Showing 45001 words to 45833 words out of 45833 words

Chapter 16 - ️MUSAYAR RUHI Complete book By Npeedy A Aji .txt

hakaba bazan iya jimiki koda qaramin ciwoba amma natanadar miki hukunci namusamman "


Yanaqarashe fad'ar hakan yajuyo hawa saman bed d'in yayi ya aje wuqar yanad'e hannun rigarshi can sama sannan yad'akko wuqar yada'ba makanshi dede dantsen hannun shi ayko jini yafara shatata saman wannan farin qyallan rumtse ido Hamut yayi sabida yadda wani irin mugun zafi yake shigar shi Siyama kuwa zaro ido tayi tanufeshi cikin sauri yadakatar da ita dafad'in


" dakata karkisake kiqaraso gareni a yau naceci kimarki badan keba sedan Ammi na nayi hakanne sabida bazan iya aikata komi dakeba dan bakikai matsayin ba "


Daga haka yamiqe yana dafe da hannun shi sabida mugun zugin dayakeyi yanufi toilet babu jimawa yafito yafita daga bedroom d'in baki d'aya bin kan bed d'in Siyama tayi da kallo sosai tsakiyar farin qyallan yajiqe da jini wata irin nannauyar ajiyar zuciya Siyama tasauke takasayin magana tunanin ta kuwa tsayawa yayi cik tsayin lokaci sannan Hamut yadawo sanye da jallabiyar bacci mai ruwan qasa dogon hannu gareta hakan yasa babu wanda zai iya ganin yankan hawa saman bed d'in yayi yakwanta daga gefe batare dayacema Siyama komiba


Itako binshi kawai takeyi da kallo qugin da cikin ta keyi yasata tashi d'aukar ledar daya'aje mata tayi tashiga kitchen tahad'o abinda zataci sannan tadawo bayan tagama tashiga toilet tayi wanka tafito tayi shirin bacci itama saman bed d'in tahau ta kwanta nesa dashi sukabar qyallan a tsakiya


Washegari


Duk yadda Jakadiya zatayi wajan sace farin qyallan ya gagara hakanan akafito dashi gaban kowa aiko kafin kace mai cikin masarautar yad'auki murna da sautukan busa sarewa wani saban shagali akashigayi su Hajiya Mariya kuwa baqinciki har zuci kimanin 2 weeks aka d'auka ana shan shagali sabida yadda akayi bikin cikin gaggawa


Turkiya


Hammat zaune cikin office hannun shi riqe da waya yanajuyata zuwacan yamiqe yabugi saman table d'in gabanshi cikin 'bacin rai yace


" wai mai Abiy yakenufi danine shida Ammi ? yau kimanin 2 Weeks amma babu wanda yakirani abun mamaki ma wai hadda Bro na kenan hakan yananufin sun manta dani kenan ' ina hakan bazai ta'ba yiyiwaba "


Cikin zafin rai yashiga kiran wayar Sarki Jabir sedayayi kira yakai sau 3 kafin yad'aga tun kafin Hammat yace komi Sarki Jabir yace


" Furuci d'aya tak nikeso kafurta min shine nasakin Hanan idan ba wannan ba to banason jin komi daga gareka "


A wannan ranar akuma wannan lokacin sabida wannan furucin Hammat yaji wani irin bugu da zuciyar shi tayi wanda shi kanshi beyi tsammanin hakanba bekuma ta'bajin irin wannan bugun zuciyar ba kashe wayar yayi batare dayace komi ba komawa yayi yazauna yanasauke ajiyar zuciya afili yashiga furta


" Hanan saki toma maiye idan nasaketa kay a a bazan iya yin hakan ba karnayima kaina wouta to amma ai basonta nikeyiba kenan Abiy da Ammi fushi sukayi dani kenan ? Idan kuwa hakane yazama dole nakoma Nigeria zancigama dazama da Hanan kodan nahuta tun yanzu nafara kasa bacci sabida tunanin wannan zumar ta Hanan komawa Nigeria yazama dole agareni Abiy na yana matuqar sona danabashi haquri zai yafemin yamayarmin da Hanan "




Hmmmm Hammat kenan to bari mugani idan hakan zai yiwu ko kamakara ko akasin hakan zamugani


Nigeria


A safiyar yau ne
Sarki Jabir yatara kowa cikin babban parlour shi ciki kuwa hadda Hajiya wato kaka bayan yabud'e taron da addu'a sannan yafara dacewa


" Alhamdulillah a yau ne zansanar dakowa wanu 'boyayyan sirri wanda babu wanda yasanshi dagani se Hajiya kilishi yau kimanin 18 years kenan a yau inaso kowa yasani cewa Hanan ba marainiya bace tanada cikakken asali mai kyau wanda kowa zaiso yasameshi kuma yayi tinqaho dashi Hanan 'yace ga Sarki Mahamud Nuhu Wanda kekan kujerar sarautar nimon a cikin qasar Merlin Hajiya abinda zebaki mamaki anan shine Nuhu shine wannan yayan naki wanda ya'bata tun shekaru da dama Hanan satota akayi a ranar sunanta agabaro qasarta da ita wannan kad'an kenan Hajiya a lokacin da aka......"


Kafin yaqarasa Hanan tamiqe cikin kidima da wani irin yanayi wanda ita kanta batasan wannene ba fad'uwa tayi asume kanta Ammi da kaka sukayi sunakiran sunanta Hanan Hanan




Masha Allah Alhamdulillahi ala kulli halin a yau nakawo qarshen Book d'in musayar Ruheey book 1 semun had'u a na 2 amma kafin nan zan bud'e saban group iya masuyin comment sune zansaka koda mutun 2 ne inde zasuyi Comment yawadatar amma duk Wanda yasan yabiya kudin wannan book d'in tun kafin namayar dashi free to yayi min magana nasakashi cikin saban group sabida saukemishi haqqin shi kuma nima in sha Allah zangyara yawan typing nima kaina nasan yayi kad'an duk wacce tasan zatayi comment sosai a book 2 na Musayar Ruheey to tayimin magana anan ne zakuga asalin musayar Ruheey


Nagode sosai masoyana Allah yabar zumunci ana tare 😊🤝🏻💖


Mameen Zarah & Sudees ce 🤝🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login