Showing 48001 words to 50838 words out of 50838 words

Chapter 17 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

kake kowa ubanka na can ya dirkawa mamanka ciki tana fama a can kai kuma ka ishi mutane da kuka yaro sai kace aljanu sai shegen fari kamar ubanka ni wllhy wannan hasken naku har tsoro yake bani in na zauna ince ayya sanda mamanshi take da cikinsa aljanu basu shigeta ba kuwa toh wai ni ina ruwana ma na zauna sai faman yin magana nake ni kadai kamar mayya kai ma ba wani magana kirki ka iya ba,


Nidai wllhy uwar adamu bata kyau tamin ba yanzu gashi aljanun daya shjgeta sanda take da cikin adamu gashi yanzu nima an haifomin jika kamar sa,


Kai kaka waye ya gaya miki aljanu ya shige maman Adam din da har zaki fadi haka matar basirta tayi magana tana karasa shigowa dakin dan tun dazu taketa sallama kaka bataji ba sai faman tsurutu take itta kadai.


Ke kuma yer nan kice lebewa kikayi kina jin a bunda nake fada ko.


A'a kaka ni bamma dade da dawowa daga wajan aiki ba ma nace bari nazo na duba ku,


Hanif kuwa tunda ya ganta ya taho wajanta yaron yayi girma kamar ba dan shekara biyu da wata biyar ba,


Dan in kaganshi ma zaka ranse kace zaiyi shekara uku da wani abu dan tsabar girman da yaron yayi.




Kaka ina wuni lfy lau kaka ta fada,


Amma gaskiya bakwa yimin adalci da kuke barina da wannan yaron ni gaskiya ku daukeshi "ku mai dashi gidan iyayensa ai banice nacewa ubansa" yayiwa uwarsa cikin da wuri ba dan haka gobe ki mai dashi,


Me mami zatayi in banda dariya .


Hoo ma haukaciya ma kika mai dani kenn a'a wallhy ba haka bane ba kaka za'a mai dashi insha allahu.


Kaka najin haka ta washe baki tace ko ke fah ai gwara a mai dashi ba suna da mai aiki ba sai ta kular musu da yaron,


Kai mami da geda eh hakane kaka. geda kai itta ma kaka tayi sukaci gaba da wani hirar.


*Gidan oncle Ibrahim*


Bayan an yanke wa Ibrahim hukuncin kisane bai fi da shekara daya ba allah yayiwa Ameera rasuwa bayan doguwar jinyar data sha.


Kafin allah yayi mata rasuwa tayi na dama sosai tayi na damar biyewa halayan mahaifiyarta hajiya Maryam,


Itta ma dai tun sanda aka yankewa mijinta hukuncin kisa tayi na dama babu inda bata nemi jannat ba saboda ta nemi yafiyarta amma bata ganta ba.


Dan a yanzu komai nasu yakare ta tsiyar da komai nata saboda nemawa ameera lfy amma bata samu lfy ba har allah ya dauki ranta,


Hatta gidan da suke ciki ta siyar ta dawo kano ta siyi karamin gida da bai wuce million daya ba,


A yanzu haka tana seda kosai a kofar gidanta dan ta rufawa kanta asiri,


Tuki yake sai sannu yake ta faman yi mata Saboda har safe zazzabin bai sauka ba shiyasa ya dauketa ya kaita a sibiti aka dubata aka bata magani shine zasu koma gida,


Zasu wuce kenan ta hango mai seda kosai sai kawai taji kosan ya burgeta,


Saya _saya habibi ai baisan sanda ya taka burki ba.


juyowa yayi ya zuba mata ido saboda shi a tunaninsa ya dauka ko jikinne.


Sai daya juya yaga sabanin haka ajiyar zuciya ya sauke ya juya yana kallon inda take kalla sai yaga mai seda kosai ne ashe.


Habibti kina son kosai ne kai ta keda okay bari naje na shiyo miki a'a habibti muje tare ina son na shaki kamshin ma dan kamshin yamin sosai.


Kai habibti sarkin fitina yanzu dan allah ki rasa ramshin da zakice yayi miki sai kamshin kosai eh ni dai ka jirani mutafi tare okay fine fito mutafi murmuchi nayi na fito.


Karasowa sukayi wajan mai kosan itta ko hajiya Maryam bata ma lura dasu ba a wajan tananan sai faman zubawa wani yaro kosai take,


Sallama Adam yayi mata dai _, dai lokacin tagama zubawa yaron kosai tana mika mai ledan.


Karba yaron yayi ya tafi sallamar ta amsa tana kallon mutanen da sukazo wajanta dan tasan dai ba kosai sukazo siya ba,


Saboda irin su basu taba zuwa siyan kosai ba.


Lfy bawan allah eh lfy lau baaba kosai zaa bani yana magana tare da mika mata dubu daya karba tayi tana cewa na nawa zan samaka na dubu dayan zaki bani baaba ido ta zaro tana kuma tambayarsa na nawa saboda ta dauka ko kunnenta ne bai jiyo mata dai dai ba sai dataji ya ambaci dubu daya sannun ta soma zuba mai,


Taga zuba mai Kennan tana mika mai idonta ya sauka akan na jannat
Da ittama tun dazu take kallonta da farko dai bata ganeta ba amma daga baya tagane mamace.




Hajiya maryam na ganin haka batasan sanda ta saki ledan kosai ta mike saye ba tana nuna Jannat da enyasu ta.








Sakeena ismail Cameroon ✍️






Comment and Sharee pls 🥰
[10/17/2023, 11:18 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 84&85


⬅️End ⬅️End⬅️ End






Bismillah Rahmani rahim






________jannat ! hajiya maryam ta furta mama!itta ma jannat ta fada jannat ina kika shiga babu inda ban nemeki ba jannat amma ban sameki ba dan allah dan annabi jannat kiyafemin wllhy alhakin kine yake bibiyarmu"cikin kuka ta karashe maganar.


Wllhy mama na dade da yafe muku dama can ban rikeki a raina ba amma kece kika koma haka ina Ameera?


Allah yayiwa Ameera rasuwa jannat yanzu kusan sheka kenan.




Ameenra ta rasu mama?


Eh Ameera ta rasu jannat itta ma kafin allah yayi mata rasuwa tace in mun hadu na nemar mata yafiya a wajanki .


Allah sarki ameera allah ya jikanta da rahma Ameen mama ta amsa amma banda Adam da fuskarsa"yake a daure kamar bai taba dariya ba.


Wai habibti tun dazu sai tsurutu kuke ta zubawa baki min bayanin komai ba.


Wannan din wacece duk dadai yagane tsarai matar wannan oncle Ibrahim din nan ne saboda yana jin sunan ameera a bakin jannat din.




Habibi wannan ittace mama matar oncle Ibrahim baban ameera da nake baka labari.


Okay kace wanda suka kashe miki iyaye.


Haba habibi mai haka.
Mai haka kamar yah ko karya nayi ba sune suka kashe miki iyaye ba.


Shiru jannat tayi tama resa abin cewa.


Mama kam sai kuka take wannan wana irin abun kunyane mijinta ya ja'a musu"itta kam duk son dukiya bata taba tunanin kashe kowa ba.


Wllhy mune bawan allah mune duk da ban sanka ba amma ina da yakinin cewa kaine mijin jannat.


Dan allah bawan allah ku yafe mana.


Tsaki Adam yayi ya juya ya kalli bangaren da jannat take tsaye.


Kinga malama wuce mu tafi in kuma bazaki tafi ba ni nayi tafiya ta dan na lura cewa baki san ciwon kanki ba.


Yana gama magana ya juya ya nufi wajan mota.


Har ya shiga mota jannat bata taho ba.


Durkusawa tayi ta dauki ledan kosai tabi bayan shi.


Shiga motar tayi kallon hannunta yayi yaga ledan kosai ne a hannunta karba yayi ya jefar dashi ta Windows.


Haba habibi taya zaka jefarmin da kosai na.


Bazakici wannan kosai ba wllhy.


Ki bari in munga wani a hayya sai mu siya ni bana so wannan nakeso"
Jannat tayi magana kwalla na zubo mata a kumatu.


Har suka karasa gida babu wanda yayi magana.


Da daddare bayan ya dawo daga sallar i'sha ne ya shigo palo babace kadai a palon gaisawa sukayi yana tambayar baba laure jannat taci a binci kuwa,baba laure tace ai tunda suka dawo daga a sibiti bata fito ba.


Toh shikenan baba laure hadamin a bincin kikawo na kaimata kai baba laure ta geda tare da mikewa ta nufi kitchen.


Hada a binci tayi da ruwa ta dawo palon mika masa tayi ya amsa ya nufi daki.


Shiga yayi ya a jiye a bincin a kan dan karamin teburin dake cikin dakin ya karasa kusa da gadon


Zama yayi yana duba idon ta dan murmushi yayi dan yasan tsarai ba bacci take ba.


Habibti tashi ga abinci na kawo miki ki tashi kici.


Na koshi wllhy baki isa ba sai kintashi kinci a bincin nan ko ke bakiya duba a bundake cikin cikinki bane.


Nifah bazanci a binci ba haba habibti wai meyesa kike hakane,


Kaga habibi dan allah ka kiyaleni.


Nasan fushi kike dani amma kisani cewa badan kowa nayi hakan ba sai danke.


Haba habibi sai kace mu ba muslimai bane.


Ko allah ma muna yi mai lefi kuma in mun rokeshi ya yafe mana toh mu meyesa bazamu yafewa wani ba kasani cewa ba ittace ta aikata ba mijinta ne,


Jikin Adam yayi sanyi tun sanda jannat ta fara magana yake kallonta har tagama bai ce komai ba.


Iska mai zafi ya busar daga cikin bakinsa".


Hakane Habibi naji dadi da kika tunatsar dani kuma insha allahu zamije har inda take gobe.


Dan allah habibi kai Adam ya geda jannat ta tsaki murmushi .


Toh yanzu an dena fushi dani ko kai jannat ta geda tana kumayin murmuchi.


Murmuchi shima yayi ya rungume abarsa"yana sauke ajiyar zuciya.


Sakinta yayi ya mike a binci daya ajiye dazu yaje ya dauko ya dawo gefan gadon.


Toh habibti ga abincin yanzu kam ai nasan zaaci tunda anyafe min kai na geda ina bude baki samin a bincin daya debo a chokali yayi na shiga taunawa a hankali ina lumshe ido dan a bincin ba karamin dadi yamin ba.


Dambun shinkafa ne daya sha kayan hadi.


Sai dana cinye a bincin tas.


Kinkoshi ko nakaro miki a'a nakoshi habibi hamma ai kai bakaci ba hararan wasa yayi mata ta saki murmushi.


Sai yanzu kika san banci a binci bane .


A'a bahaka bane habibi hakane mana tunda yau kina fushi dani toh kayi hakuri kawo plate din mika mata plate yayi ta fita bata jima sosai ba ta dawo da abinci sai ruwa,


Zama tayi a gefansa" ta shiga bashi shima har sai dayaci sosai sannun yace ya koshi.


Ka tabbata ka koshi kai Adam ya geda.


Ruwa ta mika mai yasha ya bata cup din ta kwashe kayan ta maidasu"kitchen" ta dawo dakin.


Dakinsa suka koma.
Saida sukayi wanka sannun suka kwanta,


*Washe gari*


Kamar yanda ya fada haka kuwa akayi bayan ya dawo daga wajan aiki suka shirya suka nufi wajan da sukaga hajiya Maryam a wajan.


Dan yanzu jannat bata zuwa aiki ta dauki hutu saboda laulayin da take fama dashi.


Suna zuwa suka tarar da itta tana suya kosai kamar jiya.


Tun saukowarsu daga cikin mota mama take kallonsu"har suka karasa wajan da take.


Adam ne ya fara gaisheta cikin sakin fuska.


Amsawa itta ma mama tayi suka gaisa da jannat ma.


Kasan cewa magarib ya gabato ne kuma dama tagama tana tattara kayan da tayi suya dashi sukaxo.


Tsauri tayi ta karasa tattarawa tayi musu iso cikin gidan.


Palo suka shiga gaisawa suka karayi.


Palon babu laifi yana da dan kyau dan hadda kujeru ma_ ma dai daici.
Sai karamin TV.


Ruwa da ragowar kosan data rege ta kawo musu"


Jannat kam kamar jira take ta saka plate din a gaba sai ci take Adam kam yace ya koshi",


Sai data cinye kosai tas ta kora da ruwa.


Adam yace bari yaje yayi sallah sai yazo su tafi toh jannat ya amsa ya fita.


Jannat da mama ma sallah sukayi suna idar da sallah sukaci gaba da hira suna cikin hira ya dawo.


Sallama suka yiwa mama suka tafi.


Tace itta ma insha allah zataxo in tatashi zuwa zata kira jannat tayi mata kwatance.


*Bayan kwana uku*


Jannat na zaune kiran mama ta shigo wayarta
Tana dagawa bayan sun gaisa ne take tambayar ta kwatancen gidan dan tana son zuwa gobe.


Jannat tace ta bari zata gayawa Adam yazo ya dauketa tace jannat a'a kawai tayi mata kwatancen zatazo ba sai ta fadawa Adam ba.


Daker dai Jannat ta samu ta shawo kanta ta amince sukayi sallama ta kashe wayan.


*Washe gari*
Adam daya tashi dawowa daga wajan aiki yabi ya dauko mama ya kaita gidansa kamar yanda jannat ta bukata.


Taji dadin zuwan mama sosai ba itta ta tafi ba sai bayan i'sha Adam ya maida itta gida.


Data tashi tfy babu a bunda ban bata ba su atamfofi kala_ kala sai kudi 50k dana bata Adam shima ya bata amma bansan nawa ba.


Har gida ya maita itta suna hira a hayyane kafin su karasa gidan natane Adam yake tambayarta"dalilin dayasa take seda kosai tace badan komai take seda kosai ba sai dan ta rufawa kanta asiri saboda da kudin take samu tayi chefene dashi ta kuma dinka situru.


Adam yace in dai Saboda chefene ne da kuma Kayan sawa yasa take wannan sana'ar sai da kosai toh daga yau ta dena insha allahu zai dingayi mata.


Tayi kuka farinciki da kuma kukan na dama har ta gode allah.


Tun lokacin jannat in an kwana biyu zata je gidanta"itta"ma mama tana zuwa taganta akai _akai har hanif ana kai mata ya danyi kwana biyu sun tsaba sosai da yaron.




Wata rana jannat na zaune dasu walida da Minal da yanzu kusan watan ta biyu da haihuwa sunzo dubata saboda bataji dadi ba kwana biyun nan,


Nikam aunty walida ya jikin mommy wllhy da sauki an kwantar da itta a sibitin dake cikin prison din da sukaga jikin kara rikicewa yayi sai kawai aka kaita a sibitin amimu kano,


walida tayi magana hawaye na taruwa a idonta",


Ki kwantar da hankalinki aunty walida insha allah mommy zata samu lfy da izinin ubangiji toh allah ya yerda walida da Minal suka fada Ameen jannat ta" amsa".


Anan ne suke saida mata cewa daga nan ma a sibitin zasu",


Kiran Adam tayi ta fada mai cewa zasu a sibiti dasu walida yace toh babu damuwa suje in yataso daga wajan aiki zaixo ya dauke ta tun da itta yanzu cikinta ya sufa haihuwa ko yau ko gobe.


Toh ta amsa"ta shirya suka tafi.


Suna zuwa zasu shiga aka hanasu wai jikin natane ya tashi likitoci na kanta"babu yanda suka iya ahaka suka saya a waje.


Walida da Minal kuwa suna ji ance jikin mommynsu ya tashi suka dinga kuka sakanin Minal da walida babu mai rarrashin wani.


Sai da jannat tasa baki sannun suka dan sassauta kukan nasu"baa wani jima sosai ba Adam ma ya karaso a sibitin.


Anan ne suke shaida masa cewa jikin nata ya tashi yayi addu'ar fatar samun lfy.


Kusan awa daya sukayi a wajan likitocin basu fita ba sai daga baya suka fita jiki babu kwari suna girgiza kai.


Adam suka kira suka shaida masa cewa allah yayi mata cikawa,


Salati kawai Adam yakeyi ya juya zai koma wajansu sai yaga jannat a sume awajan.


Da tsauki Adam ya karasa wajanta yana kiran likitoci bai fi mintuna kadan ba likitoci suka karasa suka dauki Jannat sai wani daki aka shiga bata taimakon gaggawa.


Ruwa suka samu suka yayyafah mata ta farfado sai kuma ciwon ciki ya biyo baya nakuda tazo dagan gadan,


Bangarensu"walida kuwa dakin da aka kwantar da mahaifiyarsu"suka shiga suka tarar da itta a lullube budeta sukayi suka dinga kuka wai ashe mommy ce ta rasu shiyasa jannat ta tsorota".


Kuka sosai suka sha waya Adam ya dauka ya kira barista ya sanar masa a bunda yake faruwa baifi mintuna 30 ba barista ya iso wajan.


Shima yayi kuka sosai yana son mommy matuka buk da wannn halayen nata amma har yanzu bai dena sonta ba a cikin zuciyarsa.


Rarrashinsu walida ya dingayi har sai daya samu suka dena kukan sannun ya barsu"


A lokacin sukaji karar kukan jaririya na tashi a dakin da jannat take ciki.


Ba'a juma sosai ba aka fito da jaririya a cikin tawal.


Saboda suna ganin haihuwa zatayi Adam ya kira baba laure ya gaya mata cewa ta tawo da akwatin haihuwa a sibiti ta shirya Idi zaixo ya dauketa toh tace ya kashe wayan.


Basu wani jima ba suka karaso a sibitin "suma.


Anan ne suke jin labarin rasuwar mommynsu" walida" sun tausawa musu sosai.


Adam na ganin baby da sauri ya karasa wajan likitan ya amshi baby.


Barista yana ganin jannat ta sauka lfy suka tattara suka koma gidanshi "tare da gawar mommy domin yi mata situra.


Su jannat kuwa umarni barista ya bawa Adam daya zauna da matarsa har sai an sallameta"


Adam ne ya roki barista daya barsa su tafi tare ai ga baba laure tana nan ga kuma Idi su zauna da itta kafin yaje ya dawo.


Haka kuwa akayi Idi ne da baba laure suka zauna da jannat dake ta bacci saboda alluran da a kamata dan ta samu hutu.


*Bayan kwana arba'in*


Kasan cewa anyi rasuwa shiyasa baayi taron suna ba.




Su Paa"ma sun zo da Maa"sunyi sati daya sun koma.


Hanif kuwa sai faman rigima yake tayi tun sanda aka haifi madina wato sunan maman Adam Kenan ana kiranta najwa.


Hanif kuma sunan baban jannat watoh Muhammad.


*Bayan shekara uku*


Airport**********


Jannat ce da Adam sai hanif da yanzu yake da shekara 6 sai kuma najwa da take da shekara uku,


Sallama sukeyi dasu baba laure sai su walida da Minal da sukazo musu rakiya.


Suna gama sallama suka nufi wajan da jirgin yake.


Jannat na rike da Najwa sai Adam da yake rike da hanif.da yake ta dagawa mama hannu dan sun saba sosai yawanci ma yana wajanta,


*Madina*


Mun sauka a madina munyi sati daya.


Makkah 🕋


Alhamdulillah munyi ibada sosai mun roki allah ya bamu zaman lfy ya jikan iyayenmu"ya kuma yafe mana kura kuranmu muma idan tamu tazo allah yasa mu cika da imani ameen allah ya bamu aljantul fildauci ameen ya allah 😭🤲






Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Alhamdulillah




Anan ne na kawo karshen wannan littafin nawa mai suna MIJIN ATTAJIRA




A bunda na fadi dai dai allah yasa mu anfana wanda kuma na fadi ba dai dai ba allah ya yafe mana Ameen 🤲




Taku a kullun sakeena Ismail Cameroon ✍️






Ina sonku sosai ma soyana allah ya barmu tare Allah yasa zumuncinmu ya kasance har a aljanna Ameen 🤲🥰




Sai mun hadu a wani sabon littafin 😍💃🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login