Showing 33001 words to 36000 words out of 61178 words
Chapter 12 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt
muka biyo bayan sa iske matan gidan namun nayi suna zazzaune duk nabi na gaishe su suka amsa mini babu yabo babu fallasa.
Sashin su Abba muka nufa Hajiya Babba da su Abba, yaya Majid, Goggo Jummai da kuma Yaaya Yusuf muka tarar zaune.
Zama muka yi kafin Abba ya yi gyaran murya ta soma faɗin"Na'ima mijinki yazo mana da maganar komawar ki makaranta, bamu da ikon hana ki domin a yanzu addini ya fifita ikonsa akan ki akan namu. Jan kunne zan miki tare da gargaɗi Na'ima ki riƙe mutuncin kanki ki sa ni wannan damar kin same ta ta silar yardar mijinki, kar kiyi wani abunda zai rusa wannan yarda. Allah ya ba ki nasara".
Sosai jikina ya yi sanyi na amsa da amin can ƙasan maƙoshina, haka Baba da Baba ƙarami ma suka ɗaura da nasu nasihan kafin Hajiya Babba da Goggo Jummai ma suka yi nasu. Sosai duk nasihohin nasun suka ratsa jijiyoyin jikina sun yi mini fatan alkhairi sosai. Muka fito nayi mamakin yaɗuwar zancen tsakanin matan gidanmu.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 1⃣9⃣
Sai da muka yi sallan as a gidan, Ummata ta bani abinci da ruwan sha na kai wa yaya Yusuf da suke tare da yaya Majid a sashin Hajiya babba. Na kai musu na dawo na tarar da Anty Zakiyya ta dawo Umma sai faɗan daɗewa da tayi take yi mata tana bata haƙuri da faɗin cewar taje ta iske baaba Asaben ne kwance babu lafiya shine tayi mata wasu ƴan aikace-aikace.
Sai da na sanya baki Umma ta lafa, domin sanannen abu ne bata ƙaunar ta aike mutum yaje ya share waje ya yi zaman sa kamar an aiki bawa garinsu.
Zaman hira muka kafa da Anty Zakiyya na labarta mata komai. Iska ta furzar daga bakinta kana ta ce dani"Na'ima tabbas na taya ki murnar kasancewar wannan abun, amma kina ganin kamar wannan fushin Anty Bintan ba zai shafi zaman ki da Yusuf ba?".
Cire leɓɓana nayi da ƙarfi sosai na gaza samun amsar da zan bata domin kaf! tinanina ya ƙare. Ban kai ga cimma samun amsar ba ta katse ni ta hanyar ɗaurawa da faɗin"Shawaran da zan ba ki shine ki dage da addu'a babu dare babu rana, ki kai kukanki ga mahaliccinki ya ba ki sa'a cikin wannan lamarin".
"In sha Allah". Na furta cikin sanyin jiki da na murya hira ta fara jana dashi har na ɗan saki jikina cikin hirar take labarta mini cewar jiya Abasiya a gida ta kwana safiyar yau su Abba suka kaɗa ƙeyarta ta koma gidan Sagiru. Riƙe haɓa nayi cike da zallan mamakin da ya bayyana ƙarara a bisa fuskana na ce"Me yayi zafi kuwa haka?".
"A to kin sa Daada bata fiye son lamarin ƴaƴanta yana fita ba, don da ta zo ma ko su Abba bata sanar ba Anty Hasina ta aika aka ƙira mata a son ransu su kaɗai su rufe maganar babu wanda yaji, sai kuma Goggo Jummai tayi tozali ta ita. Ta kuwa hau yi musu bararara har dai zancen ya bazu. Wai taga saƙo a cikin wayar Sagirun an turo masa shine ta tada hankalinta tayi masa rashin ta ido shi kuwa ya mammake ta ya kuwa ɗebo ƙafarta ta zo gida".
"Tirgashi! ita kuwa Abasiya akan wannan har zata rashin hankali da zuwa gida, kamar bata san yanayin gidan ba daga aurenta ta fara zuwa gida da sunan matsala salon ayi ta yi da ita ana yanaɗiɗi".
"Ke dai bari ai kuwa dai sai dai kar a kuma, don wannan ya afku".
Shigowar Hanifa tana shaida mini wai Hajiya tana ƙirana ya sanya mu kallon kallo ga junan mu ni da Anty Zakiyya. Miƙewa nayi na biyo bayanta, muka yi kiciɓus da Umma ta tambaye ni inda zani na shaida mata ta ce naje na dawo don su yaya Majid suna waje suna jira na.
A uwar ɗanta na iske Hajiya zaune bisa bakin gadon ƙarfenta ƙiran zamanin da, na zauna akan ledar dake malale a tsakar ɗakin na ce"Gani Hajiya an ce kina nema na".
Musgutawa tayi tana naɗe hannayenta waje guda kafin ta furta"Na'ima daman na ƙira ki ne akan wani zancen da naji yana yawo cikin gidan nan, wai mijinki ya amince miki za ki koma makarantar boko iyayenku maza ma duk sun ba ki goyan baya".
Shuru ya biyo bayan maganarta ta ƙarshe, na rasa gano inda maganganun natan suka dosa. Sai da ta ɗan zame daga zaman da tayi ta kuma cewar"Na san Binta ƴar su Yusuf mai gidanki da daɗewa nayi mata farin sani ciki da waje, a da can ƙawata ce na ƙut da ƙut halayyanta ya sanya ni janye jikina daga gare ta. Amma ko aurena na fari ita tayi min babbar ƙawa dawowa na daga saudiyya muka raba gari da ita, Binta shu'umar mace ce ta ajin ƙarshe wacce idan ta ƙwallafa rai akan abu to babu abinda yake dakatar da ita sai ta cimma burinta ko da kuwa zata haucewa hanyar Allah, na sama labarin cewar bata amince da wannan karatun da za ki koma ba a bakin mijin nakin yana sanar da Majid har yanda ya shawo kanta. A yanda na san Binta ba za ta taɓa sakar miki mara kiyi fitsari ba sannan ki bar murna don karenki ya kama zomo bar ganin Na'ima an yi mata fin ƙarfi ta amince na tabbatar da walakin goro a miya, taja da baya ne ba don ta gaza ba sai don ƙara yin wani sabon shirin".
Dam-dam ƙirjina ya bada sautin ɗas ɗas ɗas, kafin na zame na zauna dirsham a ƙasa tallafe da kuncina sam na gaza furta komai har sai da ta dafa kafaɗata ta furta mini abinda ya ɗan sanya ni jin sausaucin wutar raɗaɗin dake ruruwa cikin zuciyar dake kwance ƙasan ƙirjina.
"Ba na gaya miki hakan bane don ki tashi hankalinki, ko kuma don na tarwatsa ƙwarin gwiwan da kike dashi akan lamarin nan. Na sanar dake haka ne domin ki shiryawa komowar Binta gare ki daga ke har mijinki. Za ta iya aikata komai akan wannan ƴan-uwan natan ba, babu abinda zai gagare ta aikatawa wajen ta karkato da hankulansu sun yi mata biyayya ko da ba'a son rayukan su ba, ki sanar da Ummanki ita ma ta taya ki da addu'ar Allah ya tserar dake daga kaidin Binta".
Sosai dukkan wasu gaɓoɓin dake jikina suka yi sanyi laƙwas, tamkar wacce aka bi dukkan sassan jikinta aka sassara da adda. Cikin ƙarfin hali na cira kaina tare da jefa ƙwayoyin idanuna cikin na Hajiya na fizgo numfashina kafin na sama sararin faɗin"Na gode Hajiya tabbas kin sanar dani babban lamari a lokacin da ya dace, sai dai kaina ya kulle menene zai sanya ta aikata dukkan wannan abun?".
Sai da ta saki wani gajeren murmushi kana ta ce"Na'ima har yanzu ke yarinya ce ba ki gama sanin me rayuwar duniya ta ƙunsa ba balle kisan inda ta dosa, Binta ta wuce dukkan saninki sannan akan ƴan-uwanta babu abinda baza ta iya aikatawa ba. Da babu wanda ya yi tinanin cewar zata bar su har su kula mace balle a kai ga yin aure har su tara iyali, bata yarda da kowa ba akan wannan ƴan-uwan natan matuƙar kuwa mutum ya raɓe su to daga sannan zata sanya ido sosai akan sa".
Shuru nayi ina nazarin zantukanta da har yanzun suke yi mini amsa kuwa cikin masarrafun jina, tabbas zantukanta suna kan turba musamman da nayi la'akari da yanda take juya komai na cikin gidan ba ma kamar sha'anin Yaya Auwal da maman Hanan. Autan su Mahmud kuwa ban taɓa ganin sa sai sau ɗaya da yaya Yusuf ya nuna mini shi a hoto domin yana can sudan yana karatu ko bikin mu ma bai zo ba. Tabbas akwai ayar tambaya kan wannan batun, sallamar Nurain shi ya katse mini hanzari na dawo duniyar zahiri daga na tunanin da nayi nisan kiwo cikinsa.
"Anty Na'ima wai ki fito inji yaya Majid".
Iya abinda ya ce kenan ya ruga a guje ya fice yana baran lemon dake hannunsa da yaya Yusuf ya kawo. Cikin ladabi da girmama ƙaunar Hajiya gare ni nayi mata kyakykyawan godiya da addu'o'in gama da duniya lami lafiya sumul, ƙwarai na hangi tsagauron tausayina cikin idanunta da hakan kaɗai ya ishe ni samun tabbaci akan duk zancen ta ta faɗi mini game da Anty Bintan. Har ƙofar ɗakinta ta biyo ni tana yi mini fatan alkhairi cikin karatun da zan fara ganin mu a haka shi ya jawo hankulan sauran matan gidanmu kamar mayen ƙarfe izuwa gare ni suna taɓe baki, sallama nayi musu azalzalan da yaya Majid yake ta fama yi mini akan na fito mu tafi shi ya hana ni samun damar zama da Ummata balle har mu tattauna wannan gaggarumar matsalar da ta gusar mini da dukkan nutsuwa da kwanciyar hankalina.
Har muka isa gida bana fahimtar hirar da yaya Yusuf yake yi mini, wanda bana raba ɗayan biyu na murnar samun cikakken goyan bayan mahaifana ne don yanda bakinsa ya kasa rufuwa fara'a tamkar gonar auduga. Ban mu iske maman Hanan ba domin ƙofarta har an saƙala kwaɗo Hanan kuwa ta tafi islamiyya. Ranar gabaɗaya yaya Yusuf bai je islamiyya ba ruwan wanka na kai masa ya yi wanka sannan nima na shiga. Tare dashi muka ɗan kimtsa gida sannan na fara haramar ɗaura mana girkin dare yana daka mini albasa da attaruhu.
"Za'a yi jarabawar tantance malamai in sha Allah wani sati sannan wanda suka cancanta za'ayi musu ƙari girma a taya mu da addu'a".
Sai da na jinjina kaina na ce"Masha Allah, Allah ya taimaka Allah ya yi jagora. Tabbas zaka tsallake dukkan wannan jarabawan domin na san nawan gwani ne ko a cikin aji". Murmushin jin daɗin addu'ar tawan ya yi ya amsa da"Amin amin ya Allah ƴar aljanna, in sha Allah da zaran zangon karatun ya ƙare za'a fara ɗaukar sabbin ɗalibai kema za ki sama gurbin karatu. Na yanke shawaran kawai zan nema miki a karatan da nake koyarwa tunda haɗe yake da sakandiri gabaɗaya".
Duk da na san hakan bai wuce shiri na Anty Binta ba , amsawa nayi da"Allah ya nuna mana lokacin, hakan ma ya yi dai-dai sai muna tafiyar mu tare. Na kula da abina sosai".
Murmushin nan nasa mai ɗaukar hankali ya yi ya ce"Wai ina maman Hanan ne taje haka?".
"Wallahi ban sa ni ba don ba ta ce mini zata je wani wajen ba".
Bai ƙara cewa komai ba har muka kammala haɗa komai na miyar ɗanyen kuɓewa, ganin lokaci ya yi ya sanya fita zuwa ɗauko Hanan daga islamiyya. Sai da aka ƙwala ƙiran sallan magrib maman Hanan ta dawo, lokaci har yaya Yusuf ya ɗauko Hanan na wanke ta taci abinci tana ɗakina tana wasa da wayata. Bata bani damar tambayar ta inda take ba don tana amsa sannu da dawowan da nayi mata tayi wuf ta shige ɗakinta.
Daren ranar bacci ya gagari idanuna sai faman juyi nake maganganun Hajiya sun hana ni sakat, tinani da fargaba suka zamto abokai na. Gashi ban sama damar tattauna da kowa ba game da lamarin ba zan tunkari yaya Yusuf da zancen ba, domin hakan kamar rage mini daraja zai yi a idanunta wataƙil yayi tinanin kamar so nake na haɗa kaina da Anty Binta a fannin matsayi. Duk da kuwa zuciyata tana bani kyakykyawan tabbaci akan zai fahimce ni sai dai ta ina ma zan fara sanar dashi wannan zancen mai nauyin furtawa akan harshe?.
Miriginawa nayi da nufin gyaran kwanciyana riƙon da yaya Yusuf ya yi min gam gam ya hanani samun damar aiwatar da hakan. Duk duhun ɗakin bai hana ni hango fuskarsa ba, take naji wasu hawayen sun wadaci idaniya zantukan Anty Binta na safiyar yau yana yi mini kururuwa a cikin kunnuwana, ƙirjina ya yi bugun da ya tilasta mini runtse idaniyata da hakan ya ba wa hawayen da nake maƙale damar kwaranya. Cikin raina ina addu'ar Allah ya bani ikon kiyaye yaƙini da yardar yaya Yusuf a kaina kar na bashi kunya, sanadin wannan karatun na ƙara zamtowa abar alfahari gare shi da iyayena gabaɗaya.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 2⃣0⃣
Kwana biyu a tsakani Anty Binta ta ɗauke ƙafarta daga zuwa gidan. Addu'a na duƙufa dashi babu dare babu rana duk sanyi baya hana ni tsayiwar dare.
Rigimar da ban san mafarinta ba ta kunno kai tsakanin maman Hanan da yaya Auwal tun sanyin safiya suke mayarwa junansu zazzafan martanin da suka sanya mu fitowa tamkar waɗanda suka ji ihun gobara, kafin yaya Yusuf ya fara ƙwanƙwasa musu ƙofar ɗakin a hankali. Basu buɗe ba balle mu sanya rai ga tunanin zasu amsa ragowar zancen da yake yi illa kukan Hanan da yake ƙara ratsowa ta cikin ɗakin.
Mun daɗe tsaye a wajen kafin yaya Auwal ya buɗe ƙofar rai a matuƙar ɓace ya ɗauki hanyar ficewa daga gidan, na lura tsabar ɓacin ran da suka yiwa idanunsa lulluɓi shi ya hana shi samun zarafin kallon mu tsaye a wajen. Cikin sauri yaya Yusuf ya rufa masa yana ƙwala ƙiran sunansa, sanƙararrun ƙafafuna da naji su tamkar basa cikin jikina naja su izuwa ɗakin maman Hanan, tana durƙushe can ƙuriyar ɗakin na hange ta Hanan kuwa na yashe tsakiyar ɗakin tana rusar kuka kamar matan mamaci.
Da sarsarfa na isa ga maman Hanan sai dai tun kafin na iso gare ta ta ɗaga mini hannu cikin ƙaragin kukan ta furta mini"Dan Allah Na'ima ki fita, ki fita bana son ganin kowa ki bar ni na roƙe kiiii".
Ta ƙarishe zancen ƙarshen natan tana kuma tuntsirewa da matsanancin kuka tare da jan kalman. Kamar gunkin india da aka sassaƙa na kasa gaba balle baya zuciyata tana bugawa da sauri da sauri. Hanan na ɗauka na fice daga ɗakin wasu siraran hawayen suna gangaro mini ta gefen da gefen idanuna.
Da ƙyar na lallashe ta tayi shuru, ta kwanta bacci bayan nayi mata wanka, tisa ta gaba nayi na zagba tagumi iwa wacce aka aikowa da saƙon mutuwar uwa da ubanta.
MATAN AREWA, matan yankina kuma al'ummata tabbas suna cikin halin walagigi. Matsalar aure babu wacce bata fuskanta sannan babu mai fahimtar matsalar domin ta zamto kukan zucin da mai shi ne kaɗai yake jin raɗaɗin. Haƙuri shine kalmar da ta sama gurbin zama a harshunan iyaye da yawa ba tare da la'akarin ƙuncin da ƴaƴansu suke fuskanta a gidajen mazajensu ba. Cikin matsalolin auren da yawa ba'a taɓa sauraron ɓangaren macen sai dai ayi ta furta mata kalmar haƙuri.
Figitit na dawo izuwa duniyar zahiri daga karatun wasiƙar jakin da na faɗa, sakamakon jin fitowar maman Hanan tana ƙoƙarin dannawa ƙofarta ɗab makulli, a zabure na fito ma damƙe hannunta tare da ƙwace makulli da jakar kayan dake hannunta.
"Anty dan girman Allah kiyi haƙuri kar kije ko'ina dan Allah".
Na furta ina yi mata magiya bata kula ni ba ganin hakan ya sa ni nayi wuf naje na rufe ƙofar gidan. Na dawo ina bata haƙuri bayan na ja hannunta izuwa ɗakina.
Kallon fuskarta da ta kumbura sumtum nayi duk halittun fuskar suna sauya na ce"Anti komai na duniya sai an sanya haƙuri ake kaiwa ga cimma gaci, ban san abinda ya haɗa ku ba amma dan Allah na roƙe da ki zauna a warware komai".
Idanunta ta watsa su akan fuskana"Na'ima a zauna a warware komai fa kika ce?, waye zai warware wannan ƙullin?, babu wacce zata zo domin hakan face Anty Binta wacce ita ce musabbabin faruwar komai babu abinda za'a warware sai dai ma a ƙara jagula komai. Wallahi Na'ima nayi da-na-sanin auran Auwal nayi da-na-sanin haɗa zuri'a dashi nayi nadamar kasancewa matarsa, nayi nadama kasancewar s uban ƴata. wai shin har sai yaushe ne MATAN AREWA zasu rabu da wannan tarin matsalolin?, wallahi Allah kaɗai yasan adadin matan dake fuskantar matsala irin nawa a gidajen aurensu. Babu inda zan kai matsalarta mahaifina ya rasu tun ina da ƙarancin shekaru ni ce ƙarama a gidanmu ina da yayu mata biyu, mahaifiyarmu tsufa ya kama ta ta yanda komai sai anyi mata ba zan iya je mata da matsalolina ba domin in nayi hakan kamar na ƙara sauƙaƙa mata hanyar tafiya izuwa kushewa ne".
Iska mai zafi na furzar daga bakina ina zame hannuwana biyu da na tallafe kuncina da su, ina jin kalaman maman Hanan suna dukan kwakwalwata kwatankwacin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe. Riƙo hannunta nayi dukka na sanya su cikin nawa kafin nayi ƙarfin halin danne ruwar ƙwallar da suka ciko koramar idaniyata na ce da ita"Anty tabbas nima na fahimci irin zaman haƙurin da kike yi da abban Hanan, amma rayuwar ƴarki za ki duba wane irin tarbiya zata taso dashi bayan kin yi fatali da ita yanzun kin tafi, tun ina ƙarama nake ganin Ummata tana sulhunta irin wannan matsalolin amma yanzu na roƙe ki da ki zauna muga dawowar shi tukunan".
"Na'ima ba zan iya ba domin Auwal ya nuna baya buƙatar zama da ni, Allah ne mafi sani Auwal baya biya mini dukkanin buƙatar aure. Abin nasan tamkar da gayya yake yi, wani abin takaicin komai zai faru tsakanin mu zai ya shaidawa Anty Binta".
Haƙuri na ɗaura bata har ta ɗan lafa ba, ɗakin na barta kwance na tattare tsakar gidan sannan na ɗaura mana girki cikin rashin kuzari na gama komai kafin na ɗauki wayata na danna ƙiran yaya Yusuf har ƙiran ya katse bai ɗaga ba na ƙara ƙira a karo na biyu shima babu amsa. Da ƙyar na lallaɓa maman Hanan ta sama ta tura abincin da na girka mana cikinta ta kwanta saboda ciwon kan da ta labarta mini cewar ya adaddabe. Wunin ranar haka na ƙarar dashi tamkar wacce aka zarewa laka komai cikin sanyin jiki nake yinsa. Sai bayan sallan asr yaya Yusuf ya shigo gidan a kallo ɗayan da nayi masa na hango tsantsan tashin hankali da ya kara ɓoyiwa sai da ya bayyana ƙarara a bisa fuskarsa.
Tabarma na shimfiɗa mana domin maman Hanan na kwance a ɗakina, na kawo masa ruwa a nutse na ce"Yaya lafiya kuwa?".
Kafe ni ya yi da idanu ya cije leɓɓansa na ƙasa kafin ya furto mini abinda suka hautsina ƴaƴan hanjin cikina