Showing 27001 words to 30000 words out of 61178 words
Chapter 10 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt
tabbacin idanun Yaaya Yusuf suna kaina yake cewar"Zamu tattauna da yaya Auwal in sha Allahu za ki ji yanda muka yi".
"To Allah ya kyauta, amma ni Binta ina na taɓa jin wanga lamari duk tsawon rayuwata a duniya mutum da hankalinsa ya gindine aurensa ya kama boko ilmin nasara".
Daga ni har shi babu wanda yace ko kanzil, bamu ƙara mintuna goma masu kyau ba muka miƙe muka yi mata sallama muka tafi sai ƙara jaddada masa hatsari da rashin yiyuwar abun take yi har muka hau mashin muka nufi gidanmu.
Duk iya ƙoƙarina nayi shi don ganin na danne ɓallewa kukan dake nuƙurƙusan rai da ruhina, amma abin yaci tura dai-dai kwanan da ya karya na shiga layin mu babu shiri na tuntsure da kukan da nima kaina ban so fitowar sa ba a wannan lokacin, don har raina na son danne shi.
Tsayawa ya yi ya sauƙa ya kashe mashin ɗin, a kallo ɗaya da nayi wa fuskarsa na lura shima duk jikinsa a sanyaye yake kamar an jefi kaza da ruwan gishiri.
"Na'ima dan Allah ki daina wannan kukan domin kuwa bashi bane mafita gare mu. Ki tausaya min ki daina domin ba zan iya jurar ganin zubar hawayenki ba amanarki iyayenki suka bani don haka ni nake da haƙƙin samar miki da duk wani abunda zai faranta miki, kuma na miki alƙawarin matuƙar muna tare sai kin cika burinki a karatu da iznin sarkin da ya sanya mace ta gari ta zamto sanyin idaniya mijinta, goge fuskar ya isa haka".
Ya ƙare zancen yana miƙo mini farin handkerchief da ya zaro daga aljihunsa, sosai maganganunsa suka ratsa ni sai dai bakina ya yi mini nauyin da ba zan iya cewa dashi komai ba, karɓa nayi kamar yanda ya buƙata na goge fuskana sannan ya hau kuma ƙarisa ƙofar gidanmu. Hindatu auran Hajiya muke fara haɗuwa da ita, a ƙofar gida zata shige ganin mu ya sanya ta nufar mu tana yi mana sannu da zuwa sosai na saki fuskana gare ta. Muka shiga ciki sai da na fara biyawa ɗakin Yaya Majid ya fita ɗɗ wajen Yaaya Yusuf, kamar yanda na bar gidan haka na iske shi kowacce mace tana zaune ƙofar ɗakinta da ƴaƴanta zagaye da ita Ummata ce kawai ban hango ba don ita tun da can ba ta tsirawa kanta wannan ɗabi'ar ba. Da Anty Zakiyya nayi tozali tana wanki, ganin ta ya sanya ragowar sallamar da na fara maƙalewa a maƙoshina nufar ta nayi muka rungume juna cike da kewa.
Sai da na bi dukkan matan gidan na gaishe su, suka amsa fuska babu yabo babu fasalla kafin Anty Zakiyya ta ja hannuna izuwa ɗakin Umma har da kuka na sanya mata don tabbatar da yawan kewarta da nayi. Ban sanar dasu komai ba don sam na gaza samun ta inda zan fara. Hirar mu muke yi sosai da Anty Zakiyya Umma ta ƙara tilasta mini nace ɗakin kowacce na gaisheta bayan wanda nayi na farko, hakan nayi sannan na zarce sashin Hajiya Babba nan na iske Yaya Majid da Yaaya Yusuf, cikin son kaka da jika muka gaisa da Hajiya Babba kafin na maƙalƙale mata a jiki Yaya Majid ya yi wa Yaaya Yusuf jagoranci har sashin mu yaje ya gaisa matan gidan da Ummanmu.
Nan muka yi sallan zuhr har su Abba suka dawo muka gaisa kafin muka fara haramar tafiya, har na sanya hijabina bayan Ummata ta gama ɗaura mini wani nasihar yaya Majid ya aiko Nurain wai na jira tukunna Yaayan suna tattauna da su Abba.
Kasancewar a tsakar gida ya sanar da ni hakan, ya sanya matan gidan kallon junansu kafin wani ƙusƙus ya fara yaɗuwa wai ko ƙarata ya kawo na aikata wani laifin. Ban basu hankalina ba muka cigaba da hira da Anty Zakiyya da su Habiba da suke tsoma baki lokaci zuwa lokaci, har sai lokacin da Daada tayi wata maganar da ta baƙanta zuciyata.
"Na'ima ke kuwa daga ke har mijinki nakin kuka niƙo gari kuka zo hannu rabbana, ko ɗan tsabara a ƙannan nakin ba ki riƙo ba".
Shuru nayi kawai don sosai zancen suka dake zuciyata tare da baƙanta ruhina, Anty Zakiyya ce ta amsa mata da cewar"Daada ba daga gida suke bane shiyasa basu yi wannan shirin ba, amma ai akwai gaba zuwa kuma yanzu ta fara ai".
Taɓe baki tayi kawai ta kawar da kanta gefe, muka cigaba da hirar mu nan Anty Zakiyya take shaida mini zancen da ya faranta ruhina ainun cewar sun haɗu da wani saurayi ranar bikinmu, bata san daga rukunin wani ango yake ba amma ya nuna ra'ayi a kanta. Har gaisawa suke a wayan Yaya Majid sosai nayi murna tare da fatan Allah ya tabbatar da alkhairi.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________________
Page 1⃣6⃣
"Na'imatu ya naga fuskar nakin duk a kumbure alamar kin sha kuka kin ƙoshi, in ce lafiya lumi ko?".
Furcin Umman su Salma kenan da suka sauƙa a masarrafar ji na, sunkuyar da kaina ƙas nayi kafin na ce da ita"Umma babu komai lafiya ƙalau, daren jiya ne ban sama ishashshan bacci ba, saboda ciwon kan da ya matsa mini".
"Ai de kuwa naga alamar hakan, to Allah yayi mana mai kyau".
"Amin".
Na amsa dashi can ƙasan maƙoshina Anty Zakiyya tana taya ni amsawa.Dai-dai sa'ilin da Umma ta fito daga ɗakinta ta kallo ni haɗi da cewar"Na'ima har yanzu basu fito ba?".
"E".
Ina rufe bakin yaya Majid yana isowa inda muke ya shaida mini sun gama yana jira na a waje, sallama muka yi da Umma da Anty Zakiyya da tayi mini rakiya zaure sannan muka baro gidan. Mun iso gida ana ƙiran sallan asr don haka Yaaya Yusuf ya ajiye ni shi kuma ya wuce masallaci.
Shau babu kowa a filin tsakar gidan haka nan duk sallama da nake rangaɗawa da dushashshiyar muryata ba'a amsa ta ba, ganin hakan ya sanya ni tinanin ko Maman Hanan ta shiga makwabta ne. Har na zaro ɗan makulli zan tsura na buɗe ƙofar ɗakina kukan da Hanan take rerowa daga cikin banɗaki suka dakatar da ni ajiye jakata nayi na nufi banɗakin. Can ƙuriya na hange ta fuskarta jiƙe lijif da hawaye, cikin sauri na isa gare ta haɗi da faɗin"Ke Hanan menene?, me kike yi a nan?".
Bata ce dani uffan ba domin ajiyar zuciyar da take sauƙewa a kai a kai, ya ƙi bata damar furta mini ko kalma ɗaya. Ganin hakan ya sanya ni riƙo hannunta muka fice na wanke mata fuskarta sannan na bata ruwa tasha idanuna tar akan ƙofar mamanta da aka ja shi aka rufe. Ɗakina na buɗe bayan nayo alwala na shige da ita kafin na ajiye jakana da ɗauko sallaya har Hanan tayi bacci, taɓo wuyarta nayi naji zafi gau alamar zazzaɓi mai ƙarfi ya sauƙar mata jiki.
Tagwayen ajiyan numfashi na saka kafin na miƙe na gabatar da sallan asr. Na fito ganin ba'a sanyawa ƙofar makulli ta waje ba ya sa ni fara rangaɗa sallama shuru babu amsa na fara dukan ƙofar a hankali na ɗauki mintuna a haka kafin na jiyo motsi daga ciki,, hakan ya tabbatar mini da hashashena akan cewar tana cikin ɗakin. Sai dai meye take yi haka da ya hana ta jin sallamana balle shigowata cikin gidan, har ya toshe mata kunnuwa daga jin kukan Hanan?.
Ja da baya nayi jin ana tunkaro ƙofar za'a buɗe, kanta kawai ta leƙo ba tare da ta buɗe ƙofar gabaɗaya ba balle na sama damar ganin abinda ke wakana ciki.
"Na'ima har kin dawo?".
"E wallahi Anty na dawo tun ɗazu, ban ji motsinki ba shiyasa na;ce bari nazo naga ko shin lafiya ga Hanan can ma a ɗakina zazzaɓi ya rufe ta".
Na ƙarishe zancen ina bin ta da kallon, da yake bani damar karantar yanayinta. Tun daga kallo ɗaya da nayi mata na tabbatar da cewar akwai wata matsalar domin sam bata a ciki cikakken nutsuwa ko maganar da take yi fizgo shi take yi. Sai da ta gyara ɗaurin ƙirjin dake neman warwarewa daga jikinta kana ta furta mini cewar"Wallahi kin gan ni nan tun bayar tafiyar ku, nake fama da ciwon kai ga rashin kuzari ban iya taɓuka komai ba, nan na kwanta Hanan ta dame ni da rigima shine na shigo ɗaki na rufe".
Kaina na jinjina ina ƙaƙalo murmushin da ya tsaya iya kan leɓɓana na sakar mata, ba tare da na samu nutsuwar zuciya akan zancenta ba nayi mata yaya jikin ta amsa mini da kalmar alhamdulillah.
Ban tsaya jin wani abu ba, nayi komawata ɗaki sam na gaza samun nutsuwa da halin da naga Maman Hanan a ciki wani irin nauyin bacci ne haka da ya hana ta jin komai?. Ganin bani da amsar tambayar ya sanya ni miƙewa na cire kayan jikina na ɗaura zani na ɗauki sosona na fito ruwa na ɗiba na shiga banɗaki na watso ruwa a jikina sannan na fito.
Tabbas idanuna fitar mutum suka hango ficewar sa daga cikin gidan, cikin sauri na dawo da baya a ƙoƙarin tabbatar da abinda idanuna suka gano mini, jin ƙarar an tura ƙofar gidan a hankali ya tabbatar mini da abinda idon ganina ya gano mini. Matuƙar tsoro ne ya tanke raina nayi azaman shigewa ɗaki kamar zan kife akan hancina na dafe ƙahon zuciyata da ƙirjina yake dakan lugudan dukan tara-tara sau tara, jawo numashi nayi mai ƙarfi na fesar a ƙoƙarin samawar kaina nutsuwa. Tsawon daƙiƙu biyu ina saye a wajen kafin naja ƙafafuna da naji sun yi mini sanyi laƙwas na zauna tare da jawo robar mai na fara murzawa a fatana kafin na miƙe na ciro dogowar rigata mai sauƙi nauyi na zara.
Rurin da wayata ta soma yi ya sanya ni kai dubana gare ta. Ganin lambar Yaaya Yusuf ta bayyana cikin screen ɗin wayar da yayi saving da *ZAUJI* da kansa ya sanya ni saurin ɗaga ƙira ina karawa a kunnena.
Sai da na sausauta amon muryata nayi sallama ya amsa, yana ɗaura da"Ina fatan dai kukan nan ya tafi ko?".
Sai da na ɗaga kaina kana na ce"Babu shi Yaaya tunda kayi mini hani dashi na daina".
Cike da jin daɗin furucin nawan ya furta mini"Masha Allah yayi Albarka, kar ki ji ni shuru na wuce islamiyyar yamma ne sai zuwa dare zan dawo".
Cike da kulawa nake faɗin"Amma Yaaya baka ci abinci ba fa tun safe, inda hali dai ka dawo gida kaci abinci ko ka aiko a karɓa maka".
Ina iya jiyo murmushin da ya saka ƙasa-ƙasa kana ya shiga cewan"Karki damu Na'ima zan nema wani abun kawai naci kafin na dawo ɗin". Shagwaɓe fuska nayi kamar ina gabansa har da ɗan buga ƙafata nake faɗin"A'a ni dai gaskiya Yaaya ban yarda, ƙarfe biyar ana tashi ka dawo gida kaci abinci".
"To shikenan Gimbiya yanda kike so hakan za'ayi, shikenan ko kuma da wani abunda kike so ayi?".
Murmushin jin daɗi da ya bata wani ɗan sauti na saka cikin faɗin"Babu wani abunda ya rage Allah ya dawo da kai lafiya cikin aminci, in kaci abincin kaje islamiyyar dare ban isa Anty Binta ta ga ka rame ta hukume ni akan ban kiwata ka da kyau ba". Sosai ya saki dariya mai ƙarfi, sai da ya yi iya yin sa ya tsagaita don kansa ya ce"Amin ƙurratu aynun madalla na gode da addu'a, watau ma kiwona kike yi kenan?".
"Ƙwarai kuwa".
"To shikenan sai na dawo ɗin".
Da haka muka yi sallama sai da na katse ƙiran na mance da ban tambaye shi abinda zan dafa masa ba duk da kuwa haɗa girki muke yi amma kowacce in ita ke da girki zaɓin mijinta take girkawa. Saƙo na tura masa akan abinda yake son ci, ya dawo mini da amsar cewar ya bani zaɓi na dafa ko menene matuƙar ni na sarrafa shi ya tabbatar zai burge shi.
Fitowa nayi na haɗa garwashi ya ruru, na fara haɗin girka masa miyar ɗanyen zogale don na lura yana matuƙar jin daɗinta, ina yanka albasa Maman Hanan ta fito miƙa tayi hamma kana ta iso gare ni. Ta zauna akan tabarmar da nake zaune a kai sannu da fitowa nayi mata ba tare da na ko kalle ta ba, jawo tiran zogalen tayi gabanta ta fara tsincewa haɗe da faɗin"Yau kuma Yusuf miyar zogale yake sha'awa kenan?".
Kaina na ɗaga mata ta kuma cewar"hmm kina ji da mijin nan Na'ima, ni tun yaushe na wasar da tambayar Abban Hanan abunda za'a dafa ko kuma abinda yake biɗar ci, duk abinda naga zan iya dafawa shi nake girkawa ko yaci ko ya bari wannan ruwan sa".
"Anty kenan hakan kuma yana da muhimmanci ai tambayar ra'ayin mutum, in ya baka zaɓi sai kayi gaman kanka".
Taɓe baki tayi"Ga mijin da ya damu da hakan kenan ba, wani ma buƙatarki bai biya miki ba balle ya kula da wannan ke dai ayi sha'ani kawai, kema lokaci ne wataran ko da kuɗi aka haɗa ki ba za ki yi ba".
Cak na dakata daga yankan albasan, ire-iren zantukan nan suna ƙara dulmiyar mini da tunanina, nayi wa rayuwar aurena tanadin da sai dai wani ikon ubanjigin ya kawo rabuwa. Maganar da ta ɗaura dashi suka dawo dani daga karatun wasiƙar jaki.
"Ina Hanan take ban ji motsinta ba?".
"Tana kwance a ɗaki, ta sama bacci ne".
"Masha Allah, bari ta tashi ta sha magani ban san sanda ta shigo gidan ba domin gidan Maman Mus'ab na tura ta da ta dame ni shiyasa ma na rufe ɗakin".
"Ayya".
Shuru ya ɗan ratsa kana ta katse shurun ta hanyar furta"Yaya kula kaya da Anty Binta?". Sai da na numfasa kana na zayyanu mata dukkan abinda ya wakana. Ita ma numfashin ta furzar ta ce"Daman na sanar dake hakan Na'ima, baza ta taɓa amincewa ba in dai wannan matar ce. Lokacin farkon samun matsalana da Abban Hanan a kan ƙaurace min da ya yi tafi kowa bin bayan ɗan-uwanta sam bata ga laifin shi ba, balle ƙoƙarin ɗaura shi a turban gaskiya. Wani lokacin ɗabi'unta kamar ba jinsin mace ba don haka kar ma ki ɓatawa kan ki lokaci tare da wahalar da kanki ta hanyar azawa zuciyarki dakon abinda ba zai yiyu ba. Ba zata taɓa amincewa ba shi kuma Yusuf ba zai taɓa aikata abinda ba ta lamince masa a kai ba, don haka kiyi haƙuri kawai ki rungumi rayuwa a yanda tazo miki".
Take naji jikina gabaɗaya ya yi laƙwas kamar wacce aka zarewa laka a jiki haka muka kammala girkin tare. Sai da aka yi sallan Magrib Yaaya Yusuf ya dawo kasancewar Abban Hanan bai dawo daga kasuwa ba na zuba mana muka ci tare dashi, don ni bama yunwar nake ji sosai ba kasancewar naci abinci a gida. Muna gamawa ya fita masallaci nima sallan nayi na watso ruwa nayi shirin kwanciya hijabi na ɗaura a kai na shiga na tambayi jikin Hanan da sauƙi sosai domin tunin ta ware sai da safe nayi mata zan fita ta dakatar da ni da "Yusuf ya shigo kenan?". Kaina na ɗaga mata ina ficewa wani ɓangaren raina cike da tausayin zaman auren Maman Hanan domin Abban Hanan baya dawowa gida sai dare ya tsala haka nan farar safiya ya fice kasuwa, sam baya samun lokacin iyalinsa balle na jin damuwar su.
Na iske Yaaya Yusuf yana karatun al-ƙur'ani, zama nayi gefen sa na jona shi muka cigaba dayi. Mun ɗaɗe muna yi kana muka yi haramar kwanciya.
"In sha Allah da asuba zamu yi magana da yaya Auwal da yardan Allah zamu shawo kan Anty Binta".
Iska na fesar na ce"Yaaya dukkan alamo sun nuna babu nasara cikin wannan lamarin".
Saurin tarar numfashina ya yi"Kar ki sare in sha Allah matuƙar ina numfashi zan tsaya miki wajen ganin tabbatuwar mafarkinki, musamman yau da muka tattauna da su Abba suma sun nuna goyan bayan su sosai akan hakan kuma sun ji daɗi". Tabbas nayi zarra cikin mata da samun arzikin miji kamar yaaya Yusuf, godiya na shiga yi masa har da ƴar guntuwar ƙwallata.
MATAN AREWA
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 1⃣7⃣
Rabi da rabi baccina na daren ranar ya kasance, na zaƙu garin Allah ya waye ji matsayar zancen nan. Ƙiran assalatun farko kuwa tamkar a kunnena ladanin ya tsala shi tar na buɗe idona ko da na tashi na iske Yaaya Yusuf zaune bisa sallaya yana wurudi, bisa al'ada ko yaushe nayi sammakon tashi tabbas zan iske shi yana wurudi ko yana nafila.
Musayar kallo muka yiwa junan mu kafin na sauƙa na zaune kusan shi ina gaishe shi, sai da ya yalwata annurin dake dashe bisa fuskarsa kana ya amsa mini yana dafa kaina tare da karanto mini addu'ar da ta zamto abinda yake fara yi mini ko wacce safiya, tare muka shige banɗaki muka yo alwala nazo na tada sallah shi kuma Yaaya Yusuf ya fice masallaci. Na daɗe saman sallaya ina addu'ar samun mafita ga bahaguwar rayuwata, mafitar da zata zamto mini maslaha akan komai ya juya ƙuncin ruhina zuwa ga dawwamamman farin cikin marar yankewa. Sai da naji ƙafafuna sun yi sanyi laƙwas na shafa addu'ar ina yunƙurawa na miƙe tsaye tare da zare hijabin dake bisa kaina, haka nan na since kaina da zaba tagumi hannuwa bibiyu ƙirjina yana gudun famfalaƙin da ya haifar mini da runtse idanuna da matuƙar ƙarfi.
Lokaci bayan lokaci nake kai dubana izuwa ga agogon dake maƙale jikin bangon ɗakin, ina duba lokaci don nasan sai takwas in an tashi daga islamiyyar safe Yaaya Yusuf zai dawo, ban san dalili ba sai naga yau gabaɗaya lokacin baya gudu haka nan juyin agogon sam bana ganin saurin sa. Ganin zaman ba zai tsinana mini komai ba ya tilasta mini miƙewa na fito waje na iske Maman Hanan har ta share gidan tsaf, tana shirya Hanan cikin shirin tafiya makaranta na zauna kan tabarmar da na iske malale a wajen na gaishe ta, sai da ta kalle ni sosai kana ta ce"lafiya kuwa kamar bakya jin daɗi?".
Sai da na numfasa na sama zarafin cewa"Lafiya ƙalau Anty".
"Uhmm Na'ima kenan tabbas akwai wani abun sai dai kin ɓoye min".
Jin hakan ya sanya ni feɗe mata biri har wutsiyarsa, shuru ta ɗan yi dai-dai nan ta kammala shirya Hanan yaran makwabtan mu