Showing 30001 words to 33000 words out of 50838 words

Chapter 11 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

a yanzu,shi kadai zai taimaka min wajan nemo granny inda take,ina cikin tunani bansan sanda baccin barawo ya saceni ba,dan mugun yinwa nakeji ga gajiya duk yabi ya hademin,


Har muka iso bansani ba sai kawai ji nayi ana tashina hajiya!hajiya!!ki tashi mun iso,tashi nayi ina misissika ido,kalle kalle nayi naga dai ashe da gaske mun iso.


Jakata na dauka na fito.ina fitowa na hango wata yer karamin restored,karasowa nayi wajan nasa aka kawomin tsokora da miyar agushi.sai lemo mai sanyi ina gamaci na basu kudinsu nayi gaba a buna ina fita cikin restored din na shiga wata unguwa na kusa da restored din. hoton na shiga nunawa mutane ko allah zaisa a gano inda take amma ina duk wanda na nunawa cewa yake bai Santa ba.har magariba tayi shuru na rasa inda zan kwana,wani karamin waje na samu inda akwan mutane.sallah nayi ina nn zaune har isha'a tayi na kuma mikewa nayi sallah ina idar da sallah na jingina da jikin bishiyan da nake.sai can naga dare yayi sosai mutann da nake kusa dashu sun fara mikewa ai nima bansan sanda na mike ba.bakin titi naje na seda mai nape ina hawa nace ya kaini tasha ina zuwa tasha na sauka na bashi kudinsa"na shiga ciki,mai wajan na samu na tambayeshi a kwai mota yace babu yanzu dare yayi sosai sedai na kwana washe gari a kaini inda nakeson zuwa babu musu na amince ya nemamin wajan kwana.


*Washe gari*


Kamar yadda ya fada haka kuwa akayi gari na wayewa mota na gama cika muka dau hayyar kano bamu muka iso ba sai wajan biyar tsaura ina sauka na nemi habun hawa nace ya kaini airport muna zuwa airport wai babu jirgin da zai tashi yanzu sai nn da awa biyu, ya na iya haka na jira har awa biyu sann muka tashi"lokacin karfe 7na dare.




Tunda muka shiga jirgi gabana ke faduwa bansan saboda me ba.
Sai inna lillahi wa inna ilaihirajiwun kawai nake mai maitawa,har muka sauka,sai wajan karfe uku muka iso India.


*A gida kuwa*
Najeeb ne da na najwa sai arilin data xo dazu da yamma tunda taji lbr cewa jannat bata nn sai murta take ta nufi gidansu najeeb din tana zuwa mai zata gani najeeb ne da najwa sai Kissing din junansu "suke a fusace arilin ta karasa palon tana masifah wai lallai sai ta gayawa jannat"abundake faruwa harda yi musu barazana kan cewa ta musu vidéo kuma sai ta nunawa jannat in ta dawo,mikewa najeeb yayi a fusace ki fada mata arilin nace ki fada mata in kin fada mata nima sai na tona miki asiri kema ai kinci amanar kawarki, dariya arilin ta sheke dashi eh na yadda naci a manarta"a matsayina na kawarta 'amma kuma ai gwarani kawace kai kuma fah ?kaifa matarkace da aka daura muku aure kaga in ka zalinceta allah na gani yanzu ka ajiye mace kamar jannat kaje kana neman wancan mummunar ta nuna najwa"ke ki iya bakinki in zakuyi fadarku kuyi ku e ku kar wanda ya kuskura ya sani aciki da kike cewa ni mummunace na yedda mummunace ni amma ai nafiki kaya dama kaya shine mace,amma ke fah da kike da kyau ina kayan suke in banda najeeb da balayin son matama ni basan mai zai samu a nn ta nuna arilin..


Kunga ku dakata kunga dai dukanku kuna wahalar da kanku,bama sona kuke sakani da allah ba,kawai dai sha'awata kuke toh ko wacceku ya zauna indai a kan bunda aka tsabayi ne zam biya mukushi,


A haka dai suka samu suka tsasanta sukaci gaba daga inda suka tsaya ko bacci babu.


Mukulli na dauko cikin jakata na bude gabana sai kara sananta faduwa yake daker dai na samu na bude kofa na shiga fitilun falon duk a kashe suke a hankali na nufi daki zanyiwa jee bazata,


Kafin nakarasa naga fitilun dakin a kunne ga wasu tsurutai na tashi ko ina kanaji kasan na mata biyune ga kuma na mijina cikin fargaba na karasa,mai zan gani mijinane da kuma kawata danafi aminta da itta sai wata wacca bansan ko wacece itta ba,gasu nn kwance a kan gado ko wacce sirara kasa kallonsu nayi dan bazan iya kallon wannn kazamar abun ba.daker najaa kafata na nufi palo ina zuwa na nemi waje na zauna wani ihuuuu na kurma da iya karfina,ai a tsorice suka fito su duka
Basuma tsaya sanya kaya ba,suna karasowa palon wa zasu gani jannat ce zaune rike da kanta,mikewa nayi kamar damutsa na karasa wajanshi ta karda na dauko a cikin jakata dana dawo dashi na mika masa karba yayi kamar wani tsoko ..kaga malam ka rubutamin saki uku ba daya ba ba biyu ba uku nake bukata kayi min kuma a yanzu bazan tsake kwana a gidan mazinaci ba,yanzu beauty ni kike cewa mazinaci ?eh an fada mazinaci ,rubutawa jannat tsaki najeeb yayi ya mika mata ina duba ta kardan naga an rubuta ni najeeb nasaki jannat tsaki....




Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️



By


Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 58&59




Bismillah rahmani rahim




______"ni najeeb na tsaki jannat tsaki uku"wani ajiyar zuciya na tsauke saboda bani da zabin data wuce wannn duk da son da nakewa najeeb amma ya zama dole murabu saboda ba irin mijin daya dace na zauna dashi bane,bai kamata na zabarwa yayana uba mazinaci ba.


Ya kamata na zabo musu uba na gari,


Uwa uba ma bamu dace dashi ba,ba kuma yabon kai bane ,


Ban tsaya hada kayana ba,saboda in nace zan tsaya hada kaya ina kallon wannn mutann irjina zata iya bugawa "naxo na ratsa raina a banza a wofi,saboda in na rasa raina saboda najeeb banyiwa kaina a dalci ba,saboda koda zan mutu bai kamata na mutu ba tare dana kwacewa iyayena hakinsu ba,banida kowa a yanzu sai allah,"


Wannn akwatin dana dawo dashi kadai na dauka sai jakata da mayafina",


Bar musu gidan nayi duk da dare yayi sosai karfe ukun dare .


Ina fita na manta ban karbo mukullin motana ba,na koma ciki kamar dai yanda na barsu haka suke har yanzu basu motsa daga inda suke ba dan jikin kowa yayi sannyi ban bi ta kansu" ba na kalli najeeb nace kaga malam bani mukullin motana zan tafi ,dan bazan kuma barin mazinaci ya haumin mota ba,bai cemin ubfam ba ya juya ya shiga taki bai wani jima ba ya dawo da mukulli a hannunsa' jefamin yayi ban damuba na durkusa na dauka.


Ina fita" na shiga motana na _nayi gidansu paa"ina zuwa kofar gidansu paa kashe motana nayi sai da nayi kuka har nakoshi tukun sann na dau wayata ina duba lokaci karfe 4 hadda yan mintuna,tunanin rayuwata nake tunda nake ban taba jin dadin rayuwa ba.


Yanzu kuma na faraji gashi najeeb yaxo ya tarwasa min.


Fitowa nayi daga cikin mota na zaga bayan boots na bude na dauki kayana nayi kicin gidan kwankwa sawa nashigayi "amma shuru ba'azo an bude ba.


Wayata na tiro daga cikin hand back dina na kira maa"sai data kusa sinkewa ta daka, sorry maa jannat ce"ai maa tanajin muryar jannat"ta tashi zaune.


Hello jannat lfy naga kin kirani a wannn lokacin,yaushe ma kika dawo daga Nigeria?


Kasa bata amsa nayi dan bazan iya amsa mata a yanzu ba.


Pls maa kizo ki budemin ina bakin kofa.


Ai maa najin jannat tace tana bakin kofa ta mike zumbur"lokaci daya ta nemi baccin ta rasa.


Fitowa tayi"taje ta bude kofa tana budewa taga jannat a tsaye ga idon ta tayi jajir dashi kana ganinta zaka gane kuka tayi.


Riko hannunta maa tayi suka shiga ciki.


A palo suka zauna suna hada ido jannat kamar jira take ta fada jikinta ta saki kuka mai ban tausayi"sai datayi mai isarta sannn ta sagaita dashi.


Maa kuma bata hana taba sai data gaji dan kanta ta dena,saboda abunne mai wahala kaga jannat na kuka,


Komai ta kwashe ta fadawa maa".


Maa na gama jin a bunda najeeb yayiwa jannat"itta ma idonta ya canza ya koma ja.


Kwantar wa da jannat hankali tayi,ta kaita dakin
Tace ta kwanta gobe da safe zasuyi magana da paa "dan ko sisinta bazai ciwon kaiba najeeb sai ya biya.


Nidai bance komai ba.fita tayi tana fita na mike nashiga toilet na dauro alwala na fito.dan bazan iya bacci yanzu ba.tunda ankusa kira sallan asubaha.


Sai dana idar da sallan asubaha nayi askar tukun sannn na kwanta "
Sai dana shafi kusan 20 minutes sann bacci ya daukeni.


Bayan awa biyu maa ta shigo dakin ta _tarar ban tashi ba.sai kawai ta fita tabarni,dama kuma paa ne yace tazo ta duba in na tashi,saboda ta fada masa duk a bunda ke faruwa.kuma tayi alkawari kwacemin hakkina a matsayinsa"na barista.


Sai wajan 10 safe na farka toilet na shiga nayi wanka da brosh ina fitowa na dauki daya daga cikin kayan dana zo dasu na saka,ina gama shiryawa na fito palon kasan cewa yau Sunday ne shiyasa su paa suna gida basuje aiki ba.


Gaidasu nayi zan zauna maa tayi saurin cewa naje nayi breakfast tukun.ba musu na mike dan ni kaina ma ina bukatar cin a bincin saboda rabona da abinci tun wanda aka raba a jirgi.


Ina gama breakbeat na mike na dawo palo na zauna.


Magana mukayi dasu paa sosai a kan a bunda najeeb yamin suka kara da cewa insha allah sai sun tsaya sun kwacemin dukiyata"daga hannunsa.saboda ko sisina bazasu bari yayi ciwon kai ba.


Nidai bansan da wana baki zan godewa wayenn mutann ba.saboda in ka cire Dady barista sai su.


Maa ce taje gidan najeeb tare da dreva suka kwashe min kayana.dama ina da mukullin gidan shiyasa da zasuje basu nemeshi ba,suna zuwa kuwa suka tarar baya nn ,har suka gaba kwashe kaya bai dawo ba.
Suna gama kwashewa ta ajiye mai mukullinsa dake hannuna"dan a yanzu bataga anfanin mukullin ba.


Bayan wata biyu da rabuwarmu da najeeb.


Zaune nake ina dudduba wasu takardu,su maa suka dawo sannu dazuwa nayi musu naje na rungume su aryan da nihila,daki na wuce dasu muna zuwa kaya na tirewa nihila dan shi aryan yanzu yayi girma ba laifi,da kansa ma yake wanka yanzu,itta ma dai nihila yanzu ankusa dena mata wanka saboda ta fara girma itta ma kusan shekarunta "bakwai yanzu.


Wanka na sa aryan yayi yana fiyowa nayiwa nihila "suna gama shiryawa muka fito palo abincin dana dafa dazu dana dawo daga makaranta"na zuba musu "suna gama ci muka koma daki.


Bari mu leka gidan najeeb 😊


Bayan fitar jannat ne ya sallami su najwa da arilin
Dan ko bari gari ya waye bai ba,babu yanda basuyi dashi akan cewa ya barsu gari ya waye yace ina ai bazai yu ba.a haka dai suka tattara nasu eh nasu suka bar masa gidansa".


Bayan yan kwanaki zaune yake yana waya.
Kinga hajiya lubabatu jannat dai mun rabu da itta babu a bunda yarage kuma,


Ke kina can kina zaune baki san komai ba,kedai kawai bukatarki a kawo miki ta kardun kanfani.ko an gaya miki aikin da kika sani aiki ba mai wahala ba.


Hajiya lubabatu ce zaune a palo tana waya da najeeb ta inda take shiga batann take fita ba.wai najeeb ya yau dareta "taya zata saka najeeb aiki yace zai nuna mata ba haka ba.


Kaga najeeb kai fa baka san jannat ba sanadiyata
Kasan ta "saboda tsabar nemon mata da kakeyi kaki ka maida hankali ka karbo mana ragowar takardun.


Yanzu dai ka tabbar da kaxo Nigeria mun tattauna a kan maganan nn,humm hajiya kennn ke kina zauna a can kin hadani da aiki mai wahala, kusan shekara uku ina fama da abu daya sannn kice in baki dukiya "toh kisani ni najeeb bazan sha wahala a banza ba.dukiya dai bazan bayar ba,saboda in na kawo babu a bunda zaki bani ko rabin dukiyar ma nasan bazan samu ba.tun darko ma a bunda yasa na amince saboda na dauka aikine mai tsauki ashe dai ba haka bane.


Kinga kuwa kawo dukiya a yanzu bashi da anfani kuma dama ni ta mallakawa.


Yana gama fadar haka ya kashe waya kitt wani dariya yayi yace jimin mata sai kace dan kauye ni najeeb da hankalina na bari a cuceni humm wllhy bazai yuba.daga yauma bazaki sake samuna a waya ba.dan nn da yan kwanaki kadan ma zan bar kasar ma gabaki daya kowa ma ya wuta.


*Bayan wata biyu*


Alhamdulillah yanzu kusan kwana na biyar da gama makaranta .a yanzu nima nazama barista kamar mommy na"burina ya cika.yanzu kuma bani da burin data wuce in gano wayenda kusa kashemin iyayena
In samu in be musu hakkinsu"


Mun kammata shirinmu tsap dani da paa nan da kwana biyu zamu wuce Nigeria.


Duk da shi ba dan kasar bane amma a shirye yake da ya tsaya sharya akan a bunda najeeb ya min.yana nn yana hadawa najeeb tarkon da zai iya kamashi a tsaukake ba tare da an sha wahala ba. Dan tun lokacin da jannat ta bar gidan ya sa police sun zagaya gidan,dan gudun kar yace zai bar kasar.


Dan in har ya bar gidan zayi wuya kafin a kamashi.


Shikuwa najeeb bai ma san da yan sandar ba.


Zaune yake ya shirya kayansa' tsap.domin barin kasar gobe.


Nigeria itta ko hajiya lubabatu ta kira najeeb number din sa bata shiga
Tsaki ko tayi shi har ta gaji,jefar da wayan tayi tana wuci kamar damutsa"ni _ni hajiya lubabatu najeeb zai yaudara.in saka ka aiki ka yauda reni,kai ina hakan bazai taba yuwa ba,zan nuna ma ba'a taba lubabatu a zauna lfy,in baka tsani ba zaka tsani,


*Wacece hajiya lubabatu*


Hajiya lubabatu yace ga tsowon matar babansu Ibrahim da Muhammad (baban jannat kenn)tun bayan rabuwarta da ma haifinsu Ibrahim ta auri alhaji alhasam)alhaji alhasam babban dan kasuwane .badan komai yasa maman hajiya lubabatu auran sa' ba sai dan kudin da yake dashi.
Bayan wasu yan shekaru kadan allah ya bata hajiya lubabatu"duk da ba haka maman hajiya lubabatu ta so ba amma ba yanda ta iya a haka ta rungumi yerta tana dorata a layin mara dai_ daiciya har yarinyar ta taso da iya makirci kala ²dan zan iya cewa ma tafi mahaifiyarta iya hatsabibanci"dan itta tana kashe mutun tana dariya.


Da yer tayi girma in har zata fita waje sai ki ganta da katuwar hijabi,in ka ganta cikin hijabi zaka rance mutuniyar kirkice a zuciya kuma ina ..ba haka abin yake ba.


Kasan cewa ma haifinta mutumin kirkine shiyasa kowa yake dauka itta ma yer haka take.


Tun lokacin da barista yaganta yaji ta kwanta masa a rai,shiyasa ya fara bincike a kanta"kuma Alhamdulillah ya samu shaida mai kyau a kanta.
Daya tari hajiya lubabatu da zancan tace ya dan bata lokaci haka kuwa akayi itta da ma haifiyarta suna gano barista abokin Muhammad sosai suka amince,ba'a wani dau lokaci sosai ba aka daura auransu"ta tare a gidanta mai kyau da barista ya gina mata.da aka tashi daura musu aure sosai mahaifiyarta ta jaddada mata akan cewa kar ta kuskura ta bari barista ya gano wa cece itta dama halinta gaba daya.bata taba nuna waba suna zaune lfy duk yan gidansu barista da ma makota yabonta suke.har suka haifi walida da minal.zamansu kwanin ban sha'awa,


Tayi ²ta dora walida a wannn haiyar amma walida taki.saboda itta walida halin mahaifinta tayo.


Itta ko minal halin ma haifiyarta,saboda tana son a bin duniya.


Ibrahim bai san matar barista yer tsohuwar matar babansu ba.wacca ta reneshi kennn.


*Mumbai India*


Mungama shirya kayanmu tsap.gobe in allah ya kimu zamu wuce Nigeria.


Da yamma muna zaune a palo sai aka kira paa a waya yana dubawa yaga sunn daya daga cikin yan sandan nn ne yake kiran shi dagawar shine yake da wuya yaji dan sandan na cewa Hello Sir wllhy mutuminn tafiya zaiyi dan naganshi da akwatuna kuma da alama ba dawowa zaiyi ba paa bai saya yaji sauran maganar sa ba yace kaga rakvir ku gaggauta kamashi nima" yanzu zan taho okay sir ya fada,paa na kashe waya ya kalli jannat yace..
Tashi keje ki dau akwatinki kixo mu tafi dan yanzu nn rakvir yake gaya min yaga najeeb ya hada kaya zai bar kasar kuma da alama ba dawowa nn garin zaiyi ba saboda ya kwashe komai nasa,


Ai ina jin hakan nayi hayyar dakin dan banga ta zama ba.ina zuwa daki banfi 5 minute ba na fito da akwati na nayi hayyar waje naje nasaka a bayan mota.


Paa ma yana fitowa ya saka nashi"a kwatin sallama yayi da matarsa da yayansa.nima rungume su aryan nayi ina hawaye dan nasan in munje zamu dan dade kafin mu dawo kilama ni ba lallai ne na dawo ba,saboda ana gama zaman kotu zanje na nemo kakata a duk inda take"sakinsu nayi na rungume maa ma ina hawaye murmuchi tayi min dan itta kanta tanason yin kukan amma bata so na gani saboda tasan in na ga hawayenta kara nawa zanyi shiyasa ta daure ta hana kanta yin kuka.


Mota muka shiga dani da paa drive ya ja'a muka bar gidan.


Gidan najeeb muka nufa muna zuwa mukaga ankama shi an sashi a mota,


Shiko najeeb ya fito kennn zai shiga mota ya wuce airport sai kawai yaga yan sanda a gabanshi suna samai anko a hannu.magana yakeso yayi amma bai samu fuska ba.


Shi ya dauka ma hajiya lubabatu ce ta gano inda yake shiyasa ta tura a kamoshi sai da yaga paa da jannat a mota sannn ya gano sune.


Airport muka nufa muna zuwa paa ya sallami yan sandan ya bar rakvir kadai,dashi zamu tafi saboda ya tayamu rike najeeb.


Bamu jima a airport ba jirginmu ya daga zuwa nigeria.lumshe indona nayi ina rokon allah ya sa muyi nasara.dafani paa yayi na bude ido.karki damu my daughter muna tare dake dan kallonsa nayi nace paa naji kace kuna tare dani kai dawa ?
Murmuchi paa yayi yace nida barista mn ina jin paa ya ambaci sunn barista na ware ido nace barista kuma paa yes barista yanann da ranshi bai mutu ba....




Sakeena Ismail Cameroon ✍️






Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA🧝‍♀️




By


Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 60&61




Bismillah rahmani rahim




_____"barista yana nn da ranshi" bai mutu ba.zare manyan idanuna nayi ina kallon paa kai ya geda min yana murmuchi,kallon paa nayi nace amma paa dama kasan barista! bai mutu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login