Showing 42001 words to 45000 words out of 50838 words

Chapter 15 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

nagode sosai allah ya saka miki da alkairi kaga Ado ni ka dena kirana da hajiya ba sunana hajiya ka kirani jannat kamar yadda kowa suke kirana dashi toh na dena inshallah murmuchi nayi mukayi sallama na fita na rufo mai kofah,


Bangaren mu na nufa babu kowa a palon sai na nufi dakinmu ,na tarar da Minal kwance tana bacci kaina na girgiza na ajiye jakata da mayafina na wuce toilet wanka nayi tare da alwala kasan cewa ban samu nayi sallar la'asar ba,




Bayan na shirya nayi Sallah.


Fitowa nayi naje na hadawa Ado abinci na nufi dakinsa "ina zuwa na kwankwasa"sai da yace in shigo sannn na tura kofar a hankali na shigo yana zaune a palo yana karasa aikin da aka bashi a kanfani ,kallona yayi ya sakarmin murmuchi nima murmuchin nayi mai na karaso na ajiye abincin dake hannuna zubamai na somayi ya dagatar dani,haba ha...bude baki yayi har zaice hajiya sai ya tuna tace bataso,kinga jannat kibarshi zan zuba, murmuchi nayi dan yadda ya fadi sunan ba karamin dadi yamin ba.
Ya iya furta kalman sosai,


Ka bari na zuba maka ai ko ba komai kai babbane


Ko baka haifeni ba amma ai ka dirmeni.


Kai ya geda a bincin na karasa zuba masa na mika mai karba yayi ya faraci a hankali cikin nitsuwa yakeci ba karamin burgewa yamin ba ,waje na samo na zauna na zuba mai ido,in naga yayi kamar zai dago idanuwansa sai nayi saukin sunkuyar da kaina inyi kamar bashi nake kallo ba,shi dai Ado daya fahimci haka bai kuma dagawowa ba har sai daya gama cin abincinsa".ya dau ruwa ya shà, hamdala yayi,


Sai a lokacin ya dago,yace
Nagama ya faga a takaice,


Kai na geda tare da mikewa kwashe kayan nayi mukayi sallama na wuce cikin gidan,






Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment Sharee pls 😍
[9/24/2023, 4:47 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By


Sakeena Ismail Cameroon
(mom muwadda)




Page 72&73




Bismillah rahmani rahim




_______"washe gari ina gama shiryawa na fito palo yin breakbeat sai na tarar dasu barista da matarsa sai Minal" gaishesu" nayi na jà kujera zan zauna kenan sai barista yayi magana kinga jannat ya zaki zauna ba tare da kinje kin_ kira yayan ku ba har zance wana yayanmu sai kuma na tuna Ado yake nufi tashi nayi na nufi bangaren Adam din ina zuwa nayi sallama na shiga baya palo sai kawai na nufi cikin bedroom din a tunani na ko bai tashi daga bacci ba ai ina zuwa sai na tarar sabanin haka,jin kamar karar saukar ruwa da kuma kamshin sabulu a toilet ne ya sani fitowa na dawo palo waje na samu na zauna nayi shiru ina jiran ya fito,




Baifi 10 minute ba naji karar mude kofar toilet din da dukkan alamu ya gama wankan,sai da aka kara kusan 15 minute sannun na mike na nufi cikin bedroom din dan na tabbatar yanzu yagana shiryawa,sallama nayi kafin ya amsa na denno kaina cikin dakin ina shigowa kuwa na tarar dashi daga shi sai gajeran wando ga kuma dogon wandonshi a hannu daga gani sawa zaiyi jin motsin shigowa dakinne ya dakatar dashi daga sawan da zaiyi,




Ai Ina ganin haka nayi saurin juyar da kaina na bashi baya tare da fadin am sorry am so sorry na dauka kagama shiryawa ne shiyasa na shigo dama Dady ne "yace na kiraka kaxo kayi breakfast ina gama magana nayi hayyar fita har nakai palo naji ya kirani,


Jannat jannaaat ya kuma kira da wannan muryar tashi mai dadi,


Ai ina jin haka bansan sanda na tsaya cak ba
Har ya fito ya karasa inda nake ban motsa ba.


Har ya karaso gabana kije ki kawomin a bincin anan saboda kunyar su Dady nakeji bazan iya cin abinci dasu ba,sai alokacin na dago nayi magana humm wallahy ya Adam Dady bazai amince ba kona je na gaya masa "gwarama ka biyoni mutafi nayi maganar,


Kai Ado ya dafa ya zanyi bashi da zabin data wuce ya biyota su tafi,kai ya geda muka fita yajaa kofar ya rufe muka nufi cikin gidan,




Muna zuwa muka tarar dasu barista har sungama yin breakfast sun koma palo




Durkusawa Ado yayi ya gaida barista da mami wato matar barista kenan,


Kallo na barista yayi yace sai kuje ku karya mukam mungama namu mun jiraku har mun gaji ,




Wallhy Daddy na tarar dashi yana wankane sai dana bari ya fito sannun na fada masa" kai barista ya geda,tare da kallon matarsa mu tafi ko kai ta geda tare da mikewa har tafita suka somayi har sunxo bakin kofa sai barista ya juya ya kalleni tare da fadin yawwa jannat in kun tashi daga wajan aiki ku wuce shopping din kiyi duk a bunda na fada miki jiya zan turo miki da kudin a account dinki toh Dady"




Amma basai ka turo ba a kwai kudi a hannuna zasu isa insha allah,gidanku gidanku nace nafiki sanin kina da kudi a hannunki ai nidai na gaya miki zan turo miki da kudi Kuma kar na kumaji kince komai toh Dady na fada ina murmuchi,




Mai mami zatayi in banda dariya kai alhaji har yanzu yarinyace fah.




Naji ke kuma wuce mutafi, allah ya kiyaye Dady na fada Ameen suka amsa suka fita,


Karasa wajan cin a binci mukayi kujera na jawa Ado ya zauna sai da nayi serving dinsa sannun nayi nawa zama nayi muka somaci,


Bayan mungama cin abinci daki na wuce jakata da kuma takalmi na _na dauka na fito kallon Ado nayi nace mu tafi okay ya fadi tare da mikewa sai daya koma dakinsa ya dauko wasu ta kardu dayayi aiki jiya dasu,ya fito ya rufo kofa yayi wajan mota,


Yana zuwa ya tatar ina jiransa"shiga yayi muka muce sai dana fara ajiye shi tukun sannun nima na wuce nawa wajan aiki,




Bayan mun tashine na biyo ta wajan aikinsu Ado na daukeshi sai dana fara sayawa a Wani restored mukaci a binci sannn muka wuce shopping din,




Muna zuwa muka shiga kallon Ado nayi nace mai ya zabi duk kayan da yayi masa"kai Ado ya girgiza aa jannat ni da nasan saboda ni kikazo wanan wajan ma da ban yadda na biyoki ba,kaga dakata yah Ado badai kai bazaka zaba ba ka barni ni zan zabar maka duk a bunda nasan ya dace da Kai,ba yanda Ado ya iya a haka ya dinga bin jannat a baya har sai da tagama a bunda zata daukar masa sannun taje ta biya aka kai musu kaya niki niki a mota suka wuce gida,




Bayan mun koma gidane aka kawowa Ado motarsa"aka kumayi masa alkawai gobe za'a kaishi yaga gidan da aka bashi,




Mota tayi kyau Masha allah,


*Washe gari*


Kamar yanda akayi wa Ado alkawarin cewa za'a kaishi yaga gidan haka kuwa akayi ankaishi yaga gida yayi kyau sosai,mudai sedai muce allah ya sanya alkhairi.


*Bayan wata biyar*


Adam ne ya fito daga cikin kanfanin ya kara haske da kyau kamar ba a Ado da aka sani a baya ba dan kana ganinsa yanzu kasan kudi yana shigarsa sosai hannunsa rike da makullin mota da kuma laptop dinsa ya dufi wajan motarsa "ya nufa shiga yayi ya wuce gida,






Sakeena Ismail Cameroon ✍️


Comment and Sharee pls 🥰
[10/1/2023, 4:07 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 74&75




Bismillah rahmani rahim




_______"soyayya mai karfi ya kullu a sakanin Adam da jannat suna son junansu sosai dan yanzu kam Adam ya ajiye kunya da kuma wannan tunanin da yakeyi a dah na ganin cewa shi ba dan kowa bane bai kamata yayi soyayya da yer gidan basu kudi ba,amma yanzu kam ya fahimci cewa ba haka bane dama shi bashi da burin data wuce ya dogaro da Kansa kuma Alhamdulillah yanzu yana iya yiwa kansa komai duk da Dady yana hanashi "saboda shi yafison ya dinga mai kafin yayi aure amma da ya fahimci Adam yana son yinwa kansa"komai har ma da mutanan gidan ya gyaleshi kawai .




Zaman da Adam yayi da barista!barista!! ya kara gane halayan Adam sosai shi mutun ne marason hayaniya gashi mai hankali duk da barista bashi ya haifeshi ba amma duk wanda yagansu zai tunani shine ma haifinsa"saboda yadda suke alaka tamkar uba da dansa"gwanin ban sha'awa,






Yana dawowa bangarensa"ya wuce wanka yayi da kuma alwala ya fito shiryawa yayi cikin milk din jallabia turare ya dauka ya fesa yana gamawa ya dau laptop dinsa dake ajiye akan gado ya koma palo ya shiga yin aiki aciki.


Lokaci zuwa lokaci yakan duba agogon dake daure a hannusa'.


Bayan wasu yan mintuna ne naga ya rufe laptop din tare da mikewa ya dau mukulli yayi hayyar bakin kofa fita yayi ya rufo kofa,da alama masallaci zashi.




Bayan an idar da sallah ne suka jera da barista suka nufi cikin gidan kasan cewa masallacin ba nisa da gida daka fita kofar gidan kana ganin masallacin,




Cikin gidan suka nufa suna tafiya suna tattaunawa,




Kallon Adam barista yayi ya fara magana.




Yauwwa Adam nace yanzu kam tun da kun fahimci juna sosai dakai da jannat ya kamata mu zauna mu sa'a ranar bikin naku ko Adam kam duk kunya yayi shesa da yaji barista yayi maganar auransu amma a zuciya kam murna yake,


Sai da barista ya kuma kiranshi sannun yayi magana Dady kune iyayenmu dan haka ba sai kunyi shawara damu ba .




Kawai duk a bunda kuka yanke dai dai ne,




Dama ina da kudi dana ajiye a account dina insha allah in kungama yanke shawara komai sai kayi min magana na bawa mami kudin ta hadomin lefe murmuchi barista yayi tare da geda mai kai,




Shikenan son amma zancen hada lefe karka damu ni da kaina zam bawa mamin naku kudi taje ta hado lefe harda ma kayan dakin in yaso kai ka kawo Sadaki kawai.




Ado zaiyi magana barista ya daga mai hannu,




Kaga dakata Adam kasan dai bana son haka ko.


Kai Adam ya geda tare da fadin nasani Daddy Allah ya wuci zuciyarka.




Godiya nake sosai Dady allah ya kara girma Ameen barista ya amsa.




Karasa cikin gidan sunayi suka nufi palo ba kowa a palon sai sanyin AC ne kawai dake aiki a palon zama sukayi suna kara tattaunawa.


A dakinsu"jannat kuwa tana idar da sallah ta mike kallon Minal dake kwance a kan gado tana dedda wayan tayi kinga Minal ki tashi muje muci a binci dakatar da dedda wayan Minal tayi tare da mikwa ta kalli Jannat din tace muje,kai jannat ta geda suka fita a gyere,




Suna zuwa palon suka tarar mami ma har ta fito,




Shiyasa suma suka nufi wajan cin abinci darek.


A hankali jannat take takowa har ta karasa inda suke,


Tun fitowarsu jannat Adam yake kallon ta har suka karasa wajan bai dena kallon ta ba.




Sai da barista yayi gyaran murya sannun Adam ya dauke ido yana sosa kai dan ya fahimci tsarai dawa barista yake.


Dan murmuchi yayi _yaci gaba dacin a bincinsa"




Zama su Jannat ma sukayi suka zuba nasu suka soma ci.


Bayan sungama ci ne kowa ya koma dakinsa Adam da barista kuma suka nufi masallaci yin sallar isha,






Fitowata daga wanka kenan shiryawa nayi bayan nagama ne na hau bed dina addu'a nayi tare da shafawa.


Kwanciya ta ne yake da wiya sai naji wayata na ringing lumshe idona nayi tare da gyara kwanciya ta,


Dagawa nayi dan nasan tsarai wa zai kirani a wanan lokacin shiyasa ban ko duba ba,


Sallama nayi cikin nitsuwa Adam dake kwance shima jin sallamar tane ya lumshe ido tare da budesu"in kaji yadda yayi shiru dinan zaka zaci bazai amsa sallamar ba ko kuma ince zaka dauka ko sallamar ne bai jiba,


Jannat kuwa data saba da halin kayanta shiyasa bata damu ba dan tasan serai zai amsa,




Wslm habibtina barkanki da wanan lokacin barka dai habibi,




Ina wuni lfy lau alhamdulillah ya gajiyan aiki Alhamdulillah nima na amsa mai.


Kinsan me habibti? a'a sai ka fada kwanciyarshi"ya kara gyarawa yaci gaba da magana.




Maganar da yayi da barista ne ya kwashe komai ya gaya mata ya kara da cewa wllhy habibti har na masu ranar tazo ni kam me zanyi banda murmuchi.
Tare dafadin allah ko ?
Eh mn habibti ko ke bakiya farinciki...nayi mana ta yaya zance bana farinciki ai ina ga ko kai nafika farinciki dan duk macen data samu miji irinka dole tayi farinciki,




Humm amma baki kaini farinciki ba habibti saboda sai yanzu hankalina ya fara kwanciya saboda kin kusa zama mallakina


Amma har yanzu ina da saukan fargama a cikin zuciyata in kinga na dena farga ba toh ranar an daura mana aurene,


Haba habibi meyasa kake fadin haka tsau nawa zan gaya maka ni takace,


Nasani amma har yanzu ban yadda da hakan ba dan kullun tunani na shine ayya ban zeke dewa ba kuwa ayya na dace dake kuwa wllhy habibti gani nake kamar ban dace da rayuwarki ba saboda ke yer gidan masu kudine ni kuma ba kowa bane,gashi bani da kowa ya karashe magana kaga dakata habibi in so daga yau kayi min alkawai bazaka sake fadin haka ba kuma ka sani in har baka aureni ba toh kaine kace ka fasa aure na ko kuma mutuwa nayi in ba haka ba kuma babu a bunda zai sa na aure ka insha Allahu .


Ajiyar zuciya Adam ya sauke yama resa da wace baki zai godewa jannat sai kwai ya furta kamar haka allah yayi miki albarka jannat gaskiya ke yer aljannace. Ameen na amsa,




A haka dai sukaci gama da magana cikin farinciki da kaunar juna.




Dady barista ya zauna da mami matarsa sunyi magana sun tattauna komai da komai.


Kuma sun saka biki nan da wata biyu kacal in Allah ya yarda,




*Bayan wata daya*




Shirye shirye biki kawai ake baji ba gani a yanzu haka jannat da mami sun tafi india wajan su paa daga nan zasu wuce Dubaï suyi siyayyan kayan lefe har dama kayan daki.




Nidai babu a bunda zance cedai ince allah yasa ai biki lfy Ameen 🤲🥰






Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls
[10/5/2023, 4:21 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 76&77






Bismillah rahmani rahim




________munje Dubaï munyi siyayya bana wasa ba babu a bunda mami bata siyamin ba kaya sunyi kyau sosai dan duk wanda yaga wannn kayan yasan cewa bikin yer gata kuma yer gidan masu kudi zaayi saboda ba karamin kaya aka ciya min ba,




Munyi siyayya mun dawo Nigeria lfy.




Yau kusan satin mu biyu da dawowa daga Dubaï kuma yau ya rege sati daya kacal a daura mana aure da habibina wato Adam,




Lokacin da mukaje Dubaï ne muka dauko wata balarabiya daga can wacca ta kore wajan iya gyaran jiki a yanzu haka itta take min gyaran jiki tun sanda muka dawo.




Na kara kyau da sheki ga wani kamshi na musamman da nakeyi duk dani dama can kekkyawa ce amma a yanzu na kara wani kyau na musamman duk wanda ya ganni zai dauka nima balarabiya ce saboda wani mugun hasken da nayi mai daukar hankali ko mata ma in sun ganni baza suso dauke idanunsu daga gareni ba ballantana na miji ",




Bangaren Ado ma dai hakan ta kasance duk da ba wani abokanai ne dashi sosai ba amma ya gaiyaci abokanan aikinsa sosai maza da mata babba da yaro saboda sabar murnar da yake ciki babu wanda ya bari kowa da kowa ya gaiyata na cikin kanfanin,




Haka dai abokinsa Idi ma ba a barshi a baya ba saboda shine babban abokinsa"shiyasa"da yasamu kudi bai manta dashi ba ya dau kudi mai soka ya bude mai babban shagon sai da kayan a binci kuma Alhamdulillah shima a yanzu haka ya bar bakin Kasuwa tuni,




A yanzu haka ya samu gida ma dai daici shima ya ciya gidan yana da kyau babu yefi palone babba sai dakuna biyu a ciki sai toilet a cikin dakin sai kitchen a sakar gida.




gida yayi kyau masha allah,




*Bayan kwan shida*




Yau ta kasance ranar lahadi kuma a yaune yen uwa da abokan arziki suka shaida daukin auren a Adam abubakar da jannat Muhammad Ali
Jama'a da dama suka samu halar tan daurin auren har dama gwamnar garin kano saboda bazasu daba mantawa da alhaji Muhammad Ali ba a rayuwarsu shi mutunne mai tausayi da kuma son mutane gashi kuma babban dan kasuwa ne tako wana bangare ya shahara sosai shiyasa jama'a da dama sun sanshi ta fannin kasuwanci,shiyasa barista ya gaiyashesu ",




Bayan daurin aure ne aka guda nar da walimar cin a binci a kofar gidan barista.


Can kuwa Adam ne tare da abokansa da suke aiki a kanfani daya Har ma da babban abokinsa Idi.




Duk da ba wani fara'a ne sosai da Adam ba dan bai cika dariya sosai ba dan ba kowa ne yake ganin dariya Adam ba daga barista sai jannat da kuma abokinsa"Idi su kadai suke ganin dariyarsa"su dinma ba wai wangane baki yake yayi dariya kamar kowa ba ce dai murmuchi,




A yanzu ma dai sai sokanar shi Idi yakeyi wai angon jannat kamin wayo kayi aure ka barni shi kuma Adam sewa yake karka damu kazo kullun kaci a bincin amarya dan nasan shine mas'alar ka Adam ya karashe maganar tare dayin murmuchi mai kyau,




Wani harara Idi ya bankawa Adam an gayama ni mayen abinci ne da zakace na dinga zuwa ina cin a bincin amarya salon wataran ku koreni kuce nafiya naci Idi ya karashe magana tare da aure fuska.


Wani yar murmuchi adam ya kuma saki tare da dafa kafadun Idi haba daga taimako kuma idi banason taimakonka in dai da gaske kakeson taimakon nawa toh ka nemomin matar da zan aura nima na muta,




Tab kana nufin ni zan nemoma mata ?




Ni ai ba nemamin akayi ba ni na nemo da kaina dan haka kaima kaje ka nemo naka Adam yayi magana,






Tam shikenan Ado naji zan nemo,




Ahaka dai sukaci gaba da magana sauran abokanan Adam kam mai zanuyi banda murmushi,




Gajiya adam yayi da surutun Idi dan kansa har ya somayi masa ciwo kadan _kadan saboda shi mutun ne da baya iya jure hayaniya,




Cikin gidan suka shiga suka sha hotuna da amarya,






Dan ba karamin kyau tayi ba farin leshin ne a jikinta da gwaldin kadan _kadan ajiki sai waldin din mayafi tayi kyau har ta gaji Adam kam tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login