Showing 33001 words to 36000 words out of 45833 words
Chapter 12 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt
Hamut yace " me kake nufu bro kai dawaye ne ? "
Bece komiba yamiqe yamiqama Ammi sakon Hanan yajuya yanufi qofar fita seda yakai bakin qofar sannan yatsaya cikin kakkausar murya yace
" idan nagamayin bincikena nagane kowaye zakusani idan nadauki mugun hukunci akan komawaye "
Idasa fita yayi afusace cikin mamaki da d'aurewar kai Hamut yadubi Hajiya kilishi kafin yayi magana tace
" rabudashi Hassan kasan ayanzu baze saurari kowaba kumama komeye ya'batamishi rai sosai barshi kawai "
Jinjina kai Hamut yayi yajuya yafita bud'e takardar da Hammat yabata Ammi tayi tafara karantawa farinciki yamamaye zuciyar ta murmushi yabayyana afuskarta afili tace " Allah sarki Hanan Allah yayi miki albarka Allah yakad'eki daga dukkan sharri Allah yahad'a kanku keda Hussain "
Tanakaiwanan tamiqe tanufi dining Hamut yanakomawa part d'in shi yanufi bedroom kai tsaye toilet yashiga ganin yashigo yasa Hamidat shigowa tad'auwani uban wanka sebaza kamshi takeyi zama tayi bakin bed tanajiran yafito shiko Hamut kodayashiga tsaye yayi natsayin lokaci yanatunanin haduwa da Siyama idan akwai wadda bayason ganin a rayuwar shi to Siyama ce to amma yaya zeyi umarnin Ammi ne yazama dole yabi ganin lokaci yaja sosai yasa Hamidat miqewa nufar toilet din tayi kunnanta takara bakin qofar d'in jin saudin saukar ruwa yasa tasaki tsaki takoma tazauna tsayin lokaci sannan Hamut yafito sanye da rigar wanka ganin Hamidat yasashi jan mugun tsaki sake tamke fuska yayi sosai cigaba da tsane jikinshi yayi yafarashafa mai cikin natsuwa miqewa Hamidat tayi tanufeshi
Rungumeshi tayi tabaya jin baicemata qalaba yasa tafara bijirome dawani irin salo sumar qirjinshi tashiga shafawa shiko Hamut shasshafa mayukanshi kawai yakeyi har yagama Hamidat batadenaba miqewa yayi yatureta yadubeta yace
" Hamidat kenan kinatunanin zanji wani abu agame dakene ? ina idanma kinatunanin hakan to kibari sabida ni ayanzu banayimiki kallon mace tamkar namiji haka kike kingakuwa bakida abunda zakija hankalina dashi fitamin daga bedroom karnasake ganinki cikin bedroom d'ina "
Sosai kalmomin Hamut sukayima Hamidat zafi ganin yadda yatamke fuska babu alamar wasa yasa Hamidat nufar bakin gofa d'an tsayawa tayi tace " D dan Allah inaso naje nagaida Momy ? " d'aga kafad'a yayi alamar baishafeshi ba yacigaba dayin hidimarshi babu jimawa yashirya irin shigar da Hammat yayi shima irinta yayi sabida sunsaba hakan tun yarinta key d'in mota yajara yafita
Fuska tamke yashiga parlour ganin yadda yashigo yasa Hanan saurin duqar da kai qarasowa yayi yazauna cikin sanyin murya Hanan tace
" barka dashigowa yaya " bai amsaba dama batayi tunanin hakanba cikin shakka tasake cewa " nakawo maka abincin ? " wata muguwar harara yasakar mata cikin sanyin jiki tamiqe tiran abincin tad'akko tanufoshi kafin taqaraso yace
" tsaya anan 3 hours nikeso kiyi ahaka sabida bance kitashiba " yanagama fad'in haka yaciro wayar shi yashiga latsawa
Hamut yana isa jirgin su Siyama yana sauka babu jimawa fasinjoji sukafara sakkowa hangota yayi cikin shigar larabawa tayi masifaryin kyau gaskiya Siyama akwai kyau wai 😊 tana idasa sakkowa idanunta sukayi karo dashi take taji ranta yayi masifar 'baci qarasowa tayi cikin 'bacinrai tadubeshi daga sama har qasa tace " hmmmm inde kai ne zakad'aukeni zuwa gida to wallahi gara nahau taxi " tsaki Hamut yaja maiqarfi yace
" dako nayi farinciki sosai wallahi badan bin umarnin Ammi ba babu abinda zejamin daukar marar kunya irinki yarinya "
Tafi Siyama tayi tasake dubanshi sosai tace " sannu babba mai kunya naga kwanaki kad'an kabani yara de ko ? " iska Hamut yafesar afusace yajuya gurin dayayi parking yanufa yabud'e motar shi yashiga yajata aguje
Mameen Zarah & Sudees 🤝🏻💖👌🏻
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 53 & 54*
*S* osai aketashirya yadda wannan shagalin zai kasance dashawarar Hajiya wato kaka akaqar kwanaki 3 kafin gudanar da shagalin sabida asamu damar gayyatan jama'a a tsanake
Su Jakadiya kuwa tanatafaman nazari akan yadda wannan gubar zataje hannun Hanan tazuba batare da tashiga cikiba take wata shawara tafad'o mata murmushin mugunta tasaki nufar 'bangaran Hajiya Fulani tayi cikin sallama tashiga zaune Hajiya Fulani take tana nazarin wani littafi na addini jin sallamar Jakadiya yasa Hajiya Fulani duban qofar amsawa tayi fuskarta asake qarasawa tayi tashiga kwasar gaisuwa
" barka da hutawa Hajiya Fulani Amarya agun Sarki Jabir bakya lefi koda kinkashe Hassan k......"
" Dakata Jakadiya banason irin wannan kirarin Allah yatsareni dayin kisa akan kowa balle Hamut fad'i abinda ketafe dake sabida inada uziri "
Jinjina kai Jakadiya tayi tace
" dama akan wannan hidimar daza'ayine naga kowa yana tura gayyata amma ke babu wanda kika turamawa shine nace inaganin yakamata nabaki shawara "
Murmushi Hajiya Fulani tayi tace
" Jakadiya kenan idan har dan wannan ne to angama nima naturadatawa gayyatar kingama ga kayan had'in sinadarin abinci can d'auka kitafi dasu inaso ashirya abinci nadaban sabida mahaifiyata da qannena sunanan tafe "
Murmushi Jakadiya tayi tace
" masha Allah Hajiya Allah yakawosu lafiya amma Hajiya naceba mezehana kid'iba ma Hanan sinadaran abincin nan sabida kinsan Yarima Hammat bayacin abincin kowa kodacan itace meyime abinci idan kikayi hakan Hanan zataji dad'i sosai kuma zakisamu lada "
Jinjina kai Hajiya Fulani tayi tace
" hakane kam "
tashi Hajiya Fulani tayi dakanta tashiga d'ibar ma Hanan sinadaran abincin su kori taym sinamon dade sauransu rurin wayarta yasata tashi nufar cikin qaramin parlour ta tayi tana amsa wayar cikin sauri Jakadiya tafiddo wannan gubar tacakud'e cikin d'aya daga cikin sinadaran abincin wanda sukayi kamada juna Hajiya Fulani tad'an jima tanayin wayar kafin tadawo murmushi Jakadiya tayi cikin nuna ladabi tace
" ranki shidad'e zanje 'bangaran kuyangu naga yaya ayyukan suke tafiya kozan wucema Hanan dakayanne ? "
Girgiza kai Hajiya Fulani tayi tace
" a a Jakadiya zan kai mata yanzu sabida dama banje nadubataba "
Jin haka yasa Jakadiya jin wani irin farinciki tace
" kenan babu zargi koyaya akaina saura Hanan tunda guba ta'isa zuwa gareta yazama dole nasata tayima Hajiya kilishi abinci namusamman wanda zaiyi sanadin rayuwar ta nikuma nasamu 5 million alokaci d'aya "
Murmushi tayi cikeda farinciki
Hajiya kilishi zaune kusada Sarki Jabir dubanshi tayi sosai tace
" Rankashidad'e Siyama tadawo takuma zama likita kamar yadda kake so yakamata kayimata wata kyautar bazata tunkafin gajiyarta tagama sauka "
Gyara zama Sarki Jabir yayi yadubeta shima sosai yace
" nashirya hakan tunkafin dawowarta kyautar saban hospital amma akwai sharad'i kafin ayi bikin bud'eshi yazama dole tafito mana da mijin aure "
Sosai Ammi tashiga farinciki sosai tayi godiya" amma maimartaba kanaganin baiyi wuriba cema Siyama tafito da miji karatufa tajeyi ba soyayya ba "
Jinjina kai yayi yace " hakane amma ke kinaganin zatarasa masoyine ? Idan tarasa ay ni senanemo mata inadasu dayawa kituromin ita zuwa anjima "
Amsawa Ammi tayi had'ida miqewa tabar part d'in misalin 4:30 Jakadiya tanufi part d'in su Hammat ganin Hammat a zaune a parlour yasatajin fad'uwar gaba dubanta yayi yace
" Jakadiya lafiya ? " cikin in ina tace " lafiya lau dama nazonajine ko gimbiya Hanan tanabuqatar wani abu "
'Dan tsaki yaja yace " babu abinda take buqata kinga Jakadiya nifa banabuqatar yawan takura idan anabuqatar wani abu zamuyi magana base'andameniba zaki'iya tafiya "
Mameen Zarah & Sudees ce 👌🏻🤝🏻💖
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 55 & 56*
*J* iki babu qwari tajuya tabar part d'in cikin zuciyar ta tace
" masifaffan banza kawai kuma duk abinka senasamu nasara "
Miqewa Hammat yayi rai 'bace yanufi bakin qofar Hanan cikin kakkausar murya yace
" Hanan idan bakibud'e wannan qofarba to wallahi zan 'banlata nashigo kuma idan nashigo se ranki ya'baci kibud'e nace "
A tsorace Hanan tataso daga bakin bed tazo tabud'e tana bud'ewa yashiga jawota yayi afusace tafad'a saman qirjinshi cikin zafin rai yaturata tafad'a saman bed yabita hannu yad'aga ze mareta sekuma yafasa nunata da yatsa yayi yace
" wallahi kinci darajar bro na dasena 'bab'ballaki kitashi kije kiwankemin kayana dakika 'bata sannan kije kihad'amin lunch hadda Siyama anan zatayi lunch yau "
Ay Hanan batasan lokacin datasaki murmushi ba tace
" lah yaya dama Aunty Siyama tadawo ? "
Harara yawatsamata hakan yasata saurin duqar da kai tabi tagefanshi tabar bedroom d'in nashi bedroom d'in tanufa toilet d'in shi tashiga kamar yadda tayi tsammani kayan suna ciki dukda jikinta babu qarfi amma cikin sauri tafarayin wankin sabida murnar zuwan Siyama cikin lokaci kad'an tagama tafito ganin baya parlour yasata jin sanyi a ranta cikin sakewa tashiga kitchen tafara shirya abinci namusamman wa'innan sinadaran abincin dasu tahad'a wajan yin abincin
Se yamma sosai Hamidat tadawo cikin shakka tashiga cikin parlour sabida ayanzu shakkarshi takeyi tun lokacin datasha mari dubanta yayi yaja tsaki bedroom d'in ta tanufa kafin tashiga yadakatar da ita dafad'in
" daga yau bazakisake fita ko inaba sabida nan cikin gidan sarautane me cike da kima da daraja dan haka babu wanda zaizo mana da shashanci mubarshi "
Mameen Zarah & Sudees
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 57 & 58*
" idan kuma kikaqiji to zakisha mamakina "
Yanaqarashe fad'ar hakan yashiga bedroom d'in shi rai 'bace ko dayashiga kasa ko zama yayi zuciyar shi nagun Hanan kome yakeyi koda yayi iya qoqarin shi wajan hana zuciyar shi tunanin Hanan amma hakan baya yiyuwa hannu yasa yadafe setin zuciyar shi sabida zafi datakeyime zama yayi sabida yadda yaji numfashin shi yafara canzawa sakamakon tuna cikin da Hamidat takedashi cikin 'bacin rai yace
" ina hakan bazeta'ba yiyuwa ba na'amshi d'an dabanawaba tayaya ? Hamidat kincuceni matuqar cuta ashe dama haka soyayya take ? nikam banida sa'a akan soyayya Hamidat nasoki kamar namutu nayimiki hidima kamar wani wawa najiraki kamar wani wanda bashida abinyi amma kikacutar dani cuta mafi muni arayuwata kince zaki'iya mutuwa akaina kince zakirayu dani komi wuya amma yanzu gashi sabida Allah yad'oramin lalura kingujeni abu mafi muni kikayimin Hamidat ashe har zaki'iyabamawani kanki da igiyar aurena akanki tabbas kinyimin mugun butulci Allah zaiyimin sakayya Allah sarki Hanan
Shiyasa akace abinda babba yahango yaro ko yahau rimi bazai hangoshiba Ammi taso na auri Hanan amma sabida son Hamidat yarufemin ido nakasa gane hakan seyanzu nagane 'boyayyan so nikeyima Hanan sedanarasata sannan nagane hakan gashi inaneman haukacewa rashin bacci yafarazama jiki agareni ya Allah kakawomin mafita "
Yaqarashe fad'ar hakan cikin matuqar damuwa had'ida zafafan hawaye masu quna suna gangarowa saman kyakkyawan kumatunshi
Lokacin da Siyama taji saqon kiran Sarki Jabir sosai tayi farinciki sabida dama jiran hakan takeyi cikin wani irin taku taketafiya Siyama kyakkyawace sosai ga aji tahad'o komi sosai tayi matuqar kyau cikin shigar larabawa sallama tayi a babban parlour Sarki Jabir Hajiya hajara ce zaune kusadashi gefanshi kulolin abincine da alama abincin rana zaici kafin yaleqa fada shiga Siyama tayi takwashi gaisuwa agun Sarki Jabir sannan tazauna duban Hajiya hajara tayi tace
" Hajiya barkada hutawa "
Sosai Hajiya hajara tacika fam sabida batajidad'in yadda Siyama tagaidataba amsawatayi ciki ciki acikin zuciyar ta tace
" hmmmm ashe de Siyama iskancin naki yananan amma kiyi da kyau duk zanyi maganinkune dazaran nagama da Hajiya kilishi taku mai sauqice idan har babu Hajiya kilishi dama itace garkuwarku ay "
Jin maganar da Sarki Jabir yakeyi yasata maido hankalinta kansu
" Siyama nayi farincikin kammala karatunki hakan yasa naginamiki Asibiti namusamnan kyauta daga gareni amma inaso kifito da miji lokaci yaja sosai idan na aurar dake kinga nasauke dukkan alqawarin dana daukar ma iyayenki bawani lokaci mai tsawo zanbakiba ammafa kisani sekin fito da miji za'ayi walimar bud'e hospital d'in naki tashi kije ina sauraranki nanda d'an lokaci "
Miqewa Siyama tayi tafita amma jikinta babu qarfi cikin zuciyar ta tace
" dama nayi tunanin haka to yaya zanyi kenan amma babu komi dama Imran yamatsamin dukda banshirya yin aure yanzuba amma inason nafarayin ayki yanzu tunda yin auran shine zaicikamin burina shikenan Imran ashe burinka ze ciki dukda bawani shaquwa mukayiba sosai ay fiddawanne kawai ba aure ba "
Da wannan zantukan zucin tashiga parlour Hajiya wato kaka qarasawa tayi aguje tarungume ta cikin murmushi da nuna farinciki tace
" kakata takaina nayi missing d'inki sosai "
'Dan tureta kaka tayi fuska tamke tace
" gafara kibani guri kuwai harkun isa kuyanke abu babu shawara zakidawo amma babu wata shanarwa balle ashiryatarbarki dake da Hajiya kilishi kunanuna wariya ko sabida ke ba yar gidannan bace shine kukeyin abu iya ku kawai to zandauki mataki akan hakan dan haka fitamin "
Marairaice fuska Siyama tayi zatayi magana tadakatar da ita dafad'in " fita nace tunkafin raina yasake 'baci " dole tafita dan tasan halin masifar Hajiya amma batajidadin hakanba 'bangaran su Hammat tanufa tanashiga tasaki ajiyar zuciya sabida yadda wani irin kamshi yake tashi zaune Hammat yake saman cushion yana kallon news jin sallama Siyama yasashi juyowa qarasowa tayi tazauna cikin murmushi tace
" Hammat kenan ango sehutawa kakeyi babu ruwanka to ina Amaryar ? "
Tsaki yaja yace " aykinsan inda zakisameta ko ? " sakeyin murmushi Siyama tayi tace " nasani mana a wajanka tode yanzu duk bawannan ba ina lunch d'in dan Allah yunwa nikeji inaganin abinci nabarshi nataho nan barimakagani "
Miqewa tayi tanufi hanyar bedroom kafin taqarasa Hanan tafito tasha wanka sefaman baza kamshi takeyi ganin Siyama yasata d'anyin sauri d'an tsayawa tayi tarumtse ido sabida zafin dataji a qasanta dubanta Siyama tayi tace
" to " sekuma tasaki murmushi taqarasa tarungumeta cikin farinciki Hanan tace
" Aunty Siyama nayi kewarki sosai zomuje ciki muyi hira sosai "
Murmushi Siyama tayi tace " nima haka Hanan nayi kewarki sosai hirakam zamushata sosai amma kafinnan muci abinci tukun "
Qarasawa sukayi bakin dining shima Hammat tasowa yayi fuska tamke ya zauna zubamakowa Hanan tayi sannan tazuba nata ganin Siyama agun yasata d'an sakewa ita tafaracin abincin sabida sosai takejin yunwa takai spoon na 3 Siyama tafara d'iban abincin sabida hankalinsu itada Hammat yad'auku wajan kallon news Siyama take spoon d'in kusada bakinta tayi saurin saukewa tace
" gaskiya akwai matsala kamshin abincin nan yana nuna akwai wani abu maikamada cutarwa han........" Kafin taqarasa Hanan tasaki salati
" Innalinlahi wa'inna ilaihirraju'uun nashiga 3 Aunty Siyama ciki na "
Mameen Zarah & Sudees
Please comment 🤝🏻🤝🏻💖😊👌🏻
Love u all fans 💖😊🤝🏻
Ana tare 🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 59 & 60*
*Z* aro ido Siyama tayi cikin tsoro da furgici tamiqe itama Hanan qoqarin miqewar tayi amma takasa sekiran Aunty Siyama takeyi shiko Hammat duban abincin yayi sosai sabida shikam abinma mamaki yashiga bashi ganin yadda Hanan tafara fita hayyacinta yasashi miqewa cikin sauri kiran waya yashigayi kafin wani lokaci doctor shi ya iso
Ganin shigowan doctor yasa hadimai farayin kuskus hakan yasa har labari ya iske Hajiya kilishi miqewa tayi cikin sauri tace
" Doctor kuma a part d'in Hussain lafiya kuwa ? "
Saka abayarta tayi tafito part d'in Hammat d'in tanufa tanashiga tayi tozali da Hanan kwance kamar babu rai doctor yanadubata cikin matuqar tashin hankali taqarasa tanafad'in
" lafiya me yasameta Hussain kaine ko ? sanar dani me kayimata " dede lokacin kaka da Sarki Jabir sukashigo kafin suqaraso gurin su Hajiya Fulani ma suka'iso itama Hajiya Fulani agigice take suko su Hajiya Mariya ko ajikinsu sunzoganin kwamne kawai duban Hammat kakatayi tace
" bade wani abun kasakeyimataba ? dan wallahi daganinka ba haquri zakayiba kakeyima mutane kifi kifi da idanu "
Tamke fuska Hammat yasakeyi sosai sabida baqaramin 'bacinrai yajiba akan maganar kaka aman da Hanan tafarayine yasashi maida dubanshi gareta sosai Hanan take amai kamar zata amayar da kayan cikinta kusan 30 minutes Hanan tanayin amai sannan yalafa
miqewa doctor yayi yadubesu yace
" Alhamdulilah gaskiya kawai matsala gimbiya Hanan guba ce taci amma Allah yataimaka bataci sosai ba allurar danayimata yasa ta amayar da ita sede kuma tata'bata sosai a maqoshinta ayanzu bazatacigaba dayin magana ba sabida hadda harshenta abin yashafa zata'iya daukar lokaci ahaka