Showing 1 words to 3000 words out of 50838 words
Chapter 1 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝♀️ MIJIN ATTAJIRA 🧝♀️
By
Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)
Bismillahi rahmani rahim
Page 1&2
_________"jannat! jannat!!tashi kiyi shirin school, karki makara " baki taturo gaba, ta kara gyara kwanciyarta ..tajà bargon ta rufe har fuskanta " bazaki tashi ba ?"haba momy nifah baccin baiyi sheni ba ?"jannat ta fada.
Shikenan...
indai hakane ashe bakyason kizama lawyan kamar yanda kike fada ?"
"Ai tanajin an ambaci sunn lawya tamike ,da tsauri 'sauka tayi daga kan gadon ta riko hannun momynta, momy "muje kiyi mun wankan toh tunda natashi ?"dariya matar ,data kira da momy tayi_ ta lakuci hancinta ,taya za'a miki wanka ba'a cire kaya ba ?"
Matsowa jannat tayi momy ta cire mata Kaya tasa mata rigar wanka daukar ta_ tayi cak bata direta ako ina ba sai gaban toilet ,bruch tafara mata tana gamawa tayi mata wanka ta kuma daukarta "suka koma dakin dazu ,mai ta shafa mata ta saka mata infome dinta Pink colour sai hijabinta fari kal dashi powder da turare ta fesa mata"riko hannunta- tayi 'suka nufi palo ,danning sukaje kujera tajà mata ta zauna ?"tea ta hada mata_ ta bata ,Chips and egg ta zuba mata a plate tura mata tayi a gabanta "yauwa baby kici bari naje na duba Dadinki in yagama shiryawa sai muwuce ko ?"karki makara ,okay momy,zata wuce daki ta duba mai gidanta kenn sai gashi ya fito sanye da kananun kaya kana ganinshi kaga dan boko"dagashi har matar tashi, ba wani babba bane ba dan ko shikaru arbayin ba zai kaiba !bezai wuce talatin da biyar haka ba,itta kanta matar tashi,bata wuce ashrin da hudu ba,dan jannat dince kadai yersu ittama shekarunta "hudu kacal a duniya..
karasowa yayi yana kallon matarsa cikin soda kauna yake magana ?"haba Ashe babyce tatashi shiyasa aka manta da Dadi a daki,dariya jannat' tayi !
Haba Dadi taya momy zata manta dakai bayan yanzu zataje kiranka sai gaka kafito ?"toh naji yer gidan momy dama nasan sai kinyi magana yi sauri ki karasa cinye abincinki kada mumakara,okay Dad" jannat ta fada tare daci gaba dacin abincin ta..
kallon momy Dadi yayi !wife "zubamun abinci,zubo mai tayi ta zauna suka faraci, suna gamawa ya kalleta yace kusameni abakin mota,toh ta fada,tawuce daki mayafinta,da kuma jakarta ta dauko ta dawo palo, riko hannun jannat tayi suka fita ..
Budewa jannat bayan mota Dadi yayi "tashiga ya rufo mata,kodai na bude mikine wife ?"
Dadi ya tambayi momy, girgiza kai tayi,na wutasheka yau kam.
Amma banda gobe,dariya yayi 'shikenn yace,suka shiga mota mai gadi ya bude musu get suka cilla hancin motarsu awaje..
Driving yake amma gaba daya yau ya resa gane kansa tundaya tashi.
daurewa kawai yake ?"
Momy jannat ce"ta kalli Dadi,lfy kuwa man?"taiwa Dadi tambaya,dan dubanta. Dadi yayi,wllhy gabanane ke ta faduwa tun sanda natashi..dan marairaice fuska momy jannat" tayi,
wllhy Nima haka,kawai de bangaya maka,bane saboda banason nasaka cikin damuwa..
Toh muyita mai maita inna lillahi wainna ilaihirajiwun,haka dai ?"
Ko wannensu ya dinga maimaitawa"har suka isa makarantarsu jannat "
Sauka Dadi yayi yaje ya budewa jannat murfin mota,fitowa tayi_ ya rufo murfin motar,hannunta ya kamo suka fara tafiya,momyce ta fito daga mota _ta
kwallawa"jannat" kira,baby!baby!!haka suke kiranta dashi dan bako wana lokaci suke kiranta da jannat ba ?"
Dan juyowa jannat" tayi..
Ta zubawa momynta"wayenn dan zarà !zarà !! idanuwan nata _tana kallonta,
Dan yarinyar badai kyau ba,dan in nace zan kwatanta muku" kyaun da allah yamata,bata lokacine..
Kekkyawace ajin karshe.
Farace sosai,tana da dogon hanci,dakuma karamin baki lebanta jà jawur dashi,tana da siraran hakora da dan karamin wushriya,idonta fararene tass kamar madara,tana da kwanceccen gashi a goshinta duk da hijabin data saka amma ana iya hango ta gaban.. goshinta,kina gani kinsan gashin mai laushice,
Har yanzu bata dauke idonta daga kallon momy da takeyi ba?"
Karasowa mommy tayi ta rungumota,sai kawai ta saki kuka mai suma zuciya,itta ma jannat kuka tasa,saboda a duk lokacin da taga momynta na zubarda hawaye toh,hadda nata hawayen sai sun zume,
Ai momy naganin haka ?"ta share nata hawayen, ta janye jikinta daga rungumar dataiwa jannat" din.. sharewa jannat hawaye tashigayi"
Saida taga jannat ta dena kuka,sann ta riko kumatunta duga biyun,
Tafara magana,babyna ina so kizama jarima,kisawa ranki" koda mu.. ko babu mu..
Zaki iya rayuwa,kiyi mun alkawari bazaki karayin kuka ba,dan ko bana kusa dake in kinyi kuka nima zanyi,
Girgiza kai jannat tayi tace nayi miki alkawari momy bazan kara kuka ba,saboda in nayi kince kema zakiyi koda bakiya tare dani amma kina ganina in nayi kuka,
Nikuma kinsan momy banason naga hawayenki"
Murmuchi momy tayi tace yauwa babyn momy shiyasa nake sonki dayewa, jannat tace nima ina sonki momyna..
Amma momy ina zakije kike fadan irin wayennn maganganu ?"jannat ta jefawa momynta wannn tambayan,
Babu inda zani babyna"
Kawai dai..nasan wata rana ba Lallaine mukasance tare ba,kuma banason ki kuma.. tambayata ina zanje kinji ?"toh momy" jannat ta fada,hawayene suka soma subo mata tayi sauri gogewa, tana murmuchi,dan kar momynta ta fahimci tana kuka,kuma tayi mata alkawari bazata karayin kuka ba "
Jannat karamar yarinyace amma saboda tsabar wayonta in tayi wani abu sai ka ranse ka dauka babba tayi..
Ahaka dai momy ta mike daga durkusawan datayi,
Ta kalli jannat,baby kitafi aji karki makara,ki kuma dinga tunawa da alkawari na karki manta kinji ko?"toh momy daga mata hannu momy tayi"Dadinta ta riko hannunta"suka wuce cikin makarantar,shima tausayin yarinyar yakeji sosai kuma,baisan meyasa ba, yau yafi jin tausayinta fiyeda ko wana lokaci,sai da ya kaita har gaban ajinsu kamar yanda ya saba yayi kissing dinta,bye! bye!! Dadi jannat ta fada.
Bye !baby kiyi karatu sosai karki manta da'a bunda momynki ta fada miki_ kinji,okayDad..sai data shige cikin aji sannn ya juya ya koma wajan mota,yana zuwa ya tadda momy tana saye.
A inda aka barta..hannunta ya kamo ya bude murfin mota yasata,ya zaga shima ya shiga ya tada motar suka bar wajan..?
Kallon agogo yayi yaga har tara tsaura.amma basu bar garin ba har yanzu..yana kuma bukatar kafin su jannat su tashi daga makaranta su dawo.. amma har yanzu ko gakinma basu bari ba..
Rasuwa akayiwa daya daga cikin yan kanfaninsa shine yakeso suje musu gaisuwa a kauye ne mahaifiyar yaron da yake aiki a kanfanin nasu take,shine zasuje kauyen..
Gudu ya dan kara saboda suyi saurin dawowa,
Yana cikin tuki wani katon mota na mai ya nufosu gadan!gadan!!
In Dadi yayi kokarin bashi hayya sai mai motan yabishi.suna cikin hakane sai kawai mai motan ya kuma tahowa gadan!gadan,!! Wannn karan Dadi bayi yunkurin bashi hayya ba har seda mai mota ya karaso wajan,babu abunda kakeji sai wani kara kuuuuuuuuuuu.....
Wanene Dadi ?"
Wacece momy?"
Me kuka ya samesu ,a hayyarsu ta zuwa gaisuwa ?"
Kubiyoni a sannu ahankali gaku gane ko wanene su...
Sakeena ismail Cameroon ✍️
Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝♀️
By
Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)
Bismillahi rahmani rahim
Page 3&4
*Wanene Dadi*
Sunnsa na gaskiya "Muhammad (Dadi)dan asalin garin kano ne a kano aka haifeshi yayi" karatu ,kuma a kano yayi girma yana da shekaru sha takwas yagama cegondris school dinsa,sai iyayensa suka turashi, jamiya a kasan Singapore acan ya hada digrinsa,na daya dana biyu, ya karanci harkan kasuwanci,bayan yagama ne ya dawo gidan Nigeria.
Bai dade da dawowa ba allah yayiwa ma haifinsu rasuwa sakamakon ciwon koda dayake fama dashi "shekara da shekaru",dama kuma mahaifiyarsu ta dade da
Rasuwa ,sanda take nakudan kaninsa Ibrahim",a hannun kishiyar uwa suka taso,yakusa gama... segonderi ne,babansu ya rabu da matarsa"..mai suna halima"halima nada wani mugun hali,har ta .. koyawa Ibrahim",saboda baka isa ka ajiye kudiba,dan.. kana ?"ajiyewa zata dauka,ga kuma bakar zuciya da take da itta,tun lokacin da mahaifinasu ya gano,ya yanke igiyar?" aurensu,saboda a.. tunaninsa kar ta bata mai yaro,shiyasa kawai ya rabu, da halima.
Da allah yayiwa mahaifinsu rasuwa "Muhammad yayi!yayi!!
Ya cansawa kaninsa wannn halin , halima daya- dauko amma ina sam.ya kasa ganewa karatun ma?" daker ya kammala.
Bayan rasuwar iyayensu,kasancewa Muhammad yayi girma ya mallaki hankalinsa shiyasa ya_ yanke shawara" ya bude kanfani"
Da dukiyar da.. mahaifinsu" ya bari da.. shi kadai zai taimakesu a nn gaba,
Ya bude kanfanoni taban- daban dan a yanzu haka ya na da" kanfanoni kusan guda biyar,a kasar Nigeria,
Da yagadai suna zaune dagashi "sai kaninsa"sai kawai ya- yanke shawara ya nemo matar aure"haka kuwa akayi wata rana aiki ya kaishi " garin adamawa"acan ne ya hadu da hajiya asma'u ,
Har soyayya mai karfi ta kullu a sakanisu,
Kawunsa ya gayawa bayan sun gama dai! dai!! tawa da iyayen asma'u aka daura musu aure suka tare ann garin kano.
Ibrahim kuwa ganin yayansa yayi aure shine.. yace a bashi" kudinsa "way shima aure zayi?..
Alhaji Muhammad bai hanashi ba "yace yaje -ya kawo mai matar ya gani?"yaje- ya kawo matar amma da alhaji Muhammad ya bincika iyayen yarinyar ya gano cewa ashe ma yer uwarsu halima sohon matar babansu,babu yanda Alhaji Muhammad baiyi dashi akan ya rabu da yarinyar" ya nemo wata ba,amma yaki,ahaka ya dauki dukiyarsa ya dangamai ahannunsa yakuma kara mai da nasiha"
Amma bai wuce shekarunsu uku kacal da aure ba suka cinye kudin da matarsa,
Kasan cewa kuma Ibrahim din ya riga Muhammad hayyuwa.
Ahakama ranar suna sukayita.. almubazzaranci,da kudin har. kufi yakare.
Ya koma wajan yayarshi Wai dan allah ya taimakamai da kudi,amma Alhaji Muhammad yasan alinsa tsarai,inya dauki kudi ya bashi cinyewa zai kumayi
"Shiyasa yace yaxo yayi aiki a kanfani,
Ibrahim ba haka yaso ba.
Dan babu yanda ya iyane kawai"yasa ,ya fara aiki a kanfani yayansa.
Yana zuwa kanfani yayansa yaga irin ci gaban da ake tasamun a kanfani, wani mugun bakinciki yaji,
Ahaka ya dinga almubazzaranci da kudin kanfanin, in anyi mai magana "sai yace ai kudin yayansa ne,ina ruwansu.
Haka mutanen suka kyaleshi.
Sai wata rana da alhaji Muhammad ya samu labari,sora kiris ya koresa daga kanfaninsa"?..
Da'ger dai Ibrahim ya samu ya lallaba yayarsa akan cewa bazai sake ba.a sannn ya hakura ya barshi,yaci gaba da aiki a kanfanin?"
*Bayan shekara daya*
Itta" ma -matar ?"
Muhammad, wato asma'u allah ya azurtasu "da yah mace"jannat,amma sunfi kiranta baby,suka dauki son duniya suka daurawa yarinyar, jannat "nada shekaru uku kacal a duniya , Dadinta ya dauki biyu daga cikin wayenn kanfanonin nasa ya mallakawa jannat"da taimakon lawyansa akayi komai,dan Bayan matarsa da lawya babu wadda yasan da zancen.
A yanzu haka jannat nada babbar wayarta da iyayen suke kiranta dashi
In bata nn,saboda basa iya awa daya batare da sunyi waya da itta ba..
Itta ma dai hajiya asma'u tana aiki ,babban lawyace ita shiyasa tun lokacin da jannt ta taso taga mahaifiyarta "da kayan -yake bata sha'awa,shiyasa akullun take da buri itta ma tayi karatu ta zama lawya kamar ma haifiyarta..duk da karacin shekarun jannat amma allah yayi mata baiwa sosai,ta fanni da dama,dan in'tayi wani abu zaka rantse babbace tayi !
shiyasa,a kullun iyayen suke alfahari sosai da yer tasu ..
*Cigaban labari*
Ai babban motar nn na gama hankada motarsu alhaji Muhammad,ya juyar da hancin motar sa"
Yana dariya waya ya dauka,yayi kira' naji yana cewa ai oga "sunriga 'da sunkone,dan ko nimfashi babu alamarshi,dariya suka sheke dashi da wadda aka kira da oga,
Toh shikenan oga"ina.. jiran cikon kudina,yana gama -magana ya kashe waya,ya kuma rushewa da wata dariya..?
Nn da nn mutane suka cika awajan,
Kama daga yen jaridu,motar kashe gobara.ko.allah zaisa a samesu suna da rai..
Amma ina ,ana fiddasu.
Suka tarar gaba daya sun kone gawar ya koma baki kirin daker suka ganesu.
Ai ,yen jaridu suna.. ganin,babban dan kasuwa nn dayayi kaurin sunn,nn da nn,su gomna dasu seneto sun cika a wurun,dan duk wanda yasan Alhaji Muhammad Ali?"
Yasan mutunne mai son" jama'a da kuma yawan taimakon al'umma ,da talakawa..
Kowa kukan mutuwann yake..
Ai ana cikin hakane kaninsa ya karaso wajan.
Kuka sosai yake gonin ban tausayi,
Sai rarrashin sa"ake amma ina sai kace cemai akayi ya kara sautin kukan nasa..
Sai can mutane sukaga ya mike"tambayara yan jaridu sukeyi ina zashi?"
Ya amsa musu da cewa,yarinya na makaranta" zaije ya dauko ta.
Allah sarki kowa na bukatar yaga yer Alhaji Muhammad Ali.
Kallon wani abokinsa Ibrahim yayi -ya umarceshi daya nunawa yan ambulance gida akai gawarwakin nasu"bari yaje ya dauki jannat a makaranta"kuma,kar wanda ya sanar mata da mutuwan nasu "saboda yarinyace?...
Yana gama magana,ya shiga motarsa,yabar wajan,yana tafiya yana hawaye ,saboda yana mugun tausayin jannat sosai..
Bai san ,wana karya zai mata ba,
Ahaka dai har ya karasa school din nasu "duk da dai lokacin tashisu baiyi ba,amma yayiwa malamin nasu bayanin komai"sannun aka kira jannat "..
Fitowa tayi daga cikin ajin nasu,kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Sai kace tasan abunda yake faruwa?"
Ann kuwa babu a bunda tasani,alamune kawai taji a jikinta,
Karasowa tayi inda Oncle Ibrahim yake tsaye,kallonsa tayi, Oncle Ibrahim ina Dadi da momyna,meyasa basuzo sun daukeni da kansu ba?"..
Ta jefamai wannn tambayar Duk alokaci daya, Oncle Ibrahim" kam yama rasa wanne zai amsa wanne kuma zai bari,
Murmushi ya kirkira ya ,kalleta,baby ai momy da Dadi sunyi tafiya,amma suna hayyar dawowa,shiyasa sukace nazo na daukeki kinga in' sun dawo basai sun kuma zuwa school daukarki ba,saboda kinga agajiye suka dawo,nasan kuma kina son momy da Dadi sosai bakiyaso su gaji deyewa ko,geda kai tayi _tana murmushi duk da- dai bahaka taso ba,itta kam a gaskiya tafison iyayenta suxo sudauketa...
Kallon Oncle Ibrahim ta sakeyi, Oncle Ibrahim "amma ya naga kazo daukata tun Kadin lokacin tashimmu yayi ?"
Saboda biki akeyi a gidana shiyasa nace bari naxo na daukeki,kinga ameera ma nacan na jiranki ,ameera yer wajanshi ce, ta bawa jannt shekara daya,
Salle tayi ta rungume Oncle dinta,tana ta murna,wai zataje biki..
Riko hannunta Ibrahim" yayi suka bar cikin makarantar,inda yayi parking motar sa suka nufa,suna zuwa ya bude mata gaban mota tashiga,ya rufe shima yazaga tama zaunin driver ya shiga,
Yana tuki amma hankalinsa gaba daya maya kansa,har suka karasa kofar gidan n'a.....
Sakeena ismail Cameroon ✍️
Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝♀️
By
Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)
Page 5&6
Bismillahi rahmani rahim
_________"Suna zuwa gidan oncle din nata ya bude murfin mota ya fita ya zaga ta bangaren jannat"ya bude mata"ta fito tana kallon mutann dake kofar gidan oncle din nata,ta juya ta kalli Oncle"oncle "ya naga mutane deyewa a kofar gidan naka ?"jannat" ce tayiwa oncle din ta wannn tambayar?"
"Jannat kin manta nace miki ana biki a gidana, ohhhh na manta wllhy oncle "jannat "ta fada tana dariya ,tace gaskiya oncle daga gani bikinn zatayi dadi,kwarai kuwa jannat "oncle din ya bata amsa...
Mushiga ciki ameera" na can na jiranki, toh amma oncle da wana kaya zanje biki?"ban zo dakaya bafah,ta marairaice fuska kamar zatayi kuka,ki kwantar da hankalinki baby" baga kayan ameera ba sai kisaka kafin a kawo miki kayanki ko?"murmushi jannat tayi tace toh oncle,amm dai oncle su momy da Dadi "nama ,in sun dawo zasuxo bikin ai ko?"sosai ma baby,zasuxo suna dawowa,zaki gansu suma...
Tsalle tayi ta rungume Oncle dinta "dariya yayi- mata ya riko hannunta-suka shiga cikin gidan..
Suna shiga cikin gidan nan madai mutanene sosai,yauwa baby ga kakacan taxo, kitafi wajanta nima ganinn zuwa yanzu kinji?"toh Oncle,tsakin hannunta yayi"ta nufi wajan kakarta -ta bangaren uwa dataxo ittama dazu,kowa na kuka ,amma ganin jannat ne yasa suka dena..?"
Karasowa jannat tayi- tana dariya jin dadi na ganin kakarta ma taxo biki,haye cinyarta tayi,ta fara magana,kaka ashe kema kinxo biki ?"
Eh naxo "kin dawo?",keda kai tayi,kakarta- ta mike ta riko hannunta suka shiga daki cire mata infome dinta da zakarta,
Ta shiga toilet tahada mata ruwan wanka tayi mata taxo ta dauki kayan ameera" tasa mata, wadda kayan yawanci Dadin jannat ne yake dinka musu shi,
Kallon kakarta tayi -ta fara magana kamar haka
Kaka ina ameera banganta ba ?"ameera bata dawo daga school ba jannat"amma yanzu itta ma zata dawo,
Toh amma meyasa ni aka daukoni da wuri?"
Ai ke Dadinki da momynki basa nn shiyasa aka je daukarki da wuri,géda kai tayi-ta nemi waje ta zauna ta rafka uban tagumi...
Kallonta kaka tayi- tace jannat ya naga kinyi tagumi kuma?"
Babu komai kaka,amma meyasa har yanzu su momy basu jawo ba jannat "ta tambaya?"
"Zasu dawo yanzu insha allah kinji ?"toh jannat tace..bayan mintuna kadan aka -kawo mata abinci taci takoshi"ta kwanta akan cinyar kaka nan dann bacci ya kwasheta,.
Kallonta kaka tayi tana zubar da hawaye,
Dan bakamin tausayawa jannat take ba,yanda ta shaku da iyayenta dinan..
Kafin a samu ta koma normal gaskiya zasu sha wahala sosai,
*"Bayan awa daya*
Angama yiwa su Dadi sutura,andaukesu za'a tafi a tsadasu da gidansu na gaskiya😭
allah sarki rayuwa 🥺
Andaukesu za'a tafi tazu kenn mutane sai kuka suke,cikin bacci jannat taji tsautin kukan mutane sama!sama !!
Da farko dai ta dauka ko mafarki take"sai daga baya taga abun yayi- yawa,dan bude ido tayi kadan "ta kuma rufewa..ai wann budewan da zatayi kadan dinnn ta dan hango wani abu,ai batasan sanda takuma bude idonta tar ta zubawa abunda taga andinko ba,mikewa tayi
Ta nufir wajan mutanen da suka dauko gawar su momy gadan ! gadan !!...
Dakatar da fita da gawar! wakin!! Nasu mutane sukayi....
Suka zubawa jannat" idanu har ta karaso, inda suke,tsayawa tayi ta zuba musu ido,
Ko giftawa batayi,kallon su tayi -ta fara magana ?"..
Oncle waye mutu kuma?"
Dan na taba ganin irin wannn abun ta nuna abun daukar gawa.da aka saka su momy aciki .
Tana nuna musu da yenyatsan ta,kallon ta Oncle Ibrahim yayi ya kirkiro murmushi,
Haba baby waye gaya miki sai wayenda suka mutu ake tsawa a ciki..
Haba Oncle nafah taba gani a film,nida momy aka saka wata,aciki naji suna cewa ta mutu sai kuka sukeyi...
Shine zakace bamutuwa ba,
Kuma ba gashi dukanku kuka- kukeyi ba..
Nidai bari na duba suwaye ma cikin ne..
Dan matsowa kusada gawan tayi,tasa hannunta zata bude, sai Oncle Ibrahim yayi saurin kama hannunta,,yana murmushi "haba baby "wann fah nagaya miki ba mutuwa bace,kawai liloh muke musu "bakiga abun yayi kama da gado ba,ai tana jin haka tayi dariya,tace toh nima zan hau Oncle nima inaso aimun lilon.
Su ! su!!sauka nima na hau aimun lilon.
Tana gama fadan haka tasa hannu ta yaye abunda aka rufe gawan dashi,tana yayewa 'idon ta yayi tozari da fuskar momynta"ai bata san sanda ta kurma ihuuuu ba,da karfi,tana girgira momynta amma ina,shiru.babu alamar motsi,zuwa tayi ta yaye na Dadi ai tana ganin haka,sai ta fadi kasa a tsume....jinjigata "kaka da Oncle suka tsomayi amma shiru,sai kawai suka dauketa suka wuce da itta a sibiti..
Wasu kuma suka tafi da gawarsu momy"suje su binne...
"Suna zuwa a sibiti likitoci suka karbeta "aka shiga bata taimakon gaggawa amma ina shiru ko motsi batayi...
Wannn abun dannawan
da ake sawa mutane a irji likitocin suka" sa mata"amma