Showing 18001 words to 21000 words out of 49582 words

Chapter 7 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt

mata zafi, Amma tasan komai lokaci ne in lokacin yazo ko bataso sai anyi "



" Da Asuba Safeer ne ya fara bude ido kasancewar dama sama - sama yayi bacci yau, A hankali ya zare Shukra a jikinsa ya kwantar da ita sannan ya shige toilet don yin alwala "

" Ko da ya fito bata farka ba saboda haka ya karasa kan bed domin tashin ta "


" Hannunta na dama ya kama yasa a bakin sa yana tsotsa a hankali, sun kai kusan 2 mints a haka kafin Shukra ta fara bude idonta a kansa "


" Yana ganin ta bude ido ya mikar da ita zaune yana karanto mata addu 'ar tashi daga baccin "


" Bin addu' ar tashiga yi har suka kammala sannan ta mike ta yi hanyar toilet din "

" Yi sauri Shukra kiyo alwalar kizo muyi jam 'i

"To tace sannan ta shige toilet zuciyarta cike da farin cikin kulawar da Safeer ya soma bata "



" Koda ta fito tarar wa tayi ya fito mata da hijab ya kuma shimfida musu abin sallah "



" Karasawa tayi ta dauki hijab din ta hau abin sallah shi kuma ya soma ikama "


" Koda Su kazo Sujjadar karshe Safeer ya dade yana musu addu 'ar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a sabuwar rayuwar su"




"Bayan sunyi addu' a ne Shukra ta mike zata fita "

" Kamo Hannunta yayi ya jawota ta fada jikinsa ya rungume ta hade da dora kansa akan nata "


" Ina zaki kuma? Ya tamvaye ta murya can ciki "



" Duk sai taji ya kashe mata jiki da kyar ta iya cewa ' breakfast zan hada mana "



" No ki bari sai zuwa 10:00am in mun tashi a bacci kyayi kinji ya fada yana shafa smooth cheek nata "

" Office dinfa ta tambaye shi a kasalance "


" Bazani ba kin manta ni Ango ne "



" Nan ta fara kokarin tashi daga jikinsa, yasake mai data ya kwantar "

" Ina zakije ne wai? Ko toilet zaki "ya rada mata a kunne"


"ji tayi wani abu na yawo a jikanta jin hucin bakinsa a kunnenta "

" Bacci zanyi ta bashi Answer da kyar "


" To kiyi kwanciyarki zansa kiyi bacci kinji "


" Komai bata ceba sai kara lafewa datayi a jikinsa hade da lumshe ido "


" Bayan ta ya shiga bubbugawa a hankali kamar yana son yasa baby bacci, A hankali baccin ya kwasheta "


" Saukar numfashinta daya fara ji a hankali ne ya tabbatar masa tayi bacci, Don haka ya je ya kwantar da ita a tsakiyar bed din shima ya kwanta ya rungume ta sai bacci "


" sai gurin 11:00 suka farka Shukra tayi hanyar kitchen shi kuma ya nufi dakinsa "


" Breakfast me rai da lafiya ta hada musu sannan tayi wanka, Tayi shirin ta cikin wasu English wears riga pink, skirt blue tayi parking gashinta da pink ribbon dama shukra bata son kitso a rayuwar ta "


" Pink din hijab tasa karami tasa blue slippers ta fito palour a gurguje, Suna hada ido ya sakar mata murmushi, murmushin itama ta sakar mai sannan ta wuce dinning ta kwaso breakfast din ta kawo palour...........







SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/10, 5:48 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻






WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA








Dedicated to Miemie bie 💞



2⃣0⃣



"Cikin plate daya ta zuba musu abincin, haka ma tea a cup daya ta hada musu, Haka sukaci Abincin Safeer ba bawa Shukra Labarin Haiydar da Miemie sai dariya take kyalkyalawa abinta, shiru yayi yana kallon yadda take dariyar bilhakki Sai yaga ta masa kyau, ita ko jin shirun yayi yawa yasa ta dena dariyar tana kallon shi "


" Meye kake kallo na "Ta fada tana murguda masa baki"


"Shi abinma dariya ya basa kamar wata karamar yarinya har da murguda baki "


" Shiru sukayi dukansu har suka kammala cin Abincin, sannan Shukra ta kwashe kayan ta kaisu Kitchen ta fara wanke wa "


" Jin shirun da Safeer yayi ne yasashi bin Shukra kitchen, Tana jikin sink tana wanke wanke abinta, Ya karaso yana tattare hannun rigarsa "


" Kawo in taya ki "


" Jiyowa tayi tana kallonsa "ka tayani me?

" Wanke wanke ya bata answer yana kokarin karban sponge din hannunta "


" A a kabarshi wallahi "


" Bakya so namiki jika -jika ko shiyasa bazaki bani bako "



" A a ba haka bane hutar da kai nayi wanke wanke ae sai mata "


" To ae ni ko a gida ran duty'n Aysher nike mata wanke wanke da shara tayi girki "


" Ah lallai Miemie fa baka tayata "


" Mtwsssssss ni sa 'an tane to "?

" Ni kawai ki bani na tayaki kinji "


" Haka ta bashi yana wanke tana daurayewa sai ta samu kanta cikin nishadi bata san cewa Safeer yanada sauki har haka ba "



" Bayan sun gama gyara kitchen dinne suka fito palour donyin kallo, Shukra ta zauna a One sitter amma Safeer ya dage wae anan yake son zama "



" Mikewa tayi ya zauna, Gashi nan na barma gurin shknn ko "


" A a ya fada yana janta zuwa jikinsa "


" Ae Kema Anan zaki zauna "

" To ae ya mana kadan ka bari na zauna a can ta fada tana nuna masa two sitter dake opposite dinsu "


" A a kiyi zaman ki a nan ya fada yana kwantar da ita a jikin sa "


" Bata kara masa musu saima lafe da tayi ajikinsa kamar wata marar lafiya (sub-conscious mind) "


Yinin ranar Safeer beje ko ina ba sai da yamma ne yace da Shukra ze tafi gidan Mamah"


"Ko da tace zata bisa kin yarda yayi wae Amarya bata fita ae"


"To shknn zanje gurin Ibteesam kaji "



" To kije amma karki dade "

" Yawwa tnx"


"Har bakin motar sa ta raka sa saida taga fitar sa sannan ta dawo tayi shirin zuwa gidan ibtee "


" Bata wani dade a gidan ibtee ba ta koma gida don ta naso tayi girkin dare da wuri "


" plantain rings tayi sannan tayi fruit salad tayi ginger drink tasa a fridge, sannan ta shiga wanka "



" Wani coffee and milk material nata ta saka dinkin riga da skirt kayan sunyi dai dai da jikinta ta saka milk din Ear ring tayi parking kanta da Ribbon milk colour, Bata wani yi makeup da yawa ba tadai shafa powder da lipstick sannan ta feshe jikinta da turare ta fito palour "



" Wayarta ta dauka ta hau online tana karanta wani novel na MIEMIE BIE mai suna #Yar gata ce, sai murmushi take ita kadai abinta tana son writern nn tanajin dadin novels dinta"



"Fusge wayar ta da akayine yasata waiwayowa da sauri "


" Kai ya Safeer ni kabani wayana YAR GATA CE fa nake karantawa ta fada a shagwabe "


" Yanzu saboda Allah Shukra bakiji sallamar da DAN GATAN Ki yaketa bugawa ba kin kafawa waya👀kinata murmushi "


" Sannu da ya Safeer wallahi banji ka dawo ba novel din ne ya tafi da Imami na "



" Zan baka amma sai kayi wanka ta fada tana jansa zuwa dakinsa "


" Da kanta ta hada masa ruwan wanka ta kuma rakasa har kofar toilet, sannan ta dawo ta fito masa da kaya ta turare su ta zauna a gefen bed tana jiran fitowar sa "



40minutes ya dauka a toilet din sannan ya fito, straight gaban dressing mirror yaje ya dauko cream dinsa ya dawo kusa da Shukrah ya zauna"



"Shukra cute tayani shafa cream din nan hannuna ciwo yake ya fada wane zeyi kuka "


" Dariya take yi kasa kasa sannan ta karbi cream din tana shafa masa "


" Baki shafamin a baya na ba "


" Cream a baya kuma ya Safeer ta fada tana mika masa kayansa "


" Turo baki yayi gaba kamar wani karamin yaro 'Ni bazansa kayan bama wasu zan dauko tunda bazaki shafamin a baya ba "


" Yi hakuri dan Allah ya Safeer zo in shafa maka to "


" To yace sannan ya juya mata baya ta hau shafa masa, bayan an gama ne ya shirya taja Hannunsa sai dinning "


" Tun da yaji kamshin plantain rings din nan ya kasa sukuni burinsa kawai yaji shi a bakinsa "


" Ae yana fara ci yahau mata santi ita ko sai dariya take masa harda yi masa waigi da serving spoon "




" Bayan sun gama ne Shukra ta kai komai kitchen ta dawo ta sameshi a palour "



" Yana ganin ta fito ya mike ya karaso gurinta hade da rike hannunta "


" Shukrah cute zo muje mu kwanta ni bacci nakeji "


" To kawai tace shikuma ya ja hannunta sai dakinsa"


"A bakin bed ya zaunar da ita sannan ya fita yaje dakin ta ya debo mata wasu sleeping dress iya gwuiwa, sannan ya dauko mata brush dinta ya fito ya sameta kwance akan bed "



" Tashi kiyi wanka kinji shukra ya fada yana mika mata towel dinsa, batayi musu ta karba har sleeping dress da brush nata ta shige toilet "


" Cike da kunya take kallon kanta a mirror, anya zata iya fita a haka kuwa?

"Mutuwar tsaye tayi lokacin da taji safeer na turo kofar hade da kiran sunanta "




" Shukra kiyi sauri ki fito mana nima fa wankan xanyi ya fada sanda ya shigo toilet din"



"Baki sake yake kallon ta tayi masa kyau, Besan sanda ya daga ta sama yana guyi da ita ba kamar wata baby "

" Kinyi kyau ya fada mata cikin kunnenta "


" Nagode tace tana sauka daga jikansa "



" Be wani dade B ya fito yasaka farar jallabiyarsa ya hawo gadon inda shukra take "


" Jikinta ya shige yasa hannunsa cikin gashi kanta yana shafawa a hankali "


" Shukra najinsa ta mishi shiru, shi duk tunanin sa bacci take, saboda da haka ya dunga bin ko ina na jikinta yana shafawa"


"Shukra fa taji kanta cikin wani ya nayi saboda haka ta kara kankame Safeer wane zata shige cikinsa "


" Bakiyi bacci ba Shukrah ya fada yana dago kanta da hannunsa "



" Dakyar ta iya tattaro nitsuwar tace EH "


" Ok tashi muyi Nafilah to ya fada yana mikarda ita zaune "



" A tare suka shiga toilet suka daura alwala suka fito danyin Nafilar Ma'aurata...............







SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/12, 5:41 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻





WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA






Dedicated to miemie bie 😘


2⃣1⃣



"Sun dade sosai sunayin sallar, sunawa kansu addu 'ar samun zaman lafiya, Bayan sun idar ne Safeer ya fuskanci Shukra ya fara mata Tambayoyi akan Addinin ta kuma Alhamdulillahi yaji Abinda yake sonji, kasan cewar Shukra Ma' abociyar Addini ce "



" Tashi ki kwanta kinji Shukra "


" To tace sannan ta cire Hijab dinta ta hau gadon ta kwanta "


" Sai da Safeer ya karayin Sallah raka 'a Biyu ya kara rokon Allah kan ya basu zaman lafiya sannan ya musu Addu' ar samun zuri'a dayyiba"


"Daf da Shukra ya kwanta har tana iya jin numfashin sa akan fuskarta, Hakan ne yasa ta Runtse idonta sosai "


" Shafa kan Shukra yake A hankali har zuwa jikinta, Sannan yasa bakinsa akan nata yana tsotsa a hankali "

" Wani nishadi Shukra taji tanaji bata masan cewar ta iya kiss ba sai yau Kawai jitayi ta fara mayar masa da martani "


" Ganin da nayi Safeer na kokarin zame rigar jikin Shukra ne yasa na jawo musu kofar na dawo palour na zauna "



" 4:00Am inata gyangyadi nafara jin kukan Shukra nace barin leka ko za a nemi taimako na "


" A zaune Safeer yake yayinda Shukra ke rungume a jikansa yana aikin lallashi "

" Sannan Shukra kinji kwanta bari na hada miki ruwan wanka "Ya fada yana kwantar da ita"



"Toilet ya nufa ya hadawa Shukra ruwa me zafin Gaske yasa Dettol a ciki sannan ta fito"



"Cak ya daga Shukra be direta ko inaba sai cikin ruwan zafin, Ae Shukra najin ta A ruwan zafi ta Kankame Safeer sosai hade da Sakar masa kuka sosai "



" Hankali tashe shima ya kara Kankame ta yana mata sannu "


" Kiyi hakuri kinji Shukra in kika shiga ruwan zafin nn zaki dena jin zafin kinji "



" A hankali ta gyada masa kai hade da runtse idonta "



" Sai da Safeer ya gama Gasa Shukra sannan ya hada mata ruwa ta tsarkake kana, ya dauke ya maidata kan gado wanda dama ya changer bed shirt din tun tana wanka"


"Toilet din ya koma shima yayi wanka sannan ya fito ya kwanta a kan gado ya jawo Shukra jikinsa yana lallashinta yana kuma gaya mata How sweeter she is "


" A haka dai bacci ya kwashe su dukansu, Sai Asuba sannan suka farka "


" Daga ta yayi Cak kamar dazu ya kaita toilet ya zaunar sannan ya zuba mata ruwa tayi Alwala "


" Jiransa tai yayi Alwalar shima sannan suka fito tare, Shine ya shimfida musu abin Sallah ya daukowa Shukra Hijab tasaka sannan ya tada Ikama "


" Sai da su kayi Nafila raka 'a 2 sannan sukayi Sallar Asuba, kafin suka koma gado suka kwanta rungume da juna "


Shukra ce ta fara yin bacci ta barshi yanata tunanin Daren jiya, Yayi matukar farin ciki da ya samu shukra virgin, Dama yasan Shukra kamila ce ya kuma sa ran samun budurcinta"



Sai gurin 11:15Am suka farka Shukra ce ta mike tana takawa a hankali kamar wata me koyan tafiya tayi hanyar kofa "


" Riko hannunta yayi yana tambayar ta inda zata "


" Zanje kitchen ne ta fada masa kanta a kasa don wani kunyarsa taji tanaji, Batajinma zata iya hada 👀dashi "


" No kibarshi kawai ki koma ki kwanta zansa Aysher tayi mana breakfast din ko Miemie sai ta kawo mana"


"A a ba sai ka basu wahala ba zanyi da kaina"

"Sai yaji ta burgeshi sosai ya kuma kara mata matsayi a zuciyarsa "


" Haba Shukra kinfa gaji taya zakiyi wani girki, Tunda nace zansa Aysher tayi ki hakura kawai "



" Gani tayi bazata iya cigaba da musu dashi ba saboda wani zazzabi daya ke neman rufe ta sai kawae ta cire hannunta a nasa ta koma kan gadon ta kwanta "


" Parlour ya fito ya zauna sannan ya kira Aysher ya fada mata tayi musu breakfast ta aiko miemie dashi Shukra batajin dadi"



"Bayan kamar minti Arba'in Shukra ta fito daga wanka kenan sukaji ana knocking a kofar parlour "

" Safeer ne ya mike daga kwancen da yake ya fita ya bude kofar, Miemie ya gani tsaya a bakin kofa rike da basket "


" Karban Basket din yayi sannan yace 'ki gaida Mamah yana kokarin rufe kofar "


" Shammatar sa tayi a shige parlour' n tana masa dariya, Ae da sauri yayi kanta yana cewa'Zo ki fita malama "




" Da gudunta ta kara sa dakin Shukra ta sameta kwance a kan bed ta lumshe idonta kamar me bacci "


" Aunty wai bakida? Ko dai haihuwa zakiyi ne ta fada tana shafa cikin Shukra tana neman baby"


"Mikewa Shukra tayi zaune ta cire hannun Miemie dake kan cikinta "

" Miemie ina Mamah?


"Tana Gida tace na gaisheki "


" Ina Answer wa "


" Miemie Harda kara matsowa kusada Shukra tana tambayarta
'Aunty wae inji Anty Aysher wae bakida lafiya?
'Aunty ciki ne da k..... "


"Shigowar Safeer ne ya katse wa Miemie surutun ta"

"Har gaban Miemie yazo yaja kunnenta har sai da tayi kara yace

"Wae me yasa bakya jin magana ne, Ba ce miki nayi ki tafi gida ba shine harda fakar ido na ki shigo da gudu kina min dariya ko"


"Yi hakuri yaya dan Allah Sakar min kunne da zafi fa ta fada tana goge kwallar data zubo mata, Dan sosai take jin zafin rikon da yayi mata "


" Bazan sake ki ba sai kin fada min me kike cewa kika ganni kikayi shiru"


"Shukra ce ta janyo miemie tana goge mata hawayen fuskarta"


"Kai ya Safeer yanzu kan tazo muna hirar mu shine zaka sa ta kuka fisabilillahi Shukra ta fada kanta a kasa hk kuma murya can ciki don sosai take jin zazzabi da ciwon kai "


" Ni Gulman tane banaso shiyasa ya fada yana fita daga dakin"



"Tare sukayi breakfast din harda Miemie dan dama batayi ba ta tawo "



" Zazzabin daya rufe Safeer ne yasa shi yin bacci, sai bayan la 'asar sannan ya farka yayi sallah ya koma bacci"



Ganin duk suna bacci ne yasa miemie tayi musu Tuwon semovita miyan agushi tasha busashshen kifi da ganda😋, A flask tasa tajera a dinning sannan ta koma dakin Shukra ta samu bata tashi a bacci ba "


" Kayan jikinta ta cire tashiga toilet tayi wanka, Ta fito ta shirya sannan ta koma parlour ta zauna tana jiran Safeer ya tashi ya maidata gida"


"Sai bayan magrib dukansu suka farka inda Safeer ya jasu sallah dan bayajin ze iya zuwa masallaci "


" Sai da sukayi Dinner ne Safeer yace Miemie ta taso ya maidata gida dan yasan inya barta zata iya cewa zata kwana"


"Dukansu suka fito harabar gidan, Inda Shukra ta shiga gaba Miemie kuma baya suka kama hanyar gidan Mamah.............









SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/14, 12:42 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻





WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA





Dedicated to Miemie bie 😘




2⃣2⃣



"Cikin lokacin da be wuce minti Arba 'in ba suka karasa gidan Mamah "



" A tare suka shiga cikin gidan dukansu inda suka tararda da Aysher kadai a parlour tana karatun wani hand out "


" Mikewa tayi da fara' ar ta ta riko hannun shukra suka zauna sannan ta shiga gaida ta cike da ladabi "



" Sama taje ta kira Mamah sannan ta dawo suka cigaba da hirar su, Bayan kamar minti 3 sai ga Mamah Da Abbah sun sauko a tare "



" Shukra ce ta sauko daga kujerar da take suka shiga gaisawa da surikanta Kanta na akasa, Sannan Safeer ma ya gaisa da iyayen sa "



" Shukra ya jikin "Mamah ta tambaya

" Jiki Alhamdulillahi ae naji sauki "


" To Allah ya kara lafiya "

" Ameen suka ce dukansu kafin Aysher ta tashi ta kawo wa Shukra ruwa da lemo "



" Da kinbarshi ma Aysher muda zamu tafi yanzu ta fada kasa _ kasa kuma a kunyace"


"Lah bakomai Wallahi Aunty "


" Bayan kamar minti goma Safeer ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login