Showing 30001 words to 33000 words out of 61178 words
Chapter 11 - MATAN AREWA Book 1 Complete Document .txt
suka shigo suka tafi tare, don yau Yaaya Yusuf ya yi lattin dawowa har takwas ta gota. Rungume ni Hanan tayi domin wannan ne hanyar da muke sallama da ita ko yaushe idan zata fice.
"Na'ima kenan har yanzu kina nan kafe akan wannan ƙudurin nakin, to Allah ya ba ki sa'a ya basu nasarar shawo hankalin Anty Binta".
Muryata a karye na amsa da"Amin ya Allah na gode".
Tare muka yi karin kumallo sannan na haɗa wanke-wanke nayi, ina wanke ƙafafuna Maman Hanan ta fito saɓe da hijabi a kafaɗa tana faɗin"Na'ima zan shiga gidan Maman Anwar yanzu zan dawo".
Gajeran murmushi nayi haɗi da cewar"Anty na lura akwai aminci sosai tsakanin ku da Maman Anwar ɗin nan, ba garin Allahn da zai waye bata zo gidan nan ba kema baki je mata ba".
"Na'ima kenan ke dai kawai ayi sha'ani amma tsayawa faɗin irin amincin dake tsakanin mu da Maman Anwar ma ɓata lokaci ne. Duk yanda kike tinani ta wuce hakan a gare ni domin tayi min abinda har ƙasa ta rufe min idaniya ba zan mance da halalcinta gare ni ba, ta share min hawaye a lokacin da ko ƴan-uwan da muka fito ciki ɗaya dasu uwa ɗaya uba ɗaya suka gaza fahimta ƙuncin da zuciyata take ciki, ke dai sai na dawo kawai".
Ta faɗa cikin sausauta amon muryarta kafin ta fice fu kamar iska ba tare da ta bani damar cewa komai ba. Da kallo na bi ta raina cike da juyayin maganganunta duk me hakan yake nufi?, meye kuma Maman Anwar ɗin ta aikata mata da har take ikirarin ko ƴan uwan jininta basu yi mata ba?.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya na sauƙe kafin na miƙe zan shige ɗaki, sallamar da aka rankaɗa da suka sauƙa a masarrafan jina suka dakatar dani baki sake na zura a guje na rungume Balkisu da Abasiya da suke tsaye tare da Asma'u.
Sam bakina ya gaza rufuwa na ja hannayensu izuwa ɗaki na kawo ruwa kallon sha'awa na bi Abasiya dashi domin tayi bul-bul abin ta ga wani haske da sheƙin da fatarta take fitarwa baki sake nake faɗin"Abasiya wannan kyau haka kin ganki kuwa? ko dai Sagiru ya yi ajiye ne?". Fashewa muka yi da dariya ni da Balkisu har da tafa hannu fari Abasiya tayi da iya idanu kana ta ce"Ba wani sirrin da ya ɗara kwanciyar hankali da kuma soyayyar mijina, ga cima mai kyau naci mai kyau na sha mai kyau meya wuce haka kuwa".
Murmushi nayi taƙaitacce ina sunkuyar da kaina ƙasa, sai naji maganganunta sun yi mini kamar da ba'a take yi mini don haka na kawar da zancen ta hanyar faɗin"Abasiya kenan Allah ya kyauta, ya Salma fa kuna magana da ita?, tunda tazo tayi mini sallama shikenan".
"Lalala Salma in gaya miki tana can Katsina da Abdallah, rannan da naje gida ta ƙira Ummansu har mun gaisa na karɓa lambarta".
"Allah sarki Salma nima zan karɓa lambarta in sha Allah, karɓi ki sanya mini".
Na miƙawa Balkisu wayata ta sanya mini lambar, sosai muke hirar mu na yaushe gamo cikin raha da kewar juna. Annuri da dariya ya ƙi yankewa daga fuskana har sai izuwa lokacin da Abasiya tayi wata maganar da ta daki kwakwalwata ta kuma munana ƙalbina, na nema dukkan annurin nan na rasa kamar anyi kuka an ɗauke.
"Na'ima ina ita facalan nakin?, naga tun zuwan mu bamu ganta ba. Hmm yanzu haka kike haƙurin zama da facala wanda kaidinta yafi na kishiya yo wallahi ni da in zauna da facala gwara Sagiru ya auro min kishiyoyi uku rigis lokaci guda mu zauna tare. Cabɗijam ina zan zabari wannan wahalar".
Taune leɓɓana nayi kafin na furta"Abasiya kenan ni wallahi duk babu wannan cikin zamana da Maman Hanan, dan Allah kar ki sake zuwar mini da makamanciyar wannan zance. Yanzu idan da tana cikin gidan nan taji wannan zancen me kike tinanin zai faru?, gaskiya bana son irin hakan".
"Gaskiya kam Abasiya kiyi wa bakinki linzami in taji wannan zancen ai sai ki haddasa musu rigima cikin zaman su". Furcin Balkisi kenan na ɗauke kaina gefe ban jiyo ba sai da tayi wata zancen.
"Ƴar-uwa yanzu daga gida muke nake jin wani zance wai Malam Yusuf yaje sun tattauna da su Abba akan maganar komawar ki makaranta. Gaskiya naji miki daɗi wallahi burinki zai cika koda mu bamu sama damar yi ba ke in kin:yi kamar mu dukka ne muka yi, wataƙil ta sanadiyarki ma su Abba su fahimci muhimmancin karatu ga ɗiya mace har sauran ƙannen mu na gida suma su sama damar yi".
"Haka ne Balkisu amma har yanzun akwai sauran rina a kaba domin akwai wata babbar ƴaƴar su wacce bata amince ba kuma basa gudanar da wani abun ba tare da amincewarta".
Dafa kafaɗata Balkisu tayi tare da sausauta murya ta shiga faɗin"Na'ima in sha Allahu ina ji a jikina sai kin cika wannan burin nakin, duk wata nasarar da za ki ai ƙara ɗaga kimar gidanmu za ki yi. Nima da ina da irin kwakwalwarki ai da na roƙi Aminu na jona amma ina".
Murmushin dole na sakar mata ina hange Abasiya da ta yi mana kunnen uwar shegu tamkar bata jiyo abunda muke faɗi, daga bisani ma ta shiga latsa wayarta.
Mun ɗau lokaci muna hirar mu har aka yi ƙiran sallan zuhr na ɗaura mana girki muka ci, har yanzun Maman Hanan bata dawo ba tare da Hanan yaaya Yusuf suka dawo suka gaisa da su Abasiya, Balkisu sai tsiya take masa wai ya mayar dani matar kulle ko gidajen su ban je ba tun bayan biki. Murmushi kawai ya yi musu tare da alƙawarin cewar duk zan je musu.
Wanke Hanan nayi na sauya mata kaya taci abinci sannan nayi mata shirin islamiyya, Abasiya sai faman tsaki take tsirgar mini tana faɗin"Ke dai Na'ima wallahi rayuwarki ta shiga uku, ke ba ki haifa ba amma an barki da reno ko amarci ba ki gama ci ba an barki da renon ɗiyar wasu, ke kika ga za ki iya aikin wahalar da ba sannu balle madalla".
Murmushi kawai nake sakar mata har na gama shirya Hanan ta wuce islamiyya har wannan lokacin mamanta bata dawo ba, har su Abasiya suka tafi na gyare gidan tsaf nayo alwalan sallan asr Maman Hanan ta dawo sannu da zuwa nayi mata nayi shigewa ta ɗaki nayi salla.
Sai da aka yi sallan magrib Yaaya Yusuf ya dawo tunin na haɗa masa ruwan wanka na kai masa ya shiga ya yi sannan na ciyar dashi abinci. Kallo ni ya yi ya ce"Ba ki tambaye ni yaya muka yi da yaya Auwal ba?".
Sai da na sauƙe numfasi na ce"Yaaya kenan so nake ka huta sannan na taso maka da zancen".
"Na sama shi mun tattauna akan batun kuma ya bani dukkan goyan baya akan hakan. Mun sama ƙanin mahaifinmu da maganar shima kuma ya amince ya kuma tunkari Anty Binta da zance har ya yi nasarar shawo kanta, yanzu dai a taƙaice ta aminc....".
Ban bari ya ƙare zancen ba na bi na ƙananneye shi ina jero masa kalaman godiya. Bai dakatar dani ba sai da na tsagaita don kaina kana ya ɗaura da"Har wajen su Abba ma naje kuma alhamdulillah suma sun amince, kar kiso kiga murnar da yaya Majid ya yi, sun ce gobe na kai ki".
Sosai naji jikina ya yi sanyi lura da hakan ya sa shi tabbatar mana da cewar babu komai. Gama bashi abincin nayi a gurguje ya fice masallacin sallan isha'i. Da murnata na fito ina shaidawa Maman Hanan, sosai na ke iya hango tsantsar murna ita ma cikin idanunta har rungume ni tayi, tana yi mini fatan alkhairi hakan ya ƙara tabbatar mini da cewar tabbas nayi sa'ar samun facala saɓanin yanda ƴan-uwana suke tunani tare da yi wa dukkan facala kuɗin goro. Na raya daren ranar da sallan dare sosai tare da addu'ar Allah ya sa na fara wannan karatu cikin sa'a da nasara.
Wayewar safiyar ranar muka yi waya da Salma taji daɗin ƙiran da nayo mata sosai, na shaida mata komai sosai tayi mini fatan alkhairi. Sallamar Anty Binta da suka yiwa ƙofofin kunnuwana dirar mikiya ya sa 1ni sakin wayar ba tare da na katse ƙiran ba, saboda matsananciyar bugun da ƙirjina yake yi tamkar zai faso nama da fatana ta fito waje.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un". Na furta cikin sarƙafewa harshe ina jawo numfashina da yake cushewa da matuƙar ƙarfi.
MATAN AREWA
©Maimunah TIjjani Iyam
_________________________________________
Page 1⃣8⃣
Tun kafin na fito naji wasu zuffa mai maiƙo ya jiƙa mini goshina. Ajiyar wayan nayi na fito da hanzarina tana tsaye a tsakar gidan Maman Hanan tana shimfiɗa mata tabarma, sai da na rusuna na gaida ta ƙara yatsine fuska tamkar wacce taga ɗanyen kashi sakin yau, bata ce da ni uffan ba ta wuce tayi zamanta bisa tabarman da Maman Hanan ta shimfiɗa. Ban yi ƙasa a gwiwa ba na kuma jan ƙafafuna na zauna na buɗe baki da zummar ƙara yi mata wata gaisuwar da sannu da zuwa ta dakatar dani ta hanyar ɗaga mini hannunta alamar bata son jin komai daga gare ni kafin ta shiga faɗin"Ba gaisuwar ki ce ta kawo ni cikin gidan nan ba, abinda ya kawo ni shi zan yi nayi ficewa ta na bar muku gidanku. Tunda yanzu kowa ba ganin kimata yake yi ba balle ayi mini kallon mai gashi".
Bugun da ƙirjina yake ni ya tsananta wanda nima kaina na gaza gano dalilin harbawan natan. Zancen da Anty Binta ta ɗaura dashi a harsale shi ya dawo dani daga karatun wasiƙar jakin da na dulmiya.
"Auwal da Yusuf sun nuna min iyaka ta akan su, sun nuna min ban isa ga gidansu ba balle ku iyalansu".
Tsagaitawa tayi na wucen gadi na ɗago kaina cikin sanyin jiki muka haɗa ido da Maman Hanan kafin muryar Anty Binta ta katsar damu"Yau kimanin shekaru goma sha bakwai da rasuwar iyayenmu tun Mahmud bashi da wayo, nake riƙe da ƙannena har aurena na farko ya sama matsala domin su amma ban karaya na yatsar da amanar su da iyayenmu suka damƙa min ba. Basu taɓa yi min musu ba balle bijirewa umarnina ko kara na ajiye basa tsallake ta balle suyi yunƙuri keta hukuncina. Sai yanzu har zamu yi musayar yawo tsakanina da Yusuf da Auwal har da kai ƙarata gaba, duk akan ki Na'ima kin cuce ni kin tarwatsa min kan ƴan-uwa duk domin cimma muradin ranki wanda ko a addinance na san bani da laifi don na hana ki komawa boko kamar yanda kike so, sha'awar samun rabauta nayi miki ta hanyar inganta miki gidan aurenki amma kika saka ƙafa kika shure. Burinki ya cika tunda Yusuf ya haɗa ni da wanda babu yanda na iya dashi kije kiyi bokon amma ki sa ni dukkan abinda ya taso sanadin wannan karatun wallahi ba zan ɗauka ba, haka nan Yusuf ko da amincewarsa ko babu zama a tsakanin ku zai zo ƙarshe".
Dirsham nayi zaman ƴar bori take jikina ya ɗauki rawa ba kaɗan ba kalamanta suka daki kwakwalwata, ban iya cewa da ita komai ba illa Maman Hanan tayi ƙarfin halin furta"Haba Anty a matsayinki na babba mai kamace ki ba furta irin wannan kalamin, ita ƙaddara babu abinda yake tare ta ko hana wanzuwanta cikin mu babu wanda yayi zaton hakan zata kasance. Kiyi mata fatan alkhairi domin kamar yanda shi Yusuf ɗin yake jininki ita ma fa haka take abar so ce ga ƴan-uwant..".
Katse ta Anty Binta tayi ba tare da dire zancen da ta ɗauko ba, sai ta kalle ta tsaf kana ta ce"Dalla rufa min baki ke har me kika sa ni game da zaman duniya, yaushe ma Lamin ta haife ki aka yi auran nakin?. Ko don kinyi haihuwar wuri kafin ki rufa shekara?. Anyi min fin ƙarfi akan lamarin nan amma ga fili ga mai doki ina nan ina zaune za'a je a dawo wata matsalar zata kunno kai a dalilin wannan bokon, yayin da zan zame kaina na sulale kamar kifi babu wanda zai sa ni".
Kamar kazar da aka kwararawa tafashashshen ruwan zafi haka na jawo jikina na matso gabanta, cikin rawar jiki da na murya nake cewar"Anty dan Allah kiyi haƙuri bani da wani mungun nufi ko wani mummunan ƙuduri game da wannan lamarin, Allah ne shaida ta sannan shi ya san abinda yake ɓoye cikin raina shi kaɗai zai iya yi mini adalci. Ban tirsasa Yusuf akan wannan batun ba hasalima shi ya ƙara bani ƙarfin gwiwa, da ban sama goyan bayan sa ba tabbas babu yanda na iya dole na haƙura. Ina roƙon ki da ki bini da fatan alkhairi da addu'ar samun nasara in sha Allah zan kare mutumcin kaina da igiyoyin auren da suke kaina".
Miƙewa tayi tsam! haɗi da cewar"Ai yi dai mu gani in tusa zata huta wuta". Tana gama furta hakan ta ja ƙafafunta ta fice daga gidan rai a matuƙar ɓace babu shiri naji wani kuka ya turniƙe ni, na kuwa sake shi da matuƙar ƙarfi Maman Hanan tana aikin lallshi na tare da bani baki. Cikin sarƙafewar harshe nake cewar"Anty na fara karaya na gaza gano inda maganganunta suka dosa tana tinanin ba zan iya riƙe kaina ba kenan?, Wallahi bana ɗaya daga cikin irin waɗannan matan Anty ki yarda da ni". Na ƙare cikin matsananciyar kuka lallashi na ta cigaba dani har na tsagaita da kukan kamin ta ce"Na'ima dukkan nasara bata samu sai an fuskanci ƙalubale masu tarin yawa, duk wanda kika gani a tudun nasara tabbas ya wuce bigiren tudu da gangare masu wuyar tsallakewa don haka kar da ki sare. In sha Allah wataran za ki cika burinki".
Shuru kawai nayi ba don maganganunta sun sama gurbin zama a cikin kaina ba, tashi nayi naje na wanko fuskana na gama wasu aikace-aikace na duk jikina babu kuzari har yaaya Yusuf ya dawo daga islamiyyar safe ban gama warewa ba. Smai dai ban bayyana masa komai ba duk yanda ya kai ga tambayar dalilin canzuwar yanayin nawan cewa dashi nayi kaina ne ke yi mini ciwo, haka nan na roƙo maman Hanan akan bana so Abban Hanan ko Yaaya Yusuf su san da zuwan Anty Bintan bana son ta dalilina su sama rabuwar kawuna. Da ƙyar na zaunar dashi yaci abinci don sam baya son cin abinci, sai da ya gama ci ya ce dani na shirya da ya dawo zamu je gidanmu.
Ranar na wuni jikina gabaɗaya babu kuzari, lura da haka ya sanya Maman Hanan bata fito ko'ina ba ko gidan maman Anwar ɗin da bata fashin zuwa bata je ba. Har Yaaya Yusuf ya dawo muka shiryo zamu tafi na leƙa ɗakinta nayi mata sallama ta rako ni har ƙofar ɗakin tana faɗin"Da na san da fitar ai da tun daren jiya, na tambayi Abban Hanan izni mun je tare".
Murmushi na ƙaƙalo na ce da ita"Babu komai Anty wataran sai muje".
Sai da muka tsaya a hanya yaaya ya saiwa su Abba kankana da su abarba Hajiya Babba da su Ummata kowa nasu daban sai dariya nake yi masa haka nan muka wuce gida a ƙofar gidan ya faka. Kallon shi nayi ina ɗage masa ido ɗaya ganin ya tsaya a ƙofar gidan"Lafiya Yaaya ka tsaya a nan ba zaka shigo bane?".
"Ki dai shiga kiyi wa yaya Majid magana ya fito ya yi min jagora wajen shiga wajen su Abba".
Dariyar dole zancen nasan suka sanya ni"Lalle Yaaya wannan kunyar nakan sai ka ce wata mace, ai yanzu an zama ɗaya nan fa gidan ku ne to meye sai anyi maka wani jagoranci kuma?". Na ƙare zancen har da ƴar shagwaɓata murmushi ya yi kamin ya ce"Haka ne kam su Abba iyayena a gare ni, tunda suka haifo min macen ƙwarai kamar ki".
Murmushin jin daɗi naji ina rausayar da kai, na wuce gaba yana biye dani ɗakin yaya Majid rufe yake an danna masa makulli don haka sashin Hajiya Babba muka fara shiga ta tarbe mu cikin fara'a da matuƙar jin daɗi, tsabar murnar ganin mu har rasa inda zata ajiye mu tayi kamar zata maida mu cikinta.
Mun daɗe a wajen ta har sai da Baba ƙarami ya shigo muka gaisa, na miƙe izuwa sashin mu da mamakina na tarar da tsakar gidan kamar anyi shara domin babu kowa daga matan har ƴaƴansu.
Ɗakin Ummata na nufa kaina tsaye, na iske ta da wasu mata biyu gani na ya sanya ta sallaman su a gaggauce. Matsowa jikinta nayi na gaishe ta a ladabce ta amsa mini tana bina da kallo a ƙoƙarin son karantar yanayin fuskana. Katse kallon nayi ta hanyar faɗin"Umma ina Anty Zakiyya fa tun shigowata ban gan ta ba?".
"Na aike ta gidan Asabe karɓo min saƙo amma na tabbatar duk inda take yanzu tana kusa da gida, yaushe kika zo ke ɗaya ce ko da mijin nakin?".
"Mun ɗan daɗe a sashin Hajiya Babba muka zauna tare muke".
Kanta ta ɗaga ta ce"Lafiya ko?, don naji zuwan nakun yau a bakin Baban ku sai dai bai sanar dani dalili ba".
Ƙululu naci cikina ya bada ƙara sai da na musguta na sanarwa Ummata komai, cikin kuka na ƙare zancen ina faɗa mata abunda ya faru safiyar yau furcin da Anty Binta ta jefa mini akan nazo na raba mata kan ƴan-uwa.
Jawo ni jikinta tayi cikin sigar lallashi take cewar"kiyi haƙuri Na'ima yanzu kuka ba shine mafita ba, tabbatar mata da saɓanin tinaninta a game dake za ki yi ta hanyar kame kanki bisa wannan damar da kika samu nayin wannan kararun. Na'ima na hore ki da ki riƙe mutuncin kanki da na aurenki har ki tsinka yarda da mijinki yake dashi a kanki, zan yi fushi dake a duk lokacin da wani ab....".
Saurin rufe mata baki nayi ina jijjiga mata kaina"Umma kar ki ƙarisa don Allah, in sha Allah zan tsare mutumcina ba zaku same ni da aikata wani mummunan abun ba. Ku yarda da irin tarbiyan da kuka bani ko hakan ma ba zai bar ni na kauce hanya ba".
"Haka ne Na'ima Allah ya ba ki sa'a yasa a fara cikin nasara".
A sanyaye na amsa da kalmar amin kafin Yaya Majid ya ɗago labulen ɗakin yana shaida mana su Abba suna neman mu ni da Umma, miƙewa muka yi