Showing 48001 words to 49582 words out of 49582 words

Chapter 17 - AUREN BAZATA COMPLETE BOOK BY ZAINAB YAKASAI.txt

tare da ya damu da jinin dake zuba a jikin taba, yanasata a mota ya zagaya ya shiga yayi reverse ya fita da gudun gaske"


"Kai tsaye ya wuce Standard (Asibitin Dr.Mariya galadanci) cikin sa a ya samu Dr.Zainab zata fita, Zainab ganin halin da Shukrah take ciki yasata karbar ta tawuce da ita labour room"


"Ba karamin tashin hankali Safeer ya shiga ba ganin awan shukrah uku cur a labour room amma ta kasa haihuwa ko kuka ta kasa sai innalillahi wa innailayyi raji'un take fadi ,nan danan ya kira Mamah ya fada mata sannan ya kira Ammii ma ya sanar da ita, bayan kamar minti goma wata nurse mai suna Salmah tazo tace masa dole fa sai Shukrah tasha inducing drug saboda HK yaje ya nemo,ba tare da yasan Inda zai samu ba ya fito duk Air condition din dake cikin dan karamin hospital din nn amma Safeer ya jike da gumi,kicibus sukayi da Haiydar Wanda Mamah ta kira ta sanar dashi zancen haihuwar,Haiydar ya dafa Safeer cikeda tausayawa yace haba Safeer be a man mana duk ka wani rude ka gigice, cuta ae ba mutuwa bace"


"Dafe kai kawae Safeer yayi don bayason magana ma gaba daya zuwa can yace inducer zaka samo min Haiydar ,Shukrah tana cikin wani hali.. Pls help me I can't afford loosing her, I just love her

"Da sauri haydar ya wuce be Dade ba sai gashi da inducer yaje ya mikawa wani Nurse yace ya kai musu sannan ya dawo gurin Safeer yana bashi baki,"


"Cikin ikon Allah Shukrah nashan inducer ta nemi ciwo ta rasa ji tayi kamar zatayi amai, ta kira nurse tace mata

"Amai zanyi kamani inje toilet"


"Yi aman ki Anan kinji tace mata, kakarin Aman Shukrah tashiga yi nan danan sai ga baby ta fado ta sa kuka kuwa Shukrah ta koma ta lafe sai bacci,cikin bacci Shukrah taji bayanta ya wani amsa,ta bude ido a firgice ta fara kuka jitake kamar zata mutu ga baby tana gani nurse tana gyarawa, sake sakin ihu tayi sakamakon mararta da bayanta da suka kuma kullewa tace wayyo Allah ka taimakeni, duk likitocin suka yo kanta, Dr Zainab ta matsa cikin ta tace Salma zo akwae wani acikin nn da alama, Salma ta karaso da sauri tarike Shukrah tace yi nishi kinji Shukrah yanzu babyn zai fito, Shukrah ta marai raice tace vazan iya ba wallahi ni mutuwa zanyi ki kiramin other half muyi sallama"


"Cikeda tausayi Dr.zainab shiga shafa kan Shukrah,tace cutafa ba mutuwa bace Shukrah kiyi hkr kiyi nishi ko guda days ne please"


"shukrah bata San sanda ta kankame Dr Zainab ba tayi wani nishi ae ko sai ga baby nan placenta ta fito, an an aka shiga gyara babyn cikin kokaci kadan aka jerewa Shukrah twins dinta duk mata, sai anan aka bar Safeer da haiyar su shigo,Shi Safeer bamaya yin ta Twins shi ta Shukran sa yakeyi ya karasa da sauri ya rungume ta yana mata sannu, shiko haiydar Twins yaje ya hade ya rungume yana kissing dinsu nan da nan suka shiga ransa, yashiga snapping face nasu yana turawa mutane, kafin kice kwabo asibiti ya cika da yan uwa da abokan arziki, zuwa dare aka yi discharging nasu suka tafi gida "


" Washe gari tun safe mutane suka cika gidan ba masaka tsinke Safeer ko wanka be samu yayi ba sai gidan Haiydar ya tafi yayi acan, haka dae gida ya cigaba da cika har ana gobe suna, da sassafe Aunty Maryam Anas ta aiko da trolleys uku cikeda kayan babies dana maman babies, da kuma raguna guda biyu, "

" Ranar suna da asuba safeer ya fadi sunayen da yayi yaransa huduba da, ta farkon yasamata *Fateema*za a dinga kiranta da ( *Afaf*) sunan Ammii 'n Shukrah ta biyun kuma *Maryam*( *Anan*) taci sunan Aunty Maryam Anas, haka aka sha shagalin suna kowa sai murna yake, don har yan uwan su Shukrah na kd, dana maid, dana Damaturu sai da suka zo, haka yan Adamawa duk sunzo, Washe gari da yawa suka tafi wasu kuwa sunce sai next week "


" Safeer baya samun ganin Shukrah kwata kwata amma be damu ba kasan cewar shikansa bashida lokacin kansa don aikin company yayi nisa sosai kuma akwai bukatar lallai yaje gurin saboda hk kullum inya fita da safe baya dawowa sai dare "


" Yau sati biyu da haihuwar Shukrah kuma yau aka kammala ginin company 'n Safeer, Yan uwa duk sun koma sai Shukrah kadae da twins don labeeba da labeeb an tafi dasu gidan Ammii acewar ta wae basaji zasu iya buge mata yaranta, wanka tayi ta shirya cikin wani material blue tasa ear ring pink da bangles pink colour ta shafa powder kawae da lip stick ta daura pink din karamin veil a kanta ta dauki *AFAF* Tana feeding dinta, safeer ne ya shigo cikin dakin hannunsa rike da shopping ya ajiye yana mata murmushi , karasowa kan gadon yayi ya zauna ya kura musu ido yana jin son su sosai aransa, dauko *ANAN* Yayi ya daura kan cinyarsa yana shafa gashin daya rufe mata goshin ta, yace Other half wannan yarinyar tana kama dake duk nafi sonta cikin yaran nn 4 "


" Dariya Shukrah tayi tana kallon *AFAF*Tace Nikuma nafison wannan saboda da kai take kama wallahi, murnushi yayi yace mummuna da ita kuwa sannan ya dauko wayarsa yayi snapping Shukrah a yadda take tana feeding *AFAF* bata rai tayi wane zata yi kuka tace wallahi banaso me yasa zakimin hoto a hk, sai wasu sun gani ko, ta zare *AFAF*daga jikinta sannan ta gyara rigarta ta ajiye ta ta mike da niyyar fita, yayi Saurin ajiye *ANAN* Yazo ya rungume ta tabaya yace meye nayin fushi kuma, ungo wayar kiyi deleting da hannunki kinji tawan"

"Karbar wayar tayi tayi deleting pictures din sannan ta juyo ta rungume shi tayi masa kiss a forehead, Saurin rike fuskarta yayi yashiga kissing din ko ina na fuskar kafin ya gangaro bakinta yafara tsotsa kamar wani mayunwaci "


" Yau akayi bikin bude company'n safeer, bikin daya samu halartar manya manyan mutane yawanci abokan Abbah ne sai ko abokan aikin Safeer din, *Ahmad da Azeeza* ma sun zo, zokuga murna gun Shukrah jitake kamar ta goya *Azeeza* ta rasa inda zatasa kanta sai hidima take da ita, haka aka bude company mai suna *MAI LAFIYA GROUP OF COMPANY*, haka taro ya watse washe gari kuma aka yi saukar Alqur'ani mai girma akayi addu ' ar kariya sannan aka tashi"




"Bayan kwana arba' in Shukrah ta koma aikin ta don miemie ta dawo gidanta da zama ynx tana ss3 sun gama waec suna jiran Neco saboda hk bata zuwa ko ina sai zaman rainon twins"


"Bayan shekara uku "


An samu nasorori masu yawa a company'n Safeer haka ma Shukrah tasamu nata nasororin don ynx tayi suna sosai kan kwarewarta a fannin ido, Mutane da dama Shukrah ta dauki nauyin musu aiki haka ma glasses kyauta takewa mutane (Nima ita tayi min nawa kyauta), sosai take samun albarka gurin mutane, haka ma Daddy ya naji da ita yana kuma alfahari da ita"



Yau Aysher ta haihu, sai dai dan bezo da rai ba, haka aka sha kuka aka barwa Allah, "



" Yau graduation din su miemee, zo kuga rawar kai sai da Shukrah Ta mata dinki kala biyar na get together da zasuyi, haka Mamah ma set uku ta dinka mata"




"6:20pm Miemie ta gama shirin tafiya Get together, riga tasa body hug pink da jeans blue tayi rolling da pink din veil tasa pink flat shoe tadau wata pink purse tasha makeup kamar wata makeup artist maryam tafida ce tayi mata, parlour ta fito ta kalli Mamah, Mamah yanzu zamu wuce ina car key dinki zanbiya in dauki Amatullah mu wuce"


"To Allah ya kiyaye hanya, Mamah tace tana mikawa Miemie car key dinta, kaci bus sukayi da safeer yana kokarin shigo wa karemata kallo yayi sannan yace 'gidan ubanwa zaki a hk'?, tura baki tayi sannan tace get together zani, kwada mata lafiyayyen mari yayi yace ke mahaukaciyar inace? A hk zaki fita ko to wallahi ba inda zaki, har gaban Mamah ya kaita yayi mata fada yayi mata nasiha sosai har sai da tayi kuka sannan ya wuce ya bar gidan"





"Labeeb da labeeba ne suka shigo cikin gida da gudu daga school Shukrah da safeer suna zaune suna hira a parlour suka fado kansu"


"Labeeb cikeda ihu yace mamy kinsan yau me akayi mana a skul, Shukrah ta girgiza kai alamar a a, yace wild animal
1.LION
2.TIGER
3.LIZARD

Labeeba tayi Saurin katseshi tace mamy karya yake lizard reptilian ne, Labeeb da bayason raini ya buge bakinta yace waye makaryachi, ta bare baki zatayi kuka Safeer yayi Saurin cewa selfie🤳🏻 da sauri duk suka dawo bayansa ya kashe musu selfie kuwa"



" *ALHAMDULILLAHI*

*ANA NAKAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN DUK WANI KUSKURE DANAYI, READERS IDAN NAMUKU BA DAE DAE BA KUYAFE MIN, ALLAH YA YAFE MANA GABA DAYA*

*I DEDICATE THE WHOLE BOOK TO THE CHARMING, PIOUS, FAMOUS, GENTLE, TALENTED AND SUPER AMAZING SOUL MIEMIE BIE, MAY ALMIGHTY GOD DOUBLE FOLD YOUR UNDERSTANDING AND LEARNING, MAY GOD MAKES THE BEST OUT OF EVERY THING FOR YOU SWEETHEART, ILYSM BEYOND YOURS AND EVERY BODY EXPECTATIONS*


*CANT FORGET WITH YOU GUYS*

*ZEE ZEE (JEWEL)*
*SOFTIE*
*H. JIDDAH*
*SAFIYYA GALADANCHI*

*BILKISU GALADANCHI*

*EESHATULLAHI GONI*
*AUNTY SIS*

*LUBNAH SUFYAN*

*MEELA, MURJA TIJJANI DA*..

*AND THE REST DABAN FADOKUBA KNOW THAT YOU ARE ALWAYS IN MY HEART*

*YAN TASKAR NOVELS DA SHUKRAH NOVELS GROUP DA MIEMIEBEE NOVELS DA SHUKRAS KITCHEN DA EESHATULLAHI NOVELS DA KHALEESAT HAYDAR NOVELS KUNA RAINA*



*SHUKRAH YAR GATAN MIEMIE BIE CE KE MUKU FATAN ALKHAIRI*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login