Showing 1 words to 3000 words out of 61178 words

Chapter 1 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

 MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, maƙagin rayuwata. Wanda cikin ikonsa, yardarsa, amincewarsa tare da aron numfashin da ya bani na rubuta wannan littafin na MATAN AREWA. Bayan kammala littafina na SALON ƘADDARATA. Ina roƙon Allah da ya tsare mini hannayena, wajen rubuta abinda zai zamu cutar ga al'ummar musulmai tare da tarbiyar su.




Oh my fans i'm back no more waiting, ku shirya zama don ban zo da wasa ba, wannan karon salon na daban ne kamar yanda zubin labarin yake na daban kuma na mussamman, wanda suka karanta SALON ƘADDARATA da UWATACE SANADI shaidu ne akan hakan.




Page 0⃣1⃣


Hayaniyar da ya karaɗe yalwataccen filin tsakar gidan mu da carar da zakara ya tsala, su suka zamto ababen farkon da suka fara sallama a ƙofofin kunnuwana a wannan asubahin. Mirginawa nayi ina toshe kunnuwana da hayaniyar matan gidan mu, da ya zamto tamkar ibada idan har suka kuskurewa yin sa to sai in ba lafiya, suka cika mini ƙofofin kunnuwana. Kafin na miƙe ina sakin wata miƙa na fito daga ɗakin.


"Tun daren jiya Salma ta sanar dani ta ga shigowar Kubra cikin gidan nan, ina da tabbacin cewar a nan ta kwana. To menene abin ɓoyewa in ma sakin ta Habibun nan ya yi ai banga abi......".


Furcin Umman su Salma kenan da suka yiwa kunnuwana dirar mikiya. Yayin da nake ƙarisowa inda suke tsaye cirko cirko, duk sanyin asubahin da ake busawa hakan bai dakatar dasu daga fitowa daga ɗakunan su ba. Bata ƙarisa zancen ba Umman su Anty Kubra tayi hanzari faɗin"Bakinki ya sari gumtun kashi, karyar ki wallahi Hadiza dukkan mungun nufin ki akan ki zai juye ba akan ƴaƴana ba. In sha Allahu sai Mariya ta dawo cikin gidan nan tayi zawarci kafin Kubra tayi".


"Wannan kuma ƙarya ne hatta bokan nakin ya yi ƙadan wallahi, Mariya zama a gidan mijinta daram-daram, yanzu ma aka fara".


Sai da suka gama ciwa junan su zarafi, sai a sa'ilin Ummata da take tsaye daga gefe ta soma baki"Haba Umman su Salma menene amfanin hakan a gaban ƴaƴanku?, ku tsaya kuna ciwa junan ku zarafi. A kan maganar yaran da ba lalle bane ya zamto gaskiya ba".
Harara Umman su Kubra ta watso mata haɗi da faɗin"Malama waye ya saka dake balle ki ɗauki babban kashi?, ai bamu aike ki ba balle muga daɗewar ki, ko don saboda ba ki san ciwon ƴaƴa ba tunda ga zarkaɗeɗiyar budurwa kin garke ta a ɗaka har yanzu babu miji dole ki faɗi haka. Duk gidan nan an sawa ƴaƴana ido".


Dai-dai lokacin da lasifikan masallacin dake kusa da gidan mu suka sallame sallan asubahi, Abban mu da su Baba ƙarami suka shigo cikin gidan a jere har suna karo da juna. Ganin su ya sanya kowa shiga taitayinsa.


A zafafe Baba yake faɗin"To Allah yayi dare gari ya waye an fara sana'ar karnukancin ko?, ana sallan asubahi amma ku kuna nan kuna tada wa mutane hayaniya. Wai shi ku kam yaushe za kuyi hankali ne?, ga ƴaƴa guɗai-guɗai a gaban ku amma har yanzu baku san annabi ya faƙu ba, nasan duk wannan fitinar daga kece Zainabu".
Ya ƙarishe zancen cikin ƙololuwar ɓacin rai, yana nuna Umman su Anty Kubra da ƴar manuniyar yatsarsa.


"A'a kar ka soma ɗaura mini laifi, daga shigowar ka baka ji ba'asin abinda yake faruwa ba ka ce laifina na".


Gyaran murya Abba yayi yana ɗaurawa da cewar"Menene yake faruwa?".
Cikin zafin rai Umman su Anty Kubra take faɗin"Kama Hadiza da ɗiyarta Salma nayi suna gulmar Kubra wai ta kwana a gida".
Na lura sai a sannan duk idanunsu suka sauƙa akan Anty Kubra, da take rakuɓe jikin ƙofar ɗakin su, Baba ƙarami yayi mata wani kallo yana cewar"Ke Kubra meye kawo ki gidan nan?".


"Baba ƙarami mun sama saɓani ne dashi Habibun shine ya ce na taho gida".
Tsawa ya daka mata"ki tafi kai tsaye ki sanar dani abinda take faruwa kai tsaye, kafin nan kowa ya wuce yaje yayi salla".


Dukkan mu barin wajen muka yi, bayan an gama wurgawa juna harara da kallon uku saura kwata kowa taja zugar ƴaƴanta suka nufi ɗaka. Ummata da Anty Zakiyya muka shige ɗaki bayan mun ɗauro alwala muka yi sallan asubahi. Aikin daya kallafa a kaina na fito nayi na koma ɗaki nayi kwanciyata.


Gidan mu gidan gandu ne da ya haɗa dukkan ahalin mu waje guda tun daga kan kakanin mu har izuwa iyayen mu. Da kuma mu ƴaƴansu hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin matan gidan, da kuma gasa a tsakanin mu ƴaƴan dangin. Su biyar Abba suke a wajen iyayensu shine babba sai Baba sai kuma Baba ƙarami, ragowar biyun mata ne Goggo Suwaiba da Goggo Jummai da auran ta ya mutu ta dawo gidan da zama. Dukkanin su babu mai mata ƙasa da biyu Abba ne kawai mai mata biyu, Allah ya azurta dangin da yalwan ƴaƴa mata babban namiji Yaya Majid ne kawai sai kuma Nurain ɗan ɗakin su Anty Kubra, da bai wuce shekaru biyar da haihuwa ba. Mu uku ne a wajen Umman mu yaya Majid, Anty Zakiyya sai kuma ni, Daada kishiyar Umma ƴaƴanta uku ita ma Anty Maimuna, Anty Hasina da kuma Abasiya. Yayin da duk sauran ƴaƴan nasu Baba ƙarami da Baba ne.




Kawai gasa sosai a gidan mu da son ganin cewar kafi kowa. Al'ada ce a gidan mu duk wata ɗiya mace bata rufa shekaru goma sha biyar ake aurar da ita. Anty Zakiyya ce kawai ta kai shekaru goma sha tara ba a cikin ɗakin mijinta ba, hakan ya zamto abin tsegumi da yafice a tsakanin mutanen gidan mu. Abin nema ne ya samu wai matar ɗan doka ta haifi ɓarawo gori da shaguɓe babu irin wanda ba'a yiwa Umma da Anty Zakiyya ba.


Ina zaune a uwar ɗaka ina biya karatuna Umma ta dawo daga zaman da suka yi tare da su Abba, da kallo na bi ta har ta zauna kusa dani tare da cewar"Na'ima ki tashi ku tafi islamiyya ga can su Abasiya sun shirya".
Zumburo baki nayi gaba kafin na kai ga furzo zancen cikina, ta ɗaga mini hannu alamar bata son jin komai daga gare ni, na miƙe na fice daga ɗakin a tsakar gidan nake jiyewa kunnuwana dalilin zuwar Anty Kubra gida. Wai sunyi faɗa da mijinta ne ta turo shi ta saman bene ya karairaine.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciyar da ta tokare mini ƙirjina na sauƙe, ina ƙara jinjina lamari a raina duk irin romon soyayyar da Anty Kubra suka kwankwaɗa da yaya Habibu, a lokacin bikin su har wani ji da kai Ummansu ta ƙaro tana ganin Allah yayi wa ɗiyarta ilhama zata auri mai hannu da shuni mai gida da mota. Yanda suke soyayya abin zai ba wa kowa sha'awa amma yau ita ce da zuwan gida da sunan matsala.


Kwanon abincin da Umman su Salma ta dangwafa mini a gabana, na ɗauka na koma ɗaki kasancewar su Salman da muke ci tare yau kowa a ɗakinsu zata ci, nan na iske Anty Kubra zaune da Ummata gefe kuwa Anty Zakiyya ce tana naɗe kayan wankin da tayi. Gefe na samu nayi wa kaina mazauni ina kafe Anty Kubra da idanu da take maganar cikin zubda ƙwalla.


"Umma nasan kai kaɗai ce za ki gaya mini gaskiya a cikin gidan nan, wasu ma murnar dawowa na gidan suke yi. Dan Allah abinda nayi shine dai dai ko kuwa na aikata kuskure?. Umman su Na'ima da nasan haka aure yake da ban yi shi ba, akan gadona Habibu yake waya da wata yana faɗa mata wasu kalamai marasa daɗin ji da nauyi akan harshe wajen maimaitawa. Masu cike da batsa me na rage Habibu dashi da zai yi mini haka?".


Ta ƙare zancen tana kuma sakin wani kukan dake bayyanar da raunin dake cikin ƙalbinta, ina iya jiyo ɓoyayyiyar ajiyar zuciyar da Umma ta sauƙe kafin ta riƙo hannuwan Anty Kubra cikin nata ta riƙe sosai, kana ta soma cewar"Kubra shi aure ɗan haƙuri ne ko wacce kika ganta cikin ɗakinta har ta kai wani matakin da take burge ki, take baki sha'awa to haƙiƙa haƙuri shine tsanin da ya kawo ta wannan tudun. Kaso arba'in daga cikin MATAN AREWA su suke ɗaukewa kan su dukkan ɗawainiyar su da na ƴaƴan su, a gidan miji kama daga ci, sha da kuma sutura. Kaso ashirin na MATAN AREWA basa tarar da soyayya da kulawa a gidaden auren su, basa samun kulawa daga mazajen nasun saɓanin hakan ma sai dai a tarar da kishiyar hakan. Ki ga aure shekara ɗaya wani baya ma rufa shekarar an rabu. Kaso talatin na MATAN AREWA basa samun biyan buƙata na auratayya daga wajen mazajen nasun wannan dalilin ya sa matan aure da yawa zama karuwai a cikin gidajen su, saboda rashin sauƙe haƙƙi daga mazajen nasun. Kubra kar kiyi mamakin jin cewar cikin kaso ɗari kaso ashirin ne kaɗai suke samun kaso ashirin da biyar bisa ɗari na ababaɗen da na zayyano miki su".


Sai da ta sauƙe ƙatuwar ajiyar numfashi kana ta ɗaura da faɗin"Cikin wannan lamarin akwai rashin kyautawa daga ɓangaren Habibun, amma kema akwai laifin ki Kubra komai ya faru bai kamata ki ɗauki wannan matakin ba".


Langwashe ƙafafuna waje guda nayi sam na kasa kai koda loma ɗaya na abincin cikin bakina. Bana jin ko nayi yunƙurin hakan zai sama damar wucewa ta maƙoshina da nake jin yawun bakina ya ɗauke ƙaf. Tabbas MATAN AREWA na cikin wani yanayi mai wahalar fassarawa cikin kalmomin da fatar bakin kan iya furtawa, idan har a auren soyayya a na samun irin wannan matsalar to ina ga auren dole?. Tambayar da na jefawa kaina kenan da na gaza cimma amsarsa, har izuwa lokacin da Anty Kubra ta katse mini hanzari ta hanyar faɗin.
"To yanzu Umman Na'ima ta yaya zan kaucewa wannan matsalolin, da yake ciwa ko wacce mace daga cikin MATAN AREWA tuwo a ƙwarya?".


Murmushin su irin na manya Umma tayi kana ta ce"Kubra wannan dalilin ya sanya aka ce shi aure bauta ne na ubangiji, kuma hanyar da mace kan iya samun aljannarta matuƙar tasan abunda take yi. Duk wani abu mai muhimmanci ba'a samun sa cikin sauƙi, Allah ya ɗaga darajarki ta hanyar ba ki mijin aure yau ga Zakiyya nan babu wanda ya taɓa tsayawa a ƙofar gidan nan da zummar zuwa wajenta, ki nitsu kiyi tinani har ki gano matsalar ki ki gyara domin ta hakan ne kawai za ki gyara ɓarnan da kika yi".
Izuwa yanzu sosai hawaye suke gudu a fuskar Anty Kubra, ta buɗe baki da zummar faɗin zancen da ta maƙale a maƙoshinta. Ummansu ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo tamkar an cillo ta. Sai da ta ƙare mana tanadin kallo tsaf kafin ta wurgawa Anty Kubra dake durƙushe kusa da Ummata harara tana ɗaura da cewar"Ke kuma meye kike yi a nan?. Zan yi miki kashedin ƙarshe kar ki kuskura dai-dai da rana ɗaya kar ki yi gangancin tunkaran ɗaya daga cikin matan gidan nan da matsalar ki, domin dangin yanzu basa rufe kattara don haka tashi ki wuce mu tafi".


"Haba Zainabu ai ni da su Kubra da Na'ima ɗaya na ɗauke su, babu wani bambamci a tsakanin su".


Tsaki mai dogon zango ta saka tare da finciko hannun Anty Kubra da bata da niyyar tashi. Suka fice daga cikin ɗakin da hakan ya yi dai-dai da bugawan da ƙirjina ya yi da matuƙar ƙarfi tare da bada sautin ɗas ɗas ɗas.
Na kallo Umma na ce"Umma wannan haƙurin tun kafin auren Anty Kubra ake faɗa cewar shi zata yi a gidan aurenta in an kai ta. Shi rayuwar mace duk akan hakan yake kenan?".
Anty Zakiyya ce ta tanka mini a wannan karon, da tun ɗazu bata ce uffan ba"Na'ima bana son wannan yawan zancen nakin ki tashi ku wuce islamiyyarki". Ta faɗa tana yin kici-kici da fuska. Umma ta ɗan dara kafin ta ce"Barta Zakiyya ai tambayar abinda zai amfane tayi ita ma kwana nawa ne idan Allah ya fito mata da miji za ayi nata, kinga kuwa don ta tambaya ba zamto laifi ba".


Tunin naji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniya na tsani wannan furcin. Idan aka yi mini ita gusar mini da dukkan annurina take yi, ban sa ni ba ko don na taso ina ganin yanda sauran ƴaƴan gidan mu suke zuwa da matsalolin gidajen auren su babu ƙauƙautawa, hakan ya sanya aure ficewa daga raina oho.
Ƙananun maganar da Daada Umman su Abasiya ta fara wai na shige ɗaki nayi zamana, har suna neman yin latti ya sanya ni tashi na ture kwanon tuwon dake gabana na zara hijabina tare da ɗaukar al-ƙur'anina nayi wa Umma da Anty Zakiyya sallama na fito. Abasiya, Salma da Bilkisu da duk suke sa'anni na tarar duk sun gama shirin su.
Na iske Goggo Jummai suna ta mayarwa juna martani, da Umman su Salma wai akan ta zuba mata abincin karin bai ishe ta ba, tayi magana kuma ta gaya mata baƙar magana wai tunda ba gidan mijinta bane bata da wannan ikon duk abinda aka dafa aka bata kawai ta karɓa taci.


Sai da muka biya sashin Hajiya Babba kakarmu muka gaishe ta sannan muka fice izuwa islamiyyar safe da muke zuwa, idan na ce na gane abu guda ɗaya takamanme cikin abubuwan da aka koyar damu haƙiƙa nayi ƙarya, na kuma faɗi son raina ne kawai. Domin tunda muka je har aka tashe mu ban fahimce komai ba, hankalina duk yana ga tinanin da na dasawa raina na matsalar Anty Kubra.


Taɓo kafaɗata da Salma tayi ya sanya ni dawowa daga tunanin da na fara nisan kiwo a cikinsa. Na wurga mata wata uwar harara na ce"Menene?".
Cikin gatse da son maido mini da magana ta ce"Uwar meye kuwa? kawai munga muna ta zancen bikin mu ne ke kinyi shuru kin sa fa su Abba sun ce tare za'a haɗa mu. Ke har yanzu ko tsayayye ba ki dashi, ga Malaman Yusuf na ajin ku duk ya nuna miki alamar so amma kin tsaya masa wani jan aji".
Tsaki Bilkisu tayi cikin taɓe baki take cewar"Ƙyale ta bari ajin ya tsinke muga yanda zata yi". Hararar nima na maida musu dashi kafin na ce"Kwaji dashi don ni nan tinanin yanda zan tunkari su Abba da batun bokon da nake son......".


Tun kafin na ƙarisa naga duk sun tintsire da dariya har da riƙe ciki da tafawa, ƙololuwar gejin ɓacin rai suka kai ni a zafafe na ce"meye hakan ku kuma?, kuna tafe kuna wannan dariyar kamar sabbin shiga hauka".
Sai da suka tsaigata Abasiya ta ce"Ince kanki ɗaya ko Na'ima?, yanzu ke don ba ki da hankali da rashin kunya sai ki tunkari su Abba da zancen kina son kiyi boko? cab lalle kam".


"Kyale ta banda tsaurin ido irin nata, shi kuma auren jingine shi zata yi a gefe kenan ko meye oho mata".


Ɗauke kai nayi daga dukkan abunda suke faɗa, don yardan su Abba kawai nake buƙata. Duk cikin maganganun nasun babu wanda ya sosa mini rai kamar na Salma da take faɗin.


"To ban da abin ki Bilkisu meye don ta ce boko zata yi ba za tayi aure ba.tunda ga nan Anty Zakiyya ma har yau babu aure ai don ita Na'ima ta ce baza tayi ba, ba abin mamaki bane tunda abin daga na sama yake farawa yana bin ƙasa, har wanda suka biyo bayansa su ƙwaiƙwaya".


Sosai idanuna suka rufe bana da haƙuri ko kaɗan, domin bana barin ta kwana da an taɓo ni nake mayar da martani babu ɓata lokaci. Cikumo wuyar hijabin Salma nayi ina bin ta da ƴatsa domin bakina ya gaza furta mata koda kalma ɗaya ce. Da ƙyar Bilkisu da Abasiya suka ɓanɓare hannuwana daga cikumar da nayi mata, ina sakin ta ta fara tari babu ƙauƙautawa kallo ɗaɗɗaya nayi musu na ɗauki hanyar gida ba tare da na kuma waiwayar su ba balle jiran su, mu koma tare kamar yanda muka saba.


Matar Baba ƙarami ta biyu Umma su Anty Hajara da mu ke yiwa laƙabi da Hajiya, kasancewar ance kafin aurensu da Baba ƙarami tayi zaman saudiyya. Na iske a tsakar gidan tana wanki gefe guda kuwa Anty Jummai ce zaune ta miƙe ƙafafu ƙofar ɗakinta tana curin kalwarta, tana rero waƙar a kama sana'a mata a kama sana'a mata cikin ɗaga murya.
Ciki ciki nayi sallamar da ba lalle kunnuwansu su iya jiye musu ba, tare da yi musu sannu da gida na yi wucewa ta cikin ɗakin Ummata.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________


Page 0⃣2⃣


Ban iske Umma a ɗakin ba illa Anty Zakiyya tana tilawar karatunta, ko da kanta ban bi ba na faɗa kan gadon Umma nayi kwanciya ta. Duk tambayar da take jera mini akan lafiya ban amsa mata ko ɗaya ba, hakan nan hakan bai sanya ta ta daina ba.
Shigowar Yaya Majid yana tambayar ta meye ya faru, ta ce bata sani ba ya sanya shi daka mini wani gigitacciyar tsawan da ta haifar mini da kaɗawan ƴaƴan hanjin cikina. Babu shiri na tashi na zauna.


"Menene yake faruwa ana miki magana kinyi wa mutane banza?".
Cuno baki gaba nayi kafin na ce"Su Bilkisu ne suka ɓata mini rai cɗan ma na baro su a hanya?".


"Meye haɗa ku dasu?".


Ya kuma tambaya cikin tsare gida, na amsa da cewar"cewa suka yi wai babu wanda ya taɓa cewa yana son Anty Zakiyya gashi yanzu har ana shirin bikin su".
Ajiye alƙur'anin hannunta da yake neman suɓɓulewa gefe guda Anty Zakiyya tayi tana tallafo kuncinta da hannayenta, kafin ta kai ga sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi da ya tokare mata maƙoshi. Kallo ɗaya nayi mata na kawar da idanuna gefe guda, tunin kifiyar tausayin yanda ƙaddararta tazo ta harbi raina daren jiya duk rabin daren sallan dare take yi, a bayyana take addu'ar in akwai rabon yin aure a rayuwarta kafin ta koma ga mahaliccinta Allah ya fito mata da miji na gari.
Tsabar haushin da ya zarge raina ko tashi banyi ba balle na taushi zuciyarta, don gani nake yi da nata laifin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login