Showing 42001 words to 45000 words out of 61178 words

Chapter 15 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

a haka har nayi sallan zuhr na haɗa wuta na tafasa mana doya fara nayi ƴar miyar tomatur da albasa marar wahala da ɗaukar lokaci, dai-dai ina kashe garwashin wayata ta soma ruri zumbur na shige ɗaki na ɗauko ta, Yaya Yusuf ne na ɗaga ina saisaita nutsuwata.


"Qurratul aynun ya jikin nakin?".


"Da sauƙi sosai yaya".


"Alhamdulillah dan Allah ki kula min da kanki kuma ki tabbatar kin ci abinci sannan kin sha magani, nima ba wani daɗewa zan yi ba zan dawo".
"To in sha Allah, Allah ya tsare mini kai cikin tsarewarsa ya kuma dawo mini da kai cikin aminci, ya kauda idon duk wata macen daga gare ka".


Na ƙare zancen ƙarshen ina sausauta muryata, ban yi zaton yaji ba sai ji nayi ya dara kana amsa mini cikin faɗin"Amin amin kar ki damu domin ko sun kalla ma ni ba zan san suna yi ba duk inda nake ke kike mini gizo a idaniya".
Murmushi nayi ƙasa-ƙasa kana muka yi sallama tare da datse ƙiran, alƙawarin da nayi wa yaya Yusuf akan zanci abinci shi ya sanya ni zubo doyar na tisa ta a gabana sam bana jin sha'awar cin komai.
Na ƙyar naci yanka uku ana huɗun naji sallamar Salma sun ratsa masarrafan ji na, kafin na miƙe har ta faɗo ɗakin. Muƙut na haɗiye doyar ina jin tana sukan maƙoshina tamkar wacce ta haɗiyi ƙarangiya.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


__________________________________________




Page 2⃣4⃣


Fit na fice daga ainihin hayyacina har mazari jikina yake yi nake duban ta duk ta rame ta lalace tamkar kazar mayu,da wasu haƙwaran da suka yo gaba a bakinta yangau kamar wacce tayi karo da mota. Duk fuskarta ta kumbure idanunta sun yi luƙu-luƙu, kamar zasu faɗo ƙas.


"Salma lafiyarki kuwa?, ke da waye kike tafe?, menene ya faru?. Ki sanar dani kin bar ni cikin duhu".


Ganin bata da niyyar amsa mini ko guda cikin jerin gwalon tambayoyin da na watsa mata, sai ma tsananta ƙafin sautin kukan natan da tayi da ya karaɗe dukkan kusurwan ɗakin bai ɗaya da tayi, kamo hannunta nayi na zaunar da ita kafin na fice a hanzarce na ɗebo mata ruwa na kawo mata da kaina na kafa mata a bakinta ta ɗan zuƙa kafin ta ture kofin tana janye bakinta.
Ajiye kofin nayi gefe guda ina mai ƙara fuskantar ta da kyau na ce"Yi maza Salma ki sanar dani abinda ya faru wallahi zuciyata harbawa take da sauri-sauri, a dalilin tozali dake cikin wannan halin da idanuwana suka aika mata". Rinannun idanunta da tsabar kuka har wani ƙanƙancewa suka yi suka ƙara zurmawa ciki ta kafe ni dasu, kafin ta kuma tuntsirewa da wani sabon kukan tana faɗowa jikina. Ban iya lallashin ta ba domin nima hawayen nake shara sai da muka yi muka gajiya don kawunan mu kafin nayi ƙarfin halin ɗago ta daga jikinta tare da tallafo haɓarta na furta"Sanar dani menene, domin bana son ki ba wa zuciyata gaskata hashashenta na saƙa mini rabuwa kuka yi da Abdallah".


Sai da ta fesar da zazzafan numfashi ta bakinta da naji ɗuminsa bisa kuncina kana ta ce"Abdallah ne Na'ima, ya cuce ni ya zalunci ni ya bar min tabo cikin zuciyata wayyo Allahna ina zan nufa da wannan abun?".
Sosai ta ƙara firgita ni gami da ruɗewa na cakumo ta na riƙe gam"Meye Abdallahn ya yi miki?, yana ina shi Abdallahn?, sannan menene dalilin wannan zuwan nakin?".




"Nima ban san inda yake ba, ban sani ba gidan iyayensa ya kai ni tahuwar nan ma da nayi basu sani ba domin babu iznin su".


"Ina ya tafi? menene dalilin kai ki gidan iyayensa bayan naji an ce ya yi ginin yayin bikinmu?".
Duk na gama hautsinewa ina ganin tamkar bakinta ba zai yi gaggawan samar mini da amsar tambayoyin da suke bakina ba cikin sauri, ji nake kamar ta buɗe mini zuciyarta na hango komai. Sai da ta zuƙe majinar kukan da suka taho mata kana ta ce dani"Haka ne ya yi gini sai dai gidan gadonsu ne ya gina shi da ƴan-uwansa aka wara masa nashi ɓangaren, wanda muka sauƙa a ciki da muka koma garin. Kwanan mu goma da komawa na fara fahimtar sauye-sauye daga Abdallah ko baccin kirki baya samu ya yi domin duk duhun dare na farka zan iske shi zaune ya zagba tagumi iwa wanda aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da uba, na tambaye shi yafi sau shurin masaƙi amma a duk lokacin da na jefa masa tambayar ko na nuna masa damuwata game da hakan, kalmar babu komai ita ce take fitowa daga bakinsa".
Sai da ta numfasa kana ta ɗaura da"Haka muka cigaba da zama wataran ya dawo ba tare da motarsa ba, da na tambaye shi dalili sai ya kada baki ya ce dani ya sayar da ita buƙata ce ta taso masa ta ujila. Daga baya ya umarci ni akan na shirya zamu je gaida iyayensa sai da muka je ya ce zan zauna nayi kwana biyu da yamma ya haɗo mini kayana ya kawo mini. Kwanana biyu tare da iyayensa wata yammaci ya turo mini saƙon cikin waya".


Daga hakan ta dakata, sai da taci kuka son rayinta hakan ta ɗaura daga inda ta dakarata"Na'ima kar kiyi mamakin abinda za ki ji bakina ya furta domin babu kuskure cikinsa. Duk abubuwan da Abdallah ya yi yayin bikinmu duk aro kuɗi ya yi kama daga kan lefe da ma komai gabaɗaya. Cikin saƙon yake shaida mini cewar wanda ya ranci kuɗi wanda zai iya kaiwa kimanin miliyan biyar sun matsa masa, har suna yi masa barazanar maka shi a kuto inda bai mayar musu da kuɗin su ba, dalilin hakan ya sanya shi sayar da motarsa gidanmu ma ya sayar da nashi ɓangaren. Ba zai iya zama ba don haka shi ya shiga duniya na cigaba da zama da iyayensa har izuwa lokacin da Allah zai nufe shi da samu wannan kuɗaɗen ya dawo gida. Wai alƙawari ya ɗaukarwa kansa cewar komai rintsi komai wuya sai ya aure ni kuma ya cika burinsa tunda na zamto matarsa".
Ƙara fashewa tayi da wani azababben kukan da suka ni na runtse idanuna da suka yi da suka yi mini nauyin gaske. Da ƙyar na iya haɗiye wani miyau mai ɗan karen ɗacin da naci ɗacin ya wanzu a dukkan kusurwan bakina. Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wasu mintotin da ba zasu gaza goma ba kafin na iya cira kaina haɗi da cewar"Menene dalilinki to na dawowa gida?, kin sanar da iyayensa hakan?".


"Ba zan iya wannan zaman ba, shiyasa zuciyata ta bani shawaran zuwa na sanar da nawa iyayen. Iyayensa kuma duk sun sani domin wani lokacin ma su suke tausa na a duk lokacin da na yunƙuro da nufin zuwa gida, ko tahowata yanzu ma basu da masaniya domin zagawa nayi kawai na zarce tasha na hawo mota da kuɗin wayata da na sayar cikin tashar".


"Tirƙashi wannan shine ana wata ga wata!. Lalle Abdallah ya ratsa yardar da yaƙinin da nake dashi a kansa, meyasa bai yi haƙuri da abinda Allah ya wadata shi dashi ba ya aure ki a hakan?, meyasa yazo miki ta wannan fuskar?".
Sai da ta sanya hannayenta ta tare ruwar ƙwallar da suka wadaci kurmin idaniyata kana ta sama zarafin cewa dani"Tambayoyin da nima kaina na gaza cimmawa kenan, meyasa Abdallah zai min hakan shin sanda zuciyarsa take kimtsa masa wannan lamarin meyasa bata yi min adalci ba?. Ta hanyar tinanin halin da zan iya faɗawa anya Na'ima ya san yanda nake son shi kuwa?, kayan lefena duk iyayensa sun sayar dasu a cewar su zasu rage bashin da ya ciwo haka nan ma kayan ɗakina duk sun sayar dasu su riƙe kuɗin, ban san meyasa ba ko Ummata na kasa sanar da ita sau da yawa na sha ƙiranta a waya da nufin sanar da ita komai sai naji tamkar an riƙe min maƙoshi. Ke ma na sha ƙiran wayarki bakya amsawa daga baya kuma a kashe, ke kaɗai zuciyata ta nutsu da na tunkare ki tare da neman shawararki tun gabannin tahowata Na'ima wallahi ina cikin matuƙar tashin hankalin da ban san yanda zan furta shi da kalmomin da bakin kan iya furtawa ba, meyasa Abdallah zai yi min haka meyasa zai tafi ya barni ni ba aurarriya ba ni ba sakakkiya ba".


Jinjina kaina kawai nayi domin ji nayi na rasa abin faɗi kan lamarin saboda ya girmewa kwanyata, tsoro da fargaba da tausayin al'ummar yankina da suka ɗauki aure tamkar wasar yara suka ƙara shige mini can ƙololuwar raina. Lallashinta na fara yi har dai na yi nasara ta tsagaita kukan da take yi tamkar ranta zai fita, hakan ya yi dai-dai da ƙiran sallan asr na zuba mata ruwa a buta ta fito tayi alwala sannan nima nayi, koda ta idda sallar raguwar doyan nan na ɗebo mata ta nuna mini sam ba zata iya cin komai ba, da ƙyar da suɗin goshi na samu taci yanka biyu ta kwanta saboda zazzaɓin ta sanar dani ya rufe ta.
Zama nayi jugum ina nazarce-nazarce cikin raina ni kaɗai, na saƙa wannan na ware wannan kafin na kai ga sauƙe wata ƙatuwar ajiyar zuciya.
Wai meye al'ummata suka ɗauki aure ne?, meye suka me da ita wasar yara koko karkatacciyar bishiya mai daɗin hawa?, da zaka hau ta a sanda kaso kuma ka sulo izuwa ƙasa yayin da kayi niyya. Anya maza sun san ainihin manufar addini da ya wajabta aure ga dukkan mai hankali matuƙar yana da hali domin kaucewa faɗawa haɗarin zina?, Da yawan samari gani suke su sauƙe sha'awarsu tare da matayensu da addini ya halalta musu shine kawai ma'anar aure, auren kawai ake yi kara zube tare da haifan ƴaƴan da za'a kasa ɗaukar nauyinsu balle har a gina su bisa kyakykyawan tubalin tarbiyyar da zasu zamto ababen alfahari tsakanin al'umma. Su waye suke da haƙƙin gyara wannan ɓarnar da ta zamto tamkar gobaran da ta faro daga teku maganinta Allah, da take ƙoƙarin cinye MATAN AREWA domin ruwan yazo musu har wuya suna linƙaya a cikin sa. Matan ne ko mazan ko kuma iyayen koko malamai suke da haƙƙin kawo gyaran game da wannan lamarin?.


Zancen zucin kenan da nayi nisan kiwo cikinsa, har kunnuwana suka kumurce daga jiyo sallamar yaya Yusuf. Sai da Salma ta taɓo ni na dawo a firgice.
"Ana sallama kamar malam Yusuf ne ko?".


"E shine".
Na faɗa ina miƙewa na fice daga ɗakin, na iske shi a falo sannu da zuwa nayi masa ya amsa mini kamar kullum fuskarsa yalwace da wannan murmushin da ya saba shigo mini da ita cikin gida yana tambayata yaya jikin nawan?.
Da kalmar "Alhamdulillahi" Na amsa masa ina miƙewa naje na kawo masa ruwa na zuba masa tare da miƙa masa ya karɓa sai da ya kurɓa ɗaya ya ce"Naga kaman gidan da baƙuwa shiyasa na dakata daga nan".
Sai da nayi nisa kana na ce"E Salma ce tana ciki".


"Ah Lalle kice mutanen katsina ne yau a gidan namun, tare suka zo da maigidan natan kenan?". Sai da na sauƙe numfashi na sama damar faɗin"A'a ita kaɗai tazo".
Ban sani ba ko yanayin da nayo maganar ce ta sanya shi saurin jefo mini tambayar"To lafiya kuwa naga kema duk yanayinki ya sauya?".


Ban ɓoye masa komai ba duk na zayyanu masa domin ko bai tambaya ba nima ina da tawa niyyar faɗa mishi. Musgutawa ya yi yana haɗe hannayensa waje guda kana ya ce"Tabbas Abdallah bai kyauta mata ba, kuma tayi kyan kai da ta garzayo domin sanar da iyayenta halin da ake ciki, domin shi ice tun yana ɗanye ake lanƙwasha shi idan ya bushe sai dai ya karye. Zan fita masallaci yanzu idan na dawo ma ƙarisa zancen daman nima akwai zancen yaya Auwal da maman Hanan da nake son mu tattauna a kai".
Fatan dawowa lafiya nayi masa bayan na gabatar masa da abinci ya nuna mini sai ya dawo zai ci, ya fice ni kuwa na koma ɗaki wajen Salma. Kumburarrun idanunta na zubawa ido da suke rufe kirif kafin na kai hannuna saman goshinta zafi gau jikinta ya ɗauka da hakan ya ke tabbatar da nisan da zazzaɓin ya yi a jikinta. A gaugauce na ƙira yaya Yusuf na sanar dashi akan ya taho mata da maganin zazzaɓi in zai taho.
Sai da aka yi magrib na tada Salma tayi salla tana kan sallayan yaya Yusuf ya dawo na amsho mata maganin tasha, sannan ta fito suka gaisa sosai ya bata wasu shawarwarin domin samuwar mafita game da wannan lamarin.
Nan ta kwana a cewar yaya Yusuf sai gobe muje gida gabaɗaya, Yau ma yaya Auwal tare da Mahmud suka dawo yaya Yusuf kuwa a falo ya kwana.
Ko da gari ya waye zazzaɓin natan ya ɗan sauƙa ba kamar daren jiya da ta kasa runtsawa ba, sai da na shawarce ta akan ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallan nafila ta miƙawa Allah kokenta. Tun kafin ƙarfe tara na gaba komai na kimtsa gidan tunin yaya Yusuf ya fice islamiyya daga can kuma zai tsaya boko, tare da Salma muka nufin gidan ni kam da niyyar wuni domin yaya Yusuf ya ce sai da yammaci in an taso daga islamiyya zai zo ya ɗauke ni muje gidan Anti Binta.


Har ƙofar gida mai adaidaitan ya sauƙe mu hannuwan mu sarƙafe cikin na juna muka shiga gidan, tare da sakin sallamar da Goggo Jummai da Umman su Anty Kubra suka haɗe baki wajen amsa ta.


"Salma sauƙe yaushe inji maƙi baƙo?".


Goggo Jummai ta furta da hakan ya jawo hankulan sauran yaran dake wasa filin gidan suka rugo a guje suka rumgume mu. Hakan ya sanya Umman Salma bankaɗo labule ta fito turus ta ja ta tsaye ganin mu tare.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________________




Page 2⃣5⃣


Tabbas na hange tsananin firgici kwance cikin idanun Umman Salma da na gaza rabe takamanman na menene. Na tozali da ƴarta cikin wannan halin na rashin nutsuwa ne ko kuma na ganin mu tare?.
"Ke Salma lafiya? a ina kuka haɗu da Na'iman?, yaushe kika zo garin? ko jiya na ƙira wayarki bana samu".


Ta kai ƙarshen zancen tana nufo mu, kuka Salma ta ɓarke dashi tana duƙar da kanta bisa kafaɗun Ummanta. Ɗago ta tayi tare da jan hannunta da ƙarfi suka shige ɗaki tare da bankaɗo ƙofar ɗakin ta rufe da ƙarfin da sai da ya bada wani sautin gam.
Sai da na sauƙe numfashi kafin nima naja ƙafafuna da suka sanƙare na nufin ɗakin Ummata, kusan karo muka yi da Anty Zakiyya tana fitowa daga ɗakin gani na ya sanya ta washe baki haɗi da faɗin"Ke ce tafe Na'ima?".
Kaina kawai na ɗaga mata na shige ɗakin, Umma na zaune bisa sallaya da alama sallan walaha ta iddar rusunawa nayi gabanta na gaishe ta, ta amsa mini cikin kulawa sannan na gaida Anty Zakiyya ma.


"Kamar sunan Salma naji an ambata ko?".


Anty Zakiyya ta watso mini tambayar sai da na langwashe ƙafafuna waje guda kafin na ce"e ita ce tare da ita muka zo". Zaburowa tayi tamkar wacce aka tsikara da allura ta ce"Ina kuka haɗu da ita ke ɗin?".
Dukkanin abinda ya wakana na baje musu, ina iya jiyo sautin ajiyar numfashin da Umma da Anty Zakiyya suka saka kusan a tare kafin Umma ta fuskanto ni da faɗin"Innalillahi lalle rayuwar nan ta ƙara zama abin ban tsoro, ƙarya ya yawaita gaskiya ya yi ƙaranci yayin da farashin tarbiyya ya yi tsada riƙon amana kuwa ba'a ta nasa. Dole Salma ta shiga cikin ruɗu tabbas".


"Wallahi kuwa Umma ba ki ga yanda duk ta fita hayyacinta ba duk a birkice take".


Haka muka cigaba da tattaunawa a tsakanin mu, ciki na shigowa Umma da zancen da muka yi da Hajiya game da Anty Binta tabbas na hango tausayi da zallar soyayyar da babu algus a cikinsa a cikin idanunta, ta kwanta mini da hankali sosai da har sai da na koka ga duk wanda ya yi rashin samun abokiyar koka matsalarsa uwa ta gari.
Sai da nayi sallan zuhr yaya Majid ya shigo muka gaisa dashi, mun ɗau lokaci muna hira dukkan mu kafin na miƙe na shiga sashin Hajiya Babba muka gaisa sosai taji daɗin gani na sai tambaya take yi yaushe zan fara zuwa makaranta. Murmushi nake sakar mata kafin na ce"Hajiya ai tukunna da ɗan sauran lokaci, sai zangon karatun nan ya ƙare sannan za'a ɗauki sabbin ɗalibai".
"Ah to masha Allah, Allah ya nuna mana lokacin muna cikin rayayyu kuma lafiyayyu".


"Amin amin Hajiya".


Nan na zauna har Baba ƙarami ya shigo ya iske ni na gaishe shi yana tambaya ta dalilin zuwana. Duƙar da kai nayi don haka nan naji na rasa ta cewa wani ɓangaren ina mamakin ta yanda basu san zuwan Salma gidan ba. Domin na tabbatar ko Hajiya ma bata sani ba domin da ta sani tabbas zata yi mini zancen. Ganin bani da wani zaɓin sama da na sanar dasu ya sanya ni faɗa musu komai sosai ran Baba ƙarami ya ɓaci ya fusata aihun fu ya fice kamar wanda iska yake jan sa ya fice daga ɗakin.
Da kallo daga ni har Hajiya muka raka shi, kafin ta shiga cewar"Allah dai ya sauwaƙa hali irin na Zinaru, ace har wannan abun ya faru amma ba zata sanar da uban yarinyar ba?. Waye zai tsaya mata in ba shi ɗin ba, duk lalacewar uba ai dashi ake ado ba da uwa ba".
Zugum nayi kawai ina jin sauran zancen natan suna sauƙa a kunnuwana tamkar busar sarewa. Miƙewa nayi na fice na koma sashin mu ina sanyo ƙafata idona suka sauƙa cikin na Umma Salma idonta ƙulu-ƙulu alamar ta sha kuka bisa masifar da Baba ƙarami ya balbale ta dashi. Harara ta zabgo mini haɗi da faɗin"Kin gama bin sashi-sashi ina yaɗawa?, Allah wadaran rayuwar da ɗan uwanka shine zai yayata sirrinka ga wasu baren".
Caraf na jiyo muryar Baba ƙarami daga bayana, ya fito daga sashin su ya amshe zancen da faɗin"Zinaru menene laifin Na'ima cikin wannan lamarin?, don ta samar mata da wajen fakewa a gidanta ko meye?. Kuma da kika maganar bare duk cikin mu nan waye bare?. Tun wuri ki dawo hayyacinki kafin ruwan da kike niyo a cikinsa ya cinye ki".
Yana gamawa ya kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login