Showing 27001 words to 30000 words out of 50838 words
Chapter 10 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt
sanyaye shi yama rasa ta inda zai godemin saboda tsabar kaunar da nakemai har zan iya bashi dukiyata.kodai ma farki yakene.mota muka shiga saidana ajiyeshi a gidan sann na wuce makaranta.
Pls kuya hakuri da wann kainane yakemin ciwo.
Sakeena ismail Cameroon ✍️
Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝♀️ MIJIN ATTAJIRA 🧝♀️
By
Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)
Page 52&53
Bismillahi rahmani rahim
*Washe gari*
______kasan cewa yau Sunday shiyasa muna tashi tare muka shiga kitchen mukayi breakfast
Muna gama karyawa TV muka kunna muka zauna muna kallo sai mukaji ana buga kofah har zan tashi naje nabude sai yace min inyi zamana bari yaje ya duba ,yana zuwa ya bude wa zai gani arilin ce,itta ko arilin tana ganin shine ta zaga ta bayanshi ta shiga cikin falon ta barshi a tsaye. Bude baki najeeb yayi yana kallon ikon allah .a zuciyarsa kuwa cewa yake ko maiya kawo ta gidana ? Babu amsa.
Sai kawai ya rufo kofa ya koma cikin falo,yana zuwa yaga jannat sai murna ganin arilin take,
Shiko yana ganin haka yace bari ya shiga ciki
Dakinsa' ya nufa yana zuwa ya nemi gefan gadon ya zauna yayi ta gumi.humm beauty baki san waye kawarki ba da kinsan wace itta da baki saki jiki da itta har haka ba.kai da kinsan lalata mijinki takeyi' na tabbata ko minti biyu bazaki bari ta kara a gidanki ba,
Niko nace Najeeb gyara kalamanka tana zuwa kuna lalata juna ko tana lalataka?allah dai ya shiryi masu halin irin naku ameen.
Bayan tafiyar jee takine na mike kitchen na shiga na dauko lemo da glass cups guda biyu na dawo falon,dan a nn in kayi bako ko baki tare zaku sha lemo ko ruwa.shiyasa nima na dauko cup guda biyu.
Zama nayi kusa da itta zuba mata juice din nayi na mika mata nima na zuba nawa muka fara sha.kurba daya nayi na ajiye cup din nace mata bari na dawo.toh ta amsa min na mike na shiga takin jee ina shiga na tarar dashi zaune ya zuba takumi kara tsowa nayi har na zauna kusa dasi bai sani ba har saidana rikemai hannu
Ya dago ya zubamin ido.
Ga idon yayi jajur saboda shaawarsa daya motsa "
Niko nace gaskiya Najeeb kai jarababbene.
Da yake nasan halin kayana tsarai in har naga idonsa ya canza kolo to nasan a bunda yake bukata, amma wann karan yi nayi kamar ban san a bunda yakeso ba saboda in nace zamuyi wani a bu ga arilin can a falo bai kamata mu barta itta kadai mu dawo daki mu zauna ba.kallonsa nayi ina tambayarsa me yake damunsa "humm beauty kennn yanzu so kike kice min bakisan a bundake damun mijinki ba?kema dai kinsan in har kince baki san a bundake damuna ba toh kinyi karya wllhy.
Kallonsa nayi ina dariya kasa² oh dariya ma kikeyi ko tam shikenn ya mike zai fita nayi tsaurin rikemai hannu ina bashi hakuri.
Kaxo muje ku gaisa da itta kaga daga nn sai mu sallameta in ta tafi sai mu dawo na baka hankinka ko.murmushi yayi yace yauwa koke fah my beauty hannusa na kama muka fita falo.
Itta ko arilin dama a bunda take jira kenn.sai kuma gashi ta samu a tsaukake.dama tana so na tashi ta zubamin maganin baccin dataxo dashi ta samu Najeeb ya biya mata bukatarta.sabosa tayi kiwarshi sosai.yanzu kusan wata daya da yan kwanaki bata sashi a ido ba.shiyasa tazo yau.dan bazata bari ta chuchi kanta a banza a wofi ba.
Har tagama zuba maganin a cikin lemo la girgiza tana jiran fitowar jannat amma taji shuru
Bata fito ba,kilama suna can suna shan soyayyar su sun manta da itta.
Sai kawai taji wani mugun bakin ciki har bata ma san sanda ta kuma fito da maganin baccin ta kara a kan wanda ta zuba dazu ba.
Tana cikin girgiza lemon taji takun takalman su suna fitowa tsauri tayi ta goge gefe gefen cup din
Ta gyara zamanta,wayarta taciro daga jaka ta fara dannawa ,har suka karaso.
Dago fuskarta tayi tana kirkiro murmushin karya.
Nima murmushin nayi mata muka nemi waje muka zauna a kujera daya dani da jee dina
Sorry arilin mun barki ke kadai ko nayi magana.ba komai ai,ku da kuke sabbin ma haurata kinga dole na daga muku kafa ko.bance komai ba sai murmushi kawai dana danyi.dan tsatar kallon jee nayi naga ya kulu iya kuluwa dayaga nama manta dashi sai hira nake da arilin ,ina juyawa muka hada ido dashi naga sai wani cin magani yake .lumshemai indo nayi alamar bada hakuri.dan murmushi yamin ya saki hannuna ya mike ya koma dakinsa".
Bayan tafiyar Najeeb dakine arilin ta dau wann lemon ta mikawa jannat ba musu jannat tasa hannu ta karba suka fara sha lokaci zuwa lokaci arilin takan daga ido ta kalli jannat"taga sai sha take.can dai taga jannat ta ajiye lemo tana dan yacine fuska . jannat lfy baki shanye lemonki ba ?wllhy arilin ji nayi test din lemon ya canza kamar bashi nake sha dazu ba.sorry beb arilin ta fada tana wani irin shumin murmushi.duk da dai jannat din ba wani sha tayi sosai ba.amma dai da alama maganin ya fara aiki dan har ta fara geggedi a falo,kallon arilin nayi nace bari naje na dan kwanta toh tace min tana mikewa tace bari ta taimaka minki na kaiki daki bam mutsa ba dan nima naga alamar ina bukatar taimakon.mikewa nayi arilin ta kamani ta kaini har daki ina zuwa na hau gado nan da nan bacci ya daukeni tana zaune har sai data tabbatar baccin nawa yayi nisa sann ta tashi tana murmushi ta fita,
Bata tsaya ko ina ba sai dakin najeeb tana zuwa ta tarar tashi zaune rike da kansa.ga kuma haushin jannat da yakeji
Na kin sallamar arilin da batayi ba.
Yana cikin tunani yaji takun ta kalmi shi a tunaninsa jannat ce ta xo ai yana daga ido yaga arilince tsaye akansa.
Mikewa yayi yana nunata da yenyatsa kece dama meya kawoki dakina arilin? koso kike beauty ta shigo ta gammu tare ne dan allah kixo ki tafi gidanku karki jaamin mas'ala duk ya rikice.arilin kuwa rungume hannu tayi tana ganin ikon allah bata katseshi ba har saida yagama tukun ta tsauke ajiyar zujiya ta fara magana..ka kwantar da hankalinka baby beauty take kowa tana can na zuba mata maganin bacci a lemo tana can na kaita daki tana bacci,wani haushi najeeb yaji bai san sanda yafita ya nufo dakin jannat ba yana zuwa yaganta kwance ya kira sunanta ta bude ido ta kuma kuma rufewa taci gaba da baccinta "yana ganin haka ya gyara mata kwanciyar tata ya juya ya fita ya rufo mata kofa,
Dakinsa ya koma yana zuwa ya samu arilin kwance a kan gado babu komai a cikinta.shi kuwa dama sha'awarsa ya motsa tun dazu yana ganinta haka sai kawai ya biye mata suka aikata abunda suka tsaba aikatawa.yana samun nitsuwa ya korota ta tafi.
Bata damu da korar da najeeb yayi mata ba tun da dai ta samu a bunda takeso.
Bayan tafiyar arilin toilet Najeeb ya shiga yayi wanka shap.shap ya fita ya nufi dakin jannat yana zuwa yaganta kwance har yanzu bata tashi ba kwanciya yayi gefenta ya rungumota saboda wai in ta tashi ta gansu tare bazata zargin wani abu ba.daga kwanciya dai shima baccin yayi awan gaba da shi.
Bayan yan mintuna.
Bude idona da sukayi min nauyi nayi na saukesu akan jee yana kwance rungume dani.shuru nayi ina tunanin a bunda ya faru kafin nayi bacci amma ban tuna komai ba,a bunda na tuna kawai arilin taxo muna shan lemo naji ina jin bacci bazan ina tuna komai ba bayan wann.
Toh amma yaushe nayi bacci ,kuma ma ba a falo nake ba waye kawoni daki kodai jee ne ya kawoni.humm inaga shine amma ina arilin toh?
Zare jikina nayi a hankali na nufi falo ina zuwa banga arilin ba.
Daki nakoma naje nayi alwala nayi sallah ina idar da sallah na mike na shiga kitchen na dora mana a binci.ina kitchen yaxo ya sameni.
*Kano Nigeria*
Gidan oncule Ibrahim.
Ameera ce kwance ba lfy mamanta tayi ²ta itta ta tashi suje a sibiti amma taki.tace itta lfyrta qalau babu inda zata,dama kuma can ta rena iyayen nata.saboda duk sanda taso gaya musu magana take babu a bunda ya dameta wai itta ta dubi wayenn iyanenta ne!babu.
Tashi tayi ta shiga toilet wanka tayi ta fito,ta shirya tana gama shiryawa ko sallama batayiwa mamanta ba ta kama hayya tayi tafiyarta "hajiya maryam na fitowa ta leka daki bataga ameera ba. guntun hawayan data zubo mata ta sharo tana rokon allah ya shirya mata ameera.dan itta yanzu dawowarsu abuja batayi mata rana ba.duk da dai a can kanon ma tanayi amma bai kai n'a nan ba.
Ameera kuwa tana fita bata tsaya ko ina ba sai a sibiti.
Tana zuwa a sibiti ,ta gaisa da ma aikatan data saba dasu saboda yawan zuwan da takeyi a kai ²ana zubar mata da ciki
Suna gama gaitsawa ta wuce cikin office din doctor Yusuf.tana zuwa ta tura kofar kai tsaye ta shiga ta maida kofar ta rufe.kalle ²ta shigayi amma bataganshi ba.waje ta samu ta zauna tana jiranshi.dan ta dauka ko fita yayine.can taji sambatu na tashi daga cikin dakin dake office din.da kuma tsautin mace.runce ido tayi ta mike a hankali ta nufi dakin tana lekawa tagansu sunanan suna aikata zinansu komawa tayi da baya ²har taje bakin kofah har zata fita sai ta tuna infa bata tsaya ancire mata wannm cikin ba toh kilama abbanta inyaji ya koreta.komawa tayi ta zauna tana jiransu "sai da sukayi kusan awa daya sann suka fito doctor ne ya fara fitowa,yana fita ya ga ameera zaune suna hada ido yayi mata murmushi,a zuciyarsa kuwa cewa yake yau yana da tsa'a ashe mata har biyu.kara tsowa yayi ya zauna,ameera waye bude miki kofa ?harara ameera ta banga masa .
Ai dole kace waye bude min kofah sai yanzu kasan baka rufo kofaba kenn.tayi magana shiko doctor sai yanzu ya tuna ashe bai rufe kofa da mukulli ba.
Yadade da tsanin Ameera na sonshi saboda yanda take nuna kishi a kanshi.
Fitowa budurwar tayi ta tsaya tana karewa ameera kallo,kallonta doctor yayi kije zan nemeki anjima kai kawai budurwar ta geda tayi hayyar kofa ta fita.fitar tane yake da wiya doctor Yusuf ya mike yaje ya kullo kofa saboda kar ya manta irin na dazu.
Yana gama kullewa ya dawo cikin office nuni yayiwa ameera da tatashi su shiga ciki ba musu ta mike tabi bayanshi..
Sakeena ismail Cameroon✍️
Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝♀️
By
Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)
Page 56&57
Bismillahi rahmani rahim
_____yau bamu tashi da wuri ba sai wajan 5 muka tashi ina ta tsauri ²na dawo gida na bar jee da yinwa danma ya iya girki.nasan bazai bar cikinsa da yinwa har izuwa wannn lokacin ba .
Ina dawowa tun daga bakin kofa wani kamshi mai dadi ya bugi hancina na lumshe ido na karasa.
Kasan cewa ina da mukulli a jakata shiyasa ban kwankwasa ba na dau mukullin na bude.
Ina shiga nayi sallama ba kowa a palon kallon palon nayi naga ko ina kal Anshare angoge shi tas ga kamshin turaren wuta na tashi ko ina ya hadu da sanyin AC ya bada wani irin kamshi mai dadi.murmushi nayi na karaso cikin palon ba kowa sai kawai na wuce dakinshi ina zuwa naga baya ciki dakina na nufa ina shiga na ajiye jakata da maya fina,na nufi kitchen kafin na karasa naji kamshin girki na tashi,tunda naji kamshin girki na fahimci yana kitchen din na dinga tafiya kamar barauniya saboda karyaji takun takalmina har na karasa cikin kitchen din ina shiga naje na rungumeshi ta baya ai a tsoroce jee ya juya yana ganin nice ya sauke ajiyar zuciya.ya rungumeni nima rungumarsa nayi da kyau.saida muka dauki yan mintuna sannn ya sakeni.kallonsa" nayi na kuma kalli girkin da yakeyi.jee kace girki kake mana,yess beauty girki nake mana kedai kije kiyi wanka kafin nan na karasa humm jee kenn amma me kake defa mana haka?kedai kije kiyi wanka,dan na tabbata in kin dandana a bincin kunnenki sai ya kusa tirewa,a lallaikam naga alama dan tun shigowata gidan nn naji wani kamshi na tashi shiyasa ni duk na kosa naci wannn girkin wallhy ,allah ko,eh mn toh yanzu dai kije kiyi wankan tukun .. tam shikenan bari naje nayi wanka .
Ina shiga ciki toilet na fada ,wanka nayi na fito na shirya cikin kananun kaya mara nauyi.ina gamawa na fito naga kulolin abinci akan danning da alama ya gama ,tashi nayi naje na bubbude shinkafa ce da miyar vegetable yayi ina duba a bincin ya fito daga dakinsa "da dukkan alamu dai wanka yaje yayi,kallona yayi yana murmushi, beauty kinga a binci ko,toh zauna na zuba miki ,kujera ya jamin na zauna a binci ya zubamin spoon na dauka na dandana ai bansan sanda na topar da abincin a hannuna ba,jee ko tsauri yayi yana tambayata "lfy beauty ko dai a bincin nawa baiyi dadi ba,kai na geda masa ina kara yasine fuska spoon ya dauka ya dan dandana a bincin amma kuma ai beauty banga laifin wannn a bincin ba.dariya na kwashe dashi nace kai jee kaima dai kasan bazaka dafa abu yakiyin dadi ba,ka kwantar da hankalinka a bincinka yayi mugun dadi,barima kaga na kara ina, wllhy baki isa ba.hannu yasa Zai karbe spoon din nayi tsaurin mikewa bayana yabi muka dinga zagaye palon dashi..
Bayan yan kwanaki kamar yadda mukayi shawara dani da mijina
A kan cewa zaije ya siyar da dayan kanfanin inyaso yaxo ya bude wani a India saboda munfi zama ann bazaiyu yaje yayi aiki a Nigeria ya banni ni daya ann ba.bayan dawowarsa "da kwana biyu ya bude kanfanin seda jiragen kasa kuma alhamdulillah allah ya sawa abun albarka yana tafiya yanda ake bukata,kasuwanci sai kara habbaka take.
*Bayan shekara daya da wata shida*
Bayan dawowata daga makaranta kennn zaune nake a palo ina duba wasu ta kardu dan mun kusa gama makaranta nan da wata uku zuwa hudu in allah ya yarda zam zama cikekkiyar lawya " ida nuna na daga ina kallon inda bangaren dakin jee yake.
Dan bashine kallon na farko danayiwa dakin ba.
Dan zaman da nayi a palo na kalli gakin yafi tsau shidda.amma har yanzu shuru bai fito ba,ni na rasa gane kan mijina a yan kwanakinn,saboda a duk sanda aka kirashi a waya sai ya mike dan ya dena waya a gabana
Sabanin da kuma duk wayan da zaa mai ina zaune amma yanzu kam sam babu hakan.
A bunda yafi komai daure min kai kuma akwai wani lokaci da zan shiga dakinsa"naji yana waya bai san ina wajan ba sai kawai jinayi yana cewa haba haba ba nace kibani lokaci ba indai dukiyane ai yana hannuna,dan ma tana da wayo sosai.zaici gaba dayin magana yaganni.sai kwai yacewa wanda suke wayan dashi zai sake kira anjima.
Yanzuma dai da naga shuru mikewa nayi na nufi dakin ina jin maganar mijina da...yayi mugun dagamin hankali bansan sanda na koma palo ba,gaskiya dole dolena nage Nigeria dan ina bukatar yin wani abu akan wannn al'amarin amma bazan nuna mai komai ba.
Bayan yan mintuna kadan ya fito murmushi yamin nima na mayar masa.zama yayi yana kallona beauty ya naganki haka mai yake damunki ?mai kagani ni gaskiya babu a bundake damuna tunanin gidane kawai ya motsa ina son naje Nigeria na nemo granny dina duk da dai na shafe shekarun masu yawa ban sata a idona ba amma ina bukatar na nemota "toh ai beauty banga ta zama ba yazama dole muje tare tunda yanzu mun zama daya,karka damu jee bazan wuce kwana biyu ba.ina gama a bunda nake zan dawo.kai duk a bunda ake ciki zan kira na fada maka.tam shikenn beauty tunda kin takura lallai sai kinje ke daya amma dan allah in kinje ki kularmin da kanki kina sauka kiyimin waya ki fadamin,kar ka damu insha allah zan kiraka.
*Washe gari*
Da wuri na tashi ina gama shiryawa muka nufi airport 'kuma dama tun da daddare nakirasu" paa na fada musu,bamu jima da zuwa ba jirginmu ya daga zuwa kasar mu ta Nigeria.
Najeeb na ganin dagawar jirginsu yayi wani murmushi ya shiga mota yayi gida yana zuwa ya kira najwa a waya dan duk cikin yammatan da yake nema babu wanda yakejin dadin kasancewa tare da itta kamar najwa.
Kuma ya rigada ya gaya mata madam zatayi tafiya zataxo ta tayashi zama, in taxo kwana zata mai.shiysa data Tashi zuwa ta taho da wasu kaya.
Tana zuwa ta shiga kitchen tayi musu a binci.suna gama ci suka shiga daki suka dingayin a binda suka tsabayi in sun hadu.
*Kano Nigeria*
Ina sauka dama a wata karamin trolley na saka kayana kala uku sai karamin jakata dana rataya.titi na nufa ina zuwa na tari mai taxxi na fadamai gadon kaya zani
Na kwatanta mai sunan layin ai kuwa har cikin layin ya kaini ina sauka na bashi kudinsa zai bani canji nace ya barshi.
Ina karasowa bakin gete dinsu oncule Ibrahim.na tsaya ina yiwa mai gadi magana na fada mata wanda naxo nema yace ai nan Babu mai sunnn ann gidan sai karamin yaron gidanne sunansa Ibrahim Amma ba mai gidan ba,na nemi dana gana da masu gidan zaiyi mum gardama na tiro 5k na bashi ai yana ganin haka ya barni na shiga ina shiga cikin gidan na hadu da matar gidan muka gaisa muna gama gaisawa na fada mata a bundake tafe dani itta ma dai kamar yanda mukayi da mai gadi toh haka mukayi da itta ma.
Godiya nayi mata na fito gidan jiki Babu kwari na tsaya a bakin titi sai danayi kuka mai isata sann na tseda mai keke nape nace ya kaini Tashan da ake hawa motar adamawa.muna zuwa tasha
Na hau motar adamawa.
Tunda muka shiga nake ta tunani yanzu in na sauka waca unguwa zanje na nemo granny
Nidai nasan a adamawa take bayan wannn bansan komai ba,kallon hoton dake hannuna nayi hoton mommytace da Granny ranar sunana sukayi hoton kana ganinsu zaka fahimci ya da uwane saboda tsabar kama da sukeyi.
Da wannn hoton kawai na dogara