Showing 3001 words to 6000 words out of 45833 words

Chapter 2 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt

bakin bed tadubeta sosai tace


" ke Hamidat garama kibar wannan kukan dan kam yazama dole kurabu keda Hamut ahalin dayake ciki yanzu babu wata macan dazata iya zama dashi ni nasan yanayin ki banzama daga cikin iyayennan wa'inda basusanin yaya rayuwar yaransu takeba nasan abinda zaki'iya jurewa dakuma Wanda bazaki'iya to tabbas bazaki iya jure zamada Hamut ba "


Sosai Hamidat taji kanta yad'aure sosai tadubi Momcy tace " towai maiye matsalar dan Allah kisanar dani " batare dajin wata shakkaba tasanar da'ita komi kuka Hamidat tasaki tace " kungani ko gashi kun tabani magunguna harma sunwuce qa'ida nashiga Uku "


Miqewa Momcy tayi tace " ina sauraranki naji wace shawara kika yanke idan kince bazaki zaunaba to ina bayanki 💯 idan kuma kikace zaki zauna tobana tare dake "


Daga haka Momcy tafita kasa miqewa Hamidat tayi sabida tsananin razana da lamarin tana nan a zaune tsayin lokaci har su Hamut suka qaraso cikin tamke fuska Hammat yadubi qawayen Hamidat yace


" to ay yakamata kutafi ko bakuji anfara kiran sallar magrip bane kuje driver yakaiku gida bayan Hamut yashiga cikin bedroom Hammat yakira Ansar yace yaje part d'in shi yad'auki kud'i yabama qawayen Hamidat hakan kuwa yayi suna qoqarin shiga motar yabasu sosai sukayi mamakin yawan kud'in bin cikin bedroom d'in Hamut yayi da kallo sabida yadda akatsara komi duban saman bed din yayi wasu had'addun kayane aka'aje mishi da'alamu wa'inda zaije wajan d'aurin auran dasune saurin kauda kanshi yayi yashiga toilet yayi wanka yayi alwala yafito cikin sanyin jiki yashirya cikin bedroom yayi sallah har issha'i sannan yad'auki kayan yasaka woow gaskiya yayi masifar yin kyau wayyo Allah ahaka kamar babu wata damuwa ajikin shi fita yayi yanufi bedroom d'in Hamidat zaune take tarasa abinda yakemata dad'i jin kamshin turaranshi yasata saurin d'ago idanunta tazubasu kanshi take taji jikinta yadauki shauqi buqata tafara taso mata


Qarasowa yayi gareta yasaki murmushin qarfin hali yace " my B sorry seyanzu kike ganina haka Allah yaso zomuje wajan iyayenmu susakamana albarka idan mukadawo zansanar dake komi nasan bazaki barniba koda girman qaddarar yafi haka " ta'be baki Hamidat tayi tace " basekace komiba nasan komi amma gaskiya banajin zan'iya jurewa zanbada d'an lokaci qalilan idan naga babu labari to kam zannemar ma kaina mafita " sosai Hamut yaji wata irin faduwar gaba sabida baiyi tsammanin Hamidat zata'iya furtame hakan ba


Comment and share please


_Marmyn Zarah CE_
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*




*NA*




*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_






```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*




AND NOW
```MUSAYAR RUHI```






*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








*Page 5 & 6*








*S* osai jikin shi yayi sanyi sake dubanta yayi yace " kina nufin zaki'iya barina dukda irin son dakike iqirarin yimin ? " kauda kanta tayi tace " zakaso na'aykata zina ? " sosai maganar tadaki zuciyar shi amma seyayi qoqarin shanyewa " yace " lna roqon Allah yakareki daga aykata hakan har abada amma tsayin lokaci bakida aure kinkumayi haquri maiyasa yanzu bazakiyiba ? ajiyar zuciya tasauke tace " wannan yazama dole nayi haquri sabida banida miji amma yanzu inadashi kaga kenan haquri baikamaceniba " jinjina kai yayi yace " hakane nikuma zanyi iya qoqarina wajan samar miki mafita muje mugaida su Ammi "


Kama hannunta yayi suka fita wajan Maimartaba sukafara zuwa bayan sungaidashi suka zauna kiran jakadiya Maimartaba yasa akayi yasata takira duka matanshi babu jimawa kowa ya halarci parlour addu'a Sarki Jabir yayi sannan yafarayimusu nasiha bayan nan yabama su Ammi dama itama nasiha tayimusu sosai anazuwa wajan hajiya hajara da hajiya Mariya cewa sukayi aysu basuda abincewa duk sunfad'i abinda yakamata amma ni inadawata tunasarwa cewar hajiya hajara auran Yarima Hamut shine aure nafarko kuma auran babban magajin Sarki amma banga anshirya wasu daga cikin al'adun cikin masarautar nan ba musamman shinfid'a farin qyalle asaman gadon Gimbiya dan tabbatar da cikar kamalarta dakuma tabbatar dacewa takawo kimarta cikin masarautar nan to yaya abin yake ko akwai wata matsalane ? "


Nisawa Sarki jabir yayi yace " kemakince al'ada ba addiniba don haka babu wannan maganar yin hakan baidaceba zamani yacanza abubuwamasun canza dan haka anbar wannan shirman kuta....... " hakan bazai yiwuba yazama dole ayi Jabir ina raye bazakuzomin dawasu sauye sauye ba dan haka Jakadiya kije kitanadi farin qyalle kamar yadda akasaba sannan kitambayi gimbiya idan tana cikin tsarki idan kuma tana cikin lalura irin ta mata toki tambayeta yaushe zatayi tsarki semujira zuwa lokacin dazatasamu tsarki se a aywatar da lamarin " Mahaifiyar Sarki Jabir kefad'in haka duban Sarki Jabir tayi tace " koda bayan raina banyarda ajanye wannan al'adarba " zama tayi tashiga yima Hamut fad'a shida Hamidat shiko Hamut sosai hankalinshi yatashi sabida bayaso kowa yasan matsalar dayake ciki ayanzu itama Ammin sosai hankalinta yatashi bayan tagama aka sallamesu suka koma part d'in su


Suna shiga Hamidat tanufi cikin bedroom d'in ta cikin 'bacinrai bin bayanta Hamut yayi zama yayi bakin bed yajawota jikin shi cikin lallashi yace " my B dan Allah kiyimin wani taimako d'aya kicema Jakadiya kina cikin jinin haila sannan kice kwanaki 7 kikeyi kuma jiya kikafara in sha Allah nanda kwanaki 6 zansamu mafita gobe doctor zezo daga China inasaran samun lafiya da taimakonshi da yardar Allah dan Allah My B kiyimin wannan koda shine alfarma taqarshe dazakiyimin arayuwata "


Fesar da iska tayi daga cikin bakinta tace " shi kenan amma idan lokacin yayi babu wata mafita fa yaya zakayi " sake dubanta yayi yace " haba B yakikeyin abubuwa kamar babu soyayya tsakanina dake kisanifa danke nikeyin komi hatta aykin pilot kekinsan bashine ra'ayinaba bakuma shine ra'ayin iyayenaba nawa ra'ayin irin na bro nane ra'ayin iyayena kuwa nazama doctor kekuma nazama pilot shine burinki sabida girman son danikeyimiki nabar ra'ayin iyayena nabar nawa nabi naki sabida nazo gareki nayi gaggawa sanadin hakan nafad'o yau gashi sanadin zamana pilot nacikaro da wannan muguwar matsalar wadda zata'iyasaka kimata raguwa nayi tunanin kece mai lallashina kece maizama dani har abada amma segashi ko kwana 1 kinaneman kigagara zama dani kinbani mamaki Hamidat wallahi kinbani mamaki kintambayeni idan kwanaki 6 suka qare bansamu mafitaba yayazanyi ko to kiji da kyau zan sakeki kuma nasanarmakowa cewa banida lafiya ni Hamut bancika namiji ba bazan iya kusantar mace ba zanyi hakan koda kuwa sanadin hakan baqinciki zaisa narasa rayuwata sannan zuciyata zatababbatar mini cewa nafad'i a soyayyar dana gina da yarinyar datun tana 12 yrs har zuwa 23 yrs amma nasamu fad'uwa godiya zanyi miki ko me Hamidat kodiyar tadace dake Thanks har abada hakan zanta furtawa agareki " yaqarashe fad'ar hakan cikin rawar murya yamiqe yafita afusace


Bayan fitar shi Jakadiya tashigo tambayar Hamidat tayi tabata amsa akan cewa tana cikin jini shiko Hamut fita yayi daga part d'in yanufi part d'in Ammi kaitsaye cikin bedroom d'in ta yanufa zaune yasameta itama tana cikin nazari kwanciya yayi saman bed d'in yad'aura kanshi saman cinyarta yasaki kuka maicin zuciya hatta numfashinshi kaucewa yashigayi sabida tsananin kuka sosai Hankalin Ammi yatashi dafa qirjinshi tayi tashiga yime addu'a tsayin lokaci sannan tace


" Hassan daure kaitafad'in Innalinlahi wa'inna ilaihirraju'uuuu koda acikin zuciyar kane kaji Hassanuna dan Allah nasan zuciyarka akwai taushi da sanyi kaji " fad'i yashigayi cikin zuciyar shi ahankali yaji zuciyar shi tanayin sanyi har yafara furtawa a fili tsayin lokaci sannan yatashi zaune yadubi Ammi yace


" Ammi Hamidat zatabarni Ammi ashe Hamidat bazatayimin halacci ba nafara sarewa inaji kamar bazan warkeba kenan bazan iya amsa sunan...... "


Dakatar dashi Ammi tayi tace " haba Hassan nasanka dahaquri kasani idan Hamidat taqika inada tabbacin Allah zaisakamaka dawadda tafita kuma in sha Allah zakasamu lafiya bakata'bayin tunanin Allah zaijarafceka dawannan laluraba kuma segashi yajarafceka kuma in sha Allah zaisake jaraftarka da sauqi ammafa idan ka'amshi wannan qaddarar hannu 2 kayi godiya ga Allah kayi haquri Huseen yacemin gone doctor zaizo in sha Allah zamusamu mafita zaka warke kaji kaje kaci abinci kayimin alqawarin zakaci " jinjina kai yayi sannan yafita binshi dakallo Ammin tayi cikin tausayawa


Hajiya Fulani yau itace da Ayki kamar koda yaushe tashirya tsaf tanufi part d'in Sarki Jabir tana shiga yamiqe daga zaunan dayake zaishiga bedroom cikin sauri tasha gabanshi dandanan hawaye suka cika idanunta tace " dan Allah Maimartaba idan wani abu nayimaka kasanar dani tsayin wasu shekaru baka kulani idan kasakenine kasanar dani dan Allah nasan matsayina " tsaki yaja yabi gefanta yawuce batare dayace komi ba






Inasake tunasar daku cewa banayin typing ranar Friday


Comments and shine please


_Marmyn Zarah Ce_ 👌🏻🤝🏻
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*




*NA*




*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_






```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*




AND NOW
```MUSAYAR RUHI```






*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








*Page 7 & 8*








*S* osai zuciyarta taqara shiga qunci jikinta yayi sanyi sosai fita tayi daga part d'in jiki babu qarfi tana shiga part d'inta tanufi bedroom kai tsaye dubanta Fadil yayi cikin damuwa sannan yamaida dubanshi kan Fadila kafin yace komi Fadila tace " a a yaya basekace komiba mucigaba dayima Mom addu'a Allah yayaye mata damuwarta kaji " daga haka tamiqe cikin damuwa tashiga bedroom shima miqewa yayi yabar part d'in baki d'aya sosai hankalin Hanan yayi matuqar tashi sabida jin sautin kukan Hamut datayi a cikin bedroom d'in Ammi kasa kwanciya tayi hakan yasa dole tafito tanufi bedroom d'in Ammi bayan taji fitar Hamut d'in bakinta d'auke da sallama tashiga jin sallamar Hanan yasa Ammin saurin share hawayen fuskarta zama Hanan tayi fuskarta d'auke damatuqar damuwa duban Ammin tayi cikin raunin murya tace


" Ammina tabbas akwai damuwa atare daku da yaya Hamut dan Allah Ammi meke faruwa koda bazan'iya yin komiba wajan kawo mafita ba amma zan'iyayin addu'a dan Allah Ammina meke faruwa ne ? "


Ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " haba Hanan babu komi kinji kinsande halin rayuwa watarana farinciki watarana baqinciki dole akwai haka cikin rayuwa karki damu kinji zewuce in sha Allah nan kusa "


Jinjina kai Hanan tayi tace " hakane Ammina amma bakisaba 'boyemin komiba duk abinda yake damunki kafinsu yaya Hamut susani ni nasani ina tunanin dan nakasance mace d'aya tak acikinsu shiyasa kike fad'amin damuwarki sukuma kiboye musu amma yau gashi Ammina tana'boyemin damuwarta amma tabbas zanshiga damuwa sosai yayana Hamut wanda yake sakarmin fuska yayimin murmushi idan inacikin damuwa yasani farinciki yau gashi yanacikin damuwa banida hanyar sakashi murmushi tabbas dole nashiga damuwa " miqewa tayi jiki a sanyaye zatabar bedroom d'in har takai bakin qofar Ammin tace


" Hanan dawo kizauna " komawa tayi tazauna cikin sanyin jiki yimata nuni tayi tada kwanta saman cinyarta kamar yadda tasaba babu musu takwantar dakanta saman cinyar Ammin ajiyar zuciya Ammi tasauke sannan tace " tabbas inada damuwa Hanan kuma damuwar akankine sauran kad'an kikammala karatunki dakin gama aure zakiyi bansan kokinada wanda kikesoba nikuma banason tauye miki dukkan abinda kikeso amma bazanji dad'iba idan baki aure wanda nikeso ki'auraba tsayin shekaru nike jiran wannan ranar amma bazan iya tusasakiba dukda faruwar hakan zaitona wani sirri wanda banaso yafita amma yin hakan shine zai dauwamarmin da wacce nike tsananin qauna ataredani har abada dukda cewa zan fuskanci qalubale sosai acikin Masarautar nan amma zanjure dan cimma burina kinji damuwata Hanan shikuma Hassan bansan meye damuwarshi ba nima yaqi sanar dani hakan yasakesakani cikin damuwa "


Tashi zaune Hanan tayi tashare hawayen fuskarta tace " Ammin koda akwai wanda nikeso kamar raina wallahi zanfitar dashi na'amshi za'binki zankumayi farincikin za'bin Ammina balle babu kowa ataredani Ammi karatuna nasaka agaba Ammina na'amshi za'binki tun yanzu Ammina kiyi farinciki shikuma yayana Hamut muyimai addu'a babu abinda yafiqarfin addu'a sannan Ammina wane sirrine zaitonu kuma wace irin matsala zaki fuskanta ? "


Murmushi Ammin tayi tarungumota cikinta tace " karki damuwa zuwa lokacin zakisan komi ayanzu banida amsha nayi farinciki sosai kuma nasakeyima Allah godiya dayabani ke matsayin 'ya agareni Allah yayi miki albarka tashi kije ki kwanta kinji " murmushi Hanan tayi tasumbaci kuncin Ammin sannan tamiqe tayimata sedasafe sannan tafita


Jiki sanyaye Hamut yashiga part d'in nashi bin inda akajera kayan abinci dana motsa baki yayi sakejin damuwa yayi cikin bedroom d'in shi yanufa yana shiga yarage kayan jikin shi yashiga wanka tsayin lokaci sannan yafito yana dafe da mararshi sabida yadda yakejin ciwo ko yaya yamotsa shiryawa yayi cikin shigar bacci sannan yafito bedroom d'in Hamidat yashiga zaune yasameta tanayin waya da momcy ta cikin sanyin murya yace


" idan kingama kifito parlour ina jiranki " zuyawa yayi yafita wajan abincin yanufa leder dayagani agefe yabud'e kajine manya guda 2 aciki da yoghurt mai sanyi sekuma nau'ikan abinci kalakala agurin kasa koda qwaqqwaran motsi yayi sabida yadda yaji zuciyarshi tasake shiga qunci sosai tuno maganar Ammi yayi da alqawarin dayayi mata akan zaici abinci hakan yasa yashiga zuba abincin cikin sanyin jiki yafara d'ibar abincin yanaci badan yanajin dad'in shiba sedan alqawarin dayayima Ammi kawai yasa yakeci dede lokacin Hamidat tafito ahankali take taku kamar maitausayin qasa sanye take cikin kayan bacci masu bin jiki sun bayayyana surar jikinta sosai tana qarasowa tazauna daf dashi sosai kwantar dakanta tayi saman kafadarshi tad'aura hannunta saman sumar kirjinshi wadda takwanta luf cikin lokaci kad'an taji kasala tamamaye jikinta ajiyar zuciya Hamut yasauke yace


" yakamata muci abinci ko ? " shagwa'be fuska tayi tace " jikina babu qarfi please kabani " rumtse idanunshi yayi sannan yace shikenan gyara zaman naki ahaka bazai yiwuba " gyara zamanta tayi ledar kajin yajawo yabud'e duban kaji tayi tace " a a my D wannan basuda amfani agareni ayau kabari sezuwa ranar daka warke aranarne zanjini amatsayin cikakkiyar amarya ba yauba yanzu irin abincinka zanci " sosai maganar tadaki zuciyar Hamut amma beko iya cewa komiba bata nashi abincin yashigayi har taqoshi sannan yamiqe yanufi bedroom batare dayacemata komiba yana shiga yakwanta saman bed idanunshi nakallon sama hawaye suka shiga gangarowa tagefan fuskarshi babu jimawa Hamidat tashigo cikin bedroom d'in hawa tayi saban bed d'in takwanta saban qirjinshi tashiga shafa sumar qirjinshi ganin hawaye nasauka tagefan fuskarshi tace


" haba my D nifa karkaga lefina iya gaskiyata nafad'a idan na'boyemaka najekuma na'aykata kuskurefa yaya zakad'aukeni ? Wallahi bazan iya jure lokaci maitsayi batare dasamun kulawar namijiba My D kafahimta naqosa namatsu dazuwan wannan ranar yawancin dare inakasayin bacci sabida tasowar shi'awata tunaka kawai zanyi naji yanayina yacanza My D balle yau gani gaka dan Allah kasanaji sassauci koyayane tunda har kaga na'iyafurtawa duk irin kunyar mace tabbas akwai matsala please help me my D "


Wani irin kunlewa yaji zuciyarshi tayi gawani irin zafi datashigayime jan numfashi yashigayi dasauri dasauri dafe setin zuciyar tashi yayi yashigayin magana cikin wahala


" karkidamu My B nayimiki alqawarin bazan bari kicutuba koda bansamu lafiyaba zansamar miki damafita in sha Allah kuma yau zanyi iya iyawata nasaki kibanbance sauran dararan dasukawuce abaya da wannan daran nayau " daga haka yajawota sosai yasaka bakinshi cikin nata yafara sarrafata sosai yake aykamata saqonni cikin salo ahaka kamar zai'iya aywatar dakomi amma kass itako Hamidat sosai tarikice sake mannewa takeyi ajikin shi sosai yatsinci kanshi dajin tausayinta Zameta yayi daga jikin shi yashiga toilet cikin Sauri tashi tayi zaune tanasauke numfashi sosai takecikin tsananin buqata Shiko yanashiga zama yayi yadafe kanshi yanasakin muguwar ajiyar zuciya gazafin zuciya yanaji sosai Kamar zuciyar tashi zata qone sabida zafi tsayin lokaci sannan yad'auro alwala yafito bai Kalli inda takeba yashinfid'a abin Sallah yatada sallah sauka Hamidat tayi daga bed d'in tabar cikin bedroom d'in Cikin wani yanayi Shiko Hamut kwana yayi sallah awannan daran hakama Hammat da Ammi duk sunayime addu'ar samun lafiya


Washegari misalin 3pm doctor ya'iso Nigeria kasancewar tun jiya yataso Hammat neyaje filin jirgi dakanshi yataho dashi koda Suka'isa cikin masarautar nanfa gulma tatashi kowa yanatambaya me wannan d'an China yazoyi cikin masarauta ayau Kiran jakadiya hajiya Mariya tayi cikin part d'inta itama hajiya tana cikin part d'in duban jakadiya sukayi hajiya Mariya tace


" jakadiya tabbas akwai abinda ake 'boyemana acikin masarautar nan naga hajiya Salma tashigo cikin masarautar nan jiya afusace hadima larai tacemin taji tanacema gimbiya Hamidat bazai yiyuba bazatabari 'Yarta tazaunada namiji irin maimatsala ta Hamut ba tabbas akwai wata aqasa dubada daga airport akawuce dashi asibiti wai yasamu accident segashi yadawo babu alamar ciwo jikinshi Sekuma maimartaba yafara qoqarin hana aywatar da al'adar shinfid'a farin gyalle bayan haka gimbiya tace tanayin jini senan dakwanaki 6 bayan Kowa yasan yanzu ba'ayin haka anatsara komi a yadda yakamata Lalle akwai wani abu hmmmm ayau kam nizan rikita komi jakadiya inaso kiyi duk yadda zakiyi kigano mana wani abu idan kikayi hakan kinada kaso maitsoka nikuma zanje wajan hajiya nazugata Sena rikita komi "


Tashi jakadiya Tayi tace " nikuma sena ganomuku komi "fita tayi cikin sauri part d'in Hamut tanufa zaune tasamu Hamidat itada hadimanta gaidata tayi cikin girmamawa sannan tad'an zauna jim bataga alamar cewa Hamut yana cikin part d'in ba hakan yasa tatashi tafita zuwa part d'in Ammi nanma babu Hamut ba Hammat se Ansar da Hanan zaune gaida Ammi tayi sannan tace


" Allah shi taimakeki Allah yaqaramiki lafiya dama zuwanayi natambaya naga anyi baqo maiyakamata akawo mishi tunda naga shi bad'an Nigeria bane dole za'asamu banbancin cima "


dubanta Ammi tayi tasaki murmushi tace " a a wannan baqon Husain ne kuma lamarine na aykinsu dan haka shi yatanadar mishi komi kuma kinsan halin Husain bayason anashiga cikin harkarshi idan kuma zakishiga tojeki kitambayeshi babu ruwan hajiya kilishi "


zaro ido Jakadiya tayi tace " ina nina isa yarima Hammat a a nabarki lafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login