Showing 18001 words to 21000 words out of 45833 words
Chapter 7 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt
inamai baka haquri kasake miqa komi ga Allah kaji Hassan "
Tashi yayi zaune yadubi Ammi sosai idanunshi sunyi jah sosai yace " Ammi Dan Allah kibarni nasaki Hamidat dama tanemi hakan nace tabari semundawo gida kuma gashi mundawo Ammi ayanzu bandamu da kowama yasan lalurata ba aybanine nad'aurama kainaba Ammi ganin Hamidat a cikin idona yanzu mugun baqinciki ne agareni dan........ " tabbas nima banyarda Bro d'ina yazauna damata irin Hamidat ba Ammi gaskiya......."
" dakata Hussain kamar yadda nace abikomi sannu to abi nima banyarda yacigaba dazama da Hamidat ba amma akwai lokaci kaji " miqewa Ammi tayi tafita zuwa part d'in Sarki Jabir bayan fitar Ammi Hammat yadubi Hamut fuska tamke yace
" Gaskiya Hammut kanabani mamaki wai nikam wannan Hamidat d'in itakad'ece mace ko idan karasata shikenan kadena rayuwa toma wallahi gara kadawo rakiyar mace yadda kakeson Hamidat idan da haka takesonka bazata ta'ba bama wani kantaba koda kuwa itace sugabar masu mugun shi'awa bazan iyayin rayuwa irin takaba Hammut kacanza dan Allah kacanza zuciyarka "
Yanagama fad'ar haka yajuya zaifita kamo hannunshi Hammut yayi cikin rauninmurya yace " kayi haquri d'an'uwana amma inaso kasancewa ita soyayya makauniyace tanashiga lokaci d'aya amma fitarta baya yiyuwa alokaci d'aya tanad'aukar tsayin lokaci kafin tabarka musamman soyayyar mutun ta farko aduniya tabbas Hamidat tayimin butulci a rayuwa ko cikin mafarki banyi zaton kwatankwacin haka daga garetaba amma Hammat zuciyata tanatuhumata da lefi inaji kamar nine sanad'in saka Hamidat ta'aykata zina da'inada lafiya dabatayi shi'awar aykata hakanba kuma danasaketa dabatayiba tunda tasan zata auri wani kum........"
" dakata Hammut ko kayarda koma karka yarda dole Hamidat mailefice itad'in jahilace koda bata ta'ba zuwa Islam ba tata'bajin cewa aykata zina haramunce balle mutun mai aure lokacin datake gidansu yayatayi da shi'awar tata seyanzune zatakasayin haqurin kadawo Nigeria kurabu tunda ita tacire rai da samun lafiyarka Hammut Allah natsani Hamidat batun yauba balle yanzu dako qaunar ganinta banayi "
Sosai zuciyar Hammut tasake karyewa sabida aduniya duk abinda d'an'uwanshi bayaso to shima jiyakeyi yatsane shi maganganun Hammat ayanzu sunsake sashi jin tsanar Hamidat sosai
Cikin tashin hankali Sarki Jabir yamiqe tsaye sabida tashin hankalin jin wannan mugun labarin tsayin lokaci yanakaiwa yanakawowa sannan yadubi Ammi yace
" tabbas Hamidat tayima Hassan mugun butulci amma kamar yadda kikace abi komi sannu ko babu komi mahaifin Hamidat qanine agareni amma duk da wannan dangantakar bazaisa nayarda Hassan yacigaba dazama da Hamidat ba " daga haka yafita daga part d'in cikin 'bacinrai
Hanan zaune cikin parlour Kaka kuyangu sungama tsaramata kwalliya sefaman kamshi takeyi wooow masha Allah gaskiya tayi matuqar yin kyau dama abu gurin mai kyau fitowa kaka tayi daga bedroom tadubi Hanan sosai tace masha Allah gaskiya Hammat yadace damata qarasowa tayi tace " Gimbiya Hanan zakije part d'in Hammat yanzu tareda rakiyar hadimai don kai gaisuwa agareshi bayan kindawo shikuma zaizo dan tayaki hira irinta masoya tashi kije zakitafi da madara mai sanyi sabida yajiqa maqoshi wannan al'adar cikin masarautar nan ce damasauran wasu kuma yazama dole ayisu duka tashi kije hakan zesa kowa yasan cewa Hajiya kilishi tabaku tarbiyya " sosai Hanan taji zuciyar ta nabugawa
Marmyn Zarah Ce
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 25 & 26*
*C* ikin sanyin jiki Hanan tamiqe ahankali take d'aga qafarta sabida yadda zuciyarta takeyin mugun shakkar nufar Hammat tareda rakiyar kuyangu sukanufi part d'in Hammat sallama sukayi abakin Part d'in amma shiru babu amsa dama sunyi tunanin haka sosai zuciyar Hanan tasake karyewa amsar madarar tayi sannan tace
" zaku'iya komawa kunsan bayason hayaniya " cikin sauri suka juya sabida dama kam basaqaunar koda hanyace tahad'asu dashi sakeyin sallama tayi tashiga abin mamaki yana kwance saman doguwar cushion yad'aura qafarshi saman d'aya hannunshi riqe da wayarshi yanalatsawa wata irin nannauyar ajiyar zuciya Hanan tasauke qarasawa tayi ta'aje Cup d'in madarar aqasan lallausan Carpet din makeken parlour shi gyuwoyinta aqasa hakama idanunta aqasa cikin muryarta mai taushi tace
" barka dahutawa yaya Hammat gamadara mai sanyi Kaka tace nakawo maka " wani irin mugun tsaki yaja yatashi zaune shure Cup d'in yayi daqafarshi cikin zafin rai yadubeta yace
" Allah yasauwaqe naci wani'abu daga hannunki ada de kam naci shima dan inakallonki matsayin hadimatane shine yasa yanzu kuwa bamakikai wannan matsayinba kinga qasqantacciyar baiwa to tafiki matsayi agareni sabida ni tun lokacinda Ammi tad'akkoki daga gidan marayu natsaneki fiye daduk wani abunqi narayuwa ina hangen daud'ar zina ajininki sabida babu wanda zai haifi d'ah yakai gidan marayu idanhar d'an mai asaline d'an sinnah Allah yasade kar'ayi gadon zina kitashi kigogemin wannan madarar dan kinsan ni bansaba da qazantaba kiyi gaggawar gogemin kifita kibarmin part sabida natsani ganinki "
Yanagama fad'ar haka yamiqe yashiga bedroom Hanan kuwa kasa miqewa tayi sabida yadda gyuwowinta sukayi mugun sanyi wani irin zafi taji yataso mata cikin zuciyarta gawani irin qaton abu dataji yataso mata yatokare mata zuciya sotakeyi tayi kuka amma takasa cikin sanyin jiki tashiga gyara gurin tafita tana fita part d'in Ammi tanufa sabida zatafijin dad'in zamancan shiko Hammat yanashiga yanufi toilet wanka yayi daruwa mai sanyi sosai dukda kasancewar lokacin sanyine kumaga sanyin AC dake cikin part d'in nashi fitowa yayi d'aure da towel sefaman rawar sanyi yakeyi sumar qirjinshi takwanta luf sumar kanshi kuwa ruwa yasa takwanto har saman idonshi kya dagasama har qasa Hammat namiji ne tsayayye mijin nunama sa'a sabida tako'ina yahad'u sosai badan bayason Hanan ba senace gaskiya Hanan tayi dace had'ida babbar sa'ar miji irin Hammat qara sanyin AC yayi sosai sannan yashiga goge jikinshi da qaramin towel kwanciya yayi saman bed yana kallon sama rumtse ido yayi had'ida cije lips d'inshi naqasa tsayin lokaci sannan yamiqe yashiga shafa mayamayan shi cikin sanyin jiki yakeyin komi kamar basojaba konace kamar wani abu yasashijin mutuwar jiki shiga yayi tamanyan kaya sosai yaqarayin matuqar kyau sefaman kamshi yakeyi kamar ayau yake ango d'aukar wani key d'in mota yayi wanda yake cikin leda sabo dal taku yakeyi ahankali cikin isa da qasaita dakaganshi babu ko tantama kasan cewa jinin sarauta nayawo cikin jijiyoyin jinin shi bayan yafito parlour yanufi wata 'yar qaramar wodrop yabud'e wani kyakkyawan abu yad'auka wanda akayi silin d'inshi dawani kyakkyawan abu dakagani kasan kautace tamusamman wato gift
Fita yayi yanufi part d'in Kaka bayan Hanan tashiga Part d'in Ammi zaune tasameta a parlour ganin Hanan yasa Ammi saurin miqewa rugowa Hanan tayi tarungumi Ammi se'alokacin tasaki kuka maisauti sosai rungumeta Ammi tasakeyi sosai tashiga lallashinta tsayin lokaci amma Hanan takasadenayin kuka seda Ammi tace idan batayi shiruba tofa itama zatayi kukan sannan Hanan tayi shiru ajiyar zuciya Ammi tasauke tace
" haba Hanan meyekuma nayin kuka sanar dani damuwarki idan kuma bakison wannan auran ne zansaka adakatar dashi kinji auta ta " ajiyar zuciya Hanan tasauke akaro na babu adadi shanye sauran kukan nata tayi tace " a a Ammi na babu komi amma nide nafison zama anan bagun kaka ba ina kewar mahaifiyata "
Nannauyan numfashi Ammi tasauke sannan tasaki murmushi tace " Haba Hanan haquri zakiyi ayke yanzu kinzama baquwar Ammi kinga daga wajan Hajiya se d'akin mijinki haka al'adar cikin masarautar nan take idan har yakasance angon da amaryar duk 'yan cikin masarautar ne tofa yazama dole Amayar tazauna wajan hajiya har zuwa lokacin daza'a d'auketa zuwa d'akin mijinta maza muje namaiyar dake tunkafin acemin banida kawaici kuma kinga yau ne zakuyi hira tamusamman keda Hammat a parlour Hajiya muje ko Auta ta karki bani kunya mana Hanan zakiyi hira da Hammat agaban Hajiya da d'aya daga cikin Matan Maimartaba dakuma Jakadiya ayaune za'a sheda cewa Hammat zekuladake kamar yadda zekula dakanshi kema atabbatar zakiji dashi kamar yadda kikeji dakanki sannan atabbatar da cikakkiyar soyayyarku gajunan ku dan Allah karkibani kunya karkibari kunyarki tasaka amana dariya muje kar suhalarci gurin babu ke "
Sosai Hanan tasake tsurewa dajin haka tanaji aranta cewa tabbas Hammat seya 'bata komi kuma tayaya tsoranshi zaibarta ta'iya aywatar dahaka ?
Sunyi sa'a babu kowa har Hanan tashiga bedroom sannan Ammi takoma part d'inta babu jimawa Hajiya hajara tayi sallama cikin part d'in kaka itada kuyangunta kaka dake zaune a parlour babu jimawa dafitowarta tadubi Hajiya Hajara tata'be baki tace " ikon Allah lalle Hajara to'ay kokece sarki jabir d'in sehaka tayaya zakishigomin da kuyangu har cikin parlour na sannu uwar saurauta maza kufitarmin dake dasu kicema Mariya tazo amadadinki zuwa gaba seki kiyaye "
Cikin sanyin jiki tamiqe dan babu yadda zatayi tasan ba'ayima Kaka musu amma cikin zuciyarta cewatayi " hmmm nide ko kikayima haka nasha alwashin sakaki 'bakin ciki kema babu jimawa Jakadiya tashigo gaisuwa takwasha sannan tanemi izinin shiga tafito da Hanan zuwa parlour bata izini Kaka tayi tamiqe cikin sauri tashiga bedroom zaune tasamu Hanan a bakin bed zuciyarta sefaman bugu takeyi murmushi Jakadiya tayi tace
" hmmmm yau zamugani idan dagaskene Hammat yanasonki kuma zamugani idan marar asali tasan yadda zatakula da miji tashi muje jiran shigowar yarima Hammat kawai ake jira " cikin sanyin jiki Hanan tamiqe sukafita parlour bayan sunzauna itama Hajiya mariya tashigo Hammat yayi sallama tunkafin yashigo kamshin turaranshi yagarwaye part d'in rumtse ido Hanan tayi cikin takunshi na'isa yashigo gaida kaka yayi cikin girmamawa itako Hajiya Mariya kalloma bata'isheshiba Cushion d'in da Hanan take zaune yanufa rumtse ido yayi yajawo natsuwarshi sannan yace
" Assalama alaikum Princess " ajiyar zuciya Hanan tasauke jin dayadda Hammat yazo yasata jin karfin zuciya tace
" Amin wa'alaika salam My Prince "
Saukowa tayi daga saman cushion d'in tadurqusa tace " nasan kashawo hanya hakan yasa natadanarmaka wajan hutawa mailaushi sabida gajiyar dakataho da'ita tagudu tabarmin Prince d'ina " rumtse ido Hammat yasakeyi sannan yakuma dakewa murmushi yasaki sannan yazauna aje kayan hannunshi yayi agefanshi yakamo hanunta yace
" zonan kizauna sabida zamanki akusa dani shine zaisaka duk wata gajiya danataho da'ita tagudu tabarni kinsan kuwa yadda kike agareni kinsan wane irin so nikeyimiki princess ? "
Cikin sanyin murya Hanna tace " a a Prince dukda zuciyata tanahasasomin yadda kake tsananin sona to amma nasan zata'iyayin kuskure taragemin yawan soyayyar tawa agareka zanso naji daga gareka sabida na'aminta dacewa zuciyarka dabakinka basayin qarya "
Ajiyar zuciya Hammat yasauke had'ida matse hannun Hanan d'in wanda yake riqe dashi tun lokacin dayace tazauna cikin zuciyar shi yace
" lallema yarinyar nan tasamoni yaya zanyi kenan idan nabayyana soyayya agareta nayi qarya kenan idan kuma naqiyin hakan tozan kunyata mahaifiyata yaya zanyi kenan ? "
Marmyn Zarah Ce 👌🏻😘
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 27 & 28*
*A* jiyar zuciya yasauke sannan yaqaqalo murmushin yaqe yace
" fad'in yadda nikesonki abune wanda baki bazai iya furtawaba sabida yayi kad'an ya'iya bayyanashi kuma baikamata wasu suji sirrin zuciyar Hammat ba jin wannan manyan furucin se nidake kawai princess "
Murmushin qarfin hali Hanan tayi sabida zafin da hannunta yakeyi matsemata hannun yayi badawasaba cikin sanyin murya tace
" nima natabbatar dahaka Prince zuciya tagasgataka inasonka fiye dakomi nawa yakamata nabaka wani abu maisanyi kasha sabida tattakin dakayo zuwa gareni "
Jin haka yasa Hammat jin wani irin mugun haushi sabida yasha alwashin bazaisakecin abu daga hannun Hanan ba miqewa tayi hakan yasa yasaki hannun nata cikin sanyin jiki takeyin taku har zuwa wajan freezer cikin wani kykkyawan Cup tazubomai madarar tadawo zama tayi yadda zatafuskanci furkarshi sosai cikin shakka da fargaba tanufi bakinshi da Cup d'in madarar dole ya'amsha badan yasoba sedan karya kobsa amma cikin zuciyar shi cewa yayi
" hmmmm duk wannan abun dakikesani inayi senayi mugun hukuntaki akanshi "
Sau 3 ya'amshi madarar sannan yace " hakama yayi princess tabbas kinbani abu namusamman lalle kin'iya tarba sabida inason madara maisanyi sosai nima yakamata nabaki gift namusamman key d'in sabuwar motar hannunshi yamiqamata yace " wannan kautar sabuwar motace tamusamman agareki sekuma wani gift namusanman wanda yafi motarnan muhimmanci agareki bakowane yakamata yaganiba seke sabida abune nadabanne agareki zankoma princess zantafi dakewar kallon kykkaywar fuskarki zankiraki naji muryarki kafin nakwanta bacci hakan zaibani damaryin bacci mai dad'i sosai nabarki lafiya "
Miqewa yayi taku d'aya yayi kaka tadakatar dashi dafad'in " lalle Hammat katabbatar manadacewa Hanan tamusammance agareka kema Hanan muntabbatar zakikulada Hammat sosai Allah yaqaramuku son juna "
Murmishin yaqe Hammat yayi sannan yabar parlour Jakadiya da hajiya Mariya kuwa kamar suhad'iyi zuciya haka sukaji sabida basuyi tsammanin son da Hammat yakema Hanan yake hakaba itako Hanan cikin sanyin jiki tabar parlour zuwa bedroom kallon wannan gift d'in tashigayi zuciyarta nasota'bude don ganin abunda yake ciki amma tanajin tsoro cire kayan jikinta tayi tashiga toilet bayan tafito tayi shirin kwanciya sannan tashiga bud'e gift d'in wasu sabbin hankacif ne guda 3 aciki sewani turare dagani yanada tsada sosai sewata letter cikin shakka dasanyinjiki tashiga bud'e wasiqar rubutune kamar haka
_Hmmmm nasan zakisojin maiye dalilin baki hankacif har 3 ko tanadin abin sharar hawaye ne nabaki sabida zasuyimiki amfani sosai tundaga yau dan kam tunda kika za'bi zama dani zakikasance cikin kukane har abada inayimiki barka dashigowa cikin rayuwar qunci wannan turaran kuwa kiyi amfani dashi sabida duk duniya babu turaran danatsana kamar shi asha kuka lafiya_ "
Ajiyar zuciya Hanan tasauke dukda tana qoqarin danne hawayen nata amma takasa afili tafurta yaya Hammat wannan wace irin qiyayyace kakeyimin haka ya Allah inaroqonka idan aurena da yaya Hammat ba alkairi bane Allah kakawo silar dakatar dashi nahuta " haka Hanan taita roqon Allah cikin wannan daran
Shiko Hammat yana shiga cikin part d'inshi yacire hular kanshi yajefar itama rigar yacire yajefar yanufi bedroom irin wankan dayayi d'azu shi yasakeyi niko nace ikon Allah koma sanyi bayaji cikin mugun 'bacinrai yakwana amma yad'aukarma zuciyar shi alqawarin seya quntatama Hanan fiye da tunaninta
Hajiya Mariya tadubi Jakadiya tace
" Jakadiya inaso kiyi duk yadda zakiyi kid'akkomin wannan gift d'in da Hammat yabama Hanan sabida inaji araina wani mihimmin abune aciki idan kika d'akko nikuma ya'isheni nakulla wani makircin dashi " cikin girmamawa Jakadiya tace " angama " sannan tafita
A 'bangaran Hamut kuwa ko kallon Hamidat bayayi becemata komiba gameda maganar cikin hakan yasata cikin damuwa sosai jiki babu qarfi tashiga cikin bedroom kulle qofar tayi sannan tabud'e wayarta layin muhseen takira bugu 3 yad'aga kafin yace komi tafashe dakuka tace
Marmyn Zarah CE
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 29 & 30*
*M* uhseen inacikin matsala babba ayanzu haka cikine dani kuma kasan nakane sannan maganar gaskiya don yakamata kasan komi ayau sabida kanemomana mafita gaskiya Hamut ba yayana bane kamar yadda kad'auka mijinane kum......." Dakatar da'ita yayi cikin mamaki " haba Hamidat dagaske kikeyi ? to amma tayaya kuka 'boyemin dagake har shi sedekuma bazanyi mamakiba tunda babu budurci nasameki kinga kenan wannan cikin banida tabbasd'in nawane " cikin tashin hankali Hamidat tace " haba muhseen wallahi wannan cikin nakane naji babu budurci kasameni amma wannan cikin nawa bashida wani uba se kai sabida Hamut baita'ba kusantataba kaga kuwa banida hujjar sewa nashine " sosai Muhseen yacikada mamaki cikin mamaki yashigayimata tambayoyi
" to amma ay babu Wanda yasan cewa baita'ba kusantarkiba dan haka naji zan'amshi babyn amma idan zakiyimana abu d'aya kinsande Hamut yatara gari maiyawa wato yanada tarin dukiya taban mamaki inaso kisamar mana koda rabin wannan dukiyarne tahanyar sashi yayi sarnin wasu manyan kadarori nashi dasunan d'an dakika haifa koda cikin rashin sanine sabida nasan bazaiyi hakan acikin hankalinshiba sannan kitsaya akan cewa lalle wannan babyn nashine koda kuwa kowa zeji sabida kowa yasan tsakanin mata da miji se Allah kuma bashida fita tunda kunsha kwana cikin part d'aya amma duk yadda zakiyi karki yadda ayi gwaji koda andage akan haka kisan duk yadda zakiyi kisiye doctor kar afad'i gaskiya bayan munsamu wa'innan kud'ad'an sekizo muyi aure kinga bamuda matsalar komi "
Ajiyar zuciya Hamidat tasauke tace " shikenan amma fa wannan lamarin akwai riski idan akasamu matsala tofa nice zankwana ciki " karki damu inde inanan babu wata matsala kuma zan'iyayin komi akan kud'i senajiki " daga haka yakashe wayar shiru Hamidat tayi tanasakeyin nazarin lamarin zuwa can tasaki murmushi tamiqe fita parlour tayi hangen Hamut tayi zaune saman cushion yayi shiru yana nazarin yadda rayuwa tajuyomai ahaka tunanin yakeyi ko akwai wani lefi dayayima Allah yasa Allah yajarafce shi da wannan masifar jin maganar Hamidat akanshi yasa yaji wani irin 'bacin rai itako murmushi tasaki tace
" haba My D duk kacanzamin nicefa Hamidat taka wadda kake matuqar so kuma nasan har abada bazakadena sonaba yakamata katsaya nayimaka bayani akan yadda kasamar da wannan babyn naka dan kam bashida wani uba samadakai kuma kasan......."
Cikin zafin rai yad'auketa dawani zazzafan mari wanda yasa sedata baya kamar zatafad'i nunata yayi azafafe yace
" kai Hamidat kishiga cikin hankalinki idan kikace zakikawomin wasan yara anan senayi mugun maganinki sannan kisani nadenasonki har abada natsaneki kuma idan duk duniya zatataru akan cewa nine baban wannan shegen cikin naki tofa bazan ta'ba yardaba koda kuwa zan