Showing 18001 words to 21000 words out of 61178 words
Chapter 7 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt
yanda hakan ya zamto wata al'ada na ahalin mu, duk sanda aka tashi auren da ƴaƴa mata Hajiya Babba ita take ɗaukar nauyin yi musu gyaran jiki da wasu gyare gyaren. Kasancewar ta jinin kanuri gaba da baya.
Zuwan Goggo Suwaiba sai abun ya ƙara armashi, don sosai ake mana duk wani gyaran da ya kamata. Wanda bai wuce zarafi da cutar da lafiya ba. Duk muna zaune, yaya Majid ya bogo sallama zai shigo Goggo Suwaiba ta dakatar dashi.
"Malam dakata mana ai ba'a shigowa kai tsaye menene?".
Sai da ya dara kamin ya ce"To Malam Yusuf da Abdallah ne a waje suna son kallon amaran su".
"Yau naga ƴaƴan zamani kaje ka ce musu ba zasu sama damar gannin su ba suyi haƙuri".
Furcin Hajiya Babba kenan sai faman sababi take yi tsabar nacin tsiya ba zasu bari a gyara musu matan tsaf ba zasu zo su tsaye mata a ka. Duk murmusawa muka yi muna jiyo Goggo Suwaiba da take ba wa Yaya Majid saƙon yaje ya sanar dasu bayan magrib su dawo.
Sosai muka tsummu ƙiran sallan magrib da aka fara yi, ya samu miƙewa muka fice izuwa ɗakin mu alwala nayi. Nayi salla sannan na fito ɗakin Ummata tunda bikin ya rage saura sati biyu take yi mini nasiha haka nan ma yau ita ce ta ƙara yi mini, da ya haifar mini da tsiyayar da ƙwallar idaniya.
Na faɗa jikinta ina rero kukana tare da faɗin"Umma wallahi tunda aka sanya rana na da Malam Yusuf, na gaza samun nutsuwa naso sai an fara auran Anty Zakiyya kafin nawa. Amma haka Allah ya tsara zuciyata tafasa take yi inda na tina cewar na kusa tafiya na barta da zantukan mutan gidan nan da basu san ƙaddara ba balle suyi wa wanda ya faɗa kansa uzuri".
Bubbuga bayan ta soma yi cikin sigar lallashi a haka har bacci ya ɗauke ni, Koda Malam Yusuf yazo sashin Hajiya Babba na kai shi suka gaisa har da su Goggo Suwaiba, ɗaya bayan ɗaya matan gidan mu suka fara zuwa suna gaisawa kafin aka koma ga kan ƴaƴansu.
Daga nan sashin su Abba muka garzaya ya gaisar da su Abba. Umma kam fir taƙi yarda su haɗu, Anty Zakiyya kam sosai suka gaisa har faɗin wai ta damƙa masa amanata in yaci shi da mahaliccinsa.
Rakiya nayi masa ya ɗauki dubu biyar ya bani wai nayi hidimar walimar sauƙar mu, na nuna masa ya barshi kawai shi da yake da hidimar biki a gabansa. Yanda naga ya yi kici-kici da fuska ya tilasta mini amsar kuɗin.
Koda na koma gida na iske an kafa dandalin yi dani. Wai yafi ni kyau da aji nisa ba kusa ba ban tanka musu ba nayi wucewa ɗaki ina jiyo zancen da su Daada suke yi akan jinkirin kawo lefena da ba'ayi ba, kuma ya ce a shirye yake amma har yanzu shuru.
Wasa wasa walimar mu ta ƙarato. Duk munyi ankon atamfar da hijabi mun wanke kawunan mu, lalle ne dai kam Goggo Suwaiba ta ce kar muyi don ba zai fita ba nan da sati ɗaya har muyi na biki. Ranar sauƙar Abba, Baba, Baba ƙarami suka kawo shinkafa kwano biyar aka dafa, matan gidan mu da suka je suka taho dashi. Sosai walimar namun ta sama halaltar manyan baƙi, ciki kuwa har da mai martaba sarki da wasu jigajiga a gwammatin garin mu. Ni nayi ta ɗaya Balkisu na biyu sannan Salma. Abasiya kuwa tana cikin jerin mutane biyar da aka ba wa kyautar alqur'ani izu talatin, bayan na sauƙa da aka basu.
Munsha kyaututtuka daga baƙi su Salma ma duk samarin su sun zo, lattin zuwan da Sagir ya yi kuwa Abasiya har da kukanta muka ta yi mata tsiyar ashe duk zancenta ƙarya ne na ciki na ciki. Haka taro ya watse muka rabo cike da kewar yan ajin mu da duk suka yi mana alƙawari zuwa bikin mu, da yake sati mai zuwa in sha Allah.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1⃣1⃣
Daren ranar duk wanda ya gan mu sai ya yi sha'awar mu domin an ture komai a gefe. Kowa sai yi mana fatan alkhairi yake yi babu babba babu yaro, sauran yayan mu mata da suke gidan mazajensu na nisa har sun fara isowa Anty Hajara da Anty Maimuna, sai kuma Anty Hassana su kam tun yau suka iso. Ragowar ma duk sun halalci walimar tamun, amma sun koma gidan su sai ana saura kwana huɗu ɗaurin aure zasu zo.
Daren ranar Malam Yusuf yazo munyi hira sosai dashi har ya ƙira yayarsa a waya muka gaisa da ita. Don ya shaida mini cewar bashi da ƙanwa mace, su huɗu ne a wajen iyayensu da duk sun rasu yanzu.
Babbar su mace ce sai wansa da zamu zauna gida ɗaya da matarsa yaya Auwal sai shi sannan autan su Mahmud.
Kayan kataho kama daga kan gado da kujeru duk Abba da Baba ƙarami ne suka ya yi mana dai-dai ƙarfin su wanda kuɗin su bai wuce munzali ba. Ledar tsakar ɗaki dasu labulaye kuwa Goggo Suwaiba da Goggo Jummai ne suka yi mana, yayin da Baba ya sai wa ko waccen mu firig da keken ɗinki a cewar sa duk mu kama sana'a.
Hajiya Babba ta yi mana turaren wuta kuɗin sayan kayan kitchen kuwa kowacce sadakinta akan damƙawa uwarta, ta saya mata abinda ya kamata dashi. Nan hankali ya kuma tashi don duk cikin mu sadakin Salma ya ɗara na kowa. Ni kam ma har yanzu ba'a kawo leden ba . Hakan ya ƙara rura wutar tsegumi a tsakanin mutan gidan mu yayin da uwar kowacce a cikin mu fafutukanta bai wuce ace ta haɗawa ɗiyarta kayan kicin ɗin da ya zarce na kowa ba.
Da kuka naje wa Ummanmu sakamakon wata maganar da naji a masarrafar jina ta fito daga ɗakin Umman Balkisu. Wai wataƙil ma malam Yusuf ba aurena zai yi da gaske ba kawai wasa yake mini da hankali, in ba haka ba meyasa har yanzu ba'a kawo lefe ba balle a kai ga maganar sadaki, tunda mu a gidan mu duj tare ake kawowa. Kuma gashi ya nuna cewar a shirye yake.
"Umma na shiga ukuna zuciyata zafi take yi mini wallahi, wai shin da gaske Malam Yusuf ba da gaske yake yi ba?, yaudara ta kenan zai yi?. To ma meye dalilinsa na aikata hakan a gare ni?".
A jere na jefa mata tambayoyin, ba tare da na samar mata da wani damar da zata amsa mini na farkon ba balle na biyu duk na haɗe mata su.
Sai da ta fesar da numfashi mai ɗumi daga bakinta ta sausauta muryarta kana ta soma faɗin"Na'ima ki kwantar da hankalinki in sha Allahu komai zai daidaita, kiyi masa uzuri tunda ya furta cewar cikin satin nan za'a kawo to mu sanya ido mu gani".
Sai da na zuƙe majinar kukan da ta zo mini, kana na ce"Umma duk maganar da ake yi kenan a cikin gidan nan, ɗazu har Asma'u sai da ta jefa mini magana akan hakan a faƙaice".
Ina iya jiyo yanda ta sauƙe ajiyar zuciya a ɓoye, kafin ta ce dani"Kar wannan ya dame ki dududu kwana nawa ne ma suka rage miki a cikin gidan nan".
Saurin taran numfashinta nayi ba tare da ta dire zancen natan ba"To Umma ke da wasu kuɗin za ki sai mini kayan kicin?".
"Na'ima Allah zai yi kinji ki daina damun kanki".
Shuru kawai nayi ba tare da na kuma cewa da ita uffan ba. Domin ita ma kanta tasan da cewar a irin wannan lokacin ban da ikon hana zuciyata shiga damuwa game da wannan lamarin. Wunin ranar Abasiya bata zauna a gida ba domin sai jele zuwa kasuwa suke yi, Anty Maimuna ta tsaya kai da fata wajen sun kammala dukkan shirin su. Haka nan ma Balkisu Anty Hassana da wasu ƴan uwan Ummansu da suka fara zuwa suna tsaye akan lamarinta.
Kamar ko yaushe bayan sallan magrib yaya Majid ya ce dani Malam Yusuf na waje yana jirana, sai da na ɗan kimtsa kana na fita yana tsaye inda ya saba tsayawa jikin mashin ɗinsa. Na iske sa ya amsa sallamar da na isa dashi ɗauke a bakina cikin sakin fuska.
Tun kafin na gaishe shi ya marairaice fuska yana sauƙe ajiyar zuciyar da kunnuwana suka jiyo mini sautinta da ƙarfi.
"Maƙagin wannan zuciyar shi kaɗai ya san irin azabtuwan da tayi na rashin sanya ki cikin idanuna kwana biyu".
Duƙar da kaina nayi cike da jin kunyar zancensa na kaucewa maganar ta hanyar gaishe shi, sai da ya murmusa kana ya amsa.
Nan yake sanar dani cewar gobe in sha Allahu za'a kawo lefe, daman jiran zuwan wasu dangin mahaifiyarsa da suke nisa shi ya hana a kawo tuntunin. Tagwayen ɓoyayyun ajiyan zuciya na sauƙe, ina faɗi cikin raina an gama da wannan matsaalar.
"Allah ya kaimu, kuma Allah kawo su lafiya".
Na fara a zahiri ya amsa mini da cewar"Amin".
Shuru ya ɗan ratsa kamin ya yi gyaran murya ya ce"Ina son sai miki waya ko da ƙarama ce ta yanda zamu dunga yi magana da juna a kai a kai, kema ko kya huta da rubutun wasiƙa".
Babu shiri wata gajerar murmushi ta suɓɓuce mini, na kuwa yi ta don jin ya takalo abinda ba zai yiyu ba. Ban gama darawa ba ya katse ni ta hanyar cewa"Maganan tawa ce ta sanya ki dariya haka?".
Tsagaitawa nayi don dole na ce"To ai wallahi in dai wannan zancen ya kai ga kunnuwan su Abba sai an karairaya ni. Wai wai ai mu dukkan mu bama karɓa abin hannun saurayi ko da kuwa an sanya muku rana, a cewar su Abba ya tanada miki komai sai kin je cikin gidansa".
Jinjina kai ya yi"Madalla da gidan tarbiya tabbas hakan shi ya kamata, yanzu nima dole na ba wa tawa zuciyar haƙuri akan ta rage zumuɗi har a ɗaura sanda za ki shigo gidana a matsayin mallakina".
Na buɗe baki da zummar bashi amsa fitowar Abasiya daga cikin gida tana gaishe da Malam Yusuf ya sanya ni sararawa. Bata ce dani uffan ba nima ban yi gigin cewa da ita wani abun ba, tayi wucewarta sai yanzun na lura da Sagiru da yake tunkaro wajen cikin motarsa da fitillunta suka dalle ƙofar gidan mu.
Sai da ya gama daidaita parking nayi zaton shi zai fito sai nayi arangama da saɓanin tunanina. Naga Abasiya ta ɓalle marfin ƙofar ɓangaren mai zaman banza ta shige. Maganar da Malam Yusuf ya ɗora dashi da suka yiwa ƙofofin kunnuwann diran mikiya daga sama ya sanya ni figitit na dawo daga kallon da nake yiwa Abasiya har ta shige motar.
Sunkuyar da kai ƙas nayi ina sauraron ragowar zance da ya ɗaura dashi, ƙiran sallan isha'i da lasifikan masallacin kusa da gidan ya ƙwala ya tilasta mana yin sallama da juna. Duk da kuwa har raina ni naso hakan domin na tabbatar ko shakka babu Abba ko Baba ko Baba ƙarami ɗaya daga cikinsu ya fito ya iske ni da Abasiya duk muna tsaye da samari a ƙofar gida ranar ba mu ba hatta uwayen mu ma sai lamarin ya shafa.
Sam basa lamintar tara samari a ƙofar gida, in dai bai wuce mutum ɗaya ba amma ya zamana duk mu ɗin muna tsaye da samarin mu shine abinda suka yi hani.
Haka muka yi sallama da Malam Yusuf akan gobe danginsa zasu kawo lefe gidan mu, ina komawa ciki na sanar da Umma tayi murna sosai wanda baya rasa nasaba da farin-cikin da tayi tozali dashi malale a saman fuskana.
Haka nan ma Anty Zakiyya ta nuna zallar farin-cikinta, ciki kuwa ba ya yaya Majid da yake ta faman faɗin kalmar"Alhamdulillahi kwana biyu an canja daga maganar ki da ake yi lungu da saƙon gidan nan, kai Umma in dai haka wasu dangin suke babu rufawa juna asiri sai ma fatan sirrin juna ya tono Allah wadaran s....".
Saurin kwaɓan sa Umma tayi"Kul Majid kar na ƙara ji ka furta wani abun makamancin haka".
Shuru kawai nayi shima kenan da yake namiji wanda sai ya wuni baya cikin gidan. To mu kuma da muke zaune ko yaushe dasu fa?.
Wayewar safiyar ranar sosai gidan mu ya ƙara cika kasancewar lokacin biki sai ƙara gabatowa yake yi yau saura kwana biyar. Ƴan-uwan Umman ma da yawan su sun zo domin bata taɓa aurar da ɗiya ba sai a kaina hakan ya sanya su yi mata kara, kwan su da ƙwarƙwatan su duk sun zo.
Da yammaci sai ga ƴan*uwan Malam Yusuf a gidan mu, sun kawo lefe kuɗar da aka rankaɗa shi ya tabbatar mini da isowar su ina zaune daga cikin ɗakin. Zumbur su Salma duk suka miƙe suka fice wai zasu kallo.
Sashin Hajiya Babba aka kai kayan kamar yanda aka yi yayin da aka kawo na sauran, an musu tarba na ban girma da mutunci da suka tashi tafiya aka basu tukwuicin naira dubu goma.
Ina zaune inda suka bar ni zuciyata tana dakan lugudan tara-tara, Habiba ta faɗo ɗaki a guje harara na zabga mata"Meye hakan?".
Sai da ta mayar da numfashin gudun da ya taro mata, kana ta ce"Anty Na'ima kin ga kaya kuwa?, akwatuna masu taya har guda khuɗu danƙare da kaya".
Sakake nayi ina kallonta kafin na bata amsa Balkisu da Salma suka shigo.
"Kai gaskiya Malam Yusuf ya yi namijin ƙoƙari, wannan lefen kaɗai ya isa fayyace gaskiyar zancensa cewar a shirye yake".
Furcin Balkisu kenan kan na furta wani abun Salma tayi caraf"Gaskiya kam son barka wallahi akwati huɗu duk da kaya. Zannuwa fa sha takwas Goggo Suwaiba ta irga hijabai kuwa takwas cif, takalmi biyar ga sarƙa da ɗan kunne da ƙanana kaya ban da su kayan kwalliya kai tufarkalla".
Daɗi, farin ciki ko murna cikin ukun nan na gaza rabe wanne ne ya zo mini a wannan lokaci, kuka mai ƙarfi da ban san dalilin zuwansa ba na ɓarke dashi wiwi na shiga rero shi.
"Dalla banza kuka meye kike yi?".
Salma ta furta tana fizgo ni jikinta duk da yanayin da nake ciki hakan bai hana ni wurga mata harara ba ita ma ta rama.
Ranar naga tsantsan baƙin-ciki tuburan daga mutanen gidan mu, don kuwa babu wacce ta buɗi baki tayi wa Umman mu Allah ya sanya alkhairi.
Duk hakan bai ɗaɗani da ƙasa ba balle ya dame ni, kuka Abasiya tayi tsakanin ta da mahaliccinta wai a ƙira Sagir ace masa ko ya ƙara mata lefe ko ta fasa, domin daga lefen Salma da Abdallah ya yi mata akwatuna shida da wasu a baho har da na uwa da uba. Sai nawa domin Balkisu da Abasiya duk nasu uku uku ne, Daada da Anty Maimuna suka ƙwaɓe ta.
Washe gari aka je mana jere kowacce da dangin uwarta ake je gudun tsegumi amma sai da aka yi, har rigima aka so haɗawa tsakanin dangin Umman su Balkisu da dangin Daada.
Ana gobe ɗaurin aure su Abba suka haɗa mu gabaɗaya suka yi mana nasiha mai ratsa jijiya da ɓargo ta yi kane-kane cikin jiki. Haka nan ma Hajiya Babba tayi mana nata kafin Goggo Suwaiba da Jummai suka ɗaura dashi sa'an nan uwayen mu mun sha kuka har muka godewa Allah.
Da zazzaɓi na wayi gari ɗinkin leshi ruwan toka da zanen baƙi-baƙi Baba ƙarami ya saya mana aka ɗinka mana shi muka saka. Yayunmu matan suka haɗa kuɗi suka ɗauko mana mai kwalliya aka tsantsara mana, muka fito fes yaya Majid kuwa ya kawo mana mai hoto aka tayi haska mu. Ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka ɗaura aure a ranar su Abba suka ce kowacce za'a kai ta gidan mijinta. Laffaya Hajiya Babba ta ɗaura mana aka kai mu ga uwayen mu domin yi mana nasihar ƙarshe.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________
Page 1⃣2⃣
Sosai nake kukan bilhaƙƙi da dukkan gaskiyata ko kalma ɗaya na gaza furtawa illa kukan da na tsananta yin ta. Da ƙyar na iya ƙarfin halin faɗin"Anty Zakiyy...".
Ragowar suka maƙale mini a maƙoshi ba tare da na ƙarisa ba. Rungume juna muka muna sakin wani irin azababben kukan da ya ɗarsar da tausayin mu a zuƙata duk mutanen da suke wajen. Bamu taɓa rabuwa ba sai wajen kwana cikin mu babu wanda ya taɓa tafiyan kwana biyu, dukkanin rayuwar mu tare muka taso zaman kusa da kusa wai zaman gira da ido inji masu hikimar sarrafa zance. Amma yau zan tafi tafiyar da ake yi mini fatan zama dindindin sai dai mutuwa ta raba.
Tabbas aure yaƙin mata in ba shi meye zai raba soyayyar nan dake tsakanin uwa da ƴa. Ya raba ƙarfin ƙaunar dake sarƙafe tsakanin ƴan uwa.
Da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikin Anty Zakiyya aka fita da ni izuwa sauran ɗakunan matan gidan, ba yabo babu fallasa duk suka yi mini addu'ar zaman lafiya da samuwar zuri'a ɗayyaba.
Kiciɓus da muka yi da yaya Majid a ƙofar gida ya sanya hawayena ƙara ƙarfi ƙamar burɗaɗɗan famfo sosai shima ya yi mini nasiha, Dai-dai sa'ilin nan aka fito dasu Balkisu ma za'a kai su. Fizgewa nayi daga riƙon da yaya Majid ya yi wa hannunawa na isa gare su muka rungume juna sosai dukkanin mu muke sakin ƙwallar rabuwa da juna, duk da kuwa duk a garin za mu zauna. Salma ce kawai zasu wuce jahar mijinta kasancewar ba ɗan nan bane aiki ya kawo shi. Mun ɗau sakanni a haka kafin aka wuce da kowa ga motar da mijinta ya kawo domin ɗaukar amarya.
Yaya Majid ya sanya ni cikin ɗaya daga cikin motoci biyu da Malam Yusuf ya turo domin ɗaukar amarya.
Goggo Jummai da dangin Ummata mutane uku sai kuma su Habiba su kenan suka kai ni. Anty Zakiyya bata je ba saboda matsanancin kukan da take yi Goggo Jummai tance ta zauna kawai. Bani da yawan ƙawaye domin duk ƙawayen su Salma ne. Tsiraru daga cikin su muke zumunci dasu.
Har motar ta taka burki ban tsagaita daga kukan da nake yi ba wanda ya taimaka wajen ƙara sauƙar mini da wani zazzaɓi mai ƙarfi. Hannuna riƙe cikin na Goggo Jummai gefen haguna kuwa Adda Huriyya ƙanwar Ummata muka shiga cikin gidan, shigowar mu ta sanya matan da suka yi dandazo a gida sakin guɗa sosai, sai da aka fara kai ni