Showing 39001 words to 42000 words out of 61178 words

Chapter 14 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

jama'a. Daskarewa nayi a wajen sam na gaza taɓukawa kaina komai babu shiri juwa suka shammacin ƙafafuna da suke rawa tare da nuna butulcewar su ga ɗaukar nauyin gangar jikina. Idona ƙar akan Hanan da duk kamamninta suka sauya har izuwa lokacin da yaya Yusuf ya dawo da polices ɗin da case ɗin ɓacewar Hanan yake hannunsu, suna tafe su na shaidawa yaya Yusuf kuskuren da suka tafka na rashin sanar dasu tun farkon ganin ta.


Sai a sannan aka fara ba wa Hanan taimakon gaggawa, tunin likitoti suka rufu a kanta tare da iya ƙoƙarin ganin sun dai-dai fitar numfashinta. Suka bada tabbacin cewar fyaɗe aka yi mata cikin rashin adalci.


"Hanan! Hanan! Hanan! dan Allah ku kai ni na ga ƴata".


Furcin da ya fara fitowa daga bakin maman Hanan kenan a sa'ilin da ta buɗe ido bayan tabbatacin da likitoti suka bamu zuciyarta ta kumbura ta kuma kai matakin gajiya da aiki da tana cikin hatsarin bugawa a ko yaushe.


Anti Sadiya da Anti Zuwaira ne suka isa gare ta tare da kwantar mata da hankali ta hanyar sanar da ita Hanan na nan a raye. Da ido kawai nake bin ta ina jin nauyin da ƙirjina ya yi mini tamkar anyi mini dutsi mai nauyin gaske, raina cike da tausayin MATAN AREWA da fyaɗe ya zamto tamkar wutar daji ruwan daren da bai tsaye kan matashin saurayi dake kan ganiyar ƙuruciya ba balle tsohon da ya ba wa shekaru hamsin baya. Babu budurwa balle yarinyar da bata san kanta ba, an yiwa tsohuwa fyaɗe an tare ƴan mata a hanyar dawowa daga makarantu anyi musu fyaɗe, waɗanda suke killace cikin gida ma basu tsira daga wannan masifar ba balle waɗanda suka ke yawon titi da sunan talla. wai shin sai yaushe wannan abun zai zo ƙarshe?.


Tambayar da na jefawa kaina kenan, da na gaza cimma amsarta har izuwa lokacin da ihun da maman Hanan ta rangaɗa suka suyi wa ƙofofin kunnuwana sallama.
Yanka jiki tayi ta faɗi baya a sume bayan ta gama faɗin"Wallahi idan Hanan ta rasu, na gama aure da Auwal har abadan abada".


Ihun ƙwalawa likitan ƙiran da Anti Sadiya tayi shi ya sanya su shigowa a hanzarce. Da sauri na fice daga ɗakin ina tare ƙwallar da suka ciko koramar idaniyata, na samu wani wajen can na zauna naci kukana son rayina. Sai a sa'ilin naji sanyi a raina ko yaya na rufe idon Hanan nake hangowa wanke cikin ciwo wani rashin imani ne yake tasiri a zuƙatan al'umma da babu tausayi balle tsoron sanin ubangiji yana kallon bawa ko ina ya ɓoye kansa za'a hakkewa ƙanƙanuwar yarinyar kamar Hanan.
Sai da aka ƙwala ƙiran sallan zuhr na tashi daga wajen, domin gabatar da salla kiciɓus nayi da yaya Yusuf da yake shirin fitowa shima, ja da baya nayi don sosai yanayin da nayi tozali dashi suka ƙara jefa ni cikin tsoro da firgici.


Idanunsa sun ƙara ƙanƙancewa tare da rikiɗewa izuwa launin ja sosai, yanda ya datse leɓɓensa sai da nayi tinanin ya ɓula su don da matuƙar ƙarfi ya yi hakan. Babu shiri naji ya fizgo hannuna tare da ja na cikin sauri muka bar wajen bai tsaya ko inna ba sai bayan ɗakunan da ake kwantar da majinyata masu lalurar hawan jini kamar yanda idanuna suka hango mini rubutu a wajen.
Kujerun da suke shirye a wajen na ginin siminti ya saki hannuna ya zauna yana dafe goshinsa, danne tsoron dake taso mini nayi na zauna kusa dashi tare da aza hannuna bisa nashi dake dafe da goshinsa.


"Yaya Yusuf menene? dan Allah ka samarwa kanka nutsuwa ta hanyar ƙarfafa kanka akan wannan lamarin shima yaya Auwaln ɗin duk a ɗimauce yake. Wanda wannan wani hali ne da duk wani uban zai faɗa yayin da wannan ƙaddarar ta faɗawa ƴars..".
Yanda ya ɗago yana kafe da idanunsa suka tilasta mini haɗiye raguwar zancen ba tare da na furzo su wajen ba. Damƙar da ya yi wa hannayena suka ƙara girman tsoron dake raina cikin wata iriyar hargitsatstsiyar murya yake faɗin"Na'ima uba fa kika ce?, yaya Auwal bai cancanci amsa wannan sunan ba domin matsayin ne mai girmar da ba kowa yake amsa sunan ba. Har sai yaushe irin wannan matsalolin zasu kau a tsakanin ma'aurata?, Allah kaɗai ya san illolin da irin hakan yake haifarwa a tsakanin al'umma gabaɗaya. Allah ya ɗauki rayuwar Hanan shikenan kowannan su sai ya huta sun yi sanadiyar rayuwarta.
Ya ƙare zancen yana sakin hannayena. Ɗif abinda ke taimaka mini wajen yiwo sautikan zantukan mutane mabambamta ya daina nashin aikin, domin daga wannan kunnuwana basu kuma jiyo mini ko kalma ɗaya daga raguwar furcin da yaya Yusuf ya ɗaura dashi ba sai dai ganin bakinsa yana motsawa da hakan ya tabbatar mini da cewar zancen ya ɗaura dashi.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".


A faɗi cikin raina da yake mini soyar da ta sanya ni dafe saitin ƙahon zuciyata da yake harbawa da sauti da sauti. Sunkuyar da kaina nayi da hakan ya ba wa ƙwallar da suka wadaci idaniyata damar tsiyaya. Daga ni har shi babu mai lallashin wani domin kowa mabambamtan tunani ne cushe cikin ransa bayan raɗaɗin rasuwar Hanan da yake ratsa mu, a nawa ɓangaren takaicin al'ummar da nake rayuwa a cikin su ne da basu da maraba da dabbobi saboda rangwamen hankali da rashin tasirin imanin a ƙirjinansu nake yi, na shi ɓangaren kuwa bana raba ɗayan biyu takaicin yaya Auwal ne ke nuƙurƙusan sa bisa yanda ya nuna halin ko'in kula har wannan lamarin ya faru duk da kuwa ƙaddara ta rigayi fata kuma bawa baya gujewa ƙaddararsa.
Ƙiran wayansa a kai a kai da ake jeranta yi, ya sanya mu tashi muka koma cikin asibitin. Zazzaɓi mai zafi ya rufe ni a daddafe nayi sallan zuhr na haɗa da na asr domin lokacinsa ya gabato. Bayan sallan magrib aka yiwa Hanan sutura aka kai ta izuwa makwancinta har izuwa lokacin mahaifiyarta bata tashi ba domin ƙarfin allurar dake aiki a jikinta.
Sai asubahi ta farka hannayenta ta fara motsawa kafin wangale marafan idanunta da suka kumbura sumtim tamkar ƙwayoyin idanun zasu faɗo ƙasa.
Anti Zuwaira da wata ƴar-uwansu da tare tun maraice tazo asibitin suke ta yi mata nasiha tare da nusar da ita yarda da ƙaddara mai kyawu ko kishiyar hakan yana daga cikin cikar imanin mutum wanda dukkan mumunin ƙwarai ya kamata a same shi da hakan, ko da aka sanar da ita rasuwar Hanan ɗin idonta ɗaya ne ya zirar da hawaye kafin ta yunƙura ta tashi zaune daga kwanciyar da take. Idonta ƙaf ta kallo Anti Sadiya cikin dushashewar murya ta ce"Na sani damar rasuwa zata yi, naji a jikina shikenan hankalinsa ya kwanta ya yi min sanadiyar rasuwar ta. Ku tashi mu tafi gida ba zan iya zama cikin asibitin nan ba ba zan iya ba".
Yanda ta ƙare zancen ƙarshen cikin matuƙar ɗaga murya ya sanya Anti Zuwaira umarta ta da na je wajen likita na karɓo mata sallamar da ta buƙata, da rawar jiki na shaidawa likitan komai domin su yaya Yusuf basa asibitin suna can wajen karɓan gaisuwa. Tare dashi muka dawo ɗakin ya shaida mana cewar ba zasu sallame ta ba domin har yanzun lafiya bai wadace ta mussamman zuciyarta da ta kumbura akwai buƙata zamanta a asibitin tana karɓan kulawa da shawarwarin likitoti har izuwa sanda komai zai dai dai.
Yanda ta kuma birkicewa ya sanya shi dole rubuta mana sallaman, tare wasu magungun sai dai ya labarta mana cewar tana zuwa asibiti domin binciken lafiyarta. Waya nayi wa yaya Yusuf na sanar dashi ya ce muje gidan Anti Binta a can ake mata suke. Sai da muka fito daga asibitin maman Hanan ta dake akan ba zata koma gidan yaya Auwal ba daga nan sai gidan su, a wanna karon ta sama goyan bayan ƴan-uwanta domin na lura duk suma a fusace suke game da lamarin aihun. Hakan suka tari adaidata suka wuce suka barni a wajen tsaye kamar wacce aka sassaƙa, jan ƙafafuna nayi nima na nemi abin hawa ya kai ni unguwar Anti Binta gabana yana tsananta bugu.
Cincirundon ƴan-uwansu na nisa da na kusa na tarar a gidan, duk na bisu da gaisuwa yanda naga Anti Binta bata tambayen ni ina maman Hanan ba hakan ya ƙara tabbatar mini da hashashen zuciyata na cewar ta san komai. Wata zuciyar ta kimtsa mini ko ma yaya za'a yi baza ta sani ba.
Nan na kwana washe gari sai ga matan gidanmu sun zo bisa jagorancin yaya Yusuf Umma ke faɗa mini jiya da su Abba aka yi jana'iza, basu daɗe ba suka tafi jikina ya ƙara yin sanyi laƙwas yayin da na gani kuma naji yanda duk suke karkata laifin ga maman Hanan, tare da wanke yaya Auwal watau ita ce karkatacciyar bishiyar kuka mai daɗin hawa?. Sai da aka yi sadakan bakwai yammacin ranar yaya Yusuf ya ce na shirya zamu koma gidanmu, sai a lokacin na sama damar ganin autansu Mahmud wanda naji ance tun washe garin ranar rasuwar yazo. Mun gaisa dashi tare da jajantawa juna abinda ya faru sannan ya yi mana rakiya gida


MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________


Page 2⃣3⃣


Wani abu ne naji ya zarge mini ƙalbi da naga ƙofar maman Hanan da aka bugawa kwaɗo jikina duk ya mutu, na wuce ɗakina na ajiye kayana sannan na fito nayi wanka tare da ɗaura alwalan magrib nazo na gabatar da sallan na daɗe ina addu'ar nemawa maman Hanan sauƙi da sausaucin halin da take cikin domin nasan duk inda take tayi hannun riga da kwanciyar hankali balle samun cikakken nutsuwa. Ƙirjina ya buga da ƙarfi tare da bada sautin ɗas ina runtse idanuna, ina tinanin dalilin wanda ya aikatawa Hanan wannan rashin imanin ba tare da tunanin cewar akwai ranar da zai koma ga mahaliccinsa ba har ya yi masa hisabi bisa aiyukan da ya shuka a nan gidan duniya lokacin da yake raye. Jin gidan ya yi mini shuru sosai babu motsin maman Hanan haka nan yaya Yusuf da yaya Auwal suna can, Mahmud kuwa tunda ya rako ni shima juyawa ya yi tsoro sosai ya yi mini mamaya.
Miƙewa nayi na ɗauko wayata da na kashe ta tun kwanakin da suka gabata na kunnata, jikina na rawa na shiga lalumar lambar maman Hanan domin kawar da ƙishiriwar raina da yake ƙawata mini kwaɗaituwa da son jin halin da take ciki. Shigowar ƙiran Salma ya dakatar dani
kafin na ɗauka wayar ta mutu bayan ta nuno mini gargaɗi na gama zuƙe cajina. Wuf na fice daga ɗakin na jawo ƙofar na fito bayan shima ƙofar gidan na danna masa makulli na faɗa gidan maman Anwar don ba zan iya zaman gidan ba.


Sallamar da na shiga da ita bisa harshena ta amsa, na zauna saman tabarmar da na tarar da ita zaune a kai kana na gaishe ta ta amsa tana ƙura mini idanuna haɗi da cewar"Na'ima yaushe kuka dawo gidan?".


"Ɗazu muka dawo".


Sai da ta musguta tana ba wa wata matashiyar budurwar da na gani a tsakar gidan umarnin kawo mini ruwa, na hutar da ita ta hanyar faɗin alhamdulillah. Sam na kasa nutsuwa da zaman gidan sai dai dole ce ta saka hakan, domin ba zan fara gangancin saɓan ƙafata na koma gida ba sai yaya Yusuf ya dawo zancen da ta ɗaura dashi suka katse mini hanzari daga saƙa da warwaran da zuciyata take ƙulla mini.
"Maman Hanan kuma ashe gidan su ta koma?, naje har sau biyu nayi mata ta'aziyya".


"E wallahi tana gidansu".


Riƙe haɓa tayi"Lamarin nan sam bai yi daɗi ba ko kaɗan, Allah dai ya kawo daidaituwa in da rabon akwai sauran zama a tsakanin su Allah ya kawo sanadin da zata koma ɗakinta, domin ko zuwana na ƙarshen nan ta furta min ba zata komo gidan Auwal ba ta gama zama dashi har abada gwara ta ƙare rayuwarta gaban iyayenta ko da kuwa babu sauran maza a duniya sai shi".
Tagwayen ajiyan numfahsi na fesar ina ƙara lanƙwashe ƙafafuna wajen guda kafin nayi ƙarfin halin faɗin"Haka dai ta ce amma muna fatan gyaruwan lamarin tunda ƙaddara ce ta riga fata duk babu wanda ya yi tinanin faruwar hakan".


"Ai dama haka ne in Allah ya ƙaddaro abu babu mai canja faruwarsa, sai daga baya ayi ta tinane-tinanen daman kaza aka yi da kaza bai faru ba, Allah dai kawai ya sa mu dace".


"Amin".


Muka haɗe baki tare da budurwan wajen faɗi, da hakan ya sanya ni na cira kaina na bita da kallo daga ita sai ɗaurin ƙirji ta zage ƙarfinta yana wanki da hasken filillan da ya haske filin tsakar gidan. Wani mamakin ya cika ni domin a yanda maman Hanan ta sanar dani ba ta da ƴa mace gabaɗaya ƴaƴanta uku ne duk maza, ban bari nayi nisa da tunanin ba domin bana cikin sukunin yin hakan. A anan nayi sallan isha'i kafin wani yaro ya shigo ya ce yaya Yusuf ya mini magana sallama nayi wa maman Anwar na fice.


Ƙofar gidan na iske yaya Yusuf ya yi riƙo da ƙugunsa a sanyaye na isa gare shi bakina ɗauke da siririyar sallama. Shima ciki-ciki ya amsa sallamar tawan na zara ɗan makulli na buɗe gidan muka shiga kai tsaye muka wuce ɗakin. Ƙululu cikina ya bada sautin sakamakon tinanin da ya faɗo mini cikin kwanyata tamkar faɗuwar aradu tinawan da nayi cewar ban yi girki ba. Jin sautin muryar yaya Yusuf sun baƙunci ƙofofin kunnuwana ya sanya ni figigi na dawo daga wannan tinanin


"Zauna mana tinanin meye kike yi?".


Murmushin dole na ƙirƙiro kafin na ce"Girki zan ɗaura ne, tsoro ya hana ni zama cikin gidan ɗazu gashi wayata ta ɗauke babu caji shiyasa na shiga makwabta ban ƙira ka na sanar maka ba". Shima murmushin ya maido mini dashi haɗi da faɗin"kar ki damu girki kuma sai dai in ke kina jin yunwa don ni bana sha'awar ma cin abincin".
Zama nayi kusa dashi ina sauƙe wani gwauruwar ajiyar numfashin da ta tokare mini maƙoshi, sai da na fuskanto shi sosai ina karantar yanayin fuskarsa da ya jinginar da kansa jikin kujerar zaman mutum biyu da yake zaune kai, ya lumshe idanunsa har wani ƴar rama ya yi cikin kwanaki bakwai ɗin nan. Tausasa amon muryata nayi cikin sanyi nake cewar"Haba mijina duk wannan damuwar ta mecece?, dubi yanda ka koma cikin ƙasa da kwanaki bakwai. Dan Allah ko dan lafiyarta ka sausata ma kanka wannan tinanin". Watsu mini idanunsa ya yi, na ɗage masa nawa guda ina faɗaɗa zancen nawan"E lafiyata duk abinda zai shafi lafiyarka ai tamkar nawa ya taɓa".
Caraf naji hannayensa cikin nawa kafin ya jawo ni na faɗa ƙirjinsa lamau na kwantar da kai daga ni har shi cikin mu babu wanda ya ce uffan, illar sauƙar numfashi da fitarwa da muke yi a tare.
Haka muka zauna har zuwa wasu mintoti, muka yi shirin kwanciya bayan na tirsasa masa zuƙar ruwan shayi mai kaurin da na haɗa masa. Sai da muka jira dawowar yaya Auwal na jiyo muryar Mahmud da nake kyautata zaton cewar tare suka taho da yaya Auwal, kenan shima nan zai dawo da zama?.


Dawowar yaya Yusuf daga rufe gidan da ya fita yi ya sani kawar da zancen muka kwanta. Da ƙyar na iya tashi wayewar safiyar ranar sakamakon wani ciwon kai da na jiki da ya sauƙar mini da rashin kuzari a jikina ta yanda ko ƴatsar hannuna bana ƙaunar ɗagawa. Da taimakon yaya Yusuf nayi wanka nasha shayin da ya haɗa mini kana na kura magani. Dole na fito nayi dukkan aikin gida kamar yanda ya kallafa bisa kaina duk yanda yaya Yusuf yaso na koma nayi kwanciyata zai haɗa mana abin kari ƙiyawa nayi, domin ko ba komai yaya Auwal da Mahmud suna cikin gidan sai zuciyata take ayyano mini rashin dacewar haka su fito su iske shi yana aikace-aikacen cikin gida.


A daddafe na kammala girka mana dafa dukan tafiyar hausa, yaya Yusuf na biye dani tamkar inuwa domin ranar ko islamiyyar safe bai je ba, haka nan na lura bashi da niyyar zuwa ta bokon duk kuwa saboda rasuwar nan ya ɗauki hutu amma yau ne cikar wa'adin ƙarewar hutun kamar yanda ya furta mini. A haka na tusa abincin duk da bana jin ɗanɗanonsa bisa harshena sai don kasawa da tsarewar da yaya Yusuf ya yi mini akan lalle sai naci, sai hantsi ya fito suka fita tare dasu yaya Auwal izuwa gidan Anti Binta domin yin sallama da waɗanda suka zo ta'aziyyar da zasu koma.
Ina kwance tunani barkatai suna ziyartar cunkushashshen curin ƙaramar ƙwaƙwalwatar dake cikin ƙoƙon kaina naji yo rurin da wayata da ban daɗe da kunna ta ba ta tsala alamar tana neman agaji. Mirginawa nayi kafin na jawo wayar ba tare da na duba mai ƙiran ba na ɗaga tare da karawa a kunnena.
Muryar Salma cikin kuka da suka yiwa kunnuwana dirar mikiya suka sanya baccin idona wartsakewa saf, na tashi zaune a ƙoƙarin furzo mata tambayoyin da suke cike da bakina na datse harshena.
Muryarta ta kuma dukan zuciyarta, cikin tsanata kukan da take yi ta furta"Na'ima gani yanzu a hanyar zuwa gid..".


Ba ta sama damar ƙarisawa ba sakamakon wani kukan da ya turniƙe ta, tamkar kazar da aka jefa da gishiri haka nan duk jikina ya yi la'asar. Na shiga kokawa da numfashina da yake carkewa a iya ƙirjina kafin na sama zarafin faɗin"Lafiya Salma? ke da waye zaku zo ɗin?, ina Abdallahn naji ki kina kuka?".


A jere na jefa mata dukkan tambayoyin lokaci guda, ba tare da samar mata da wata damar da zata amsa ta farkon ba balle na biyu.


"Dogon zance ne Na'ima, nayi ta ƙiran wayanki bakya ɗagawa tun kafin na taho yanzu dai zan sauƙa a gidanki".


Iya abinda kunnuwana suka jiyo mini bakinta ya furta kenan, kafin na daina jin komai sai faman faɗin"Hello hello hello Salma kina jina?". Na ke yi kafin daga bisani naji ta datse ƙiran, haka na dinga ƙira amma bata ɗagawa bugun ƙarshe da nayi nayi wayar a kashe. Tunin naji ƴaƴan hancin cikina sun murɗa, ƙirjina ya shiga lugudan dukan tara-tara sau tara tamkar zai fito waje ya daka rawar disko. Dukkan raguwar kuzarin da ya yi saura ga gangar jikina ya kau na nema nutsuwata na rasa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login