Showing 39001 words to 42000 words out of 45833 words
Chapter 14 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt
" wato Hajiya kilishi yazama dole mununama duniya gatan Hanan kodan Hammat yasancewa Hanan tafiqarfin wulaqanci a cikin idan kowa "
Zaro ido Ammi tayi cikin mugun tashin hankali tace
" Maimartaba banason narasa Hanan ina kallon Hanan kamar rayuwata kumafa kasan akwai yarjejeniya tsayin wa'innan shekarun munjure ganin yadda Hajiya dasauran matanka sukeyima Hanan se yanzu ne zamukasa jurewa Maimartaba nayi alqawarin samarma Hanan wanda zai sota fiye dakomi nashi dan Allah karka tona wannan sirrin "
Cikin damuwa Sarki Jabir yace
" kiyi haquri Hajiya kilishi bazan iya cigaba dajure hakan ba yazama dole kowa yasan cewa Hanan tanada gata "
Yana qarashe fad'ar hakan yabar gurin tsayin lokaci sannan doctor yafito nufarshi sukayi suduka cikin sauri doctor yace
" Alhamdulillah komi yazo dasauqi ayanzu de babu wata babbar matsala sede afurgice take munyi mata allurar bacci zatajima tanayin bacci idan tafarka zakuma iya tafiya gida zaku'iya shiga kuganta amma please karku d'aga sauti "
Farinciki sukayi sosai bayan doctor yawuce kaka tadubi Hamut tace
" kai Hamut wai inashi Hammat d'in yake ? Wannan yaro akwai banza hali atare dashi "
Jin tambayar kaka yasa Sarki Jabir saurin cewa
" am Hajiya yasamu kirane daga office d'in su inagama bakin ayki zaikoma kuma kinsan yanayin aykin nasu basajira "
Dogon tsaki kaka taja tace
" to Allah shi kyauta shiyasa natsani aikin soja yanzu sabida Allah matarshi tanacikin wannan halin yatafi kay gaskiya wannan aikin nashi baiyiba "
Hakade kaka taita surutu har sukashiga cikin room d'in tunda Ammi tad'aura idon ta akan Hanan takasa saukewa wasu siraran hawaye sukashiga gangaro mata cikin damuwa Siyama takamo hannunta tace
" Ammi kiyi haquri in sha Allah Hanan zatasamu lafiya "
Jinjina kai kawai Ammi tayi amma takasayin magana duban Hamut Sarki Jabir yayi yace
" Hamut kad'auki Siyama kuje gida kuhad'oma Ammin ku kayan jinya sabida inaganin baikamata koda Hanan tafarka mutafi da ita gida yau ba gara mubari muga yanayin jikin nata zuwa gobe "
'Dan sosa qeya Hamut yayi yace
" amm inaganin basemuntafi tareba nikad'ema zan'iya "
Cikin d'an fusata Sarki Jabir yace
" bashawara nanemaba karde har yanzu bakucanzaba wai nikam Hajiya kilishi wane abune yajefa rashin jituwa a tsakanin su kinqi sanar dani tuni amma zanyi maganin ku "
Babu yadda suka'iya haka dole sukatafi suna fita Siyama tabud'e baya tashiga afusace Hamut yariqe murfin motar yace
" ke mekike nufi ni driver kine ? dallah tashi kidawo gaba "
Yatsina fuska Siyama tayi tace
" au damakai akasin haka kad'auka hmmmm to kasakeyin tunani "
Jin haka yasake fusata Hamut damqo hannunta yayi cikin zafin rai ganin yadda Hamut yadamqi hannunta yasata d'an razana sabida irin damqar dayayimata batawasa bace jin muryar d'aya daga cikin driver maimartaba yasa Hamut sakinta yajuyo cikin girmamawa yace
" Allah ya taimakeka Yarima dama Maimartaba ne yace nakaiku gida kaida Gimbiya Siyama "
Jinjina kai Hamut yayi sannan yakalli Siyama yayi qwafa yace
" Allah yatemakeki da yau sena muje wannan mararkunyar bakin naki "
Dalla mishi harara tayi tace
" hmmm dad'in abinde ni nafiqarfin ayimin mazurai sabida nagama sanin komi "
Juyowa Hamut yayi cikin zafin rai yashiga cikin motar yaja marfin yarufe yajawota jikinshi sosai yamatseta cikin fusata yace
" wato kinsan komi ko ? to ai shikenan wanda yasan komi naka ay kenan babu wani shamaki a tsakaninku to barinaji adadin yaya girmanki yakai yanzu "
Yana qarasa fad'in haka yad'aura hannun shi saman qirjinta wata irin qara Siyama tayi had'ida fad'in
" nashiga uku idan kanayima girman Allah kayi haquri dan Allah kad'auke hannunka ajikina "
Murmushin mugunta Hamut yayi yace
" a she rashinkunyar taki qaramace daga yau idan kikasakeyimin rashin kunya senayimiki abinda yafi haka "
Sakinta yayi yabud'e motar yafita cikin takaici Siyama tace " Allah ya isa mugu kawai " d'an dawowa yayi yace " me kikace " zaro ido tayi tace " mefa ni babu abinda nace " murmushi yasaki yace " hmmm kimace kuma kiyi sauri kifito muje " d'an tsaki Siyama tayi tace " aykuma wallahi baka'isa kadinga kafamin dokaba badan Maimartaba ne yaceba kai harkama isa " tanafad'in hakanne a lokacin data tabbatar tafito daga cikin motar qwafa Hamut yayi yajinjina kai yace " zanriqekine yarinya " daga haka sukanufi d'aya dagacikin motocin dasu Maimartaba sukazo sukashiga
A cikin asibitin kuwa bayan fitar su Siyama kaka tadubi Hajiya kilishi tace
" sanar dani dalilin rashin jituwarsu sabida banaso nayimusu hukunci da kah "
Jin haka yasa Hajiya kilishi cewa
" a shekarun baya lokacin Hassan befi 14 years ba itakuma Siyama 13 dawasu watanni Hassan yashiga bedroom d'ina daniyyar zai shiga toilet yayi wanka sabida nasu Hussain yashiga shikuma Hassan yanayin sauri yanashiga yanufi toilet nikuma a lokacin nafita sannan adede lokacin Siyama tanaciki kumabatarufe toilet d'in ba yanashiga yayi ido hudu da Siyama tanayin wanka ganin hakan yasa Hassan fitowa dasauri a wannan ranar Siyama ko abinci bataciba sabida takaici dukda kuwa Hassan yabata haquri taki haqura dukda irin lallashin danayimata amma besa Siyama tahuceba taita uban kuka bayanwasu lokaci tad'anama Hassan tarko yanacikin yin wanka tashiga kallon shi tayi sosai tace
" narama shikenan one one "
Hakan yasaka Hassan yimata duka bayan yafito daga wankan shikenan tundaga nan rashin jituwa yashiga tsakanin su "
Dariya kaka ta bushe da'ita tace
" Lalle kuwa wani yaga tsiraicinka hakan akwai ciwo toko lalle Hamut yakusa yaqara aure sabida kuwa babu wanda Siyama tadace dashi se Hamut "
Please Dan Allah kuyi haquri jiya banida data ne fatan alkairi ga kowa 🤝🏻😊💖
Mameen Zarah & Sudees ce 🤝🏻😊[
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 71 & 72*
*T* amke fuska Sarki Jabir yayi sannan yace
" aiko yazama dole yasaketa zankirashi bade mu zainunama iyakarmuba zansakashi yasauke wannan hayaqin dake kanshi "
Yana gama fad'in haka yabar parlour cikin 'bacin rai part d'in kaka yanufa zaune yasameta ana yimata matsar qafa ganin shigowar Sarki Jabir yasa hadimar fita daga part d'in zama Sarki Jabir yayi cikin girmamawa yace
" Allah yaqaramiki lafiya Allah ya yafemiki kurakuranki Allah yacika zuciyar ki dafarinciki duniya da lahira Allah yakaremin ke daga sharrin dukkan abin halinta nafili dana 'boye ya mahaifiyata "
Murmushi kaka tashigayi sabida tanajin dad'in irin wannan addu'ar cikin sanyin rai tace
" Amin yakai d'ana Allah yayimaka albarka Allah yacika zuciyar ka da hasken muslinci Allah yakad'e maka dukkan fituna da dukkan sharri Allah ya albarkaci zuri'ar ka Allah karyabarka da iyawarka Allah karyabarka da kanka dede da qiftawar ido dama akan maganar auran Siyama da Hamut ne nagama yanke shawara kuma nakira mahaifinta yacemin muyi duk yadda mukayi dede ne shine nace bari nasanar dakai amma banaso Hamut da Siyama susan da wannan zancan haddama ita kanta Hamidat d'in sabida banason tsegumi har se an d'aura auran kafin kowa yasani "
Jinjina kai Sarki Jabir yayi yace " duk abinda kikace Hajiya hakan za'ayi amma tayaya za'a iya 'boye musu tunda yazama dole sesunga shagalin biki kuma basusan nawayeba yaya zamuyi Hajiya ? "
Dubanshi tasakeyi sosai sannan tace " banaji kasaka a shirya wani shagaliba wanda babu gayra babu dalili shikenan se yakoma shagalin biki "
'Dan zaro ido Sarki Jabir yayi yace " to amma Hajiya dukafa kwanaki 2 sukarage zuwa lokacin har za'agama tsara komi ? "
Ayanzu kam cikin d'an fushi kaka tace " koda a yau nace inason ayishi kenan baze yiwuba ? tashi kabani guri " ganin yadda kaka tad'an fusata yasa Sarki Jabir saurin cewa " Allah yahuci zuciyar ki za'ayi yanda kikace nabarki lafiya "
Miqewa yayi yafita Hamut zaune saman cushion d'in parlour shi hannun shi riqe da waya yatsuramata ido number Hammat ce yake kallo tunanin kiranshi yakeyi to amma yanaso yayi fushi dashi dan yanunamishi cewa abinda yayi badede bane amma yanajin bazai iya hakan ba kwana 1 kawai har yafarajin babu dad'i
miqewa tsaye yayi afili yace
" nima yakamata nakoma bakin aykina konasamu sassaucin damuwa "
Adede lokacin Hamidat tashigo taci wani uban ado sebaza kamshi takeyi cikin kissa ta'isa gareshi babu zato yaji tarungume shi cikin karyayyar murya had'ida shagwa'ba tace
" please my D dan Allah kamanta komi wallahi nayi nadamar abinda duk na aykata kumafa ni badason raina duk nayi hakan ba ni inada karfin shi'awa kuma nayi zaton bazaka warkeba kamar yadda doctor yace dan ........"
Kafi taqarasa yatureta afusace yace " har abada babu wata alaqa dani dake kamar yadda nabar nonon uwata kema haka nabarki har abada wani lokaci kawai nike jira nakauda ganina daga kanki butulu kawai marar alqawari "
Yana kaiwanan yabar parlour cikin 'bacinrai
Tunda Sarki Jabir yabar gurin kaka yaje yasanar da Hajiya kilishi tayi al'ajabin hakan dan kam yayi wuri sosai to amma yaya suka iya tundaga wannan lokacin akashiga yin shirye shirye abinka da gidan sarauta akwai kud'i akwai mulki kuma akwai ikon sakawa ayi a lokacin da duk akeso Hanan zaune a parlour duk damuwa ta isheta rashin magana ay mugun abune adede lokacin Hamut yashigo zama yayi d'an nesa da ita yadubeta cikin tausayawa yace
" sannu Hanan yaya jikin " jinjina kai kawai tayi alamar dasauqi cikin damuwa yace " Hanan inaso kinatsu sosai a wannan ranar babu wanda yashigo wanda kike jin bakiyarda dashi ba ? " girgiza kai Hanan tayi ajiyar zuciya Hamut yasauke yasake cewa " to akwai Wanda yabaki wani abu ko yaya yake kituna "
'Dago kai Hanan tayi sabida tatuna kayan da Hajiya Fulani takawo mata adede lokacin kuma Siyama tafito daga bedroom
Mameen Zarah & Sudees ce
Please comment please please
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 69 & 70*
*S* aurin d'agokai Sarki Jabir yayi cikin d'an jin shakka yace
" amma Hajiya hakan bazaijawo matsalaba sabida fa babu jituwa tsakanin su hakan zai iyasa komi faruwa "
Jan tsaki kaka tayi tace
" sukashe kansu idan an had'asu "
Cikin jin shakka Hajiya Fulani tace
" amma Hajiya kwatakwata Hamut auran shi baiwani dad'e ba idan akace zesakeyin wani yanzu za ai tayin surutai ne "
Wani irin mugun kallo kaka tawatsama Hajiya Fulani kafin kaka tayi magana Hajiya Fulani tayi saurin cewa
" dan Allah Hajiya kiyi haquri idan maganar danayi ta'batamiki rai "
" ai dama kinsan zata'batamin rai kikayita daga yau idan kikasakeyimin haka zanyimugun 'bata ranki aure kuma seyayishi da Siyama kuma kokin manta dacewa ita Hamidat d'in nice nahaifi uban ta ? dan haka babu ruwan kowa duk wani maiyin surutai yazo gabana yayi kinji uwar iya "
Haka kaka taitayin mita washegari sewajan 3 sannan Hanan tafarka Ammi da Siyama ne kawai cikin d'akin jin yadda Hanan keyin mutsumutsu yasa Ammi saurin qarasowa bakin gadon
kamo hannunta Ammi tayi cikin sanyin murya tace
" bud'e idonki Hanan nice Ammin ki Hussain bayanan kuma bazaizoba bakuma zakikoma gareshiba kinji "
Bud'e idonta Hanan tashigayi ahankali tasaukesu kan Ammi nannauyar ajiyar zuciya Hanan tasauke murmushi Ammi tasakar mata qarasowa Siyama tayi cikin farinciki tasumbaci goshin Hanan tasakar mata murmushi had'ida cemata " Hanan yajikin sannu kinji Allah yasa kaffarane "
Qoqarin miqewa tashigayi tananuna toilet kamata Siyama tayi takaita bayantafito Ammi dakanta tabata abinci babu jimawa su Sarki Jabir suka iso doctor yabasu sallama sukakoma gida part d'in Ammi akawuce da Hanan cikin bedroom d'in Siyama Siyaman tashiga da Hanan itakuma Ammi tanufi part d'in Sarki Jabir kusan tare sukashiga juyowa yayi cikin mamaki yace
" ah lafiya kuwa Hajiya kilishi ? "
Jinjina kai tayi cikin d'an damuwa taqarasa hannun shi takamo tasakacikin nata cikin matuqar damuwa tace
" dan Allah Maimartaba kajanye zancen maida Hanan cikin asalinta rabuwa da Hanan tamkar rabuwa da farinciki nane dan Allah "
Dubanta Sarki Jabir yayi sosai sannan yace
" kisani koda Hanan tabar cikin wannan masarautar tofa kuna tare Hanan bazata barkiba kamar yadda kema bazakibar Hanan ba ni kimar Hanan da darajarta nikeso nafito da ita bawai rabaku nikesonyiba zanjira taqara warwarewa "
Cikin yanayi marar dad'i Ammi tasakecewa
" to yaya zamuyi da igiyar Auran Hussain dake kanta ? "
Mameen Zarah & Sudees ce 👌🏻😊
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
```MUSAYAR RUHI```
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 73 & 74*
*G* anin Hamut a parlour yasata sakin dogon tsaki qarasowa tayi tazauna tadubeshi tayatsina fuska tace " hmmm wanide ya iya aikata rashin lissafi amma yadinga nunama mutane shi d'in me cikakken hankali ne to kam magani "
Jin maganganun da Siyama keyi yasa Hamut jan qwafa yamiqe yadubi Hanan yasaki murmushi yace
" Hanan zanje zuwa anjima zan dawo kiyi tunani da kyau seki sanar dani zuwa anjima sabida ayanzu bazanji dad'in zama anan ba kinsan zamada mahaukaci se dole ko banza kasha duka idan kuma yasamu sa'a yacijeka tofa kaima kamuwa zakayi da haukan kinga kuwa garanabar gurin ko qanwata "
Duban Siyama Hanan tayi sabida tasan Hamut da ita yake dariya abin yabata sosai Hanan takeyin dariya sede sautin ta bayafita rabon dataji irin wannan dariyar tun sunatare da Ansar wato qanin su Hamut cikin fusata Siyama tamiqe tasha gaban Hamut amasife tace
" kenan kananufin ni mahaukacciyace ko to yau sekagayamin inda nata'bayin hauka ko nanunamaka qirqirarre yanzu k....."
Jin muryar Ammi yasaka Siyama yin shiru dubansu Ammi tayi tace " to kaji zakufara fad'an nakune ? kai nikam kilishi Allah yanunamin qarshen wannan fituna naku kai Hassan kaine babba amma kake biye mata ko ? "
Jin abinda Ammi kefad'a yasa Hamut fita daga part d'in bayan fitan Hamut Ammi tadubi Siyama tace
" Siyama kinsan akwai wani shagali daza'a gudanar nanda kwanaki 2 a cikin masarautar nan kuma za'a had'ane da shagalin murnar kammala karatun ki dakuma bikin bud'e hospital d'in ki dan haka inaso ki gayyato duk wata qawa taki sannan na d'akko me gyaran jiki zata gyaramin ke kifito fes kamar amarya sannan zan shiryamiki kaya tamkar lefe irin na qayatacciyar amarya me cikken gata amma inaneman abu 1 agunki duk abinda zakiga nayi anan gaba to banason tambaya sabida nariga nasanar dake komi a yanzu ki d'auki duk wani abunda kike buqata kikoma part d'in Hajiya dazama sabida a can za ayi miki gyaran jikin "
Jin maganar komawa part d'in kaka yasa Siyama d'an zaro ido kafin tayi magana Ammi tadakatar da ita dafad'in " karkice komi ki lalla'bata kurabu lafiya tashi kije "
Komawa bedroom tayi da shiryawa tayi matuqar farincikin wannan shagalin amma zuwa part d'in kaka yasakata cikin mutuwar jiki tasan dekam zatasha masifa ne bayan tafiyar Siyama Ammi tazauna kusada Hanan jawota tayi takwanta dakanta saman cinyar ta shafa gashinta Ammi tashigayi cikin tausayawa da lallashi Ammi tafara dacewa
" Hanan kiyi haquri abisa tauye miki haqqi damukayi wajan aura miki Hussain tabbas bamusan zecutar dakeba munyi zaton zai bar komi ashe bahakabane damunsani dabamuyi wannan had'in ba amma yanzu babu mai mayar dake hannun shi banama tunanin zakisake ganin shi sabida tun a jiyan yabar qasar yakoma bakin aykinshi kimanta dashi kinji Hanan zakisake shiga cikin wata sabuwar rayuwa wadda tafi wacce kike ciki a yanzu nashi kije ki kwanta kihuta sabida doctor yace kidinga samun hutu "
Cikin sanyin jiki Hanan tamiqe tanufi bedroom zuciyar ta cike da tambayoyi bin bayanta Ammi tayi da kallo miqewa itama tayi tafita part d'in Maimartaba tasake komawa a wannan lokacin riqe yake da waya sefaman juyata yakeyi kallon shi sosai Ammi tayi kafin tace
" hmmmm kiranshi kakesonyi ko ? inagayamaka kabarshi dan Allah muma mununamishi cewa zamu'iya mantawa dashi kamar yadda shima yamanta damu yatafi ayanzu de baya cikin Nigeria balle kafita kaje kadawo dashi dukda cewa kasaba binshi har wata qasar kadawo dashi to ayanzu inaso karabu dashi dan Allah watarana dakanshi zedawo da qafafunshi "
Ajiyar zuciya Sarki Jabir yasauke yace
" hakane kilishi amma kinsan dolene nadamu ke kanki