Showing 54001 words to 57000 words out of 61178 words

Chapter 19 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt

idona ga Husnan kuma zaka koma".


"In sha Allah makamancin hakan ba zai ƙara faruwa ba, Allah ya huci zuciyarki".


Na furta ina ƙoƙarin danne ƙwallar da suka ciko mini koramar idanu. Ta taɓe baki da faɗin"Ya fi dai".
"Ina Husnan?, sai tazo mu tafi".


"Ta shiga makwabta bari Amir ya ƙira ta, kafin nan ga furar da Abbansu jiya ya kawo na ajiye maka ita". Ta miƙe tana ɗauko masa ƙwayar furar. Da ɗan murmushi ya ce"ai kuwa na gode a sa min a leda mu tafi da ita".
A faƙaice ta galla masa harara haɗi da faɗin"saurin me kake yi?, a nan nake son ka shayen ta".


"To bari mu sha da Na'ima don tayi min yawa".


"Ita ma ai ba mantawa nayi da ita ba akwai nata".
Jugum nayi kamar mai karɓan gaisuwar mutuwar iyayenta, har ya gama shanye furar tsaf. Saboda hirar da take jan shi dashi ya yi hamdala kana ta ɗauki ƙwarya ta fita dashi, a kofi ta kawo mini na ce na ƙoshi ɗage kafaɗa tayi cikin halin ta kula ta ƙira Amir ta ce ya ɗauka ya fita dashi. Sai da muka jira Husna ta dawo kana muka tafi.


Muka iske yaya Auwal har ya dawo ban sani ba ko yaya Yusuf ne ya sanar dashi abinda yake faruwa. Ya ƙira Husna yana mata faɗa tare da yi mata kashedin kar ta ƙara zuwa gida ta ce anyi mata wani abu ta same shi ta faɗa masa.
Har mun kwanta muka jiyo bugun ƙofa, ya saki tsaki sannan ya zara rigarsa yaje ya buɗe Husna ce tsaye riƙe da bargonta ina jin tana faɗin wai tsoro ne ya hana ta bacci.


Nayi zaton zai je ya yi mata addu'a ne ta kwanta ya dawo, sai naga saɓanin tinanina. Don maganar da ya faɗa da suka sanya ni zargin na'uran dake jiyo mini zantukan da mutane suke furtawa ne bata naɗo mini muryarsa dai-dai ba.


"Na'ima ku kwana tare da ita kawai ni bari naje falon na kwanta".


Yana ƙarishewa ya fice tare rufo mana ƙofar, ko kallo ban ishe ta tazo ta haye gadon tare da rufuwa da bargonta tsabar takaici tamkar na sanya hannu aka na kurma ihu. Ko da asuba bata tashi salla ba har na wanke banɗaki na fita na gyare tsakar gidan, tare da ɗaura mana girki kafin ya ƙarisa na shige wanka. Ƙam na tsaya ganin gadona da yake jiƙe kamar an yi ɓari na shiga ƙwalawa Husna ƙira sai da nayi baki biyar kafin tazo.


"Me ya faru da gadon nan? inda kika kwanta".


"Fitsari nayi".


Wani hawarwasa zuciya tayi kafin tayi tsalle ta garke mini a ƙirji, sai da na ƙare mata kallon tsaf na ce"Fitsari da girmanki da bakinki? za ki wanka kiyi min fitsarin kwance?".
"In ce dai fitsarin nan kowa ya yi shi lokacin ƙuruciya har ke mai maganar".


Taku biyu ya kai ni gabanta na ɗaga hannu da nufin zagba mata marin da nake da yaƙinin da sai taga gilmawan taurari bisa idaniyata. Kafin na sauƙe mata ta zube ƙasa tana ƙwala ihun na kashe mata ido. A figice na ɗago kaina jin muryar yaya Yusuf a tsakiyar kaina.


"Subhanallahi Na'ima me nake gani haka?, me kuma tayi miki?. Dan Allah ki dunga tausayina mana meyasa ko yaushe kike son haɗa ni da ƴan-uwana ne suna ganin kamar na fifita ki a kan su".
Sororo nayi ina kallonsa kafin Husna ta miƙe ta ƙamƙame shi da saurin ta. Haƙuri ya shiga bata cikin kwantar da murya. Har da fita ya sayo mata cakuleti ban furta masa komai kamar yanda shima bai nemi ji daga gare ni ba, har muka isa makaranta cikin mu babu wanda ya ce ko ƙalla, ko da aka tashi na nufi ofishinsa mai gadi ya dakatar dani tare da bani ɗari biyu wai shi ya ce inna zo a bani na hau adaidaita shi yana da wurin zuwa.




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 3⃣0⃣


Har na iso gida ina cike da mamakin uzurin da ya tasowa yaya Yusuf, domin a sanin da nayi masa baya ƙaunar na hau adaidaita ko sa'ilin da naje gida na taho ban jira shi yazo ya ɗauke ni ba tabbas naga ɓacin ransa. Amma yau da kansa ya ce na hau abin hawa. Tana bacci a falo na iske ta na wuce ɗaki ruwa na watsa nayi sallah na fito barkono na ƙwanƙwasa na soya mana manja kasancewar babu albasan da zamu yi miyar, nawa na ɗeba ita ma na zuba mata nata na bar mata a kicin ɗin.
Tisa abincin nayi a gabana sam na gaza ci tinanin uzurin da ya tasowa yaya Yusuf ya maƙale a raina, yanka huɗu naci naje na ajiye na dawo na kwanta ban tashi ba sai gab magrib.


Koda nayi sallan ban tashi ba sai da nayi isha'i aka kawo wuta a hanzarce na jona wayata a caji domin na samu damar ƙiran yaya Yusuf. GZirki na ɗaura mana nayi dambu, Jugum na zauna riƙe da wayata da na tisa a gaba ƙwalla suna zirara ta gefen kuncina, na ƙira layin yaya Yusuf yafi sau shurin masaƙi amma baya ɗauka ƙiran ƙarshe da nayi masa naji wayar a karshe ɗif. Babu shiri naji wasu hawayen sun ziraro mini zuciyata tana bugawa dai-dai da tashin waƙar Ado gwanja da Husna take rerewa mai taken cas.
Tare suka shigo da yaya Auwal na zabura na tashi tsaye har ya shigo kallo ɗaya ya yi mini naga ya ɗauke kansa, nayi masa sannu da zuwa kansa ya ɗaga mini kawai yana jiwa kansa mazauni akan kujerar mutum biyu dake falon. Kusa dashi na zauna muryata cike da damuwa na ce"yaya lafiya ina kaje yau?, na ƙira wayarka baka ɗagawa duk ka sanya ni cikin damuwa".


Lumshe idanunsa ya yi haɗi da faɗin"Wani uzuri ne ya taso min, ƙiran da kika yi min kuma na gani kawai lokacin ina wani aikin mai muhimmanci ne".


"Amma yaya ko sau ɗaya da ka ɗaga kayi mini bayani ai, ka san tashin hankalin da na shiga kuwa?".


"To wai dole in zan fita kenan sai na sanar dake ko meye kike nufi?". A sanyaye na jijjiga masa kaina ya saki siririyar tsaki kafin ya furta"To wani uzuri ne ya taso min idan kuma tuhuma ta za ki yi, bismillah tunda naga maƙaryaci yau na zamto a idanunki. Duk abinda nake faɗa ba yarda kika yi dasu ba".


Duk wata gaɓar jikina tayi sanyi sosai, na sunkuyar da kaina da hakan ya ba wa ƙwallar da wadaci kurmin idanuna damar zirarowa, cikin muryarta da ta fara rawa nake cewa"A'a wallahi ko kaɗan ba tuhumar ka nake yi ba, tunda ka dawo mini lafiya alhamdulilla Allah ya baka haƙuri".


"Amin".


Ya amsa dashi kamar anyi masa dole ya miƙe zai shige ɗaki nayi saurin faɗin"Abinci fa?".
"A ƙoshe nake".


Daga haka ya shige ɗaki tare da bugo ƙofar da ya tilasta mini runtse idanuna, dariyar da Husna ta sheƙa har da riƙe ciki ya sani cire leɓɓana da ƙarfin tsiya kamar zan huda su. Tashi nayi da nufin bin sa domin na tabbatar da cewar akwai abinda yake damunsa, jin ƙofar rufe ya sani jijjiga ta hakan ya tabbatar mini da ya kulle ta ciki, tilas na dawo na zauna cike da ƙunar rai.


Raina yana amayar mini da wani balbalin tashin hankalin. Tunin naji ƙirjina ya yi mini wani irin nauyi tamkar anyi mini ajiyar wani dutse, bai buɗe ƙofar sai dai-dai lokacin da muke kwantawa ya fito riƙe da bargo da matashi bai ko kalle ni ba ya cewa Husna ta tashi ta shiga ta kwanta, ta amsa tare da miƙewa ta shige ɗakin. Kamar bai san da wanzuwana a wajen ba ya fara tattare ƙanana pillows ɗin kujerar ya ajiye su gefe guda yana ƙoƙarin kwanciya, nayi saurin miƙewa na riƙe bargon hannunsa cikin zubda ƙwalla na jefa idanuna cikin nasa da ya yi saurin kawar da nashi, duk yanda naso mu haɗa ido ya haucewa hakan. Wasu zazzafan hawayen suka shiga ambaliya a tudun fuskana, cikin ƙarfin hali na ce"Yaya menene yake faru? dan Allah ka sanar dani ko wani laifin nayi maka?".


"Ba kiyi min komai ba Na'ima dan Allah hutawa nake son nayi ki bar ni haka".
Ƙara riƙe bargon nayi na ce"Ba zan barka ba yaya ba zan barka ba, har sai ka sanar dani". Tsuka ya yi tare da fizge bargon ya yi kwanciyarsa haɗi da furto mini zancen da suka warware mini notinan kaina.


"In ba za ki kwanta ba, ki cigaba da tsayiwa a nan".


"Innalillahi wa inna ilahir raji'un". Shi kaɗai na iya furtawa kafin naja sagaggun ƙafafuna da jiri ke shirin jefar dasu ƙasa na wuce ɗaki, ko da na shiga na tarar da Husna tsaye bakin ƙofar da alama taji duk yanda muka yi dashi. Wani kallo na watsa mata zuciyata tana kwasa ta akan nayi kukan kura na shaƙe ta, kalmar A'uzibillahi na shiga nanatawa har naji sanya ya tsirgar mini a sashin ruhina. Tsawon daren ban yi iya runtsawa ba domin banɗaki na shiga naci kuka kamar ba gobe, kafin nayo alwala na fito na fara salla na daɗe kan sallayar ina miƙa kokena ga sarkin dake da ikon juya rayuwata.
Washe gari na tashi da ciwon kai amma hakan bai hana ni yin dukkan aikace-aikace na ba. Girkin safe da nayi mana ma bai ci ba, ya ba wa Husna ta ƙara akan wanda na bata. Ban ce dashi komai ba muka tafi makaranta haka muka rabu ba tare da fatan alkhairin da ya saba yi mini ba, wanda nayi masa kuwa a banza wai ƙwalawa bebe ƙira domin ko gizau bai yi ba balle nayi tinanin samun amsarsa, yau gabaɗaya rabi da rabi hankalina ya kaso har aka tashi yau ma mai gadi ne ya bani ɗari biyu kamar jiya na tari abin hawa na koma, daren ranar bai dawo ba sai ƙarfe sha ɗaya saura abinda da bai taɓa yi ba kenan tun bayan aurenmu, ana yin sallan isha'i yake shigowa gida don ko zaman majalisa baya yi.
Har lokacin ban yi bacci ba ko kallon arziki bai yi mini ba ya wuce ɗaki, sai kuma ya fito don Husna har ta kwanta a lokacin, banɗaki waje yanyi wanka ya dawo ya fara shirin kwanciya.


Durƙushewa nayi gabansa cikin zubda ƙwalla, da nake jin zafin su har cikin raina na haɗe hannayena biyu alamar roƙo kafin na ce dashi"Dan Allah yaya ka tausaya mini ka sanar dani abinda yake damunka, wallahi kayi mungun canjawa har ina ganin kamar ba mijina bai tausayi da sanyi bane nake magana dashi. Dan Allah ka sanar ni in wani laifin nayi maka mu fahimci juna".
Zazzafan iska ya fesar daga bakinsa"Babu abinda kika yi min".
"To meyasa ka canja mini?".


Na jefa masa tambayar a gaggauce, ina son haɗa ido dashi domin na lura yanzu gabaɗaya baya ƙaunar hakan.
"Ba komai tunda na ce miki ba komai to kawai ki yarda". Cikin sauƙe numfashi na furta"Shikenan na yarda da kai". Da hannunsa ya yi mini nuni akan na zauna kan kujerar nabi umarninsa ya jawo ni jikinsa kamar wanda ya tina wani abun sai kuma ya zame nashi. Dai-dai sa'ilin da wayarsa ta hau ruri ya ɗaga ban ji abinda ake faɗi ta ɗayan ɓangaren sai cewa yayi"Gani nan zuwa".


Ya katse wayar yana rarumar rigarsa ya saka tare da ɗaukar makullin mashin ɗinsa, har ya kai ƙofar fita nayi saurin faɗin"ina zaka je cikin wannan daren?".


"Anty Binta ce ke son ganina".


"Kayi haƙuri zuwa safe, yanzu fa sha biyu ake nema".


Cike da ƙosawa ya dafe goshinsa"yanzu zan dawo kiyi kwanciyarki kawai". Ya fice a hanzarce kuka mai ƙarfi na saka cike da tausayin kaina ta yanda rayuwa tayi mini juyin juya hali. Kafin na miƙe da ƙyar na tura ƙofar falon na shiga ɗaki, ban san sanda ya dawo ba sai da safe nayi tozali dashi.
Tea kawai ya nema na haɗa masa yasha kaɗan ya bani kuɗin abin hawa, ya ce na hau na tafi makaranta zai tsaya a kasuwa wajen yaya Auwal.


Haka satikai biyu suka shuɗa muna wannan zaman da yaya Yusuf, da ko kalaman bakina zasu ƙare wajen tambayarsa abinda nayi masa cewa dani yake yi babu komai. Hakan nan ko ruwan hawayena zasu kafe kamar tafki da ƙasa ya tsotse ruwan cikinsa ba zan hangi tausayina a cikin idanunsa kamar da ba, sau uku ina tambayarsa zuwa gida yana hanani wai in ya sama lokaci zamu je tare. Babu abinda yake ƙara ɗaure mini rai da igiyoyin baƙin-ciki da ƙunci kamar ko tsakiyar dare Anty Binta ta ƙira shi babu abinda zai hana sa fita yaje shi. Ya daina yarda dani na lura shima wani kallo yake min na rashin yarda akan Husna yana tinanin kamar zan cutar da ita.


Ya daina sauran damuwata ya daina jin matsalata ya daina zama muyi hira dashi, ya daina nuna mini kulawa. Ya daina bani lokacinsa ya daina sauƙe haƙƙina dake kansa ya daina kula ni, ya daina zama inuwa ɗaya dani inda ina falo to yana ɗaki in ko ina ɗaki yana falo tare da Husna domin yanzu ita ya ba wa matsayina na matarsa, da ita yake hira da ita yake dariya da ita yake nishaɗi.


Ban san meyasa ba sam na gaza sanar da kowa ko nayi yunƙuri sanar da Ummata sai naji tamkar an ɗaure mini maƙoshi ala dole na canja ma'udu'in maganar in ba haka ba kuwa na dunga kame-kame kenan. A haka har muka gama frist term nayo ta biyu a ajinmu class rep ɗin mu yazo na ɗaya, Maryam da Hafsa duk suma suna cikin goman farko. Har muka gama sss one babu abunda ya sauya zani wanda a lokacin aurenmu shekara ɗaya da watannin huɗu.


Abasiya ta haihu ba rai shima bai bar ni naje mata ko barka ba. Naci kuka har na godewa rabbi sai ƙiran yaya Majid nayi nayi masa abinda ban taya yi ba a kaf rayuwata watau ƙarya. Na ce masa bani da lafiya ne ba zan sama zuwa ba. Bilkisu ma tayi ɓari da tayi jinya kamar ba zata rayu ba da ƙyar da suɗin goshi ya barni naje duba su gabaɗaya.


Kowa ya yi mamakin baƙi da ramar da nayi abun ba daɗin gani da ido balle suffantawa da laffuzan baki. Kawar da maganar nayi da cewar makaranta ce duk ta saka haka. Duk tambayar da hajiya Babba ta jani sashinta tayi mini har da haɗa ni da girman Allah naji tsoronsa na faɗa mata abinda yake damuwa, amma na kasa sanar da ita na ce ba komai don dole ta ƙyale ni da addu'ar Allah yasa ba komai ɗin kamar yanda na ce.


Ummata kawai na faɗawa jikina har tsuma yake yi tsabar kukan da nake yi. Ita ma idanunta suka kaɗa suka yi jajir ta tsare ni da tambayar menene dalilin da tun farko ban zo na sanar dasu.


"Umma wallahi na kasa sanar da kowa, da farko nayi tinanin komai zai wuce tunda bai taɓa yi mini irin hakan basai daga ƙarshe naga abin yafi ƙarfi na".


Na furta ina ƙara tuntsire da wani matsanancin kuka, rarrashina tayi ta sanar dasu Abba suka ƙira ni domin ji ta bakina. Sannan aka ƙira yaya Yusuf sosai gabana ya faɗi jin sallamar da ya shigo da ita don babu abinda nake tsoro kamar shi, hakan nan babu abinda nake fargaban ji kamar muryarsa. A ladabce ya gaida iyayena kafin Baba ya irge masa duka abinda na sanar dasu, wani mamaki ya mamaye ni da ya hana ni kwakwaran motsi. Domin tuburan nunawa ya yi babu wata matsala a tsakaninmu har da rantsuwar sa ganin hakan ya sanya su Abba yi mini nasiha sosai wai sheɗan ne ke son shiga tsakanin mu. Ummata ce kawai ta fahimci raɗaɗin zuciyata ta dunga tausa ta bayan mun komo ɗaka ta kuma bani wasu addu'o'i ta ce nayi riƙo dasu.


Tunda muka koma gida yake sauƙe mini kwando-kwandon masifar wai kar na ƙarar sa gidan mu, abinda ya kuma yi mini ciwo har Anty Binta ya ƙira ya zayyana ta. Ta cikn wayar ta hau sauƙe mini nata har da faɗin wai inna gaji da zama dashi na fito na faɗa kowa ya kama gabansa haƙuri na bashi maganar ta mutu.
Naci kuka har sai da naji kaina yana juyawa kafin na tsagaita ba don naji sauƙin sanyi daga wutar dake tashi a ƙasan raina ba, sai don lafiyata saboda sosai kaina yake sarawa tamkar zai rabe gida biyu. Alwala nayi nazo na tada salla raka'a biyu ta nafila sannan na fara yin addu'o'in da Ummata ta bani tun daga ranar.


Ina zaune jangwaf a falo ga tvn dake aiki da na tsurawa ido ba ko kiftawa sai dai a zahiri hankalina ba gashi yake ba. Tunin nayi nitso cikin duniyar tinanin da na zurfa cikinsa Husna na zaune a gefe tana ƴar waƙar Ado gwanja na cas, dai-dai sanda ta iso baitin nan da yake faɗin"Sunyi abin ya sha musu kai cas".


Na ɗago idona sakamakon sallamar yaya Yusuf da suka ratso kunnuwana, sannu da zuwa nayi masa da ya yi mini banza. Yana washe fararen haƙwaransa ga Husna da take masa sannu da dawowan ita ma, kusa da ita ya zauna ni kuwa tamkar bai san da wanzuwa na a falon ba. Suna ta taɗin na wasu mutanen daban da ban ma san su ba sai dai nafi tinanin ko dangin su ne na nisa da ban san su ba.
Ganin da gaske bashi da niyyar kulawa ni balle cewa dani wani abun ya sani faɗin"A kawo maka abinci?".


"Naci abinci".


Cikin sauri Husna take faɗin"kawu bari na dafa maka wata shinkafan da na gani jiya a talabijin ana girkawa". Da mamakina naji ya amsa bata da"To shalelen kawu ina fatan dai ba zai ɗau lokaci ba?, don na gaji kwanciya nafi buƙatar nayi yanzu haka".
Kanta ta ɗaga masa alamar ba zai ɗau lokaci ba ta miƙe ta fice izuwa madafan wani kallo na bi shi dashi raina a cunkushe, kamar ba shi bane yanzu nayi masa tayin abinci ya ce ya ƙoshi ba. Idanuna har sun rufe tsabar baƙin ciki nake faɗin"Amma yanzu na maka tayin abinci ka ce ka ƙoshi". Ba tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login