Showing 33001 words to 36000 words out of 50838 words

Chapter 12 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

shine baka taba gayamin ba.humm daughter kennn nima sai bayan auranki na samu lbrn ,badan komai muka boye hakan ba sai dan makiya da sukeson suga bayanshi",amma paa ni ai bai kamata ku boyemin ba.jannat sarkin kigima,ba gashi yanzu kin sani ba ki bari in munje kotu zaki fahimci komai dan yanzu in na gaya miki ba ganewa zakiyi ba.


*Bayan mun saunka*


Muna sauka wani mutun da bansan ko waye shiba yazo ya dauke mu,da alama dai sun san juna sosai dashi da paa amma ni na kasa gane wanene shi".


Hôtel ya kaimu _muna zuwa paa ya kama min daki ni kadai sai najeeb da wannn dan sandan.sai nasa dakin daya kama shi kadai.yana gama kama mana ya kalleni yace duk a bunda nakeda bukata ga waya na kira na fada musu
zasu kawo min kai nageda na shiga dakin da aka kama min su kuma suka wuce nasu dakin,


Ina shiga dakin jakata na ajiye na shiga wanka ina fitowa sallar isha'i nayi ina idar da sallah na hau gado na kwanta nayi shuru har zanyi bacci sai kuma na mike na dau wasu ta kardu ina dubawa.sai dana kammala duba takardun sann na kwanta bacci,


*Washe gari*


Bayan nayi wanka aka kawomin breakfast na karya ina gama karyawa naji ana bugamin kofa tashi nayi naje na bude paa ne ya shigo da wannn mtumin jiya da naga yaxo a airport kara sowa sukayi na gaishesu muka nufi cikin daki muna shiga suka zauna a cikin daya daga cikin kujerun dake dakin.


"Kallona paa yayi ya fara magana jannat insha allah gobe in allah ya kaimu za'a fara shari'ann ki tuna dake ma baristace a yanzu karkiji tsoron kowa ki fadi duk a bunda kika sani saboda mu samu hayyar da zamu kwacewa iyayenki hankinsu dama ke kanki.
Ajiyar zuciya na sauke nace insha allah zanyi iya baki kokarina"kai paa ya geda ya kalli wannn baristan da suka shigo tare yana murmuchi yace mutafi ko kai baristan ya geda suka mike sallama sukayi da jannat akan cewa zaije nn ya dawo.kai ta keda musu",suka sa'a kai suka fice.


Najeeb kuwa tunda sukaxo Nigeria yana ganin ta kansa wajan wann dan sandan.da sukaxo dakin da aka kama musu ya kwanceshi yace in yana da bukadar wani abu yaje yayi ba musu najeeb ya shiga ya watsa ruwa.da alwala'yana fitowa ya shimfida sallaya da yagani a dakin yayi sallah yana idar da sallah a binci aka kawo masa yaci ya koshi"rakvir (dan sanda)ya umarceshi dayaje ya kwata ba musu saboda yaga alama in yayiwa dan sandann gardama kadan daga cikin aikinsa ma yace zai harbeshi dan baiga annuri akan fuskarsa ba ko kadan.gado ya hau ya kwanta yayi shuru yana tunani in ma hayfiyarsa yaji wannn maganar ya zataji sai kwai yaji hawaye na saukar masa saboda duk rashin ji da yakeyi yana kaunar ma haifiyarsa"sosai shi bai ma san meyasa ya amince da maganar hajiya lubabatu ba,dan shi tunda yake bai taba damfaran wani ba a rayuwarshi yana dai neman mata amma bayan wannn bashi da wani abu da yake aika tawa.


*Gidan oncle Ibrahim*


Zaune yake a palonsa "abun duniya duk yayi sheshi ga ameera can kwance ba lfy da sukaje a sibiti ma ance tana dauke da ( cutar mai karye garkuwar jiki)duk ta rame tayi baki,ga mahaifiyarta kullun kuka take tace alhakkin jannat ce" take bibiyarsu"dan yanzu kam har da itta wajan nemo inda jannat din take saboda ta nemi gafara a wajanta amma shuru har yau basu ganta ba,ga hajiya kaltum ma taxo tana neman jikarta tace wannn karan bazata hakura ba sai sun nema musu jikarta dan itta kadai ta rage mata ayanzu,


Wayar oncle Ibrahim ne ya shiga kara yana dubawa yaga bakon number ne kamar bazai dauka ba sai wani abu kuma yace ka dauka mana kaji koma waye' dagawa yayi _ya kara a kunne yaji ana cewa da Ibrahim nake magana ne ?eh nine wake magana,,,kana magana da barista Usman gobe in allah ya kaimu ana nemonka a kotu _kotu kuma? Ibrahim ya tambaya yes kotu dai daka sani a nn ake nemonka amma mai nayi barista da za'a nemeni a kotu,inkaxo kaji a bunda kayi in baka kawo kanka ba kuma mu da kanmu zamu xo mu tafi dakai.insha allah zanxo,toh yadai fi maka ,kuma ka tabbar goman safe ya sameka a kotu,toh amma barista wana kotu ?in kaxo kano ka kirani sai na gaya ma sunn kotun tam shikenan
Ya kashe waya,ya juya yana kallon hajiya kaltum dake zaune taji duk maganganun da Ibrahim yayi da barista, kallon ta yayi _yace wai wani baristane ya kirani yanzu yace ana nemana a kotun kano gobe da karfe 10 na safe ai kaka na jin haka tace yauwa wllhy tare zamu daga nn nima na makaka a kotun na gaya musu ka batarmin da jika kusan shekaru hudu ban sata a idona ba
Haba hajiya wann waca irin magana ce "a to karya nayi nace karya nayi ?ah.ah bance karya kikayi ba amma ai inayin iya bakin kokarina wajan ganin mun ganta.amma har yanzu shuru nasan nayi laifi,da na tsaya na kula da itta sosai da duk hakan bata faru ba,ai a bunda kayi ibrahima gwarama ace ka _kashe mutun,nidai dan allah ki bar wannn maganar indai jannat ce zan nemo miki itta",


*Washe gari*


Kamar yanda aka tsara zamuje kotu haka ko akayi,


Ibrahim kuwa yana zuwa kano ya kira barista Usman ya gaya mai sunan kotun kafin 10kowa ya hallara a wajan,


Karfe 10nayi alkali ya shigo wajan,kowa na ganin alkhali yayi shuru suna jira a fara sharya,
Alkhali la buga guduma ya nemi da lawyan mai kawo kara da kuma tawya wanda aka kai kara su tashi su gabatar da kansu"mikewa barista Usman yayi yace sunana barista Usman nine lawyan mai kara tare da abokin aikina ya nuna paa mikewa paa yayi shima ya gabatar da kansa"sann lawyan najeeb shima ya mike ya gabatar da kanshi " dama kuma oready najeeb yana gaban wajan inda ake seda mai laifi alkaline ya fara magana kamar haka...shin lawyan mai kawo kara yana da tambaya ?eh ya mai girma mai shariya toh bismillah, barista Usman ne ya fara magana kai dan saurayi ya sunan ka?
Sunana najeeb Ahmad kai barista ya geda yaci gaba da magana cin najeeb Ahmad da gaskene ka aikata a bunda ake zarginka na kwace kadarorin matar ka?shiru najeeb yayi kamar bazaiyi magana ba saboda tambayar taxo mai a bazata"yana tuna halin da ma haifiyarsa zata shiga in tagano a bunda ya aikata sai kawai ya fara magana eh na aikata
Toh meyasa ka zabi da ka yaudari matarka ta wannn hayyar ko tausayinta bakaji na ganin cewa ittadin marainiyace"?eh ina jin tausayinta"kana jin tausayinta"kuma shine ka kwace mata dukiya lawyan najeeb ne ya mike op section ya mai girma mai shariya ba abunda ya kawo mu bane ann barista bai kamata ya dinga yiwa najeeb irin wayann tambayoyin ba,dan wancan tambayoyin na cikin ginane, barista Usman ka kiyaye nagode mai shariya yauwa najeeb muna jinka.eh ba a son raina bane sani akayi dan har auran tama sani akayi shima,yanzu kana nufin auran da kukayi da jannat ba soyayya allah da annabi kake mata ba?eh da farko hakane amma da na rayu tare da itta har na sahun shekaru uku naji duk duniya Babu wanda nakeso sama da itta saboda tana da dadin zama,yanzu ma ba'a san raina na saketa ba,duk da farko dazan aureta ba zaban auran na din din din zanyi da itta ba,da dazarar nagama aikina da aka sani zan saketa na kara gaba daga bayane naji ina sonta sosai.malam najeeb shin zaka iya gaya mana Wanda yasaka eh zan iya gaya muku ba kowane ya sani ba illa matar barista daya dauki jannat kafin ta tafi India karatu wato ina nufin hajiya lubabatu kenn,ittama tana wajan ah.ah bata nn amma in kun bani nan da awa biyu zan kawo muku itta har nan saboda ni kadai nasan inda ta boye kanta "an baki dama, toh masu sauraran shariya zamuje hutu na awa biyu kafin nn za'a kawo mana hajiya lubabatu"buga guduma akayi alkhali ya mike ya tafi yana fita kowa ya mike sai nn da awa biyu za'aci gaba da saurarn shariya,


Bayan tashine aka hada najeeb da yan sanda guda uku suka shiga motar yan sandan suka wuce gidan hajiya lubabatu kafin su karasa gidanne najeeb ya nemi dasu bashi waya zai kirata ya gaya mata gashinn yaxo Nigeria ya kawo mata wayann takardun dan shi kadai ma fitan da zasu iya gano tana gida ko tafita "
Ba musu suka ara masa waya yakira tana ji yace yana Nigeria ya kawo mata takardun wani dadi taji tace mai tana gidanta yaxo ya sameta "bayan yan mintuna kadan sukaxo unguwar kafin su karasa unguwar sukayi parking din motarsu suka karasa cikin layin da kafa saboda kar taji karar jiniya ta gudu,suna zuwa najeeb ya kuma kiranta tana dauka yace mata yana waje Minal ta tura taxo ta bude kofa tana zuwa ta bude wa zata gani najeeb ne da yan sanda a bayan shi ai batasan sanda tayi baya ba,da gudu tayi cikin gidan,


Cikin gidan suma suka nufa suna shiga suka tarar hajiya lubabatu zaune ta dora kafa daya kan daya ga apple a hannunta tanaci tana kallon TV sai taga minal ta shigo a guje kamar wanda aka koro, kafin ta _tam bayeta meye faru sai taga yan sanda ai batasan sanda ta mike ta yadda apple din hannunta ba,kallon daya daga cikin yan sandan najeeb yayi yace gatann Sir ittace wann ittace ta sakani aikata komai,dama akwai yer sandan mace a cikinsu"tana jin haka ta taho wajan hajiya lubabatu"ankwan aka sa mata a hannu aka fita da itta sai Allah ya isa takewa najeeb ,haba hajiya ni bance miki allah ya isa ba saike zakice min allah ya isa.


Jansu akayi har bakin titi sai kallonta ake aka sata a mota yan sanda aka wuce dasu kotu.




Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena Ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 62&63




Bismillah rahmani rahim




______"kotu bayan awa biyu an dawo,ana dawowa aka bukaci da hajiya lubabatu ta fito ta fadi shin gaskiyane itta ta sa najeeb ya auri jannat kuma itta tasa ya dampareta?kawota yan sanda sukayi suka seda itta inda ake saida mai laifi,sunana lubabatu" Mansur banice na sa najeeb ya kwace dukiyar jannat! ba saboda jannat! nima yata ce"da taimakona taje India kaga kuwa taya zan hada baki da wani dan in cuceta karya take ya mai girma mai shariya sukaji magana a bayansu ai juyowa kowa yayi suna kallon wajan da sukaji magana" jannatce ta shigo cikin kotu shiru mutan kotun sukayi suna jiran karin bayani alkaline yayi magana..ke kuma wacece bai war allah? sunana barista jannat Muhammad Ali nice yarinyar da aka zalinta"ya mai girma mai shariya da kunuwana naji muryar wancan matar ta nuna hajiya lubabatu "suna waya da sohon mijina saboda wayan nashi a Hasparren ya saka shiyasa naji duk a bunda suke tattaunawa
Share hawayena nayi naji gaba da magana"naji tana cewa Najeeb wai har yanzu bai karbo mata tsauran takardun kanfanin ba!shikuma najeeb yace mata bai karbo ba ta dan bashi lokaci tana magana Najeeb yaji kamar motsina yace zai sake kiranta sukayi sallama ya kashe wayan,tsauri nayi na koma palo na zauna nayi shiru da naji kamar zai fito shine na ceta kaina saboda kar ya gane cewa naji tattaunawar tasu"a lokacin ne na yanke shawara zuwa Nigeria nemo dan uwan ma haifina duk da shima ba kaunata yake ba amma yazama dole na nemi inda yake,shiyasa a ranar nacewa najeeb zanje Nigeria a zahiri ya nuna kamar bayaso a badili kuma yafi kowa farincikin tafiyar da zanyi,da yace zai biyoni nace mai ya zauna saboda aikin sa"amma hakikanin gaskiya nasan komai danganen da abunda yake aikatawa dashi da kawata da farko nayi tunanin zai dena in munyi aure amma a ashe ba haka abun yake ba.najeeb ne ya bude maki yayi magana..yanzu beauty kina nufin kinsan duk a bunda muke aikatawa dani da arilin amma kika amince kika aureni a haka?kwarai nasan komai Najeeb amma in baka manta ba wani lokaci muna waya dakai kana cemin kana ciwon mara duk da a lokacin bansan me yake haddasawa maza ciwon mara ba, ina mamaki sosai in kace kana ciwon maka,saboda ni a nawa nunanin na dauka matane kawai suke ciwon maka maza basayi shiyasa na yanke shawara dana shiga Google na bincika ai kuwa ina shiga na rubuta a bunda nakeson na sani suka rubuta min komai,sai a lokacin nagane meke hadasa maza ciwon maran shiyasa da kace kanason turo iyayenka ayi maganar aure bam mutsa maka ba,na amince akayi maganar aure,kafin ayi bikinmu ne a kwai wani wata rana dana wuni ina kiranka a waya amma ban sameka ba,shine na yanke shawara danaje na duba ko lfy,tunda nasan gidan naka,lokacin da kaje daukana a makaranta ka manta wasu takardunka kace na rakaka kaje ka dauka muna zuwa na zauna a cikin mota kaikuma ka shiga ka dauka kafito ka maidani gida a lokacin ne nasan gidanka,shine na yanke shawara nazo na duba ko lfy,


Ina zuwa kuwa allah ya taimakeni kofar a bude take kila ka manta baka rufe ba na shiga naji shiru a palon na nufi dakinka saboda ni duk a tunanina ciwonka ne ya ya motsa shiyasa ka kasa fitowa ko palo,ina zuwa bakin kofar dakinka mai zan gani kaine da arilin kwance kuna aikata zina wa'iyazubillah ,sai na koma baya daker na samu na koma gida ranar, Amma ahaka nace bari na baka wata dama ko allah zaisa ka tuba ka dena in munyi aure,saboda in ka shiryu a sanadiyata"nima lada zansamu a wajan (ubangijinmu)shiyasa na amince na aure ka,da kuma son da nake makane ya jamin har muka kai ga aure amma daka tashi sakamin....?kukane yaci karfina na kasa karasa maganar dake bakina duk mai imanin dake wajan saida suka zubar da hawaye,


Alkhaline yayi magana.sorry barista jannat"zaki iya ci gaba?ya mai girma mai sharya ina so da kotu ta dubi maganata a biya mun hakkina"mun gamsu da bayananki jannat amma muna bukatar wasu kwararan hujojin da zamu gurfanar dasu"a gaban kotu,ni ina dashi ya mai girma mai sharya
In har kun bani dama?barista Usman yayi magana! bismillah barista kotu ta baka dama,nagode mai sharya
Ina so barista (dadynsu walida)ya fito yayi magana saboda shine yake dauke da hujoji kowa ya juya yana kallon bakin kofa suga ta inda zai fito jannat ma abun yayi mugun bata mamaki yanzu dama barista da gaske barista na raye itta fah ta dauka sokanarta kawai paa yakeyi ashe dai yana raye da gaske.
Itta ko hajiya lubabatu tun lokacin da taji ance mijinta na raye take zare ido taga ta inda zai fito"yanzu kam shikenn bata da wata dama data rage mata, yanzu shikenan gidan yari za'a kaita"tana cikin wanan tunani aka shigo da barista cikin keken da ake tura marasa lfy da alama wanan harbin da aka masa ya shafe shekaru masu yawa a kwance saboda duk ya rame yayi duhu kamar ba barista da aka sani a da ba.shigowa sukayi da shi har wajan.


Kallon matarsa yayi ido cikin ido yana wani shu'umin murmushi "itta ko hajiya lubabatu sai share gume take,




Sakeena Ismail Cameroon ✍️




Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 64&65




Bismillahi rahmani rahim




______"sunana barista kamal"nine lawyan ma rigayi Muhammad Ali tare muka taso tun muna yara sakama kon yawan zuwan da iyayanmu sukeyi a gida jan junansu yasa muma muka saba sosai dani da Muhammad" kasan cewa shima ma hayfina lawyan ma hayfin Muhammad ne har allah ya dauki ransu basu taba boyewa juna duk a bunda zasuyi ba bayan rasu warsu mukaci gaba da zumunci sosai dani da Muhammad kuwa mun dawo kamar yen uwa duk a bunda zamuyi mukan nemi shawarar juna"a duk lokacin da naje gidansu Muhammad bana ganin shi tare da kaninsa"Ibrahim tun ina shiru watarana dai kasa hakura nayi na tambayi Muhammad meyasa baya jan kaninsa ajiki?da farko dai kamar Muhammad bazai gaya mun ba daga baya kuma yace ai shima a bunda yake ta damusa kenan ya resa yadda zaiyi ne kawai shiyasa ya zubawa Ibrahim ido da yaga dai ban fahimci inda maganarsa"ya dosa ba shine ya fara ban labarin
Rashin jin da Ibrahim yake dashi da kuma taurin kai har dama lbrn tsohuwar matar babansu" nace mai karya damu ya dinga jaa shi a jiki yana gaya mai gaskiya wata rana insha allah zai gane cewa a bunda yake aikatawa ba dai dai bane yace min insha allah zaiyi hakan,


Tun a lokacin Muhammad ya dinga ja'a Ibrahim a jiki yana gayamai gaskiya
Wasu yayi anfani dasu wasu kuma ya watsar bayan yan wasu shekaru mukayi aure dani da Muhammad amma na riga Muhammad yin aure
Shiko Ibrahim yana ganin yayansa yayi aure tsohuwar matar babansu ta bashi shawara da kar ya yedda shima yace aure yakeso da Ibrahim yace shi bashi da budurwa ta dauki wata yer uwarsu"ta bawa Ibrahim"dayake Ibrahim kuma yana jin maganar ta sosai shine ya amince yaje ya gayawa yayansa shima aure yakeson yi da farko kamar Muhammad bazai amince da maganar ba daga baya kuma da yayi tunin cewa kila in yayi aure zai shiryu shine ya tambayeshi inda yarinyar take Ibrahim ya gayawa Muhammad! Muhammad!!najin yer uwarsu tsohuwar matar babansu"yace bazai yuba
Ibrahim kuma yace shi gaskiya itta yakeso a haka babu yanda ya iya _ya yarda akazo akayi maganar aure bayan yan kwanaki kadan aka daura wa Ibrahim aure dashi da Maryam"


*Bayan wasu yan shekaru*


Wata rana da bazan taba mantawa ba a rayuwata"shine ranar da na samu lbrn rasuwar Muhammed"a bunda yafi komai dagamin hankali shine Bayan naji labarin cewa hatsari sukayi a hayyarsu"ta zuwa gaisuwa da nayi bincike nagano cewa ashe ma a hayyar jigawace abun ya faru ,shine na yanke shawara dana je wajan ina zuwa na dudduba wajan sosai nayi bincike anan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login