Showing 9001 words to 12000 words out of 45833 words
Chapter 4 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt
ayni banga dalilin wannan tuhumar takaba tunda kamar kaga hanjin cikin su kakeji " jin haka yasa Hammat fita rai 'bace binshi da kallo Ammi tayi afili tace " ikon Allah wannan hali naka Husain Allah yacanzamaka shi "
Cikin tsananin damuwa Hamut yayi sallama cikin part d'in Sarki Jabir gaidashi yayi cikin girmamawa sannan yazauna dubanshi Sarki Jabir yayi sosai yaji zuciyar shi babu dad'i sabida yadda yaga Hamut d'in yayi muguwar rama kamar wanda yad'auki lokaci mai tsayi yana jinya ajiyar zuciya Sarki Jabir yasauke sannan yace
" Hamut dukda naga bakadawata lafiya amma hakanan zakayi haquri kajagoranceni wajan wani mihimmin taro wanda za'ayi a Jodan nanda kwanaki 3 zakatafi amma taron zai d'auki kusan 2 weeks anayin shi bayan angama inaso kazauna acan kahuta kaji idan matar ka zata'iya binka sekutafi tare idan kuma tace a a shikenan bazamu matsamataba amma tafiya da'ita zaifi kodan maganin wannan matsalar banzar al'adar zanturamaka doctor wanda zaid'inga dubaka acan nasan zakaji dad'in zama a can Hassan kasani damuwarka tamkar damuwarmuce idan kasakadamuwa cikin zuciyar ka tamkar muma kajefamu cikin damuwarne kad'auka wannan wata jaraftace daga Allah kuma Allah bayajefama bawanshi wata jarafta face se bawan yazama yanada imani idan har kayi imani tofa dele se Allah yajarafceka yagani zaka'iya cinye wannan jarabawar Hassan nasanka akwai haquri dan Allah kaqara akan wanda nasanka dashi ka'aje wannan shawarar da zuciyar ka take rayamaka akan wai Husain yayi auran sirri da matarka Hamidat wannan babu hanyar billewa acikinta kacigaba dayin haquri watarana se labari tashi kaje Allah yayi maka albarka "
Sosai Hamut yaji jikinshi yayi sanyi zuciyar shi tasake karyewa cikin rashinjin karfin jiki yamiqe yafita kai tsaye part d'in shi yanufa yana shiga idanunshi suka sauka kan Hamidat kauda kanshi yayi yanufi bedroom muryar Hamidat tadakatar dashi dafad'in
" My D ina buqatar shan iska koda nasamu sauqin abinda ke damun jikina " rumtse idonshi yayi cikin jin zafin furucinta yace " kina'iya fita sannan inaso kishirya nanda kwanaki 3 zamutafi Jordan Maimartaba yaturani zan wakilceshi wajan wani taro " tsaki Hamidat taja tace " hmmmm nikam badan Maimartaba bane yace muje danace kaje kai d'aya kawai sabida koda nabika bansan wace irin rayuwa zamuyi dakaiba matsayin mata ko qanwa amma zanbika sede inaso daga yau nazama tamkar qanwa ceni agareka ba mata ba sabida bazaka iya bani abinda miji zaibama mataba qanwa kuwa kaga babu wannan lamarin kwata kwata ammafa idan maganata tayimaka zafi kayi haquri yaya Hamut nide nasan gaskiya nafad'a dazaran mundawo yazama dole kasamu mafita kasan wannan "
Tana gama fad'ar haka tamiqe tabar part d'in sosai Hamut yaji wani irin zafi cikin zuciyar shi baisan sanda yaji wasu irin zafafan hawaye masu quna suna sauka saman kyakkyawan kumatun shi ba daqyar ya'iya d'aga qafarshi yanufi bedroom cikin kuncin zuciya
Washe gari misalin 10:am Hammat yashiga part d'in Maimartaba duban hajiya hajara yayi dake gefan Sarki Jabir yatamke fuska sosai yace " ina buqatar zanyi magana da mahaifina kuma banabuqatar kowa " cikin sauri Hajiya hajara tamiqe tafita daga part d'in duban shi Sarki Jabir yayi yace
" Wai kai Hammat yaushe zakabar wannan halin ne ? kasani duk matar datake matsayin matata tofa tamkar uwace agareka dan haka yazama dole kabama kowace mace girmanta " sake tamke fuska yayi sosai yace " gaskiya de Dad kayi haquri ammafa ni babu wata mace dazan dauka kamar uwa dama nazone nasanar daku anturani Egypt janje wani ayki kuma gaskiya zanjima zuwa gobe zan tafi " duban shi Sarki Jabir yayi sosai yace " Allah yabada sa'a amma inaso kasani dazaran kadawo yazama dole kayi aure " saurin kallon shi Hammat yayi yace " amma dad ......" dakatar dashi Sarki Jabir yayi yace " nagamayin magana " daga haka yafita zuwa fada
Marmyn Zarah ce 👌🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*Page 13 & 14*
*_Assalama alaikum inayima kowa barka da Sallah Allah ya'amshi ibadummu amin Allah kuma yamai maita mana fatan alkairi gakowa_*
*R* ai 'bace Hammat yafito cikin 'bacin rai yace " tobasenadawoba sannan har za'a matsamin akan nayi aure alokacin daban shiryaba ina nikam inama tunanin anya anma haifi yarinyar dazan aura ? " garasawa yayi part d'in Ammi dan sanar da ita Hajiya hajara cikin sauri tashiga part d'in Hajiya mariya tana shiga tadubeta ganin Haisam a zaune yasa tace " Hajiya mariya inaso muyi magana " jin haka yasa Hajiya mariya saurin tashi suka nufi cikin bedroom binsu da kollo Haisam yayi cikin zuciyar shi yace " Allah yasa kugane abinda kukeyi badede bane " daga haka yamiqe yabar part d'in suna shiga Hajiya hajara tace
" Hmmmm Hajiya mariya yau naji abinda kunnuwana suketasonji wato Maimartaba yau yayima Hammat maganar aure zaiyi tafiya ayanzu yana dawowa yace dole yayi aure kinga kenan lokaci yayi da Kumsat itama zatayi aure dan kam senayi duk yadda zanyi wajan ganin Hammat ya auri Kumsar yazama dole nayi shirin komi kafin dawowar shi " murmushi Hajiya mariya tayi had'i tafa hannu tace " yazama dole kiyi shiri ko yazama dole nayi shiri ay atunanina Hammat da Amina yadace sbaida idan kika lura ay ......"
" Dakata Hajiya mariya bangane abinda kikeson kiyiba tayaya kinsan tuni nikeda wannan burin shine kema zakizomin dawata banzar magana idan kema so kikeyi Amina ta auri jinin saurauta to ay ga Ansar nan gakuma Fadil baseki za'bi d'aya daga cikinsu ba ? Murmushi Hajiya mariya tasakeyi tace
" Ina idan kinaganin sunfi Hammat riba toke maiye zai hana kiyi hakan kumama idan banda abinki ay Amina duk tagirmesu tayaya kike ganin hakan zai yiwu karki manta kowafa yanadanashi burin ni aganina baikamata wani yaji kanmuba kowa ya'iya allonshi ay seyawanke karki manta koda nice nasamu bazan manta da abokiyar makircinaba hakama kema ina zaton haka to kar wannan yasa wasu suji kanmu "
Wani shi'umin murmushi Hajiya hajara tayi tace " hakane iya ruwa fidda Kai amma nasan tabbas nikeda nasara dukda cewa babbar matsala ta shine Mama sabida tananan akan wannan al'adartasu wadda basa auran wani bare se jinin saurauta muma dayaya tabari aka auromu " murmushi Hajiya mariya tasaki irin namugunta tace " hmmm ay kinga wannan tsohuwar yakamata museta mata hanyafa idan mukabarta tofa Allah babu abinda zamusamu cikin masarautar nan " wata 'yar qaramar shewa Hajiya hajara tayi tace" barta ankusa zuwa dede lokacin dazamu qaramata gudu zuwa lahira " haka sukacigaba da tattauna mugun nufinsu
misalin 9:pm Hajiya Fulani tashiga part d'in Sarki Jabir cikin tsananin damuwa a kishin gid'e tasameshi gaidashi tayi cikin girmamawa kamar kullum ko kallonta baiyiba balle ya amsa cikin damuwa sosai tace " ranka shidad'e dama maganar makarantar su Fadil ne naji cewa su Ansar zasutafi nanda sati 1 amma naji bakayimin maganar su Fadil ba kaga shi yad'an jima yanajira to senayi zaton had'asu kakesonyi dasu Ansar shiyasa banyi magana ba " wani irin mugun tsaki yaja yace " tashi kibani guri jin muryarki ta'isheni haka idan kuma kikacigaba dazama zakisha mamaki ........ " kamar Yaya fa Maimartaba ? " Cewar Hajiya Kilishi dake tsaye bakin qofar part d'in tun bayan shigowar Hajiya Fulani qarasawa ciki tayi tazauna tadubeshi sosai tace
" Gaskiya Maimartaba hakan baikamataba nikam abinda kakeyima Fulani yafarabani tsoroma kenan har yaran nakama abin yake neman shafa ina gaskiya ni bazan iya jurar hakanba idan har baza'ahad'a su Fadil dasu Ansar tafiya Skul ba tofa suma su Ansar d'in sede suhaqura sutazama har zuwa lokacin daka canza tsari dan kam bazan iya jurar zargin jama'a ba sabida wallahi nasan nice abin zagi tunda nice mai yara barima nace nasanar dasu sudakatar da duk wani shiri bayanzuba " tana gama fad'ar haka tamiqe zatabar parlour dakatar da'ita yayi dafad'in
" Dakata Hajiya Kilishi to meye kuma nayin fushi bayan bakiji nace hakaba nifa tare nanemar musu Skul amma senaga kamar mahaifiyar tasu batabuqatar hakan shine dalilin dayasa nike ganin kamar batashiryabane " girgiza Kai Ammi tayi tace " haba Maimartaba itakam maiye nata idan kace ayi akwai wanda zaice a a ? dan Allah kayi adalci atsakaninmu dakuma tsakanin yara dan gujema fad'awa cikin fushin Allah da azabar shi dan Allah kar kasa nima nadinga zargin kaina wajan hanaka yin adalci sabida nice babba duk cikinsu kuma munada kyakkyawar fahimta ni da Kai dan Allah Maimartaba kaji tsoran Allah "
Ajiyar zuciya yasauke yadubi Fulani wanda raban daya d'aga ido yakalleta har tamanta yace " kiyimusu duk wasu shiryeshiye tare zasutafi Ansar da Fadil Hanan da Fadila idan akwai wani abu kituromin Fadil ko Fadila susanar dani ke basekinzoba " murmushi Hajiya Fulani tayi tace " in sha Allah zanyi yadda kace nagode Allah yaqara girma ina godiya agareki Aunty Kilishi Allah yaqaramiki tsoran Allah " daga haka tamiqe tafita jiki a sanyaye binta dakallo hajiya Kilishi tayi cikin tausayawa shiko Sarki Jabir fuskar Hajiya Kilishi yake kallo dawoda dubanta tayi gareshi kafin tayi magana yace
" Basekince komiba Kilishi banada amsar baki banace ga lefin Fulani agareniba zuciyatace kawai ta tsaneta lokaci d'aya babu dalili nasha bambayar kaina meye dalili amma har yanzu nakasa ganoshi badan babu saki a gidan sarautaba idan babu wani dalili mai qarfiba datuni nasaki Fulani kodan itama tahuta to amma babu dalilin yin haka " nannauyar ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " gaskiya yakamata kadage da addu'a dukda nasan kanayi to amma kaqara Allah yashiga tsakanin nagari da mugu " shima ajiyar zuciyar yasauke yace amin dubanta yayi sosai yace " wato Hajiya Kilishi akullum jinki nikeyi sabuwa fil cikin wannan zuciyar tawa " yata'ba setin zuciyar shi kuma har qarshen numfashi ahaka zaki dauwama " murmushi tayi tace nagode sosai amma inaso acikin kasona na soyayyata dake cikin wannan kyakkyawar zuciyar taka karabashi 2 kabama Hajiya Fulani rabi zanyi matuqar farinciki idan kayi hakan " rumtse idonshi yayi yace " bazan iya hakanba kiyi haquri amma daga yau zuciyata zata dinga tunasar dani cewa Hajiya Fulani tanada alfarma awajan abar qaunata har abada yanzu tashi muje ciki wannan kamshin turaran naki yajawo miki magana ina matuqar son wannan turaran naki "
Murmushi Ammi tayi tace " ayya shiyasa yamantar dakai cewa yau ba Hajiya Kilishi keda haqqin sauke maka buqatar takaba ? Hajiya Fulani ce kabata duk kulawar da wannan zuciyar taka tayi shirin bani dan Allah " tana kaiwa nan tayi saurin miqewa tafita tana shiga part d'in ta babu jimawa tafito tanufi part d'in Hajiya Fulani tana shiga tasamesu zauna saman Cushion d'aya itada yaranta suna kallon Sunna TV sallamarta yasa suka maido hankalin su wajanta cikin sauri Fadil da Fadila suka miqe suka isa gareta rungumeta sukayi suna gaidata cikin farinciki shafa kansu tayi suduka had'ida saka musu albarka sannan taqarasa ciki nufar bedroom kowa yayi sukabar iyayen nasu cikin farinciki Hajiya Fulani tashiga yimata barka dashigowa bayan sun gaisa Ammi tadubeta sosai tace
" Hajiya Fulani ayau zanyimiki magana akan abinda yake faruwa tsakanin ke da Maimartaba gaskiya lamarin yanacin zuciyata batun yanzuba amma kasancewar lamarine na tsakanin miji da mata kuma ni ina matsayin kishiya baikamata nashigaba sabida nima dole ina cikin abun zargi sabida zaman kishi lamarin yanada wuya idan ke baki zargeniba to babu shakka wasu senun zargeni sede ni nasan har ga Allah kowannen ku zuciya 1 nike zaune dashi tsayin 18 yrs kuna zaman rashin jituwa a tsakaninku amma nayi tunanin ko wani lefi kikayi mishi to amma yau nayimishi magana akan haka abin mamaki shima bashida wani dalili hakanne yasa nazo nabaki shawara koda yau 1 ki'aje matsayin kishiya agareni kid'auka Aunty kice zatabaki shawara yakamata kisake dagewa da addu'a aduk lokacin dakikayi sujjata kidinga karanta wannan addu'ar barinayimiki misali da kaina dan nima karki cireni cikin zargi halin kishi ne
ALLAHUMMA DAMMIR KILISHI KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR HAJARA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA ) ALLAHUMMA DAMMIR MARIYA KAIDIHA WA SHARRIHA WA AMALIHA )
harama shi kanshi Maimartaba daduk wani wanda kikejin zuciyarki bata amince dashiba dasauran wasu addu'o'in neman tsari da kariya daga dukkan sharri in sha Allah zakiga kariyar Allah Allah yayi jagora sannan a garshe inaso yau kiyi amfani da wannan turaran " tamiqamata wani tsadadjen turare dake hannunta dashi nikeyin amfani akoda yaushe Sabida Maimartaba yanason shi sosai kije gareshi cike da karfin gyuwa kinji fatan alkairi Hajiya Fulani "
Sosai Hajiya Fulani tayi farincikin wannan shawara ta Ammi godiya tayimata sosai tamiqe dan rakota cikin sauri Jakadiya tabar bakin parlour daga la'ban datake tun shigar Hajiya Kilishi cikin part d'in amma takasa jin komi sabida sautin Tafsir d'in dake tashi cikin parlour nufar part d'in Hajiya hajara tayi cikin sauri
Bayan Hajiya Fulani taraka Ammi takoma part d'in ta cikin farinciki yau shiri tayi namusamman zuwa part d'in Maimartaba cikin 'bacin rai Hajiya Hajiya tamiqe tashiga kaiwa da komowa sannan tadubi Jakadiya cikin fushi tace " ayko yazama dole kibi duk wata hanya dan ganomin mai suka tattauna akai idan kikayi haka kinada kaso mai tsoka idan kuma kika kasa zan rage matsayin ki agareni zanbama wata damar shiga cikin lamarin mu na sirri " risinawa Jakadiya tayi cikin girmamawa tace angama Hajiya bani wani d'an lokaci kad'an " jinjina Kai Hajiya hajara tayi sannan tace " kya iya tafiya cikin sauri tafito wasu hadimai dake shirin shiga cikin part d'in suka dubeta bayan tawuce suka ta'be baki hadida cewa " hmmm su Jakadiya kenan iyayen kulma tunda kika ganta cikin part d'in Hajiya hajara a wannan lokaci tabbas wani munafincinne " jin kamar motsi yasa sukajabakinsu sukayi shiru suka idasa ciki
Sallama Hajiya Fulani tayi tashiga cikin part d'in Maimartaba baya cikin babban parlour hakan yasa tashiga cikin qaramin parlourn nanma bayanan kallon gofar bedroom d'in shi tayi sosai zuciyarta tashiga bugawa cikin qarfin hali tanufi qofar tsayin lokaci tana tsaye sannan tatura tashiga zaune tasameshi bakin bed yana duba wasu takardu dake gabanshi jin kamshin turaran Hajiya Kilishi yasashi saurin d'agowa amma seyaga Hajiya Fulani ce dukda bahaka zuciyar shi tasoba amma yaji wani sauyi sauke idanunshi yayi had'ida amsa sallamarta wadda yajima baya amsawa a fili sede a zuciya zama tayi agefanshi tanason yimai magana amma takasa tsayin lokaci har bacci yafara daukarta shiko kamshin wannan turaran yasa yamakasayin komi se faman juya takardun yakeyi tashi yayi yamaidasu sannan yashiga toilet tsayin lokaci yafito yashirya kwanciya dubanta yayi yakauda fuska sannan yatadata yace
" gyara kwanciyarki " mamaki abin yabata sosai sabida raban data kwanta saman bed d'in shi har tamanta babu musu tamiqe tazare abayar dake jikinta kyawawan kayan baccin jikinta suka bayyana tahau saman bed d'in saurin nufar makunnin wuta yayi yakashe sannan yadawo kwanciya yayi bayan ya kwanta cikin shakka da fargaba Hajiya Fulani tamatso jikinshi sosai yaji jikinshi ya tunasar dashi amaryar tashi amma kuma zuciyar shi tana qin haka rungume shi tayi sosai tasaki kuka tana fad'in
" Tabbas haqurina yakusa qarewa buqata tana neman halakani Maimartaba dan Allah kakulani koda zuciyar ka batason haka idan kuma babu aure tsakanin ni da Kai ne kasanar dani nasan matsayina " sake fashewa tayi da kuka tsayin lokaci baice komiba se zuwa can yace " banida dalilin sakinki sede nadena sonki amma yau zan sauke miki haqqin ki sabida dalili 2 kwai daga haka yasake rungumota sosai daga nanfa sassan jikin shi suka shiga bayyana mishi tsananin missing dinta dasukayi a wannan daran kamar wasu ango da amarya haka suka kasance sabida kowa yakasa gajiya duk da shikam zuciyar shi bataso amma yakasa hana kanshi nuna yunwarshi akan Hajiya Fulani
Bayan kwanaki 2 Jakadiya takasa samun cikakken bayanin da Hajiya hajara tasata samowa sede ta qirqiri gyarya tafad'a Hamut da Hamidat sunbar qasar Nigeria zuwa Jordan hakama Hammat yabar Nigeria su Hanan kuwa yaune suma suka bar Nigeria semuce Allah yabada sa'a madedecin gidane mai kyau da tsari iya tsaruwa yatsaru akwai komi namore rayuwa aciki aka siyama Hanan da Fadila ankuma had'asu da kuyangu sabida hidima sannan ansaka Security sabida tsaro kamar yadda akayima su Hanan haka akayima su Ansar
MAFARIN WATA BABBAR MATSALA GA HANAN
BAYAN WASU WATANNI
Kamar kullum yauma sundawo daga Skul agajiye suna shiga Hanan tanufi bedroom dariya Fadila tasaki tace haba Hanan duk gajiyarce ? Ayde kya bari muci abinci ko kumafa kinga yamma tayi karki kwanta bacci " juyowa tayi cikin yanayin gajiya tace
" Fadila kenan asumata keneman tashi yakamata nawatsa ruwan d'umi senaci abincin nasha magani sannan nakwanta ko " daga haka tashiga ciki girgiza Kai Fadila tayi tace Allah yayaye miki wannan ciwon Hanan " itama nufar cikin bedroom dinta tayi sabida kowa danashi se bayan isha'i sannan Hanan taji yanayinta yafara dedeta sabida shan tea mai dumi dataita sha bayan tasha magani parlour suka fito kamar kullum kuyangu suka dinga basu labari misalin 10:pm sukabar parlour zuwa ciki babu jimawa bacci yakama Hanan sabida yanayin jikinta itako Fadila tana zaune saman bed tana karatu
Misalin 12:10 dede Hanan taji wani baqon yanayi kamar cikin bacci amma setaji wannan abun yafi qargin bacci sede zahiri bud'e idonta tayi ayko yayi mata tozali dawani qaqqarfan Saurayi mai cikar zati da izza kasancewar babu haske sosai cikin bedroom d'in yasa bata ganin fuskarshi sosai sede wani irin mugun turare maijan hankali dake tashi daga jikin shi kafin tayi wani yunguri yatoshe mata baki tayadda babu damar tayi ihu cikin sanyin murya sa'banin yadda Hanan tazata yace
" Hanan yau yazama dole nabar miki tarihi cikin rayuwarki yadda babu Mai auranki seni to amma nidin jikinki nikeso ba ke dinba nafahimci hakanne bayan kinbar Nigeria amma sede kasss gani nakeyi kamar nafi karfinki sabida kinyi yarinya dayawa amma dukda haka zan gwada sannan daga yau zandinga ziyartarki wajan baccinki har