEBIE*


4⃣4⃣



DaKyar cikin sa'a Shukrah ta mika hannu ta dauko wayarta number Safeer tayi dialing, Safeer dake tsaye yaji vibration cikin aljihun sa yayi saurin dauko wayar yayi picking da sauri ganin Shukrah CE me kiran,
"Hello other half kazo zan mutu kawae Shukrah ta iya cewa tayi wulli da wayar sakamakon marar ta data juya mata ,rike cikin tayi tanata juyi a kasa, A bangaren Safeer ma jin shirun da Shukrah tayi yayi mugun daga masa hankali ko sallama beyiwa haiydar ba yayi ficewar sa da sauri"


"Sanda ya karasa Gidan Shukrah gaba daya ta fita a hayyacin ta, duk karfin hali irin na Safeer sai da ya goge kwalla ganin irin halin da shukrah ta shiga ga jini sai zuba yake, ya rasa yadda zaiyi, dakyar ya tattaro nutsuwar sa ya daga Shukrah cak ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login