Showing 9001 words to 12000 words out of 61178 words

Chapter 4 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

mata.


"Ke kuwa meya kai ki wannan mummunan tunanin uwata?, kiyi auren ki shine babban gatan da za'ayi miki yanzu, ƴan mata nawa ne da suka riƙi boko yanzu kuma suke da na sani?. Sun sama bokon amma sun rasa mazajen aure suna nan a gidaden iyayensu cike da nadama".


Furcin Goggo Jummai kenan da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakin kafin ta ƙarisa shigowa. Na tabbata na cigaba da zama a wajen kuka ne zai ɓalle mini, don haka nayi hanzarin miƙewa na fice daga ɗakin, cikin muryata da take rawa na furta"Hajiya ina zuwa zan dawo anjima".


Ban jirayi ta cewar ta ba na fice da sauri izuwa sashinmu kaina tsaye na nufi ɗakinmu. Ban damu da mutanen da na iske a tsakar gidan ba, balle ƙananun maganar da suke yi suna raka ni da kallon tuhuma.
Ɗaƙinmu na faɗa na zube akan katifarmu, kafin na sake wani kuka mai ƙarfin gaske da duk ɗakin ya amsa. Sosai nake rero kukan har izuwa lokacin da Anty Zakiyya ta shigo ɗakin tamkar an jefo ta.




A kiɗime ta nufo ni haɗi da faɗin"Ke ke Na'ima lafiyarki? meye ya faru? meya same ki?". A jere tayi mini tambayar wata na bin wata, maimakon na bata amsa sai ma tsananta ƙarfin kukan nawan da nayi. Ba ta gaji ba ta cigaba da jero mini tambayoyin.


Jin sheshsheƙar kukan da ta fara yi ya sanya ni tashi zaune ina share fuskana kafin na kamo hannunta cikin nawa"Ya isa haka Anty".


"To menene?".


Sai da na dai-daita nutsuwata kafin na ce"Anty Zakiyya yaya zanyi da raina?, dan Allah ki sanar dani abunda zan yi naji sanyi a sashin ruhina, damuwa ya cunkushe mini raina na rasa wanda zan fara warwarewa".




"Ina jinki menene yanzu ya faru?".


Sai da na zuƙe majinar kukan daya zo mini, kafin na ce da ita"Su Abba sun ce walimar sauƙarmu da bikinmu za'a haɗa, har yanzu ni babu wani saurayin da nake kulawa balle har magana mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu a kai ga maganar ƙulla alaƙar auratayya a tsakani. Makaranta nake son na koma amma duk wanda na tunkara rashin yiyuwar abun yake nuna mini hatta Umma da Hajiya Babba, ban sama goyan bayansu ba. Yanzu ma Hajiya Babba ta ƙara jaddada mini akan lalle na fidda miji kafin wa'adin da su Abba suka ɗeba mana ya cika".


Daga ni har ita kukan muke yi babu mai lallashin wani sai da muka yi muka gaji don kan mu. Kafin ta ƙara riƙo hannuna ta sanya cikin nata haɗi da cewar"Na'ima ko nima yanzu abinda suka faɗa miki shi zan ƙara maimata miki. Duk wanda yazo miki da nufin aure to ki gabatar dashi ga su Abba ayi magana a wuce wajen, shin ni ban ishe ki ishara ba Na'ima?. Wallahi ko maƙiyina bana masa fatan jinkirin aure mussamman idan ƙaddara ta sanya ka faɗo a cikin gidan yawa".




"Anty Zakiyya dukkanin jinkiri alkhairi ne ga wanda ya yi imani daga Allah ne, ki miƙa dukkan lamuranki ga Allah domin shine wanda ya tsarawa kowa ƙaddararsa tun kafin a san da samuwar ruhinmu a bayan ƙasa, don haka ya daina damun ki dududu nawa shekarun ki suke. Idan ana wani abun sai ka ce wacce ta shekara ɗari a gida ba tare da aure ba haba".
Taƙaitaccen murmushi tayi"Na'ima kenanke dai yanzu ki mayar da hankali akan wannan maganar da muka yi, idan Allah ya fito miki da miji kin ga ko karatun ne ma kya yi cikin ɗakin mijinki. A wannan lokacin yardarsa kawai kike nema".


Musgutawa nayi kawai ba tare dana iya cewa da ita komai ba, sai can na ce"Maman Walida ta tafi kuwa?".
Ita ma sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kana ta amsa da "Ta tafi tare da Umma, Abba da kuma Baba basu ma dawo ba".
Har na yunƙura da zummar cewa wani abun sai kuma wani tunanin ya shigo mini na kawar da zancen. Mun tattauna sosai da Anty Zakiyya, har naji ɗan sauƙi daga ƙonar da raina yake ya tsirka mini. Umma bata dawo ba sai yamma lilis, da alama a gajiye take aihun ban sama damar tunkarar ta da zancen Mama Walida ba don ta kwanta da wuri. Daren rabi da kwatansa ban runtsa ba, su Balkisu sai faman haɗa zance suke yi zasu turawa samarin su wasiƙa.


Kasancewar duk cikin mu babu mai waya, a aƙidar gidan mu babu wacce ake bari ta riƙe waya sai dai in a ɗakin mijinta in yayi ra'ayin saya mata to.


Washe garin ranar gidan mu ya tashi ciki hidiman tarban iyayen saurayin Salma, Abdallah da iyayensa zasu zo yau. Zo kaga harbin iska da habaici wajen Ummansu haka nan ma Salma sai wani kici kici take da fuska. Abinci da ababen sha aka yi musu domin tarar su, zuwa ƙarfe goma sha ɗaya suka iso falon su Abba aka kai su.


Tunin sauran matan gidanmu da ƴaƴansu, suka firfito domin ba wa idanunsu abinci, ƴaƴansu kuwa ko wacce burin ta da abinda suka zo dashi. Har jikin motocinsu su Abba suka yi musu rakiya sannan suka dawo ciki. Basu yiwa kowa maganar ba illa zarcewa sashin Hajiya Babba da suka yi. Bayan sallan magrib ina zaune a ɗakinmu ina tilawar karatuna su Balkisu suna gefe suna hirar su, ta kullum da take tusa mini takaici Nurain ya shigo ya ce su Abba suna neman mu.


Kallon kallo muka shiga aikawa junan mu kafin, muka miƙe muka fice izuwa sashin su Abba. Abba, Baba, da kuma Baba ƙarami muka tarar a falon cikin ladabi duk muka gaishe su suka amsa. Kafin Baba ya yi gyaran murya kana y soma faɗin"Yau iyayen Abdallah sun zo kamar yanda suka bamu lokaci sun cika wannan alƙawarin. Balkisu da Abasiya suma iyayenku mata sun sanar damu cewar naku zasu turo sati mai kamawa, Na'ima kece kawai bamu ji wani magana mai ƙarfi ba a kanki shin kina da tsayayye?".


Dam-dam shine saurin da ƙirjina ya bada tunin duk jikina ya ɗauki rawa. Sai da ya ƙara maimaita tambayar a karo na biyu kafin na aro jarumta na azawa kaina n ace"Baba bani da tsayayye a halin yanzu sai da..".


"Dakata har yanzu kina da saura lokaci, kiyi amfani da wannan ki fidda miji domin ba zamu saɓa ba a kan maganar aurar daku a tare da ƴan-uwanki, idan kuma ba za ki fitar ba zamu bada ke ga duk wanda muka ji hankalin mu ya nutsu da nagartarsa".


Wasu hawaye masu ƙarfi ne suka ɓalle mini jiyo maganar da Abasiya ta ɓarke dashi.


"Baba akwai wani malami a islamiyyar mu ta safe, kowa ya fahimci yana son Na'ima ita ce dai kawai bata bashi dama ba".


MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________________


Page 0⃣6⃣






Ɗago kaina na kafe Abasiya da kallo da sam ta ƙi yarda mu haɗa ido da ita. Jin sautin muryar Abba sun sauƙa a ƙofofin kunnuwana ya sanya ni kawar da idanuna daga kan Abasiya.


"Na'ima".


Cikin harɗewar harshe na amsa"Na'am Abba".
"Haka ne zancen Abasiya?".


Take wani zuffa ya fara tsatstsafo mini daga dukkan mafitar gashin dake jikina. "Ke nake sauraro".


"E haka ne Abba amma dai bai furta hakan gare ni ba, kawai dai hashashen su Abasiya".


Shuru ya ratsa ilahirin falon, kafin Baba ƙarami ya ce"zamu yi magana zamu neme ku".


Kamar kazar da aka jefa da gishiri haka na miƙe tamkar wacce aka zarewa laka a jiki. Ɗakinmu muka nufa dai-dai sannan masallacin dake kusa da gidanmu aka ƙwala ƙiran sallan isha'i. Sai da nayi salla na je ɗakin Umman duk abinda ya faru duk na fayyace mata.
Sai da na ƙare zancen na kai aya kafin ta kallo ni gami da cewar"Na'ima ki karɓa duk hukuncin da suka yanke ba zasu taɓa yi miki mummunan zaɓi ba, don haka ki taushi zuciyarki kiyi biyayya ga dukkan hukuncin da zasu zartar a kanki inji Mamana?".


Kaina na ɗaga mata ina matse ruwar ƙwallar da suka wadaci idaniyata a ƙoƙarin hana ta gano hakan, ban yi zaman mintuna ashirin ba nayi mata sai da safe kafin na leƙa ɗakinsu Anty Zakiyya ita ma kuma yiwa juna sai da safe.


Juyi kawai nake yi akan katifar namun domin na ƙudurce a raina cewar ko meye zai je ya dawo, ba zan taɓa tanka wa Abasiya akan abinda tayi ba. In ma da wani nufin ta aikata hakan a gare ni to bazan taɓa bata damar cimma manufarta a kaina ba. Ƙiran sallan asubahin farko kuwa kamar a ƙofofin kunnuwana aka ƙwala ta ko da nayi sallan kwanciyata nayi a bisa katifar mu don sam bana da niyyar zuwa islamiyyar.


"Ke Na'ima amma dai kinnsa ke muke jira ko?, aikin banza kawai ke sai wulaƙanci da shegen jin kan tsiya". Ko ɗaga kai ban yi nayi mata kallon arziki ba balle har ta sanya rai ga samun amsa daga gare ni, mirginawa nayi na kwanta ruf da jiki tare da lumshe idaniyana.


Dogon tsakin ta tsirkar mini tayi ficewar ta tare bankaɗo ƙofar ɗakin da matuƙar ƙarfi. Ko a jikina ban san meya faru ba cikin su babu wacce ta ƙara zuwa da zummar yi mini magana. Ban fito ko ƙofar ɗakin ba har sai da haske ya fara kawar da duhun asubahin da ya lulluɓe garin na tashi na share mana ɗakin. Sannan na fito nayi wanke wanke na nufi ɗakin Umma na iske ba ta nan tana sashin Hajiya Babba, don haka na gyara ɗakin kana na leƙa ɗakinsu Anty Zakiyya na tarar tana bacci.


Hakan ya sanya ni komawa ɗakinmu na fara tilawar karatuna sai da na haɗa shafi goma sha biyar, sannan Salma tayi sallama bata jira amsawa ta ba. Ta faɗo ɗakin tana jifa na da kallon uku saura kwata ban mayar da hankalina a kanta ba, har sai da Balkisu ta shiga.


"Na'ima! Na'ima".


Da kallo nake alamta mata menene?. Cike da zaƙuwa take cewar"Na'ima malam Yusuf ne gashi can a ƙofar gida yazo wajen ki".
Wani kallo na watsa mata sam na gaza furta mata koda kalma ɗaya ce, ɗauke kaina kawai nayi daga gare ta raina yana mini matuƙar ɗaci, na rasa gano dalilin su Balkisu wajen mutumin nan. Shigowar yaya Maji fuskarsa tamkar gonar auduga yana cewar"Na'ima kina da baƙo a waje".
Yana gama furzar da zance ya saki labulen ɗakin ya fice, ba don raina yaso ba na zara hijabi na. Na fice bayan na gama wurgawa su Balkisu harara.


Tsaye da yaya Majid na iske su,ɗ ganin fitowa ta ya sanya yaya komawa cikin gida, a nutse na ƙarisa inda yake tsaye da siririyar sallama a bakina ya amsa idanunsa suna kaina, kaina a ƙasa na gaishe shi ya amsa shuru ya biyo bayan zancena na ƙarshe.
Har izuwa lokacin da ya yi gyaran murya ya ce"yau ba ki je islamiyya ba, shine na tambaya ƴan-uwanki suka shaida mini suma ba ki sanar dasu dalilin rashin zuwan takin, na ce bari na biyo sawu lafiya dai ko?".


"Lafiya ƙalau kawai bana jin daɗin jikina ne".


"To Alhamdulillah daman kullum hakan ake fata Allah ya ƙara lafiya".


"Amin".


Na amsa dashi cike da ƙosawa da sauraronsa, ban sabni ba ko dan ban saɓa tsayiwa da saurayi bane, ya haifar mini da rawar jikin da nake fama dashi oho don gabaɗaya jikina ya ɗauki mazari.


Ban sa ni ba ko lura ya yi da hakan,ɗ ya sanya shi furta"To ni zan koma sai kuma wani lokacin ko?".


"To nagode Malam".


Laulausan murmurshin da ya jefo ni dashi, ya sanya ni yi masa kallon ido cikin ido ya ƙara sako mini wata kafin ya juya ya ɗauki hanyar tafiya. Sai da na sauƙe numfashi kana na juya zan shige gida, nayi kiciɓus da yaya Majid a zaure ya ce zuwa anjima nazo na same shi yana son magana dani.
Da to na amsa dashi na bashi hanya ya fice ni kuma na shige ciki, sashin Hajiya Babba na wuce na iske ta zaune tana jan carbi, kusa da ita nayi wa kaina mazauni raina cunkushe da tunani marasa adadi sam na gaza gano manufar murmushin nan ta Malam Yusuf.


Tunin naji kaina yana juyawa ban san Hajiya Babba na mini magana ba sai da taɓo ni na dawo figigi daga tunanin da na fara zurmawa cikinsa.


"Na'am Hajiya magana kike yi?".
Sai da ta ƙare mini kallo mai kama da na tuhuma kana ta ce"Tunanin meye kike yi?".




"Babu komai".


Na faɗa ina ƙoƙarin dasa ƙirƙirarriyar murmushi akan fuskana bata ce da ni komai ba, ganin hakan ya sanya ni miƙewa na gyare mata ɗakinta tsaf sannan na wanke banɗaki. Sai da na gama na fito zan wuce sashinmu na tarar da baƙin a sashinsu Abba, sai da na shigo cikin gida nake jin tsegumi wai iyayen mijin Anty Kubra ne ɗakin Ummata na nufa na gaishe ta, kallon da Anty Zakiyya take mini ya hanani sakat sai ƙunshe dariyar dake son kuɓuce mata take yi.


"Ina kika shiga ne tun bayan sallan asubahi ban ganki ba?".


"Umma ina sashin Hajiya Babba".


Wani kallon Anty Zakiyya ta kuma yi mini nayi mata alama da ido akan lafiya kuwa ta ce dani"Ke dai ki faɗi gaskiya yarinya".
Kallon rashin fahimta na bi ta dashi"to kenan yanzu ba gaskiyan na faɗa ba?".
Ɗage mini kafaɗa tayi alamar bata sani ba, kana ta zauna kusa da Umma ta ce"Umma yarinyar nan baƙo tayi ɗazu wai malamin islamiyyar su haka naji yaya Majid yana faɗa don dashi suka fara zantawa".


"Na'ima haka ne zancen Zakiyya?".


Nan take naji yawun bakina ya tsaya cak tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya ƙafe, a sanyaye cike da kunyar Umma na ce"E haka ne".


"To da yazo me kuka tattauna dashi?".


"Umma kawai yazo ganin lafiya ne yau banje islamiyya ba shine kawai fa".




Na ƙare zancen ƙarshen kamar zan fashe da kuka, murmushi na hango fal a shimfiɗe a bisa fuskar Ummata bata kuma cewa dani ko kanzil ba, hakan nan na gaza gano manufa da maƙasudin wannan annurin fuskar natan. Shigowar Nurain ya katse mini karatun wasiƙar jakin da nake yi a raina yana faɗin wai nazo muci abinci inji su Salma. Miƙewa nayi muka fita a jere dashi har ɗakinmu na zauna zaman cin abincin, ko kaɗan naƙi ba wa kowacce daga cikin su fuskar da har zata yi mini wani maganar banzan har muka kammala cin abincin.






Ɗakin yaya Majid na wuce kowacce mata tayi cirko-cirko tare da ƴaƴanta sun kafa tare da tsarewa, da son jin ƙwaƙwaf akan zuwan iyayen Habibu mijin Anty Kubra. Da sallama na tura ƙofar ɗakin ya bani iznin shiga yana zaune kan katifarsa dake yashe a ƙasa a cikin ɗakin na zauna kusa dashi. Sai da ya rufe takardar dake hannunsa ya ajiye ta gefe guda, kana ya fuskanto ni da kyau ya ce dani"Na'ima ince dai Malam Yusuf ya sanar dake dalilin wannan zuwan nasan?".
Dam-dam shine sautin da ƙirjina ya bata, kafin nayi nasarar fizgo numfahsina da yake maƙale mini a ƙirji"A'a ya dai ce yazo ne ya duba ko lafiya yau banje islamiyya ba".


Sai da yayi nisa ya ce"To ya sanar dani cewar yana sonki, kuma idan an bashi dama yana son ya gabatar da kansa ga su Abba, a shirye yake sai a haɗa bikin da na su Salma".
Banje dashi komai ba don zantukansa ya gama shayar dani giyar mamakin da har yanzun mayenta ya ƙi saki na.


"Don haka ki bashi dama za kuma a gudanar da binkici a kansa matuƙar an same shi da kyawawan halayya kinga kawai sai ya turo iyayensa". Sanƙarewa nayi a wajen ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya gagare ni, sai can na ce"Yaya Majid amma nifa bai furta hakan a gare ni ba sai nake ga kamar anyi sauri".


"Haba Na'ima menene abin sauri? ince dai ba ki manta a cikin satin ukun da ya rage yau kun cinye kwana biyar ba?. Na'ima ki amshe Malam Yusuf hannu biyu-biyu".


Sai da ya numfasa kamin ya ɗaura da faɗin"Na'ima a yanzu maza ne kawai suke auran waɗanda suke so, saɓanin MATAN AREWA da suna aura wanda yazo musu ne, kuma ya shirya yin auran don haka ki amshi malam Yusuf".




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


____________________________________






Page 0⃣7⃣




Sosai ƙirjina yake mini lugudan dukan tara-tara sau tara sai da na runtse idanuna da tunin suka wadato da ruwar ƙwalla. Kafin nayi nasarar raba tsakanin haƙwara da suke karafɗiya da juna suna bada sautin ƙas ƙas ƙas kamar sabuwar haihuwar jinjirar kazar da ruwan sama ya yi mata ɗan banzan duka.


"Yaya Majid ba wai zan bijirewa su Abba bane, ko kuma na haucewa nauyin mu da yake kansu da suke ƙoƙarin sauƙewa. Wallahi karatu nake son komawa ina son na koma makaranta ina son nayi karatu mai zurfi, ina son na zamto ma'aikaciyar aikin jarida kuma marubuciya da sila ta zan kawo sauyi ga rayuwar MATAN AREWA".
Har na ƙare zancen na kai aya bai ɗauke idonsa daga gare ni ba, sai da ya numfasa kana ya ce"karatu in kina rabo a cikin sa ko kina ɗakin mijinki za ki yi ta. Mata nawa ne suka yi karatu har suka cimma muradin ransu ahalin suna gidaden mazajensu? wasun suma uwaye ne masu ƴaƴa, abin kawai sa rai da kuma jajircewa yake buƙata".
Sosai maganganunsa suka ratsa ni nasan duk zantukan nasan suna da nasaba da irin tunanin Umma da Anty Zakiyya, kar nayi sarere da malam Yusuf na sake reshe na gama ganye. Na kore malam Yusuf kuma na rasa tsayayyen da zan tsayar a gaban su Abba.


Wayyo zuciyata zafi take yi mini raina yana mini soya, ƙirjina yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi tamkar zai ɓalle ya fito waje bayan ya ratsa nama da fatana.
"Shikenan Yaya Majid, in sha Allah in ya dawo ya furta hakan a gare ni zan bashi dama".


Na ƙare zancen cikin karyewar murya matso ni yayi sosai kana ya ce dani"Na'ima in sha Allah za kiyi wannan karatun da kike da burin yin sa, da kaina zan yiwa shi Malam Yusuf ɗin magana akan hakan kinji kar ki damu akan wannan". Kaina na gyaɗa masa ya sakar mini da murmushi, duk da halin da zuciyata take a ciki sai da nayi dauriyar mayar masa da murmushi.


Ɗakinmu na wuce bayan na ratsa matan gidan mu kaf, cirko-cirko a tsakar gida an haɗa wata rigimar da ban tsaya sauraran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login