Showing 12001 words to 15000 words out of 49582 words
Chapter 5 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt
To haka dai rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin girmama juna amma babu abinda ya taba shiga tsakanin su"
"Yau ta kama friday tun safe shukra kejin ciwon mara tana cijewa sai fargaba take kar ciwon yayi worst"
7:12pm safeer ya gaji da zaman falon da yake shi kadai, don duk yau bega shukra ba se yakejin ba dadi don ko ba komai sun saba "
" Dakin ya tura ga mamakinsa sai ya ganta kwance tana juyi da hanzari ya karasa bakin gadon yana jero mata sannu "
" Ya safeer dan Allah karka gayawa Ammii banida lafiya xata min fada wallahi "
" Bazan fada mata ba shukra bari mu tafi asibiti "
" A a bazan iya ba ka siyo min magani kawae mutuwa zanyi wallahi "
" subahannalli "Bazaki mutu ba shukra bari na kira doctor ya duba ki "
"wayarsa ya dauko ya kira, DR waheeda yasanta tun a secondry skul"
"Hello waheeda"
"Na am safeer ya gida "
" lafiya kalau doctor "
" Dan Allah idan bazaki damuba gidana nakeso kixo madam ba lafiya "
" subahanallahi "yimin sending address di gidan gani nn zuwa"
"Ba afi 40mints ba sai ga waheeda ta zo, kai tsaye bedroom din shukra ya kaita ya fito ya basu guri"
" waheeda tabawa shukra magungunan da suka dace amma tana mamakin yadda matar aure take irin wannan ciwon "
" Kasa hakura tayi sai da ta fita ta kira safeer ta hada su ta tambaye su "shin wani abu be taba hada su bane ko me?
" kunya ce ta rufe su dukansu "
" Itako waheeda masifa tai tayi musu kafin ta dawo nasiha "Haba shukra ya zaki hana mijin ki kanki bayan kinsan hukuncin yin hakan (haramun ne miji ya kiraki shimfidar shi kiki, mala'ikun Allah zasuyita tsine miki ne har ixuwa wayewar gari) ko kinason Allah yayi fushi dake ne? Ko kuma kinason mijin ki ya fara bin matan waje "
" Da sauri shukra ta girgiza kanta alamar A a kafin ta fara magana a kunyace
"To aini be taba cewa nazo dakinsa mu kwana ba"
"Tana gama fadar hk tafice daga dakin da saurinta"
"Hakane safeer" waheeda ta tambayeshi tana hararar sa "
" Nan safeer ya kwashe duk yadda akayi akai auren da kuma zaman da sukeyi a gidan har i zuwa ynx "
" sosai waheeda tayi mamaki takuma bashi shawara, kafin ya rakota har falour, nn suka sami shukra a zaune waheeda tayi mata sallama hade da karban number ta da niyyar bata shawarwari
"Har bakin mota suka rakata sai da motar ta ta fita daga cikin gidan sannan suka dawo cikin gidan cike da kunyar juna...........
SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/5, 5:17 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻
WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA
Jealousy can die we are together insha Allah #endless luv
Dedicated to miemie bie 😘
1⃣4⃣
"koda safeer ya kwanta tunani yayi tayi a ransa me shukra take nufi da tace "Ae shine be taba cewa muje dakinsa mu kwana ba"
"ke nn hakan na nufin shukra ta shirya ne ko me?
"indai haka ne to Alhamdulillahi"
"Da tunanin nn bacci barawo ya kwashe shi.
Washe gari bayan safeer ya tafi office, shukra tayi duk ayyukan gida tayi wanka sannan ta dawo palour ta kanta ta dau wayarta ta hau WhatsApp.
" bakuwar number ta gani tamata sallama sai bata answer, bayan kamar 1mint akayi kara mata sallama sai ann ne ta answer.
"Wa alaikisalam "
" DR waheeda ce"
"Eyya doctor yi hakuri banida number ki ban ganeki wlh "
" Bakomai shukra ya jikin "
" jiki Alhamdulillahi "
" Bayan sun gama gaisawa ne waheeda tashiga yi wa shukra nasiha kamar yadda ta daukar wa kana alkawari "
" sosai nasihar ta shiga shukra dan sai godiya takewa waheeda ".
" Waheeda ta kuma yi adding shukra a wani Grp na matan aure domin tasan zata karu sosai "
" Bayan da sukayi sallama shukra kwanciya tayi tana tunanin yadda zata bullowa al amarin daga hk bacci ya kwashe ta
"Knocking din da ake a kofar palour ne ya tadata daga baccin da take,".
"A nutse ta karasa bakin kofar ta bude, matashiya ce bazata wuce taba ko a shekaru take mata sallama da fara 'arta.
" Answer mata sallama tai sannan suka shiga palour suka, shukra ce ta mike ta kawo mata drinks da snacks kala - kala sannan ta dawo ta zauna"
"Sunana ibtisam, nice makociyar ki"
"Wow nice to meet you ibtee"
"nice to meet you too"
"Ina fatan za a min afuwa ni ya kamata ace nazo ba keba"
"Bakomai wallahi komai nufin Allah ne ae"
"ni kuma sunana shukra"
" Nice name"
"Thanks shukra ta fada tana daukar yarinyar ibtee, kasancewar shukra tana son yara sosai "
" Hira suka shiga yi dan da alama jinin su ya hadu sosai "
" Ibtee ce ta mike ta dauki yarinyar ta "
" To shukra ni na tafi sai kuma kinzo ko"
"To ibtee nagode sosai insha Allah gobe zaki ganni ta fada lokacin da suka fito waje"
"Har bakin gate shukra ta raka ibteesam sannan ta dawo gidan donyin girki"
"Haiydar ne ya shigo gidan su safeer da sallamar ma ya taradda Aysher a palour suna karatu itada miemie, har kasa Aysher ta gaida haiydar amma miemie ko a jikin ta cigaba ma da abinda take tayi"
"Kusada miemie yaje ya zauna yana tambayar ta ya exams"
"Sai a nn ta dago ta kalle shi,
" Lah Aunty aysher Kinga wanda zan aura wanda na baki labarin sa rannan, sai ta dawo kan cinyarsa tana mishi surutu shi kuma sai biye mata yake suna kyalkyala dariya "
" Itadai Aysher bata ce komai ba sai kallon su take yi dae "
" Sosai yaji miemie na kara shiga ransa kasan cewar miemie me farin jini duk wanda ya ganta sai ya sota kawayenta harda manya masu yaya ma kai har kawayen mamah ma kawayenta ne, takanas suke zuwa gurinta "
" Sallamar safeer ne ya katsewa miemie surutun ta "
" Da mamaki safeer kebin haiydar da kallo shiko haiydar ko ajikinsa juyawa ma yayi suka cigaba da hirar su da miemie "
" Haiydar wae dama nan zaka zo safeer ya tamvaya"
"Eh ya answer shi a takaice"
"Amma ae baka fada min ba"
"To ae yanzu gashi nan mun hadu ko"
"Buh atleast ae ya kamata ka fadamin ko"
"Kaga malam karka samin ciwan kai dama haka akace duk inda zani sai na nemi ixinin ka kikuwa"
"Ko dan nazo gidanku shine ka wani tsare ni da tambayo yi hk"
"Nidai bance ba, Allah ya baka Hakuri amma"
"Ameen"
"Aysher ina mama me safeer ya tambaye ta "
" Mamah taje unguwa amma bazata dade ba "
" Nikam gaskiya sauri nake kya fada mata nazo "
" Tom insha Allah tace mishi yayinda yake fita "
" sannu da zuwa ya safeer inji shukra da tun dazu take zaune tana jiran shigowar sa, ta miki hannu ta karbi brief case dinsa ta wuce dakinsa shima ybi bayan ta"
"Yau shukra da kanta ta hadawa safeer ruwan wanka ta kuma fito masa da kaya ta feshe su da perfume sannan ta dawo palour ta zauna"
"Bayan safeer ya fito ne shukra ta kawo musu abincin nan palour ta shiga serving dinsa"
"Kai shukra ae da baki wahalar da kanki ba keda baki lafiya"
"Bakomai ae hakki nane(niko nace 🤔😏da bakisan cewa hakkin ki bane sai yau).
" Haka dae suka kammala cin abinci kowa ya shige dakinsa "
" Haka dai rayuwa taciga da tafiya har ranar da shukra ta gama mensis"
"Da daddare suna zaune a palour su biyun bayan sun kammala cin abinci, wayar safeer ce tayi kara aiko da hanzarin sa ya daga"
"Hello babyna ya kike?
"Gaban shukra ne yayi mummunar faduwa jikanta ya hau rawa"
"Ok kina son gani na? To ganinan zuwa ynx"
"ME zan tawo miki da?
" To ganinan daga nn ya kashe wayar ya mike ba tare da ya kalli shukra ba ya dau car key dinsa ya fice da sauri"
"Ae safeer na fita shukra ta fasa ihu, kuka take baji ba gani a nn bacci ya kwashe ta batare da taga dawowar sa ba.................
SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/6, 9:29 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻
WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA
Dedicated to miemie bie 😘
1⃣5⃣
10:40pm safeer ya shigo cikin gidan, shukra ya gani kwance a palour kamar zai tasheta sai kuma ya fasa ya mata addu 'a ya tofe mata jikinta sannan ya wuce dakinsa "
ASUBA
" Karar bude kofar da Safeer yayi ne ya tashi shukra daga baccin da take, suna hada ido ta wani dauke kai ta shige dakinta, shima tabe baki yayi yayi gaba abinsa kasancewar an fara kiran sallar asuba "
" 6:50am shukra ta gama shirinta tsaf ta dauki car key dinta ta fito palour janye da trolley dinta "
" Fitowar shukra yayi dai - dai da fitowar Safeer daga dakinsa, ko kallo be isheta ba ta wuce abinta ta fita daga palour 'n"
"SHUKRA ce ta shigo cikin gidansu a kitchen ta tayadda Ammii tana hada breakfast Kawai sai ta sa mata kuka sosai "
" A rikice Ammii take tambayar ta wani abun aka mata ne? Ko wani abu ya samu Safeer, Amma ko kulata batayi ba saima cigaba da kukan ta da tayi"
"Ammii ma bata ce komai ba ta cigaba da aikin ta, zuwa can kukan shukra ya fara cimata rai, batamasan sanda ta daka mata tsawa ba,
"Dalla malama kin cikamin kunne da kuka kinajina, in kukan kike sha'awa ki fita ki bani guri kije kiyita yi tunda bakida abunyi, tun dazu sai tambayar ki nake me akai miki kinmin shiru "
" Ammii Aure fa zai yi "
" Waye zeyi AUREN wae Ammii ta tambaye ta?
"Ammii ya safeer ne zeyi Aure, jiya a gabana tayi mishi waya wae tana son ganin shi shine ya tafi ya barni, tana kaiwa nn ta sake fashe wa kuka sosai "
" To sai me aini wallahi ya burgeni, haushin ma daya bani baze wuce rashin sakin ki da beyi ba, Ae naso ma sakin ki yayi ya huta tunda ke bakida kirki bakya jin mgn kin raina mu ko "
" Ammii wallahi shine...... "sai kuma tayi shiru ta cigaba da kukan ta
" Shine me Ammii ta tambayeta a fusace"
"Komai bata ce ba sai ma kara sautin kukan ta da tayi "
" Tashi ki fita ki bani guri kafin na kwada miki mari wallahi "
" Tashi tayi ta fita tana cigaba da kukanta, kusan chin karo sukayi da Daddy.
"Ke lafiyar kuwa? "
" Daddy ya Safeer ne zai kara Aure "
" To shine me "? Daddy ya tambaya irin ko ajikinsan nn"
"Ae Wallahi kadan kika gani, badai ke kince ban isaba, Har Safeer yamin biyayya ke ki kasa min ko? Ae duk abinda kike ina sane dake zuba miki ido kawai nai naga iya gudun ruwanki gashi tun ba 'aje ko inaba kin fara kuka da idanunki"
"Shigowar Safeer ne ya katsewa Daddy maganar da yake, ya durkusa har kasa suka gaisa da Daddy Sannan Ammii "
" Yawwa Safeer yanzu nake shirin kiranki ae sai gashi kazo "Inji Daddy
" Eh Daddy naga shukra ta tawo gida ne kuma ni ba wani abu ne ya hada muba, lafiya kalau muka rabu jiya amma yau naga ta dauko Trolley ta tawo "
" Eh wae zuwa tayi dan shashanci tana kuka wae zakayi Aure "Ammii tace tana hararar shukra.
" Wace yarinyar ce zaka aura? Daddy ya tambayi Safeer "
" Sunkuyar da kansa yayi yace a office dinmu take "
" Masha Allah "Ni da kaina zan nema maka aurenta kaji dan Albarka, tashi ka tafi office karka makara kaji"
"To kawae yace sannan Y mike yana satar kallon shukra ita ko sai zabga masa harara take wane idonta zai fado kasa "
" Kuma ki tashi ki dauki kayanki ki koma gidan mijin ki kafin in bata miki rai wallahi, Daddy ya fada a fusace"
Ko motsi shukra batayiba sai kukanta take baji ba gani "
" Zaki tashi ko sai na kwada miki mari "
" Jiki ba kwari ta mike taja trolley ta fice daga palour 'n "
" Kamar kullum yau ma tayi girkin ta bayan ta gama ne tayi wanka ta tsara kwalliya tanaso taje gidan Ibtee amma kuma bata tambayi Safeer ba gashi batada number shi balle ta kirashi ta tambaye shi"
"Tana nn zaune Safeer ya shigo gidan da sallamar shi "
" Kamar bazata Answer ba sai kuma ta Answer, ta mike da kyar ta karbi briefcase dinsa da ledar daya shigo dashi ta kai komai mu hallinsa, ta dawo ta zauna abinta"
"Yau shukra sai wani share Safeer take yana bata labarin office, shiko sai nunawa yake kamar bema san tanayi ba ya cigaba da bata labarin har zuwa lokacin bacci a nn ne kowa ya tashi ya shige dakinsa"
"Yau kwana 3 kenan Safeer na fita zance, abin na matukar damun shukra, Amma idan ta tuna cewa itace ta bata rawarta da tsalle ta kanyi kuka, in ta zauna ma sai dai tayita istigfari tana rokon Allah ya yafe mata "
" Yau ta kama friday Safeer ne ya fito cikin shirinsa na zuwa office shukra ya tarar a palour idonta duk ya kumbura dan kukan da tayi "
" Ya safeer An tashi lafiya?
"Lafiya kalau shukra "
" Wani abun ya farune naga kina kuka? Ko kin gaji da zama danine?
"Girgiza kai tashiga yi tana goge hawayen da ke gangarowa daga idonta tana kuma kokarin hadiye kukan dake son subuce mata"
"Ko gida kike so ne?
"Eh ka kaini gida gurin Ammii ta fada tana fashewa da kuka "
" To naji zan kaiki amma ki bari sai na dawo daga office "
" Tom " Amma ina so in shiga makota gurin Ibteesam wadda na gaya maka tazo rannan"
"Tom shknn ki gaishe ta "sai na dawo
" Adawo lpy "
" Allah yasa daga nan ya fice daga cikin gidan
"Sallamar shukra ne yasa Ibteesam fitowa daga bedroom ae tana ganin shukra ta fara murna tana mata sannu da zuwa "
" Bayan Ibteesam ta cika shukra da drinks suka fara hira, sosai yarinyar Ibtee ta shiga ran shukra kamar ta kwace ta ta tafi da ita, sai addu 'a take itama Allah ya kawo mata masu Albarka "
" Sai gurin 03:00pm sannan sukayi sallama shukra takoma gidanta "
" Sosai taji dadin zuwanta gidan Ibtee kasancewar ta gaji da zaman gidan ita kadai, shiyasa ta matsu ayiwa su miemie hutu tazo mata"
"To Safeer ya kai shukra gida Amma Ammii bata wani sakar mata fuska ba, sama sama take kulata, sai dare sannan Safeer yazo ya dauketa suka tafi "
" Abin duniya fa ya ishi shukra ganin cewar bikin Safeer ya matso sosai sai wani sabga yake yana wani rawar kai, wani karin abin takaichi ma shine Safeer daya karbo kayanda zai sa ran DAURIN AUREN dakinta ya kawo ya ajiye "
" Yau saura sati biyu bikin Safeer saboda hk ya kawo wa shukra invitation cards ko zata gayyaci kawayenta...............
SHUKRA YAR GATAN MIEMIE BIE 💞
[4/7, 2:03 PM] 🎀Shukra yar gatan miemie🎀: 👮🏻AUREN BAZATA 👮🏻
WRITTEN BY
ZAINAB YAKASAI
SHUKRA
Dedicated to miemie bie 😘
1⃣6⃣
" Gajiya Safeer yayi da mikawa shukra invitation cards din ya ajiye mata a bedside drower ya fice daga dakin"
"Kuka kawai ta saki sannan ta private tashi ta dauki envelop din daya kawo mata ta wulla ta bayan gado ta kwanta ta cigaba da kukanta "
" Kukan da shukra tayi ne yasa ta ciwon kai sosai, Safeer ganin duk yau bega Shukra ba yasashi zuwa dakinta duba ta "
" Kwance take a kan bed tana kallon sama yayinda hawaye ke gangarowa daga idanunta "
" Bakin gadon yaje ya zauna tausayin shukra fal zuciyar sa amma ya dake ya fara tambayar ta ko wani abu ne yasameta "
" Kaina kemin ciwo "Tace a takaice
" Sannu Allah ya kara sauki, ko zamuje hospital "
" Ko kallo ma be isheta ba ta juya mai baya saboda wani mugun haushin sa takeji yanzu "
" Gajiya yayi da zama ya mike ya fice, be dade ba kuma ya dawo dauke da leda a hannunsa ya ajiye a bedside drower sannan ya fice ya dauko bottle water da glass cup ya dawo ya zauna a kusa da ita, ita dai bata ko kallo shiba "
" Ruwan ya zuba mata a cup sannan ya balla maganin ya mika mata "
" karbi kisha kinji "
" To tace sannan ta karba ta kora ta koma ta kwanta "
" Shima ficewa yayi a dakin ya wuce dakinsa don yin wanka "
" Kwana uku ne kawai ya rage ayi bikin safeer, Shukra ta rasa yanda zatayi jitake kamar ta kai kanta gurin Safeer amma tasan