Showing 21001 words to 24000 words out of 61178 words

Chapter 8 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

wajen danginsa na uwa da uba da suka haɗo na gaishe su. Sannan wajen Babbar yayarsu Anty Binta kana ɗakin matar yaya Auwal ita ma muka gaisa sannan aka kai ni ɗakina.


Nasiha sosai suka ƙara yi mini tare da nusar dani cewar shi zaman aure ibada ne kuma ɗan haƙuri ne da kau da kai ga wasu abubuwan, samuwar hakan zai ya haifar da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata.
Duk tafiya suka yi domin su Abba sun ce kar wacce ta kwana a gidan amaran. Sun tafi sun barni da kewar su maƙil a raina ga zazzaɓin da yake ƙara ƙarfi a jikina. Matan da muka iske a gidan ma, a sannu suka fara watsewa na tabbatar da hakan sakamakon jin hayaniyar da ta ragu. Sannan Anty Binta ta shigo tayi mini sallama akan zata koma gidanta tare da wasu dangin nasun sai Allah ya kai mu ta dawo.


Ina zaune kaina ya ta'azzare ni da balaƙeƙƙen ciwon, naji zaman mutum a kusa na figigi na ɗago kaina domin sam ban ji shigowar sa ba sai zaman da ya yi.


Komar da kaina nayi na sunkuyar ban san dalilin zuwan wani kuka mai ƙarfi da ya kufce mini ba. Sosai yake lallashina da dukkan kalman da yake da yaƙinin za ta yayyafawa wutar dake ci a cikin ƙirjina ruwan sanyi. Tabbas Malam Yusuf ya cika cikakken masoyi domin da taimakonsa zazzaɓin da ya lulluɓe ni ya sauƙa mun gabatar da dukkan abubuwan da ake yi a ranar da aka kai amarya ɗakinta kama daga gabatar da sallar nafila domin nuna godiyar mu ga mahaliccin mu.
Wayewar garin ranar ba laifi naji sauƙi a jikina sosai. Ina yin sallan asubahi na gyara ɗakin tun kafin Malam Yusuf ya shigo don a falo ya kwana fahimtar da ya yi tsoro ya dabaibaye ni, kasancewar ban taɓa keɓewa da wani namijin ba balle kwana ɗaki ɗaya.
Tsaf na gyare abinda na taɓa na shiga banɗakin dake cikin ɗaki nayi wanka sannan na shirya cikin riga da zanin atamfata. Na zauna nayi zuru da idanu kewar ƴan-uwana ta hana ni sakat.
"Na'ima wannan kukan ya isa haka kinji ki daina in sha Allah za ki saba".


Muryarsa da suka dirarwa ƙofofin kunnuwana ya sanya ni ɗago kaina nayi masa kallo ɗaya, kawar da zancen nayi ta hanyar rusunawa na ce dashi"ina kwana an tashi lafiya".
Sai da ya faɗaɗa murmushinsa kafin ya amsa da"Lafiya ƙalau Amarya ya kwanan baƙunta?".
"Alhamdulillah".


Na amsa dashi ƙasa-ƙasa wanka ya shiga hakan ya bani damar fita falo na kimtsa ina gamawa sallamar da matar yaya Auwal ta shigo dashi suka ratsa ni. Murmushi muka sakarwa juna sai da ta zauna na gaishe ta, ta amsa sai zolaya na take yi wai ya kuka, murmushi kawai nake yi mata kafin ta fita ta shigo mana da abin karin mu.


Sai da ya shirya tsaf ya fito muka ci abincin tare yana ɗan jana da hira. Jin hayaniyar dake tashin tsakar gidan ya ƙaru ya tabbatar mana da ƙarin mutanen da suka cika gidan, su Anty Binta ne suka zo muka gaisa tare da yin sallama da danginsu da zasu koma yau. Zuwa ƙarfe goma ƴan gidan mu suka zo har da Anty Zakiyya, sun taho mini da ragowar kayana da ba'a taho dashi ba.
Mun sha hira sosai har da matar yaya Auwal Anty Habiba da ƴarsu ɗaya Hanan. Fitar Maman Hanan ya sanya wasu ƴan-uwana Abbana da suka zo ganin ɗakina kafa hirar cewar zaman da facala yafi zama da kishiyiyo gudu goma, a cewar su sanya ido, hassada da baƙin-ciki ne yake wanzuwa a tsakanin su wasu ma idan ba'a yi dace da matan ƙwarai ba har raba kawunan mazajen na sun suke yi.


Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ni kaɗai ina nazartar yanayin Maman Hanan da yanda ta tarbe ni da safiyar yau sai dai bahaushe ya ce yau da gobe shi ke sanya mutum sanin haƙiƙanin kowa da kowa.
Sai yamma lilis suka tafi haka aka jera kwana biyu kullum sai ƴan gidanmu da baƙi sun zo ban sa ni ba ko hakan ne ya rage mini kewar su da nake yi oho.


Satina ɗaya a gidan miji ban taɓa girki bakullum Maman Hanan ita take yi. Cikin ƙanƙanin lokacin da na zauna da ita na fahimci mace ce mai sauƙin hali sam bata da wani aibu ga ta iya zama da mutane, wani lokacin sai dai naji kunya domin kafin na tashi ta gama komai na karin kumallo sai dai na taimaka mata da shirya Hanan izuwa makaranta. Domin tare suke fita da Malam Yusuf kasancewar a makarantar da yake koyarwa take.
Tare muke cin abinci mazajen mu ma nasu tare. A falonta muke ci domin yafi nawa girma da fili, dukkan biyayyar aure da ladabi babu wanda bana yiwa Malam Yusuf, zaman lafiyan da ake wa ikirarin cewar yafi zama ɗan sarki muke yi a tsakanin mu.


Wata yammacin da na cika kwanaki goma cif sai ga Salma a gidan bisa jagorancin Habiba. Zumbur nayi ina sakin kwanon samiran da nake wankewa na rungumo ta cikin tsantsan farin-cikin ganinta.


Hannunta naja muka shige ɗaki bayan sun gaisa da Maman Hanan na kuma gabatar mata da ita, sam na gaza zaune balle tsaye tsabar murna na kawo mata ruwa da ragowa cincin ɗin biki da bai ƙare ba.


Furcinta da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya suka datse duk annurin fuskana.
"Ke kuwa Na'ima meye haka kike yi?, wai meye kika ɗauki aure ne?, bautar ubangijinki ko kuma bautar wata ƙatuwar daban?. Ashe duk zantukan da nake ji gaske ne wai tare da facala malam Yusuf ya ajiye ki. Ta yaya zaku more amarcin ku ga ɗakinki ga nata haba Na'ima har wanke-wanke kike mata?".
Da idanu nake bin ta har ta dasa aya tana yatsina fuska kafin na ce da ita wani abun. Habiba ta ɗaura da faɗin"Ai wallahi Anty Salma damma ba ki ji irin zancen da ake yi a gida ba, kowa tausayinta yake yi wallahi in kin ji yanda su Goggo Jummai suke fassara wuyar zaman da facala ba za ki fara amincewa ba wallahi".


Sosai naji na tsinci zuciyata a wuya wani miyau mai ɗaci yana game mini dukkan cikin bakina. Idanuna a ƙanƙance nake cewar"Ke Habiba dakata mini bana son rainin banzan har wani tausayina ake ji to akan meye?, akan na girmama zaɓin su na son ganin na fidda miji, sama burina nayin karatu?, ko kuma akan na yarda zan yi zaman aure na sama aljannata?. Duk wanda ya fasa jin tausayina bai burge ni ba ke kuma Salma kin bani mamaki".


Na ƙare zancen ina wurga musu harara kowacce da nata.
"To abin kuma haka ya zama?, to Allah ya ba ki haƙuri ni daman sallama nazo yi miki jibi in sha Allah warhaka mun ɗaga daga garin nan sai katsina".


"Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya".


Namm furta a gajarce don sun gama baƙanta mini rai duk yanda suka so ja na da hira rasa samun kaina suka yi, har suka tafi nayi musu rakiya na dawo. Sai da na cika sati uku Ummata, Hajiya Babba da ragowar matan gidanmu suka zo ganin ɗakin, maƙalƙalewa Ummata nayi cike da kewar ta. Da wayar Maman Hanan na ƙira malam Yusuf na shaida masa zuwan su nan take yazo suka gaisa da suka tashi tafiya ya ɗauki dubu biyar ya ba wa Hajiya su hau abin hawa.
Tun kafin su fice daga gida suka fara zancen da suka je gidan Balkisu ba haka Aminu ya yi musu ba, sha tara ta arziki ya yi musu kuma ya mayar da su gida a motarsa. Duk da naji amma ban nuna musu ba nayi musu rakiya zaure inda Umma ta ƙara yi mini wani nasihar bayan ta haɗe mu tare da malam Yusuf, godiya muka yi mata kana suka tafi.


Raba girki muka yi bisa shawarar Anty Binta da ba'a tsallake dukkan zancenta matuƙar ta furta. Tare mazajen mu suke cefenan girki kowa kowacce tayi bibiyu kafin ƴar-uwarta ta amsa.


MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


____________________________________


Page 1⃣3⃣


Abu ɗaya da na lura dashi shine daga yaya Auwal har malam Yusuf izuwa autar su Mahmud. Basa tsallake maganar da duk Anty Binta tayi wataƙil saboda kasancewar su marayu ita ce kamar uwa a gare su. Soyayyata ga karatun wanda babu algus a cikinsa, haka bai hana ni yin biyayyar aure ba
Zaune muke a tsakar gida tare da Maman Hanan dafe goshinta tayi tana faɗin"wash".
Na kallota cike da kulawa ina gyara zaman Hanan saman cinyata da nake yi mata tsifa na ce"lafiya kuwa?".


"Wallahi ciwon kan nan ya matsa min ina ga gobe dole naje asibiti ganin likita".


Sai da na murmusa kana na kuma faɗin"To Anty ko dai ƙanwa ko ƙani Hanan za ta zamu?".
Ita ma sai da ta dara sosai kafin ta tsagaita ta ce dani"Na'ima kena ke dai kawai ayi sha'ani, wataƙil har sai kin yi ƴaƴa biyu Hanan ba'a yi mata ƙani ba".
Saurin taran numfashinta nayi ba tare da ta dire zancen da ta ɗauko ba"Haba Anty ke kuwa meyasa kika ce haka?".
Sai da ta sauƙe wata ajiyar zuciya mai ƙarfi da sautinsa ya sauƙa a masarrafon jina kana ta shiga cewar"Na'ima kin gani nan shekarata huɗu da aure, watana goma cif a gidan Auwal na haifo Hanan. Yanzu shekaranta uku da watanni, tun bayan da na yayeta bamu ƙara haɗa shimfiɗa da Auwal ba, tun ina haƙuri da jarumtar jurewa ta hanyar in bai neme ni ba nima ba zan kai kaina gare shi ba, har na gaza kama kaina ni da kaina zan kai kokena gare shi amma ya yi biris da ni tamkar ayi wa dutse dundu. Na kai koke gida aka haɗa mu domin jin ko bashi da lafiya ne amma ya tabbatar mana da lafiyarsa garas wai kawai yana son bada tazara ne tsakanin Hanan da wanda zamu haifa nan gaba".a
Sai da ta numfasa tann tare ƙwallar da suka wadaci idaniyarta kana ta ɗaura da"Tun ina ƙarama mahaifina ya rasu, na taso ne da mahaifiya kawai duk kunyar dake tsakanin matan hausawa da sirikansu duk Innata ta jingine wannan gefe gudu, domin da kanta take karɓo wa Auwal taimako domin har yanzu taƙi yarda cewar lafiya ƙalau yake. Burinta a ko yaushe bai wuce ta gan ni ɗakin miji ba, abinda take guje min bai wuce zawarci ba".


Jin nayi duk wani gaɓar jikina ya yi sanyi laƙwas, zuffan suna keto mini daga dukkan mafitar gashin dake cikin jikina. Tabɗijam tashin hankali wai mai takaba ta taka gawa har yanzu ashe akwai irin Maman Hanan a bayan ƙasa?, matan da zasu jure wannan abun duk don farantawa iyayensu?.


Zancen da ta ɗaura dashi ya sa ni figigi na dawo duniyar zahiri daga na tunani da na fara zurmawa cikinsa.
"Mamaki kike yi ko Na'ima?".


Kaina na ɗaga mata don sam na gaza samun abinda zan ce da ita, murmushin nan da a kewa laƙabi da kafi kuka ciwo, raɗaɗi gami da ƙuna ta sakar mini kafin ta ce"ai ke dai kawai ayi sha'ani amma wallahi kin ji rantsuwa kenan ko akwai MATAN AREWA da yawa cikin wannan halin, wanda idan ba macen da imani ya kafu a zuciyarta ba sai ta kaucewa hanyar Allah ta faɗa bin maza alhalin da igiyoyin aure ɗauke a kanta".
"Amma Anty tabbas akwai cutarwa a cikin wannan lamarin, kuma ya kamata a duba halin da za ki shiga shekara uku ba kwana uku ko uku ɗaya bane, ya dace ayiwa tufkan hancin tun kafin kwaɓar tayi ruwa".


Taƙaitaccen murmushi kawai ta sakar mini ba tare da tace dani uffan ba, sai ma ƙoƙarin kaucewa zancen nawan ta da soma yi ta ƙarfi da yaji. Ganin kamar bata so ya sa ni yiwa bakina linzami sai dai bani da iko akan zuciyata da zan iya hana ta tinane-tinane game da lamarin. Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe ina kallon Maman Hanan ta gefen ido, tabbas sai yau na ƙara gaskaka wannan zancen mai cike da hikima akan zuciyar mace ta kan iya ɗauka da jure damuwar da namiji ba zai iya ɗaukar ta ba. Ta kan jure komai ta cigaba da gudanar da rayuwarta tamkar dai-dai take, ahalin ita kaɗai ta san sukar da zuciyarta take yi mata.


Har daren ranar bani da wani cikakken walwala ballle kuzari ya sauƙa a jikina, dawowar malam Yusuf daga masallaci isha'i ya sanya ni sakin murmushin dole ina yi masa sannu da zuwa murmushin shima ya maido mini dashi kana ya zauna na zauna kusa ƙafafunsa ina cire masa safar ƙafarsa.


"Amarya kuma uwargida kin tare gaba kin tare baya daga ke babu wata".


Ire-iren kalaman Malam Yusuf kenan da duk sanda ya ambata mini su suke sanya ni nishaɗi da ƙololuwar farin-ciki. Sai dai ban taɓa yaudaran kaina akan cewar ni ce ɗaya babu ƙarin ba balle har na zari dala babu gammo na ɗaurawa kaina damuwa haka siddan. Na san romon soyayya ce a yanzu take kwasar sa kuma take yin tasiri a cikin jikinsa, duk da kuma na tanadin dukkan sirrin biyayyan da zai ja da ran kwanakin aurena.
"Tashi ki zauna".
Ya ce da ni dai-dai sanda na kammala cire masa safan dake ƙafansa, kusa dashi nayi wa kaina mazauni ya ce na rufe idona ban yi musu ba na rufe idona kirif naji ya kamo hannuna ya ɗaura mino wata leda.


Cikin zaƙuwa da son ganewa idanuna menene na buɗe idona na fara buɗe ledar kwalin waya ce sabuwa gal nayi tozali da ita sai sheƙi take yi, duk da bata cika girma ba domin ƴar ɗanne ce tecno. Amma sosai naji daɗin kyautar karo na farko kenan da na mallaki waya ta kaina a rayuwata.


"Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi ya azurta ka da halal ya ƙara nisanta ka da haramun komai ƙanƙantansa, nagode yayana".


Sai da ya ɗan tsuke fuskarsa ya ce"ni kam in ce dai na hana faɗin wannan yayan ko?".


Murmushi na saka ina duƙar da kaina ƙasa tun bayan auren mu na tsiri ce masa yaya, tun baya amsa mini inna faɗa har ya fara amsa sunan.


"To ka fara amsa addu'ar mana".


"Ai na amsa a raina ji ne kawai ba ki yi ba".


Ɗan shagwaɓe fuska nayi hakan ya sanya shi saurin amsawa yana murmushi, tare da jawo ni kusa dashi sallamar yaya Auwal da kunnuwana suka jiyo mini ya sanya ni faɗuwar gaba, hirar mu ta ɗazu da Maman Hanan ya dawo mini cikin kunyata. Taɓo kafaɗana da Yaya ya yi ya sanya ni dawowa hayyacina ya ɗage mini ido ɗaya"lafiya kuwa?".
"Lafiya ƙalau".


Na faɗa ina dai-daita nutsuwa a ƙoƙarin tabbatar masa da zancen nawan na babu komai, sai da ya ƙare mini kallon tsaf kana ya ɗauke kansa muka cigaba da hira, nan nake shigar masa da kokena akan son zuwa gida ganin Ummata da Anty Zakiyya, ya bani tabbacin sai na cika shekara cif a ɗakin miji kana naje gida a al'adar hausa haka nan abin yake.
Zumɓuro baki gaba nayi har muka fita muka ci abinci muka dawo. Da damuwar halin da auren yaya Auwal da Maman Hanan yake ciki na kwana maƙale a raina, sam na gaza samun nutsuwa mussamman da muka raya darenmu tare da yaya sai wani tausayinta ya kuma yi wa ƙalbina lulluɓi.


Safiyar ranar daga masallacin sallan asubahi Yaya ya zarce islamiyyar safe, bai dawo ba sai ƙarfe tara tarban sa nayi cikin kulawa kamar yanda na saba na kai masa ruwa banɗaki ya shiga ya yi wanka kafin ya fito na fiddo masa da kayan da zai sa na ajiye masa akan gado. Da duk wani abunda zai iya buƙata na komo falo na zauna, ina latsa wayata da har da sim a cikinta lambar Ummata, Abba da yaya Majid da na haddace su na saka a wayar da burin ina saka kati su zan ƙira mu gaisa.
Fitowar Yaya ya sanya ni ajiye ta gefe guda ina masa sannu da fitowa abincin karin kumallo na gabatar masa domin na kari basa ci tare da yaya Auwal kasancewar shi ɗan kasuwa ne da wuri yake fita.
Tare da Hanan suka fita izuwa makaranta, bayan nayi masa rakiya zaure ina bin sa da addu'ar kariya. Shigowar Anty Binta ya sanya shi dakatawa daga fitar sai da suka gaisa kana ya fita, muka dawo ciki tare da ita na shimfiɗa mana tabarma a tsakar gidan duk muka gaishe ta tare da Maman Hanan.
Ta amsa idanunta suna kaina tar, tayi riƙo da haɓarta sai da ta kalle ni tsaf kana ta ce"Na'ima rakiyar mijin ne za ki bi shi har zaure?, wanna wacce irin mayitaccen soyayya ce?. Irin haka ai sai ki fita fit daga zuciyarsa shi ɗa namiji bai cika son haka ba, ban hana ki nunawa mijinki soyayya ba amma gaskiya na lura daga ke har shi zumuɗin ku ya yi yawa sai ka ce a kanku aka fara aure ko kune tattabu iyayen soyayya sai haka".
Tunin jikina yayi sanyi ta wani gefen kunya ta hana ni sakat wani ɓangaren zuciyata ta antaya tinani ko ta ga mun yi wani abun ne da ta fassara shi da rashin kunya?. Ban cimma amsar tambayoyina ba amon muryata ta koma dukan kunnuwana.


"Ke ce daman ban sama damar sanar dake ba, amma ita Habiba ta san komai bana ɗaukar rashin kunyar ƴaƴan zamani mussamman naku ke da Yusuf da soyayya take fisgar ku, don haka ku kiyaye".


A ladabce na ƙanƙan da murya na ce"In sha Allahu za'a kiyaye Allah ya huci zuciyarki".


"Amin".
Ta amsa a daƙile kafin ta ɓarke da tambayar shin kuna yi girki kamar yanda ta tsara duk muka amsa mata da e, nan ta wuni har sai da tayi sallan asr kana ta tafi duk wani motsinmu tana ankare dashi, da ta ga abinda bai kwanta mata a rai ba sai tayi magana kansa.


Bayan tafiyarta ina alwalan sallan magrib da ya gabato, Maman Hanan ta ce dani"Sai haƙuri Na'ima halin Anty Binta sai dai haƙuri, domin komai kika yi bakya yi mata gwaninta ba balle har ta furta miki kalmar yabo. Haka take ba'a burge ta, ai ke tayi sauƙi ma lokacin ki domin ni san da nake amarya ko amarci bata barni naci da Abban Hanan ba kullum safiyar duniya tana gidan nan".


Murmushi kawai nayi sakar mata"To Allah ya kyauta".
Ta amsa mini da"Amin". Ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login