Showing 15001 words to 18000 words out of 61178 words

Chapter 6 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

yi. Ina zaune a ɗakinmu Nurain ya shigo da gudun yana faɗin"Anty Na'ima wai ana sallama dake a ƙofar gida".
Tunin ƙirjina ya fara gudun famfalaƙi na sanya hijabina na fita, inda ya tsaya jiya na iske shi na isa da sallama ɗauke a baki na.
Fuskarsa yalwace da wannan kyakykwan murmushin da yayi ta take ƙara fito da asalin kyan fuskar tasan. Ya amsa sallamar tawan.


"Na same ki lafiya, ya kuma mutanen gidan?".


"Duk lafiya ƙalau".


"Masha Allah".


Shuru ya ɗan ratsa kana yayi gyaran murya, yana ɗaura da"Na'ima haƙiƙanin gaskiya na daɗe ina son sanar dake gaskiyar wani lamari, amma harshena ya ƙi bani haɗin kai wajen furta hakan a gare ki". Sosai na nutsu ina wasa da ƴan yatsun hannuna. "Na'ima alal haƙiƙa tunda na fara koyarwa a islamiyyar nan, na kamo da soyayyarki kuma idan kika bani dama na sama karɓuwa a gare ki babu abinda zai hana ni mallakan ki na killace ki a cikin gidana a matsayin matata".
Sai da ya sausata amon muryarsa yana karantar yanayina can ƙasa ya ce"Ina sonki Na'ima kuma ina fatan na sama karɓuwa a gare ki, ba zan cutar da zuciyarki ta hanyar tirsasata zama da ni ba, komai za'a yi sai da amincewa da kuma yardanki".




MATAN AREWA

© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________________




Page 0⃣9⃣




Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe cikina yana bada ƙara ƙululu, sai dana fizgo numfashina kana nayi jarumtar faɗin"Na baka dama Malam domin a zuwa ɗayan da kayi ƙofar gidan nan duk iyayena sunyi na'am da kai, sun kuma yaba da tsarin nutsuwa da hankalinka har ma da sanin ya kamata. Duk da kuwa ba'a gano hakan a haɗuwar farko amma sun yarda da kai, bani da zaɓin da ya ɗara nasu don haka nima na aminta da kai".


"Zaɓin kanki da kanki kunnuwana suke buƙatar ji daga gare ki, shin har cikin zuciyarki kin aminta da ni da kuma soyayyata ko kuma kawai za ki yi biyayya don iyayenki sun amince dani?".


Sosai tambayar tasan tayi mini nauyi gami da wahalar amsawa sai da na haɗiye wani miyau mai ɗaci da ɗacinsa naji ya gauraye duk wata kusurwa na cikin bakina. Kana na soma faɗin"Malam nima kaina na aminta da kai sannan shaida ce akan kyawawan halayya da ɗabi'unka, ban taɓa soyayya ba sannan ban taɓa amincewa da wani saurayi ba sai kai. Don Allah kaji tsoron sarkin da ba'a ɓoye masa komai masanin sirrukan da suke ɓoye dama na zahiri idan ba son gaskiya kake mini ba kar ka ɓata mini lokaci ka cutar dani".




A raunane na ƙare zancen ƙarshen ina duƙar da kaina ƙasa don wasu zafafan hawaye ne suka taho mini. "Na'ima ɗago idonki ki kalli cikin idona domin a nan ne kaɗai za ki hange amsar tambayarki, ina sonki da dukkan gaskiyata sannan kuma so irin na aure".
A hankali na ɗago kaina nayi masa kallon ido cikin ido sau ɗaya na janye nawa ina ƙoƙarin saisaita kaina da tare hawayen da ban san dalilin kwaranyan su ba a wannan sa'ilin. Abu ɗaya da zuciyata take kimtsa mini shine burina nason yi karatu, zama marubuciya da kuma ma'aikaciyar jarida shikenan ya zamto mafarki kenan.


"kin yi shuru?".


Figigi na dawo daga tunani mai zurfin da na fara zurmawa ina ƙaƙalo murmushin dole na dasawa fuskana, a ƙoƙarin tabbatar masa da kore masa kokanto da samar masa da nutsuwa akan babu komai.


"Su Abba sun ce suna buƙatar ganin ka idan kazo".


Fito da idanu waje ya yi haɗi da cewar"Allah yasa ba kashedi za ayi min akan har na ƙara zuwa wajenki ba, ko kuma ace anyi miki miji zuciyata ba zata iya ɗauka ba". Taƙaitaccen murmushin gefen baki na saka. Ina ƙara mamakin Malam Yusuf duk tsarewarsa a cikin aji sanda ya fara koyarwa a makaranta babu yarinya ta ya taɓa buɗewa haƙwaransa da sunan dariya, hakan ya sanya har yanzu da yawa suke masa kallon mai girman kai.


"A'a ba haka bane sun dai ce suna buƙatar ganin ka".


Na faɗa ina masa nuni da hanyar shiga gidan raina maƙil da mamakin yanda ya saki jiki da baki yana wannan zantukan, daman aka ake yi zuwan saurayi na farko wajen budurwa?. Na jefawa kaina tambayar da na gaza cimma amsarta har muka isa cikin zaure. Ya dakata daga nan yayin da ni kuma na isa ɗakin yaya Majid na zayyana masa komai da sauri ya fito suka gaisa ta hanyar yin musabaha. Na wuce ciki saboda ya yi masa iso wajen su Abba.
Tun kafin na kai ga shiga ɗakinmu naka duk matan gidan suna bi na da kallo da alama magana ta suke yi shigowa ta ya sanya tsahirtawa.Su Salma na iske zaune a ɗakin ina sanyo ƙafata suka tuntsire da wata ƙarƙarfan dariya mai sautin gasken, kallon ɗaɗɗaya nayi musu kafin na ce"ince dai lafiyarku ko?".


Da ƙyar Balkisu ta tsayar da dariyar ta take yi har da riƙe ciki ta ce"Sai yanzu?".


"Bangane sai yanzu ba?".


Na tari numfashinta Abasiya ta ɗaura da"Masoya kenan sai yanzu soyayyar ta ƙare?, gaskiya zan so gani idon Malam Yusuf sanda yake furta miki kalmar so". Ƙara bushewa suka yi da wata dariya ciki-ciki nayi tsaki kamin na zauna bisa katifarmu ina faɗin"Kyaji dasi abinda ya dame ki kenan ni kam dai bashi bane a gabana, don da na sama goyan baya ma wallahi makaranta zan koma don ni ba wani son shi nake yi ba".


"Kut lalle Na'ima amma dai kin sa malam Yusuf ba tsararki bane ko?, wallahi ya fiki kyau da kuma aji ga haɗuwa da kuma sanin kimar kansa don ba kowacce yake kulawa ba, ai ke kece kika sinci dami a akala".


Furcin Balkisu kenan Salma tayi caraf ta karɓe zancen"A to gaya mata dai tana wani jan ajin banza, ban da sharrin soyayya ma ina ke ina malam Yusuf". Wata dariyar suka ƙara saka har na buɗe baki da zumma mayar musu da amsa yaya Majid ya ɗago labulen ɗakin haɗi da cewar"Kizo sun gama zai wuce".
Yana ƙare faɗin hakan ya juya a tare su Salma duk suka zari hijabansu wai zasu je gaisuwa takaici haka nan suka ɗura mini na bisu a bayadon dole. Don wallahi naso yin zamana na ƙi fitowa muyi sallaman sai naga rashin dacewar hakan. Suturu suke ta zuba mishi da mamakina naga yana biye musu abinda sam ko cikin wasa da raha baya yi a islamiyya kenan. Abasiya har da faɗin wai yanzu ta zama Antinsa tunda yana son ƙanwarta.


Ganin isowa ta ya sanya su yi masa sallama suka koma cikin gidan. Kaina a duƙe ya soma cewar"Naga su Abba kuma sun yi min tambayoyi na amsa ki taya ni addu'a Allah ya sa na cinye wannan jarabawar".


"In sha Allah zaka kaye ta".


"Allah ya sanya".


"Amin".


Na ce ina gyara tsayiwata kamin ya ce dani zai wuce sai kuma wani lokacin, fatan sauƙa lafiya nayi masa kana muka yi sallama ya ce ba fara shiga gida tukunna. Hakan kuwa aka yi sai da na shiga kana ya ja mashin ɗinsa ya tafi haka nan na since kaina cikin matsananciyar faɗuwar gaba da tararradi, ganin na gaza samun nutsuwar ruhin ya sanya ni nufa ɗakin yaya Majid yana tsaye yana ɓalle maɓalle rigarsa zai fita masallaci saboda magrib da ta gabato na iske shi.


"Har ya tafi kenan?".


Kaina na ɗaga masa alamar e, ya kuma cewar"To ya na ganki kamar ba lafiya?". Sai da na sauƙe numfashi ba tare da na shirya ba wasu hawaye suka ɓalle mini suka fara gudu akan dandamalin fuskana a tare da na yi wani yunƙurin hana hakan ba. Kalmar subhanallahi, subhanallahi, subhanallahi kawai yake ta faman maimaitawa cikin bakinsa. Kafin ya ƙariso gab da nayi yana faɗin"Ke Na'ima lafiya kuwa?".


Kaina na ɗaga masa na ce"yaya Majid yanzu shikenan inda su Abba su gama gudanar da bincike a kan malam Yusuf, har ya turo iyayensa shikenan duk burin da nake dashi akan karatu ya bi iska kenan?".


Ina iya jiyo ɓoyayyar ajiyar zuciya mai ƙarfi da ya sauƙe"Na'ima ai shi aure baya hana karatu, kamar yanda nasha faɗa miki matuƙar kina da buri akan karatu babu makawa sai kinyi shi don haka ki kwantar da hankalinki kinji ƙanwata?. yanzu zan fita masallaci inna dawo sai mu gama maganan".


Tare muka fito dashi yana ƙara kwantar mini da hankali da kuma ƙara mini ƙarfin gwiwa. Masallacin ya wuce ni kuwa na shiga ciki sai da nayi alwala na shiga ɗakinmu nayi salla, na daɗe akan sallayan ina addu'ar Allah ya yi mini zaɓi mafi zamowa alkhairi a gare ni dama rayuwata gabaɗaya.
Ko da na fito Anty Zakiyya na iske tana kaɗa miyar bushashshan kuɓewa na zauna gefen ta ina yi mata sannu da aiki, ta amsa mini fuskar nan a sake.


Nan nake tambayar ina Umma don tun kafin zuwan Malam Yusuf da naje ɗakinta sanar da ita Hajiya Babba nason ganinta, ban ƙara ganin idonta ba. Nan take sanar dani cewar Maman Walida tazo sun fita tare kaina na jinjina lamarin Maman Walida ya riƙe mini rai.
Sai da ta gama kaɗa miyar ta raba abincin ko wani ɗaki aka sanya na matar ɗakin kana na fara kai wa.
Muka ci namu tare da su Salma sai bayan sallan isha'i Umma ta dawo sai da na bari ta huta kana naje na sanar da ita duk yanda muka yi da Malam Yusuf, Anty Zakiyya da take zaune tana sauraron mu ta taso ta rungume ni ta baya, har da ƙwallar farin ciki take yi mini tana mini addu'o'in sanya alkhairi. Sosai naji zuciyata ta ƙaraya naso sai anyi nata bikin. Kafin za ayi nawa amma ga yanda Allah ya tsara komai cikin mu babu mai ikon canja ƙaddara.




Na lura Umma ma dauriya kawai take yi take lallashin mu amma ita ma zuciyarta suya take yi mata, sai da safe nayi wa Umma na zarce ɗakinmu. Ban bi ta kan su Abasiya ba da suke kitsawa Salma zance akan maganar nan da muka fara jiya na Abdallah.


Kwanciyana nayi sai dai sam bacci ya ƙaure ce mini, har aka yi ƙiran assalatun farkon ƙar a kunnuwana.
Safiyar duk mutanen unguwar mu muka wayi gari cikin matsanacin tashin hankali, da ruɗewa. Wata amarya aka kawo jiya da wayewar garin yau aka tarar da gawarta ta ƙone kanta, bayan fitar mijin izuwa sallan asuhabi, a yanda jifa jifa ya fara bazuwa a cikin unguwa wai auren dole aka yi mata ba tare da son ranta ba.


Ranar Umma da wasu mata biyu da suke aiki irin nata, da kansa mai unguwar unguwarmu ya sanya aka tara musu iyaye maza suka wayar musu da kai akan illolin auren dole ga ɗiya mace, mace halitta ce rauni da zuciyarta bata iya ɗaukan zama inuwa ɗaya da wanda ya kasance ba zaɓin ranta ba.
Har sai da aka ƙwala ƙiran zuhr kana suka tashi daga taron, har yamma muna cikin jimami kowa jikinsa yayi laƙwas tamkar waɗanda aka yiwa dukan tsiya, da yammacin ranar Anty Kubra ta koma ɗakin mijinta bayan dogon nasiha da jan kunnen da su Abba suka yi mata haka nan ma Umma tayi mata da ta shigo yi mata sallama. Haka nan ta koma ta cigaba da jinyar mijinta. Bayan sallan magrib yaya Majid yake shaida mini xuwan Malam Yusuf..


Dogom hijabi na saka, na fita na iske su tare da yaya Majid ganin fitowa ya sanyi shi yi masa wani maganar da ban iya tantance abinda ya faɗa ba, ya bar wajen sallama nayi masa ya amsa. Kafin muka shiga jajantawa junan mu abinda ya faru, duk jikina ya ƙara yin laƙwas.


Lura da yanayin da na faɗa yace"Zuwana yanzu munyi da su Abba sunce zuwa jibi idan suka kammala bincike a kaina, zasu bani damar gabatar da iyayena".


Kaina na jinjina nace"ina fatan ba'a zaurara maka ba?".


"Ko kusa in sha Allah zanyi iya ƙoƙarina, ganin na samar da komai akwai ginin da muka yi tare da yayana. Wanda yanzu haka shi yana da mata lefe da sadaki ne kawai ya tare min wanda shima akwai adashin da nake yi da na ɗauka zanyi komai".


Sosai na jinjinawa ƙoƙarinsa haka muka cigaba da tattaunawa, muka kuma ƙara fahimtar junan mu, dawowar su Abba daga masallaci ya sanya ni dawowa cikin gida, na barsu tsaye da Malam Yusuf.
Kamar yanda su Abba suka gudanar da bincike akan Malam Yusuf, ba'a same shi da wani mummunan ɗabi'a ba haka nan ya sama kyakykyawan shaida daga jama'a, sana'ar koyarwa yake yi, a mabambamtar makarantu har uku, islamiyyar mu ta safe, da na yara na yamma sai kuma makarantar primary da yake koyar da yara.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


______________________________________


Page 1⃣0⃣




Tunin shirye shiryen sauƙar mu ya kamo hanya gadangadan, kowacce daga cikin mu saurayinta ya yi bajinta wajen bata wasu kuɗaɗen domin hidimar sauƙar tamu. Don zamu yi ankon atamfa da kuma hijabi ga kuɗin da muke tarawa a wajen Malam Yusuf kullum ɗari biyu.


Duk dani ya ɗauke mini hakan, a matsayin nashin gudumawar na sauƙar kasancewar bai yi mini irin yanda samarin su Salma suka yi musu ba. Ta hanyar basu kuɗi kasancewar shi ɗin abun yazo masa a gaggauce duk da kuwa ya ce mini daman a shirye yake, amma yana buƙatar wasu kuɗaɗen.


Gashi maraya ne, shine na uku a wajen iyayensu hakan ya sanya sauran ƴaƴinsa biyu yi masa kara suka haɗa masa lefe tsaf.
Ana saura kwana goma sauƙar mu, aka kawo lefe Salma ranar mun sha kallo don har da maƙwabta. Firirita wajen Ummansu kuwa ba'a kwatancen sa, don tunda ake aurar da ƴaƴa a gidan mu ba'a taɓa yiwa wata koda kwatankwacin irin lefen Salma ba.


Ban sa ni ba ko hakan ne ya turnuƙe ƙalbin Abasiya oho. Don wunin ranar gabaɗaya ƙarar dashi tayi cikin ƙunci. Bata kwana a ɗakin mu ba ta ce a ɗakin Ummansu zata kwan, cikin mu babu wanda ya damu da hakan.
Kwana biyu tsakani aka kawo na Balkisu babu laifi Aminu ya yi ƙoƙari da bajinta sosai, kasancewar ba ma'aikacin gwamnati bane kamar saurayin Salma. Hasalima shi direban babban mota ne. Sagirun Abasiya kuwa ɗan kasuwa ne.


Yaya Majid ne ya yi mini ankon atamfar, yayin da Malam Yusuf ya yi ƙudurin yi mini ankon hijabin Ummata ta gargarɗe ni akan har na ɗaura masa nauyi, musamman da yanzu aski yazo gaban goshi. Zaune muke a ɗakin mu Abasiya tana aikin rubutawa Sagiru saƙo akan kuɗin gyaran jiki da har yanzu bai kawo ba. A cewarsa wai sai wasu kayan da yake tsammata zuwan su sun iso zai bata.


A nutse Salma ta kallo ta kafin ta shiga faɗin"Haba Abasiya ke kuwa kiyi haƙuri mana tunda ya ce zai ba ki ai zai bayar, kiyi wa Ummanku magana ko aro ne sai a nema a fara abinda ya kamata in ba yabar sai a biya".
Kamar jiran ta take yi Abasiya ta kuwa shiga furzo da zantukan dake cikinta"Ai dole kice na ara saboda ke Abdallah bai yi miki wasa da hankali ba, ya cake miki kuɗin gyaran jikinki tsaf a hannunki ai dole kice dani haka".
Sai da tsirgar da wata tsaki mai dogom zango kana ta ɗaura da faɗin"Ni wallahi da su Abba ma zasu saurara ni, da na ce dasu na fasa auran Sagir sam ya fiye mammaƙo. Da Allah zai fito min da wani hamshaƙin wallahi da tunin na mance da wani mai kama da Sagir".


Duk kallo duka tsura mata cike da mamaki har ta kammale zancen natan. Bamu gama dawowa hayyacin mu daga shayar da mu ruwan mamakin da ta yi ba, zantukan da ta ɗaura dasu suka bugin kunnuwan mu.
"Wallahi duk ya fita raina, sai yanzu ma nake hango zallar wautan da nayi. Da na zaɓi Sagir a matsayin wanda zai zama mijina mtscheew".


"Ke Abasiya ince notonan kanki basu sun ce ba ko?, Sagiru ne fa kika faɗin wannan maganar akan sa, duk soyayyar da kuka yi kin manta kenan?".


Furcin Balkisu kenan da ya sanya Abasiya ƙara tunzura ta hayayyaƙo kamar zata cinye Balkisu ɗanya"Sagirun to ubana ne shi ɗin, da ba zan iya gudanar da rayuwa babu shi ba?, ko shi ɗin numfashina ne da za ki ce ba zamu raba gari dashi ba?".


Tana ƙara zancen ta miƙe ta fice cikin matuƙar ɓacin rai, da kallo duk muka raka ta ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfi da ya sanya ni runtse idanuna. Ina mamakin meya shigarwa Abasiya kwanyar kanta da take wannan furcin, ta manta yanda Sagiru yake ɗawainiya da ita. Bata shakkar tunkarar sa da duk wani buƙatar kuɗi idan ta taso mata, kwanakin baya sai da Abba ya yi mata zazzafan kashedin har ta ƙara shigo masa gida da duk wani abunda ya fito daga hannun Sagiru in dai bashi ya yi niyya ya bata ba.


"Allah ya kyauta".


Iya abin dana furta kenan kafin muka jiyo sowan ƙananan ƴaƴan gidan suna yiwa Goggo Suwaiba barka da zuwa. Zumbur muka miƙe har muna rige rigen fitowa, tana zaune akan tabarma duk matan gida suna daga gefe ƴaƴa kuwa sun mamaye ta, don nisa ba kusa ba tafi Goggo Jummai sakin fuska da jan mu a jikinta uwa uba ga kyauta kamar bata san ciwon nema ba.




Kamar yanda kowa yake zaune kusan ta muma hakan muka yi kafin muka fara gaishe ta. Tana amsa mana cikin sakin fuska.
"Kaga Amaran nan da kwana goma".
Duk sunkuyar da kai muka yi cike da kunyar zancen natan, da hakan ya sanya ta sakin taƙaitaccen murmushi kana ta ce"nazo muku da wani sirrin gyaran jiki da idan kuka riƙe shi in sha Allah kun mallake mazajen ku, babu bin boko balle malaman tsubbun da za suta cin kuɗaɗenku a banzan, ga kuma kaucewa daga gwadaben Allah".


Wayyo Allah ai ji muka yi kamar ƙasa ya buɗe duk mu shige tsabar kunyar da tayi mana sarƙa. "Goggon yara kenan, da kin haɗowa Zakiyya ma nata haɗi ko Allah zai yanke mata wannan zaman gidan haka".


Furci Daada kenan da ya sanya ni taune leɓɓana kamar da ni tayi zancen take naji raina yana mini soya ainun. Ɗan murmusawa Goggo Suwaiba tayi"Me kike ci na baka na zuba?, ai ita ma lokacinta ne bai yi da zarar yayi babu abinda zai hana ta yi".
Zuwa yamma kamar kullum duk muna sashin Hajiya Babba, kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login