Showing 12001 words to 15000 words out of 61178 words

Chapter 5 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

maƙasudin ta ba. Abu ɗaya da kunnuwana suka jiyo mini kafin su fara jin dishi-dishi shine furcin Daada.


"Yo wani dare ne jamage bai gani ba? ai duk abinda yake cikin ɗan tsako shaho ya daɗe da sanin sa, meye bamu sa ni ba kinyi ƙulle ƙulle Kubra za ta koma gidan Habibu ƙarki ta cimma ruwa".


Cakumo Ummansu Anty Kubra da bata raina ruwan shuka, haka nan bata barin ta kwana ta kaiwa Daada. Lokuta da yawa zafin ranta da rashin ɗaukar raini, ya sanya mutane da yawa tunanin ko ita ce mahaifiyata domin akan wannan halayyar munyi tarayya. Salma kawai na iske zaune bisa kafitarmu ta zagba tagumi da hannuwa bibiyu bamu kula juna ba nayi wa kaina mazauni can gefe.


A hankali na lumshe idanuna da suke mini wani iriyar zogi. Ina kamo duk wata addu'ar da taso bakina. Ko rufe idona nayi sai na hango kaina a matsayin ma'aikaciyar nan ta jarida kuma marubuciyar abubuwan da suke faruwa yau da kullum a tsakanin al'ummamussamman akan matsalar MATAN AREWA. Abinda ya daɗe yana nukurkusan rai da ruhina kenan, ina ji a jikina idan ban sama damar da zan amayar dashi ba, ba zan sama sallamar ruhi da kwanciyar hankali ba.


Ƙarƙarfan ajiyar zuciya mai bada zazzafan sauti na saka ina fesa da iska mai ɗumi daga bakina. Hayaniyar da ta sarƙafe a tsakar gidan har tana neman kai Ummansu Anty Kubra da Daada fitta da raini a tsakanin su, ce ta cigaba da gudana ina daga ɗaki nake jiyo tashin muryan Ummanmu tana aikin basu haƙuri, amma kamar tana yi da itatuwa don babu alamar ban haƙurin natan yana tasiri a gare su.


Sai da Baba ƙarami ya shigo ya daka musu birki, tare da kafawa Ummansu Anty Kubra zazzafan kashedin ta kama kanta, ta guji tasuwar wata fitinan dafa gare ta domin matuƙar hakan ya afku zata ga zahirin fushinsa da kuma abinda zai iya aikatawa. Ko wacce mata ta lafa don sosai ake ji shakka da tsoron Baba ƙarami fiye da su Baba da Abba.
Har aka yi sallan zuhr na kasa tsinana komai nazo a gani, komai cikin sanyin jiki da rashin kuzari nake aiwatar dashi, ina iddar da sallah na nufi ɗakin Umma na sanar da ita duk yanda suka yi da yaya Majid da matsayar da muka tsaya.


Banyi mamakin jin abinda ta ce ba domin dukkan wata uwa da ta tara ƴaƴa mata a gabanta, bata da burin da ya wuce aurar dasu ga mazajen ƙwarai.


"To Alhamdulillah Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin hakan, ita ma ƴar-uwarki Allah ya kawo mata nata rabon kusa".


"Amin amin ya Allah Umma".
Sai da na ɗan nutsa na ce"Umma ya maganar Maman Walida kuwa?". Sauƙe ajiyar zuciya tayi kana ta soma faɗin"Har yanzu dai maganar tana gaban mai unguwa zuwa anjima ma in sha Allah Abbanku zasu je. An kafa masa sharruɗan matuƙar ba zai ɗauki ɗawainiyyar da Allah ya wajabta masa ba na ciyar dasu, sufatar dasu, shayar dasu kula dasu in wata lalurar ta taso ba. To za'a raba auren kawai sai dai ita Maman Walidan ne naga kamar taba son hakan tafi ƙaunar cigaba da zama dashi cikin ƙunci da uƙubar iyayensa a gare ta".


Sai da na sauƙe abinda naji ya tukare mini ƙirji, na haɗiye wani miyau muƙut kana na sama sararin faɗin"To Umma ita kuwa meyasa ta zaɓawa kanta cigaba da zama dashi?".


"Na'ima kenan nima kaina wani lokacin ina ganin gaskiyarta rayuwar yanzu ya lalace, tarbiya tayi tsada ta kuma yi wahala yaya aka ƙare ma da ƴaƴan suna gabanka kana lura da shege da fitar su ma yaya balle kayi nisa dasu. Ai sai abinda hali ya yi babu tsayayyyen uba akan su balle danginsa su sanya idanu akan su. Yanzu da take nan ma ba sauƙe haƙƙin su yake yi ba balle a bayan idonta ai sai abinda ya wakana kawai. Amma duka har da yi mata tsirara a gaban ƴaƴanta kam ya zarce iyakarsa ya kuma kamata an fuskantar dashi girman kuskuren da ya yi".


Lankwashe ƙafafuna nayi waje guda ina sauraron Umma da kunnuwan basira, tunin curin ƙwaƙwalwar dake cikin kwanyar kaina take ba wa zantukan Umma matsugina tare da yi musu kyakykyawan haddan zama daram-daram.


"To Allah ya kawo mata sauƙi, Allah yasa mu dace".


"Amin".
Umma ta amsa dashi tana karkata akalan zancen natan izuwa faɗin, zata sanar dasu Abba game da zuwan malam Yusuf. Duk jikina mutuwa ya yi na miƙe da kunya na fice sumi-sumi kamar munafuka. Sai yamma na leƙa sashin Hajiya Babba na tarar da ita ta kishingiɗa ficewa nayi na koma namu sashin raina duk babu daɗi hakan nan na nema walwalata na tsawon wunin na rasa. Sai da nayi sallan magrib na fito na kamawa Umma wasu aiyukan da suka rage bata kammala ba, tare muka gama komai na girkin kasancewar Ummansu Anty Kubra ta gama nata kwanakin ya juyo ga Umma.
Sai da aka yi sallan isha'i aka raba abincin na fara ɗauka ina kaiwa ɗaki ɗaki, kasancewar ko wacce mata ware mata kwanonta daban ake yi don basa haɗuwa suci tare, kamar yanda mu ƴaƴan gidan muke ci tare da sa'anninmu. Wanke wanke kuwa kowa na ɗakin su yake yi ba'a haɗawa.


Na Hajiya Babba na kai a ƙarshe na tarar da ita tare da yaya Majid daga kallon ta ke bina dashi, hakan ya tabbatar mini da cewar Yaya Majid ya sanar da ita zancen Malam Yusuf, ban zauna ba ina ajiyewa na dawo ɗakinmu. Muka ci namu abincin tsaf muka yi shirin kwanciya, Salma tana zaune gefe guda ta takure kanta lokaci zuwa lokaci take miƙewa ta ɗauki madubi tana duban fuskanta zuwa wuyanta tana shafawa.


Balkisu da ta gaza haƙuri sai da ta ce da ita"Wai ke ɗin lafiyar ki dai ko?, tun ɗazu kin wani canja".


"Ko dai tunanin barin gida kika fara tun yanzu?".






Kanta kawai ta girgiza hakan ya bani damar cewar"To menene? don tun ɗazu da rana kike cikin wannan yanayin".
Sai da ta numfasa kana tac e"Abdullah ne".


Haɗe baki muka yi wajen faɗin"Menene ya faru basawa ya yi ko meye?". Shuru tayi da hakan ya sanya zuciyana zuwa wuya don ta kiɗimar damu, na cafko hannunta na ce"menene yake faruwa meye Abdallahn ya yi? ko wani abun ne ya same shi?".


Sai da ta ɗan yi nisa ta ce" ɗazu ne da ya zo zance yazo min da wani magana, wai gaskiya rama ta tayi yawa shi ya fi son mace mai ƙiba dole nayi ƙiba kafin a kai ga ɗaura aurenmu".


Sakake nayi ina bin ta da na mujiya har ta kai aya na sama damar faɗin"To ke kuma meye kika ce masa?".
"Na'ima meye kuwa zance dashi shi ne fa wanda zan aura na amsa masa akan zan yi iya yi na naga abinda yake so ya samu, amma na rasa wata hanya zan bi ko maganin ƙiba zan fara sha irin zumar nan?".


Abinda na gaza ganewa maganarta ta ƙarshen neman shawarin mu take yi, ko ko sanar damu matsayar ta take yi oho. Kafin nayi wata maganar Balkisu ta tari numdashina da cewar"Tabɗijam yau ina ganin abinda yafi ƙarfina".
Sausauta amon muryata nayi kana na ce"Salma ki kwanta da hankalinki wannan ba abinda za ki ɗagawa kanki hankali bane, ki sanar dashi cewar wannan abinda yake so ɗin ba za ki iya yi ba. Cikin sigar da zai fahimce ki to shi tun da can bai gano ramar takin ba sai yanzu. Da aski yazo gaban goshi? idan kika je za ki biye masa akan hakan to wataran ke kanki gabaɗaya ce zai ce ba ki yi masa ba to a sannan kuma sai kiyi yaya kenan?".




Shuru ya ɗan ratsa tsakani ina mai saka ran cewar kalaman nawan zasu yi tasiri, dan da dukkan alamu suna aiki a jikin Salman yanda tayi shurun nan. Doguwar tsakin da Abasiya tayi shi ya sanya ni kawar da idona daga karantar yanayin fuskar Salma da nake yi.


"Aikin banza ki biye mata ke kuma tunda ƙwaƙwalwarki an sanya dusa an toshe ta, har wani wai kice masa abinda yake so ɗin nan ba za ki iya ba, tana so dai ta guntule miki alaƙar nakun ne ki shekare a gida kamar yanda Anty Zakiyya ta share wajen zama a cikin gidan. Ni wallahi a yanzu da ake gab da sanya mana rana da Sagiru, babu abinda zai ce nayi wanda bazan yi shi ba don jina nake yi kamar matarsa".


Sosai maganganun natan suka dokin raina sai dai nayi ƙoƙarin danne zuciyata da take tafarfasa na kallota na ce"To ai idan har soyayyar da yake ikirari yana mata ba a iya leɓɓansa bane har zuciyarsa ya ratsa. Ba zai taɓa cewa da ita wai dole sai tayi ƙiba ko kuma dole tayi fari ba shi soyayyar gaskiya ba ruwansa da wannan".


"Ahayye nanaye to har ke me kika sani game da soyayya?, har yaushe kika samu wanda ya ce yana son nakin ma? ko daga safiya zuwa yanzu ne duk malam Yusuf ɗin ya koyar dake wannan karatun?".


Naso mayar mata da martani sai na tuna ko ba komai gaba take da ni domin Umma ta labbarta mini cewar kwanaki huɗu cur ta bani, ni kuwa ranar raɗin sunana aka haifi Salma, ranar da aka yi arba'in aka haifi Balkisu. Murmushin da naji ciwo da raɗaɗinsa ya ratsa dukkan jikina nayi mata kafin na maido da dubana izuwa Salma"To kinji dai nata shawaran, don haka ya rage naki ki ɗauki wanda kike ga zai zamto miki mafita".


Ina dasa aya a nan na miƙe izuwa ɓangarena nayi kwanciyata hawaye suna mamala daga idaniyata, ranar dukkan darena amfani nayi dashi wajen tsayiwar dare ina yiwa Anty Zakiyya addu'ar Allah ita ma ya fito mata da miji ko ta samu ta huta da wannan rayuwar.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________






Page 0⃣8⃣




Wayewar safiyar ranar na riga kowa tashi tsaf na kammala dukkan abubuwan da suka kallafa a kaina kana nayi shirin islamiyya.
Sai da na biya ta ɗakin Ummata na gaishe ta kana na leƙa ɗakin su Anty Zakiyya na tarar da ita tare da Anty Kubra, muka gaisa kana na fito wajen su Balkisu. Har mu kai ga ƙofar fita na jiyo murnar Umman su Anty Kubra sun sauƙa a kunnuwana.
"Ke Na'ima wuce ɗakin gwauruwar nan ki ƙira min Kubra".


Cak na tsaya,ɗ sai da na ɗauki daƙiƙu kana na waigo cike da rashin fahimta nake bin ta da kallo"wacece haka?". Sai da ta tsirka mini da wata tsaki mai dogon zango alamar a zuciye take kana ta ce"wace kuwa da ta wuce Zakiyya akwai wata gwauruwar ce da ta ɗara ta?. Ɗaki kowa ya watse ya barta ta mallake shi". Taƙaitaccen murmushin gefen baki nayi duk da naji zafin maganar natan ta ratsa ni, amma kaina kawai na jijjiga na wuce ɗakin Anty Zakiyya.


Har na sanya ƙafata ɗaya a cikin ɗakin na jiyo dariya da shewar da su Abasiya suka saka suna tafa hannu, ban jiwo ba balle idanuna su ƙara gano mini wani abinda da zai ƙara harzuƙa ni. Saƙon Ummanta na sanarwar Anty Kubra nayi ficewa ta na tarar da har sun tafi sun barni don haka ni ɗaya na isa islamiyyar.


Har an fara darasi sanda na isa aji, na nema izni daga Malam Yusuf kana shiga na zauna a wajen zamana na ko yaushe ina fitto da littafina daga jakata. Sosai na fahimta darasin na yau don duk wata tambayar da aka yi ni na amsata.
Yau ma sai da aka ƙara tattaunawa akan walimar sauƙar mu, domin sai ƙara gabatowa yake yi, ga mai rai kam ma ya iso.
Harhaɗa littattafan mu muka yi kasancewar lokacin tashi ya yi har na kai ƙofar ficewa daga cikin islammiyar na jiyo dirin mashi mai ƙafa biyun malam Yusuf. Ban waigo ba illa sausauta tafiyar tawan da nake yi, har ya iso sallama ya yi mini na amsa a hankali kana na gaishe shi.


Murmushi ya yi sai da wushiryar dake tsakankanin haƙwaransa suka bayyana kana ya ce"Naga ai mun gaisa a aji ko?".


"To ai gwara yawan gaisuwa da yawan faɗa".


Jinjina kansa ya yi"Bana son magana da mace a kan titi, kuma kema nasan hakan ba girmanki bane yaushe kike gida nazo?". Sai da na ɗan yi jim kafin na ce"Ni ko yaushe ina gida bama fita in ba islamiyya ba ko aike".


"To shikenan in sha Allah zuwa yamma zanzo".


"Allah ya kawo lafiya".


Da alama yaji daɗin gajerar addu'ar tawan da bata yawaita tsayi ba. Don har wani rausayar da kai ya yi kamin ya amsa da amin muka yi sallama, da mamakina na isa ɗakinmu ban tarar da su Salma ba, ban kawo komai a raina ba don tinanina ko suna ɗakin uwayensu.


Don haka na wuce sashin Hajiya Babba kamar kullum na iske ta kishingiɗe tana tasbihi da ƴan yatsun hannayenta.
"Takwara har kun dawo?".


"Haba Hajiya har ne ma?, ko don ba kike zuwa ba?".


"Har ne mana dududu awanni nawa kuke yi?".


Kawar da zancen nayi ta hanyar yin murmushi ina yin ƙasa da kaina, kafin na fara yi mata tausa a ƙafafunta a hankali. Cikin nutsuwa ta ƙira sunana na amsa kaina yana duƙe.


"Jiya Majid yazo min da wani zancen da ya faranta min zuci". Tunin na sha jinin jikina, na kuma gano inda maganganun natan suka dosa. Don haka na ƙara nutsuwa da bata hankalina sosai.
To menene haka kuwa Hajiya?".


Sai da ta ɓantari guntun goronta, da ta since daga bakin zaninta kana ta ɗaura da cewar"Zance ne akan ki da wannan malamin islamiyyar takun da nake jin sunansa a bakin su Balkisu. Yazo nan gidan ya bayyana manufarsa akan ki ga Majid, kuma in sha Allah yau iyayenku maza za'a sanar dasu domin a fara bincike a kansa".
Shuru nayi hakan ya bada dammr ɗaurawa da"Takwara ina fatan kema ki mashe shi hannu biyu-biyu, Allah ya sa ni da wannan damuwar nake kwana na tashi cikin raina, kullum du'a'ina bai wuce kema Allah ya fito miki da miji ayi tare da ƴan-uwanki ba sai gashi Allah ya amsa addu'ata".


Sai da na sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kana na ce"in sha Allah Hajiya zan amshe shi kamar yanda kuke so anjima ma ya ce mini zai zo".
Na ƙare zancen ƙarshen ina matse ruwar ƙwallar da suka ciko kurmin idaniyata, duk wannan abun da ake tayi babu wanda ya tambaye ni ra'ayi na game da wannan haɗin ko inna son shi ko bana son shi, ko zan iya zama dashi ko akasin hakan oho. Kowa kawai burinsa na amshe shi kar na zaune a gida kamar Anty Zakiyya.


"Masha Allah zamu tattauna da iyayen nakin".


Kaina kawai na ɗaga mata ina mai cigaba da yi mata tausan a nutse ta yanda za ta ji daɗinsa. Sallamar su Abba ya sanya ni watsa idanuna a ƙofar ɗakin har suka shigo dukkansu tare da Baba da Baba ƙarami suka zauna.


Sannu da shigowa nayi musu, suka amsa sannan dukkansu suka same daga kan kujeran da suka zauna suka gaida Hajiya, fuskarta kamar gonar auduga take amsa gaisuwar ƴaƴan natan cike da annurin da ya kasa gusawa daga kan kammalalliyar fuskarta.


"Daman yanzu nake son a aika Majid ya ƙira min ku, sai kuma gaku daman wata magana mai muhimmanci nake son mu tattauna tare".


Gyara zama duk suka yi suna sauraron ta da kunnuwan basira hakan ya bata damar ɗaurawa da cewar"Dama magana ne akan Na'ima".
Ina jin hakan na miƙe sumi-sumi zan fice, Hajiya ta ce na dawo na zauna tunda magana ake yi a kaina.


"Akwai wani yaro malamin islammiyarsu ta safe da yazo gidan nan jiya, ya kuma bayyanawa Majid cewar tayi masa inda za'a bashi dama tabbas zai aure ta, ita ma kuma ta amsa akan ya yi mata shine nake son ya gabatar da kansa a wajen ku ayi bincike. Idan an same sa da nagartattun halayya kuma ya sama shaidar ƙwarai daga mutane sai kawai a bashi damar tuto iyayensa ayi a wuce wajen".




Sosai Baba yake sakin hamdala wata na bin wata kafin Abba da Baba ƙarami suma suk amshe.


"Alhamdulillah masha Allah haka ake so ai idan ya ƙara zuwa sai kice dashi muna son ganin sa kinji ko?".


Kaina na ɗaga masa alamar naji sai da na nema iznin tashi daga gare su, kana na fice bayan Hajiya ta ce dani na ƙira Ummata tazo. Ɗakinta na nufa na iske ta da wata baƙuwa na sanar da ita ƙiran da Hajiyan take yi mata. Kana na koma ɗakin mu na zauna na daɗe a zaune ina saƙa da warwara a cikin raina, tare da tinanin makomar rayuwata da burin dake danƙare ƙasan raina.


Ganin zaman ba zai amfane ni da komai ba ya sanya ni tashi naje ɗakin yaya Majid. Nayi sallama yafi sau huɗu sai a an biyar ɗin ya amsa. Na shiga yana kwance ya na sauraron wayarsa saman katifar nasan na zauna kana na ce"Tun ɗazu nake sallanma baka ji ba na ma yi tunanin ko bacci kake yi".


"A'a ba bacci bane yi ba wallahi wannan program ɗin nake saurara, shi ya ɗauke min hankalina". Kaina nasa na leƙa wayar tasan wasu mata ne biyu sun sha ado, fuskarsu sai ƙyalli take yi an zirara musu irin kwalliyar nan ta zamani. Gefe kuwa wasu mutane ne uku biyu maza ɗaya mace. Ban san sanda na buɗe baki ba ina bin su da kallon sha'awa Allah ya sa ni ba kaɗan ba suka burge ni.


"Yaya Majid su wanene waɗannan?".


Sai da ya murmusa ya ce"Wannan ta farkon BADARIYYA TIJJANI ALARAWI kenan, mai jan mayafin kuwa MADINA ƊAHIRU MAISHANU sunanta, ƴan jaridu ne ma'aikatan shashin h Bbc hausa".


Kaina kawai na ɗaga masa kamar ƙadangariya har ya kammale zance nasan, na ƙara bin su da kallo lokaci guda ina ƙara jin soyayyarsu tana ƙara girmama da yaɗuwa a cikin raina, ban sa ni ba ko don ƴan jaridu ne abinda raina yafi soyiwa kenan a kaf aikin duniya. Kuma gasu mata jajirtattu akan aikinsu kamar yanda yaya Majid ya ɗaura da bani taƙaitaccen labarin su da irin aikin su.


Ƙwala mini ƙiran da Anty Zakiyya take yi shiya katse mana zancen na fita. Tunda nayi sallan asr bugun da ƙirjina yake yi ya tsananta da bansan dalilin hakan ba gabana sai faɗuwa yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login