Showing 39001 words to 42000 words out of 49582 words

Chapter 14 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt

*SHUKRAH*


Dedicated to *MIEMIEBEE*




3⃣7⃣


"Sanda suka karasa gidan Mamah cike suka shame shi da mutane as if to say ranar sunan ne, *MIEMIE* Tazo da gudu ta rungume *SHUKRAH* tana murna da ganinta nan dae aka fara gaishe gaishe, daga nan *Safeer* ya fadawa *Mamah* ze tafi gidan su *Haiydar*don nan akwai hayaniya sosai, To kawae yace sannan suka fice "

" Saida *SHUKRAH*tayi wanka taci abinci Sannan ta kira *Amminta*, *Ammii* naganin kiran amma taki picking don ita dama me alkunya ce, Text *SHUKRAH* ta mata tace sun sauka lafiya, Bayan kusan awa daya ta mata reply tace sannun ku to"


*MIEMIE* sai nan nan takeda twins taki yarda kowa ya dauke su, wae 'ya' yanta ne


Washe gari *Ibteesam* tazo ta kawo wa babies kaya masu yawa, Hajiyar Haiydar ma tazo nan take yiwa Mamah bayani cewa tabawa Haiydar two weeks ya kawo mata kuma taga kamar be dau maganar T serious ba amma dae ta shirya bashi mamaki, don dama akwai wata yar yayarta *Zafeera* zatayi wa yayar tata magana sai a hadasu don zafeera yarinya ce mai hankali da nutsuwa sosai, dama tun farko tayi wa Haiydar sha awarta amma da taga kamar zafeera bata gabansa yasa takyale amma tunda dae yanzu yaki kawo matar toko zata hadasu, sosai Mamah ta goyawa Hajiya baya acewarta ae Haiydar ya girma, kuma ma ae shirme me zai sashi cewa wae sai ya jira Miemie, nan dae suka gama magana Hajiya tayiwa Mamah alkawarin duk me ake ciki zata fada mata, Sanda zata tafi ta ajiye wa twins Rapper na 100 sannan ta fice, Mamah ta bita tana mata godiya "

" Duk wannan shirin da hajiya takeyi Haiydar be Sani ba don shi tunda tamishi magana bata kuma yimasa ba, saboda hk yace ko dama wasa take masa shiyasa ma yasake ya cigaba da harkokinsa"



"Gobe ne suna amma har yau *Ammii* taki zuwa taga su *labeeb* ,, *Mamah* ta kirata yafi a Kirga amma kullum cewa take gata nan da taga abin bame karewa bane yasa takashe wayarta, Gidan *Ammii* ya cika da yan uwa da abokan arziki amma ba *SHUKRAH* koda sukayi wa *Ammii* maganar sunason akawo ta gidan ayi sunan anan cewa tayi ita ba ruwanta haka sukayi ta surutansu suka gaji"



"Da yamma Alh Sarakee ya duro Nigeria don dama ya dade a Senegal bayanan ma akayi haihuwar amma *SHUKRAH* ta mishi albishir din *Safeer* ya mishi takwara, Sanda ya iso ana kiran sallar la asar saboda haka saida ya tsaya yayi sallah sannan ya karaso gida, *Ammii* ta mishi girki kala kala amma saboda zumudin ganin *Labeeb*& *labeeba* Yasa koda yayi wanka be tsaya cin abinci ba ya dauki babbar trolley daya shigo da ita ya fice, Sanda yake tada mota *Ammii* ta same shi
"Yanzu Daddy fisabilillah gidan mutane xakaje ba kara ba alkunya, koni fa har yau banje ba"

"Daddy dariya yayi sannan yace to Ammii ni na hanaki zuwa ne? Akwai bukatar naga grand child's dina shiyasa kikaga ma nadawo don bayau zan dawo ba ka ida sai next week zan dawo amma na tattara komai na ajiye nazo sannan kice zaki hanamin zuwa ganin su, yana kaiwa nan yayi reversed ya fice daga gidan, jiki ba kwari Ammii ta koma cikin gidan azuciyarta tana mamakin Daddy don gaba daya yariga ya saba da turawa komai nasa irin nasu yake "

" Cikin Sa a Daddy ya samu Safeer da abbah a guest room da alama suna tattatuna abu me mahimmanci ne, Da fara 'a Abbah ya tare shi yayi da Safeer ya durkusa har kasa ya gaida shi cikeda ladabi "

" Ashe kuma an samu karuwa? *DADDY* Yace yana maida kallon sa gun *ABBAH*

"wallahi kam an samu Alh. *sarakee* D Hajiya *Khadija* Abban yace fuskarsa dauke da murna, Allah dae ya raya mana su bisa tafarkin addinin musulunci "

" Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen "gyaran murya Daddy yayi sannan yace Madallah Nagode da Girmamawa ko kuma ince da bani wani matsayi da kayi safeer, hakika kai abin alfahari ne kuma ka can can chi yabo Allah ya maka albarka, Sakamon alkhairin dakamin ka sama yaronka sunana nayi alkawarin daukan nauyin duk wani abu da za'a ci ko sha na kuma dau nauyin gurin da za'a zauna kai hatta ragunan sunanma na hutar da kai insha Allah daga nan zuwa dare za a kawo "

" Abbah yayi Saurin kallon shi yace haba Alhaji ae baza ' ayi haka ba, hidimar tayi yawa ae yau fa ka dawo kasar ma gaba daya, ka barshi wallahi zamuyi komai insha Allah "

" Murrmushin manya Daddy yayi yace bafa ku kuka Sani ba haka kuma badan bazaku iyaba yasa zanyi A a kawae dae tukwucin Alheri ne, so karku damu kudai kawai kuyi fatan ayi taro lafiya a tashi lafiya "



Godiya dukansu suka mai kafin safeer yace bari yaje yasa akawo Twins, to Daddy yace sannan suka cigaba da hirar su da Abbah"

"Sanda safeer ya shiga cikin gidan A parlour ya tararda *AYSHER*, *SHUKRAH* & *MIEMIE*, Shukrah na Rike da Labeeba yayinda miemie ta rike labeeb, hararar miemie yayi sannan yace waye ya baki ixinin daukar min yaro salon kiyar dashi ko, ke daman ba nutsuwa gareki ba, Hade rai Miemie tayi ta ajiye labeeb da karfi kan kujera har sai da yaron ya fasa kuka, Safeer ya zo da gudu zai rike ta tayi dakin Mamah da gudu ya bita, Aysher ce tayi Saurin daga labeeb tana jijjiga shi "

" Jikin Hajiyar Haiydar ta fada, Hajiya Kinga ya Safeer yanamin gori akan 'ya' yansa ko, kuma don na ajiye masa shine zai dakeni, tana kaiwa nan ta fashe da kuka kamar wadda ya daka, Shi safeer ma mamaki ne ya hana masa cewa komai shi a duniya be taba ganin yarinya irin miemie ba, Mamah tace ae sai ka fita tunda burinka ya cika kasata kuka kaji dadi, Miemie ta fakin idon Mamah tamasa gwalo tace cikeda shagwaba Mamah yaushe zaki haifar mana twins muma adena min gori "


" dariya sukayi dukansu sannan safeer ya fice yasa Aysher Da Shukrah su kaiwa Daddy twins"




WASHE GARI


Tun asuba mutane suka fara cika gidan duk da cewa a tourist camp za ayi taron sunan amma kafin7:00 gida ba matsaka tsinke, ba ayi girki a gida ba kasancewar an riga anyi order a can tourist camp din snacks kuma anyi order a me. Biggs, Drink ko Wata Aminiyar Mamah ce Hajiya Maryam Anas ce tadau nauyi "


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

12:00pm na isa tourist camp gurin ya cika sosai da yan uwa da abokan arziki, Bayan bude taro da Addu ' a da wata babbar Malama *safiyya* *yakasai* da tayi ne kuma aka vukaci D. J Yasa sauti nan fa yan *SHUKRAH NOVELS suka zage sai rawa suke ba kamar Safiyya* *Galadanchi* da *Zee* *zee*, sai da komai ya lafa sannan aka fara rabon Mutane sai karba suke, can nagano wasu mutane sun koma gefe sunata dura abinci da lemo a jaka kara matsawa nayi don ganin ko suwaye, wazan gani inba, *MEELA* *SOFTIE* *EESHATULLAH* *MAMAH* *SKY* *FEUXER* *MARYAM*& *NURIYYA* ba, suna ganina suka fara raba ido, Haka dae taro ya watse mutane sae sawa twins albarka suke "




" Sai wajen 11:00pm safeer ya samu kubewa da Shukrah, fitowarta a wanka knn tana shiryawa yakarasa ya rungume ta taba ya a tare suka sauke ajiyar zuciya, yace mata a cikin kunnen ta

"Bazan taba gajiya da yimiki godiya ba Shukrah kinmin komai a rayuwa ta, Allah ya miki Albarka kinji, yanzu ki fadamin duk me kike so insha Allah zan miki "


" Shukrah tai Saurin juyowa tana kallon shi sannan tace da gaske ya Safeer "


" Yace Da gaske "



Tace Aiki nake so na fara, yace wannan shine yafi komai sauki, akwai wata kawar Mamah tare sukayi Uni Maid insha Allah zan mata magana itace me *MARYAM* *CLINIC* Din can... .
[5/15, 7:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻




*WRITTEN BY*
*ZAINAB YAKASAI*
*SHUKRAH*






Dedicated to *MIEMIEBEE*





3⃣8⃣



" *SHUKRAH* tace karka cemin *AUNTY MARYAM ANAS*, *Safeer* ya kalleta cikeda mamaki sannan yace karki ce kinsan ta?

" *SHUKRAH* ta mishi hararar wasa sannan tace lallai yaza ayi ace bansan taba tare fa sukayi secondry skul da *Ammii* fa kuma tana zuwa gida sosai, *Safeer* yayi murmushi mai kyau sannan yace Masha Allah ynx inna fita zanyi wa *Mamah* magana insha Allah komai zaizo da sauki don *Mamah* tana bani labarin saukin kan *Mummy Maryam Anas* tun suna uni maid haka take duk da kasancewar ta over roller amma bata da girma kai, *SHUKRAH* ma murmushi tayi sannan tace Allah sarki Allah dae ya shige mata gaba, kuma nagode sosai da Amincewar dakayi *PAPA'N TWINS*, matsowa *Safeer*yayi ya rungume ta sosai sannan yace kinfi karfin komai a gurina wallahi *SHUKRAH* Allah dae yayi miki Albarka ya kuma kara miki lafiya ya kare ki daga sharrin masu sharri, sosai *SHUKRAH*taji dadin addu 'ar tasa saboda haka ta manna bakinta akan nashi ta soma kissing dinsa sundau lokaci sosai a hk kafin *LABEEB*ya fasa kuka sukayi Saurin janye wa haka kuma suka nufeshi da sauri,, *SHUKRAH* C tayi nasarar daukan sa Tasan yunwa yakeji don duk basu zo hannunta ba, shiyasa tayi Saurin yaye rigarta tasoma feeding nashi"

"sanda *Safeer* ya fita a dakin gurin *Mamah* yaje yamata bayani yadda sukayi da *SHUKRAH* kuma hakan ya mata dadi at last dae zata taimaki mutane da yawa kuma ta mishi alkawarin zatayi, *Mummy Maryam Anas* maganar a yau ba sai gobe ba, nan *Safeer* yashiga godiya sannan sukayi sallama da *Mamah* da kanshi ya kai Hajiyar *Haiydar* gida sannan sukaje ya samu *Haiydar a gida saboda hk suka zauna sunata hira Safeer* sai
Tsokanar *Haiydar* yake wae za ayi masa *AUREN BAZATA* Sai da *Haiydar* ya bata ransa sannan *Safeer* ya kyaleshi sanda ya masa sallama ma ko answer wa ma beyi ba haka *Safeer* ya tafi ya nayiwa *Haiydar* dariyar mugunta"


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


*Hajiyar Haiydar* T samu yayar ta *Hajiya Safiya* kan tana son hada *Haiydar* & *Zafeera* Aure kuma Alhamdulillahi maganar ta tasamu karbuwa a wajen *Hajiya safiya Da Alhaji mai kano* mahaifin *Zafeera* kenan Don Alhajin cewa yayi nanda wata biyu za ayi bikin acewarsa ae su suka haifi yaran kuma sunada hakki akan su haka kuma suna da ikon zaba musu abinda yayi dai~dai da rayuwar su, saboda hk ba bukatar tambayar *Zafeera* ko bata sonsa"



" *ZAFEERA* Itace 'ya mace guda daya tilo a gurin *Hajiya Safiya* shiyasa ta dauki son duniya ta dora mata"

"hajiya kawae dauriya take don sam bata son abinda zai taba *gudaliyar ta*,kuma tana tunanin yadda zasu kwashe da *Zafeera* DUK da dae tanada saukin kai kuma tasan bazata ce A a ba, Amma tana ganin dae kamar an shiga hakkin ta, da kyar ta iya bude baki tace Allah dae ya sa komai yazo da sauki "


" Ameen Hajiyar Haiydar tace "

" Shiko *Alhaji Mai kano* cewa su kashe kansu in anyi AUREN, daga nan dae ya mike ya fice, To itama Hajiyar Haiydar sallama tayi wa Hajiyar Zafeera ta fice "



" Da daddare har Zafeera ta kwanta Hajiya ta shigo ta kwashe duk yadda sukayi da Hajiyar Haiydar ta fada mata sannan tace
"kuma Baffanki yasa bikin Nan da wata biyu,"

"Zuciyar Zafeera ta bada wani *Dum Dum Dum* tanason Hajiyar ta, kuma bata jin zata iya watsa kasa a idanun soyayyar da Hajiyar take mata uwa uba kuma tarbiyyar da Hajiyar tamata, Saboda hk tace *TO* Asanyaye "

" Sosai Hajiya taji tausayin 'yar tata amma saboda batason maganar tayi nisa har tasa *Zafeera* kuka yasata mikewa tace kiyi Addu' a *Angel* sai da safe "

" nanma *To*kawai tace mata sannan ta kwanta"


"Duk wannan Abun da ake Haiydar be Sani ba don Hajiyar bata kuma yimasa maganar ba, cikin sati biyu magana ta kankama don har ta isa katsina dangin su Haiydar din kenan, Hajiyar Haiydar da Hajiyar zafeera sun shirya staf zasuje Dubai don hado lefen *Zafeera*, koda *Haiydar* ya tamvayeta inda zata cewa tayi ina ruwansa "

" Sati daya kawae su Hajiya sukayi suka hado kaya masu yawan gaske uwa uba kuma ga kyau da tsada, Sai bayan da suka dawo ne Hajiyar tace wae yazo yaga lefen shi, ko kallon kayan beyiba yayi fice war sa don wani mugun takaichi ne ya durar mishi"


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


"yau kwanan su *LABEEB DA LABEEBA* 40 A duniya amma *Ammii* bata taba sasu a idanun ta ba sai dae ko a picture shidin ma sau biyu ne, Ranar da *AREEF* Yaje ganin su yayi snapping dinsu ya nuna mata sanda ya dawo sai kuma sanda *SHUKRAH* tayi mata sending a WhatsApp "

" Wannan dalilin ne yasa *Mamah Shukrah Aysher da Miemie* suka shirya mata ziyarar *BAZATA*.. . .





*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE*💞
[5/16, 1:15 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻 *AUREN BAZATA*👮🏻
( *An unexpected marriage*)


*WRITTEN BY*
*ZAINAB YAKASAI*
*SHUKRAH*



*DEDICATED TO MIEMIE BIE*💞



3⃣9⃣



" *AMMII* Na daga cikin daki ta jiyo sallamar su, ta fito da sauri ta tare shu da fara 'arta
"Sannunku da zuwa, wannan irin zuwa na bazata haka, da kun Sani kun kira ni kun cemin zakuzo ae"


" *Mamah* ta dan harare ta sannan tace to in an kira picking kike, ae ina sane na shirya wannan zuwan bazatan sai da na kira *AREEF* Ma na tambaye shi ko kina nn ya tabbatar min kina nn din sannan muka tawo "


" Murmushi kawae *AMMII* Tayi ta wuce fridge ta kawo musu drinks, *Aysher* ta durkusa kusa da *Mamah* tana gaida *AMMII*, da fara a ta Answer sannan *MIEMIE* MA ta durkusa ta gaida ta, *SHUKRAH*ma ta gaida ta, ta Answer ba tare da ta kalle taba "

*MAMAH* Ta dawo da kallon ta gun *AMMII* Sannan tace, ae kawo muki twins mukayi tunda kinki zuwa ki gansu, Murmushi *AMMII*Tayi sannan tace ba haka bane ba, abubuwa ne sukayi min yawa, *Mamah* tace to aini gashi nan nazo da kai na"

" *SHUKRAH* ta dan kallo *AMMII* Aiko suka hada ido, Ammii tayi saurin dauke idonta, Shukrah tayi Murmushi sannan ta mike ta do rawa Mata *LABEEB* Kan cinyarta, *AMMII* Tayi saurin sa hannu ta ture shi saura kadan ya fadi Shukrah ta tare shi tana Murmushi, Mamah tace yanzu dan Allah wae sai ki ture shi haba *Ammii* gaskiya ki rage wannan kawaichin naki yayi yawa wlh ynx zamani ya canja fa, Dariya *Ammii* tayi tace to ae shi kunya, kara da kawaichi a jinin fulani yake, Amma kamar yadda kika ce na rage zan danyi kokari na rage din, yawwa ae haka akeso *Mamah* tace tana do rawa *Ammii* *Labeeba* akan cinyarta, cikeda kunya *Ammii'n* ta daga ta tana Murmushi sannan tace Allah ya raya su yasa masu jin k'ai ne"


"Hada baki sukayi dukansu wajen cewa Ameen"

"Yinin ranar duk sunyi shine a gidan *Ammii* amma *Mamah* ta kula bawata magana data shiga tsakaninsu da *SHUKRAH* a zuciyarta tana mamakin hali irin na *Ammii* kusan wata biyar fa bataga Shukrah 'n ba tun tafiyar su San Francisco gashi ynx tazo amma sai share ta take, Tana wannan tunanin ne taga *Ammii* ta mike ta shige Bed room, *Mamah*ta Dawo da kallon ta gun *SHUKRAH* tace
*SHUKRAH* tashi kibi *Ammii' nki* kuyi magana kinji "

Kamar dama jira take tayi saurin mikewa ta shige dakin da sauri, juyawa Mamah tayi azuciyarta tana dada mamakin *Ammii*, Sanda *Shukrah* ta shiga dakin lokacin ita kuma Ammi zata fito, Shukrah tayi saurin rike hannunta tace *AMMA NA* ynx kin dena sona ko? Ta fadi haka ne sanda hawaye ke fitowa a idanunta "


" *Ammii* cikeda tausayin 'yar tata tace ban dena sonki ba *SHUKRAH* ya jikin ki?


"jiki Alhamdulillahi, twins suna fushi dake tunda kinki zuwa ganin su, Dariya kawae *Ammii* tayi sannan tace ae ynx gashi nan kun kawo su ko?

Eh mun kawo su kam, sun danyi hirar yaushe gamo sannan suka fito, sai bayan sallah 'r magrib sannan suka tafi bayan *Ammii* ta cika su da tsaraba "


" washe gari da sassafe *Safeer* ya shigo cikin gidan *Mamah* ya tarar a parlour tana Karanta *Hisnul muslim* ya durkusa kusa da ita yana gaida ta, Bayan sun gama gaisawa kuma shiru ne ya biyo baya don *Mamah* cigaba tayi da karatun ta shi kuma *safeer* zama yayi yana dan Satar kallon ta, lura da hakan da *Mamah* tayi ne yasa ta ajiye littafin hannunta ta ta dawo da kallon ta gurinsa "

" Ya akayi ne *Safeer*?

"kara kasa da kansa yayi kafin yace' *Mamah* dama zuwa nayi mu tafi da *SHUKRAH* & *TWINS* Tunda sunyi Arba ' in dinko?

"Mamah ta rike ha'ba tana masa kallon mamaki sannan tace to fitsararre mara kunya ni ae nafika sanin sunyi Arba,in din, to barin fada maka baxata koma ba sai nan da two weeks don bamu gama gyaran da muke ba"

*Safeer*ya bata rai kamar zeyi kuka yace wae wannan wane irin gyara ne dan Allah, nidae kawae a barshi haka wannan ma wanda akayi mata ya isa "

" Dalla can rufe min baki mara kunya kawae sai kace bakai ake yiwa gyaran ba, ta nuna masa kofa tashi ka fita ka bani guri, haka *Safeer*din ya fita yana mita
"Wannan wace irin rayuwa ce, dan anga Mutum me hakurine sai a dinga masa yadda ake so, an cemin 40 days zasuyi na hakura amma ynx an canja magana wae sai nn da two weeks, yaja tsaki sanda ya shige motar sa ya bar gidan"


*SHUKRAH* *SHUKRAH* *SHUKRAH*, Na am *Mamah* Shukrah ta Answer sanda take fitowa daga daki, wuce kije kitchen ki dauko babbar tukunya a dora ruwan wanka, to kawae Shukrah tace sannan ta dauko ta ajiye a gaban Mamah"


"Sassaken bagaruwa Mamah ta zuba sannan ta matse lemon tsami akai tace Aysher tashi kije ki ta fasa, in yayi saiki jiya ki kira Shukrah ta shiga ciki"



"Sanda Shukrah ta fito a wanka Mamah tasa Aysher ta dauko kaskon turaren wuta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login