Showing 6001 words to 9000 words out of 50838 words

Chapter 3 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 13&14






Bismillah rahmani rahim




_______ba'a wani dau lokaci sosai ba jannat "ta farfado,kuka sosai ta dingayi tana kiran sunnn momy da Dadinta,ai barista Kamal naganin haka ta mike da hanzari taje ta sanarwa da doctor jannat "ta farfado,
Bi bayan barista doctor.. yayi suka dawo dakin tare,har yanzu jannat" bata dena kuka ba,ta na cikin kukanta "kome ta tina oho ,sukam gani kawai sukayi tayi shiru tana goge hawaye.




Murmuchin mai ciwo tayi tana kallon doctor"


Sai ta fara magana, doctor ka sallameni naji sauki gida nake son komawa"nasan mama nacan na nemana,kallon doctor barista yayi,ya fara magana, doctor,ya naga ta ambaci sunan wayenan mugayen mutane?"murmuchi doctor"yayi ya dafa kafadun abokinsa"ka kwantar da hankalinka"yanzukam ta tuna da komai" kwakwalwarta ta dawo normal kamar yarda muke fata.




Murmuchin jin dadi barinta yayi shima,yace Alhamdulillah" masha allah, yace baby ya jinkin naki?"jannat "taji dadi da sunan da barista ya kirata dashi amma bata "nuna ba,tana mamaki ina yasan sunan baby in bata manta ba, zata iya cewa iyayenta ne kawai suke kiranta da sunan baby".
Barista ina kasan wanan sunn nawa?"jannat"ta jefawa barista Kamal tambaya ?"


Jannat"ba lallaine ki sanni ba,ni abokin ma hayfinkine ,kafin allah yayi masa rasuwa nayi mai alkawari da dama,
A ciki kuwa adda aurar dake ga mutun na gari ".
Bayan wannan a kwai wani kanfaninsa guda biyu daya mallaka miki shi tun kina shekaru hudu kacal a duniya..
Babu wadda yasan da maganar daga ni sai momynki mukadai muka sani ,ni dinma saboda yerda da Dadin naki yayi da nine yasa nasani,sai kuma yanzu da na gaya miki sai kuma doctor ".barinsta na kallon doctor yace doctor ina so kayi mun alkawari bazaka taba gayawa kowa"wanan maganar ba?"barista yayi magana,haba _haba a bokina sai kace baka san halina ba, nayi maka alkawari babu wadda zai sani insha allah"murmuchin jin dadi barinta yayi yace Alhamdulillah" nagode "sosai abokina,yanzu ya jikin jannat"din,shin zan iya tafiya da itta"barista ya tambaya?"sosai ma kuwa bari na rubuta muku ta kardan sallamar dan naji jikin nata normal,godiya barista ya kumayiwa doctor ".


Ta kadan sallama doctor"ya bawa barista,suka wuce gida.




Lokacin dare yayi sosai,shiyasa barista Kamal ya yanke shawara "ya kaita gidansa kawai gobe in allah ya kaimu sai ya maita itta" gidan oncle Ibrahim" din.


Jannat" na ganin sun nufi wata unguwa daban ba nasu ba,ta juya ta kalli barista,barista ba gidanmu zaka kaini ba ?"


Jannat" bakiga dare yayi sosai ba,muje gidana inyaso gobe sai na kaiki gidan naku ko?"girgiza kai jannat "tayi tace wllhy mama zata dekeni in na kwana a wani waje daban.


Karki damu jannat "in na kaiki gidan naku gobe zanyiwa maman magana,zan gaya mata cewa bakiji dadin bane shiyasa,baki dawo ba,




Geda kai tayi amma ba haka taso ba,itta kam tafiso ta kwana a gida,
Amma a haka suka wuce gidan barista"suna zuwa,ya yiwa matarsa bayanin komai,ta dauki jannat "ruwa mai zafi ta hada mata tayi wanka kaya ta kawowa jannat "cikin kayan yayanta,ta saka,ta bata a binci taci ta dauki magungunan da barista yace ta bata -ta
Bata shima tasha.




Umarni ta bawa jannat din data kwanta "kwanciya jannat tayi nan da nan bacci yayi awan gabada itta"sai data tabbar tayi bacci,sanan ta barta ta koma dakin mijinta"...




Washe gari


Jannat "tun a subaha data tashi bata koma ba,
Kan dagon data kwanta a kai ta fara gyarawa tana gama gya kan gadon, toilet din dakin ta wanke tas, kasa ta sauka ta share falon tana cikin yin moping matar" barista" ta sauko,durkusawa jannat tayi har kasa ta gaidata "matar barista ta amsa fuska a sake..




Haba jannat"ya zaki tashi tun yanzu kina aiki keda ba lfy ce dake ba,
Murmuchi jannat "tayi tare da fadin ai mama na saba,agida da wuri mamarmu take tashina inyi aiki,shiyasa na tsaba"ko banida lfy ba barina take ta kwanta"ba kinga kuwa dole na tsaba,geda kai matar barista tayi hawaye na ciyayo mata akan kumatu,wannn wana irin zaluncine haka,yen uwanka amma zasu nuna maka kiyayya karara..


Dan dafa kafadun jannat "matar barinsta tayi tana kallon jannat", jannat"innace kidawo nan da zama zaki yadda?"geda kai jannat"tayi tace eh zan yedda cedai kuma bazan iya dawowa nan ba,saboda "mama da oncle Ibrahim"zasu hanani,yanzuma in nakoma gida bansan wana hukunci zasu mun ba,na kwana a waje...




Ki kwantar da hankalinki jannat"babu a bunda zasu miki,kuma insha allah"barista zai masa magana,kinji yata ?"
Geda kai jannat"tayi,matar barista ta umarceta data je tayi wanka,in barista zai fita zasu tafi tare,a kaita gida,toh tace ta wuce sama"itta koma matar barista"dakin yayanta "ta wuce,tana zuwa'dakin,yemmatane kuda biyu daya batafi sa'ar jannat"ba daya kuma ta dan girmi jannat "da kadan,kallon karamar matar barista tayi,ke Minal ki ban kaya zan kaiwa jannat"zata saka in tayi wanka,
Dan yasine fuska wanda aka kira da sunn Minal tayi,ta fara magana,haba momy jiya ma fah na maki kayan baccina kin kai mata,yanzu kayan baccinne da kika bayer shine zaki tsaya kina magana akai,walida tayi magana?"


Tana kallon momynsu"
Momy bari ni na dauko mata a nawa sai na kaimata "geda kai momy tayi dace allah miki albarka walida"ke kuma Minal allah ya shiryeki "mé abun duniya dan allah,kullun sai nayi miki fada akan abun duniya amma bakiyaji ko?"toh shikenan "ni nasan ta waca hayya zanyi maganinki",ta fita tabar musu dakin, kallon Minal walida tayi,kedai allah ya shiryeki da bakin halinan naki Minal" ameen minal" ta amsa ba kunya ta kara gaba.




Toilet ta shiga ta bar walida a wajan, girgiza kai walida tayi"ta bude wardrobe dinta ta daukowa jannat"kaya,ta wuce dakin momynsu,kai mata kayan,dan tasan a can momyn nasu ta sauketa,




Tana zuwa tadan kwankwasa taji shiru sai kawai ta shiga, tana shiga ta nemi gefen gado ta zauna,tana jiran jannat"ta fito daga wanka,dan tana da yakini wanka jannat"take.......






Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 15&16




Bismillah rahmani rahim


______ba'a dau lokaci ba jannat' ta fito daga toilet daure da tawol din da momynsu walida ta bata, "kanta akasa batama kula da walida dake dakin ba,har saida ta karaso dab da gadon taga kafar mutun ai batasan santa ta dago kanta ba,tana ganin walidace ta juya a guje zata koma toilet walida"ta riko hannunta tana mata dariya,sunkuyar dakai kasa, jannat "tayi saboda kunya,itta kam tunda take babu wanda ta taba ganinta a haka sai yau,duk da macece itta walidan amma sam jannat"bataji dadi ganinta da walidan tayi a haka ba.




Kai sis me haka,kunya ta kikeji ne,dama kayane momy tace nakawo miki,walida ta fada, tare da mikawa jannat "doguwar riga abaya dake hannunta",karba jannat "tayi ta mata godiya,bata jira walida ta amsa ba,tayi toilet taje ta saka rigar ta dawo dakin,


Sai a lokacin ta dago ta kalli walida sosai, murmuchi walida tayiwa jannat,tana tambayar ta ya sunanta,?" jannat ".
Jannat'din ta fata,waw suna mai dadi gashi kuma kina da kyau sosai.
Walida ta fada,dan kyau jannat"din ya tafi da imaninta sosai,




Zaki zama kawata ?"walida ta tambaya, murmuchi jannat"tayi dan itta kanta walida ta burgeta sosai...


Mutane deyewa sukeso ta zama kawarsu amma bata basu fuska ,


Shiyasa a school itta kadai take zama in anfita break kamar mayya...




Amma yau sai taji walida ta kwanta mata arai .
Bude baki jannat "tayi daker kamar batason yin magana,ta kalli walida tace..nikam ba kawance nakeso muyi ba, ina so ki zama yer uwata .. jannat "ta fada tana kallon walida".




Na yedda daga yau munzama sisters walida ta fada,dariya jin dadi sukayi su duka.


Nikam zan iya cewa ma ban taba ganin dariyar jannat "ba,sai yau.dan kullun cikin kunci take.
Amma yau hadda fararen hakoranta a waje..




Momy ce ta shigo dakin tace toh uwar tsurutu kinzo sai zuba tsurutu kike,ga abbanku can yana kira..


Mikewa walida tayi tana dariya ta fita,kallon jannat "momy tayi,tashi muje kiyi breakfast sai ku wuce ko?"mikewa jannat" tayi tabi mayan momy suka fita,suna zuwa falo,gaida barista tayi "yana tambayarta ya jiki tace da dauki,wajan zama aka nuna mata"ta zauna walida da mike ta zuba mata a binci..




Suna gama cin a binci ..
Barista ya kalli jannat ".
Jannat"tashi muje ko,mikewa jannat tayi jiki babu kwari ta wuce sama,su momy suka bita da kallon tausayi,kayan slamiyanta ta dauko da maganinta,tadawo falon rakiya suka mata "har bakin mota, tashiga suna daga mata hannu har suka bar gidan,hawaye jannat"ta goge barista ya juya ya dan kalleta yaci gaba da tuki.ba wadda yayi magana a cikinsu har suka karasa"kofar gidan...
Kishiga kiyi mun sallama da abban naku kice ana sallama dashi"kinji jannat ?"barista yayi magana,geda kai jannat tayi"ta fito daga motar kamar wata munafuka"
Ta shiga gidan,aiko tana shiga kamar dama itta suke jira, mama da ameera na ganinta suka hau masifah,


Kinganta ko mama ai dama nasan wajan sama rinta taje ta kwana bakiga har da wani kayan ma ta dawo dashi ba...
Bayan kuma da infome din islamiya ta fita dashi.


Ameera ta fada tana hararan jannat "kai seka rance itta bata zuwa ko ina,mamace ta karbi zancen,da cewa ai nagani dama na dade da sanin cewa jannat"na yawon banza, kawai dai ina jiran wannan ranar..
Alhamdulillah yau kam kuma kunkani da idonku.
Jannat "tace wllhy mama ba a bunda kuke tunani bane?"a hayyata ta dawowa daga islamiya naga wani gawa daya tunamin da iyayena"shine na yanke jiki na fadi,badan wanan baristan ba , da bansan a wana hali nake ciki yanzu ba , tunda jannat"ta fara magana suka tsareta da idanu,


Ameera tace karya take mama kinga wanan fuskan yayi kama da mara lfy ne ?"mama ta amshi zancen da cewa,ina fah kina ganinta kinsan babu wata rashi lfy da dayi, na tabbata baristan da take magana a kaima saurayinta ne suka hada baki su raina mana hankali,in da gaske meyasa bata xo tare da shi ba,ameera ta fada..
Yazo yana waje yace nayi mai sallama da abba,jannat "tayi magana,




Mamace ta fito kofar gida taje ta leka, babu ko mayafi a kanta,wata bakar mota mai kyau ta hango pake a gefen gidan nasu.
Cikin gidan ta koma,taje ta fadawa mijinta,fitowa yayi kofar gidan,yana hango motar barista ya karasa awajan,


Barista kuwa yana ganin Ibrahim ya fito daga mota,hannu barista ya mikawa Ibrahim sukayi musabaha,dama kuma sun san juna kawai dai babu a bunda ya taba hadasu ,ko zaisuwa ma bai taba hadasu ba sai yau,dan Ibrahim mugun tsana yake yiwa barista "wai barista ne yake zuga yayanshi,a kan komai har dama harkan kasuwancin sa,




Baristane ya kacewa Ibrahim tunanin da maganarsa "kwana biyu Ibrahim tun rasuwar yayanka, baka neman mutane, murmuchi mai kamar dole Ibrahim yayi,haba dai barista,kuma ai ba'a ganinku tun lokacin,da aminiyar ka ya rasu...




Yanzu dai ba wannanne ya kawoni ba,dama a kwai wani rasuwa da akayi a unguwar nan,shine naxo, zamu je zana'iza,sai ga jannat "ta fadi sakamakon ganin wannn gawar, da gudu na karasa wajan,da farko dai banganeta ba,sai dana karasa wajan,na ganeta,shine na dauketa na kaita a sibiti, alhamdulillah muna zuwa a sibiti,bamu dade sosai ba, ta farfado,a nan ne doctor yake shedamun cewa ai tunaninta ma ya dawo,ban tabbatar da zancen doctor ba,saida naji jannat"na kiran sunan iyayenta,sai alokacin na gamsu da maganar doctor..




Sanda aka sallamemu dare yayi sosai shiyasa ban dawo da itta ba,shine mukaje gidana "ta kwana,sai yanzu allah ya nufa dawowarta"...




Muma dama inaso mu tattauna wata muhimmiyar magana,daya shafeta kuma ya shafeka kaima,amma ina son musamu waje mu zauna tukun sai muyi magana..
Bismillah Ibrahim yayiwa barista "suka nufi cikin gidan,a falo suka zauna,
Ibrahim yace ina jinka barista,




Dan gyara zama barista yayi"sai ya fara magana,
Kafin dan uwanka ya rasu.....






Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By






Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)






Page 17&18






Bismillahi rahmani rahim




_______"kafin allah ya dauki ran dan uwanka, ya bani wasu ta gardun kanfaninsa da kake aiki,yace ya mallaka maka itta,da kuma gidajensa guda biyu wadda suka zauna aciki kafin allah ya musu rasuwa,da kuma wanda ke abuja,ga takardun kanfanin nazo dashi "yana mota,in na tashi tafiya sai kabiyoni mota sai ka karba"sauran ta kardunma insha allah zan kawo maka yau zuwa gobe insha allah.




Mikewa barista yayi,ni zan tafi sai na dawo goben,rakashi oncle Ibrahim "yayi har bakin mota"barista ya dau ta kardun ya mikawa Ibrahim"godiya Ibrahim yayi,sai da barista ya bar kofar gidan sannun Ibrahim ya koma ciki...


Uffam bai cewa jannat"ba,
Bayan tafiyar barista" mamace ta shigo,zaiyana mata komai, Ibrahim yayi mama taji dadin dukiyar da aka mallaka musu" sosai, zama sukayi suka dan tattauna ,




Sai daga baya Ibrahim"ya tafi kanfaninsa,tunda yanzu ya dawo mallakinshi"yau kam har wani jiji dakai yake "in angai dashi ma daker yake amsawa,




Bayan magarib jannat"ce zaune a kitchen tagama girki dare Kenn,tana zaune kome ta tuna naga ta mike falo taje,inda take ajiye kayanta"ta bude ta dauko wana abu aleda,tana kalle _kalle karsu mama su ganta "fitowa tayi daga falon ta koma kitchen din,zama tayi akan sallayan data shimfida,




Bude ledan dake hanunta"tayi sai ga karamin waya ya baiyana, dan dennawa tayi taga harda layi a ciki,


Tunani take ko maiyasa barista ya bata wannan wayan ?"babu mai bata amsa,






Dazune kafin ta shiga gida, jannat"har zata bude murfin mota ta fita" sai barista ya dakatar da itta "dan zuyowa jannat"tayi,tana kallon barista",






Karamar wayace barista ya mikawa jannat"ta karba tana kallonsa"kinga jannat"ki ajiye wannan wayan koda wani abu zai taso saiki sanar dani,karki bari kowa ya san da wayanan kinjiko?"gedawa barista kai jannat"tayi,tafita "amma ittakam ta rasa anfanin me zatayi da waya,dahar barista zai iya cewa kar ta bari kowa ya san dashi"...
Kuma in ajiyeta akusa dani,mai hakan yake nufi?"ta tambayi kanta,
Itta yanzu ya zatayi insu mama sunga wayanan ,yanzuma suna cewa yawo take zuwa,ballantana in sunga waya,




Gidan barista kamal


Zaune yake tareda iyalensa a falo,dama al'adanshi ne in yagama cin abinci ya zauna tareda iyalensa"kallon matarsa barista yayi,ya fara maga ,kinga madam bari naje gidansu Ibrahim"yanzu zan dawo,saboda gobe ina da aiki dayewa, allah kiyaye,suka masa " fita yayi "ya hau motarsa ya 'nufi gidansu Ibrahim ",


Yana zuwa kasan cewa dare ya danyi shiyasa bai samu yaron dazai aika ba,mai gadi kawai ya tambaya yace mai Ibrahim din yananan,
Shiyasa barista ya shiga darek tunda ya fada masa dazu da safe zai dawo ko yau ko gobe,
Dan zai iya yuwama ya tarar da Ibrahim" din na jiransa",dan ya sanshi sarai indai akan dukiyane,






Shiga cikin gidan barista yayi "yazo dab da shiga falo kenan sai yaji wata magana daya girgiza mai tunani"ji yayi wani mutun yana cewa,wllhy batada anfani gwara tabi iyayenta "kawai ittama,kaga in tabisu dukiya yazama naka kenan,hakane kam abokina amma kasan bai kamata muyi kisan kaiba,kadai 'nemo mana wani ma fitar daban ba wanan ba,


Shikenan abokina yanzu tunda kaki yarda da wancan shawaran, ina da wani shawara guda daya,waca shawara kake nufi ?.Ibrahim ya tambayi,a bokinsa,




Ka dauketa kaje can nisa da garinan ka jefar da itta kowama ya wuta,
Kaga sai kace bata tayi "
Dariya Ibrahim" yayi,shegen a bokina dama ka iya bada shawara haka"dariya wadda Ibrahim ya kira da aboki yayi,




Ai barista najin kamar zasu fito yayi sauri barin kofar falon,magana yayi da mai gadi akan cewa karya sanarwa da Ibrahim yazo,sanan ya dan bashi wani abu yabar gidan,


Yana barin gidan,kiran jannat "yayi har ta fara bacci,a zabure ta mike zaune, ta dauki wayan,ta kara a kunne,
Daga can bangaren kuma barista ne ya fara magana "jannat"ki fito wajan mai gadi yanzu kiyi sauki,ina jiranki "..
Karki bari kowa ya ganki kinji,toh jannat ta amsa,mikewa tayi ta saka hijabi "fitowa tayi"ta zira takalmanta " waje tayi hanzari, saboda karsu mama su ganta ,
Bala mai gadi "na ganinta yamike suka fita tare saidaya leka ya tabbatar"babu kowa a wajan "sannun suka wuce inda barista ya kwatanta masa sai da suka danyi tafiya sannan suka hango motar barista shiga cikin motar jannat tayi ",barista yayiwa bala godiya yajà motar suka bar ......








Sakeena ismail Cameroon ✍️








Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️






By




Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 19&20






Bismillah rahmani rahim




_____"godiya barista yayiwa bala yajà motar suka bar layin ,sai da suka hau titi jannat "ta kalli barista",barista ina zamuje da daddarann,wllhy in su mama suka gane bananan, dukana zatayi in nadawo "ta fada kwalla na cikowa a idanunta"ki kwantar da hankalinki, jannat "ba wani waje zan kaiki ba,
Gidana zamu,kuma a can zakici gaba da zama har allah ya fito miki da miji kiyi aure,


Babu wadda zai kuma musguna miki,kafin allah yayiwa mahaifinki rasuwa ya danga a manarki a hannuna,shiyasa bayan rasuwarsa "da naji kinmanta komai bazaki iya tunawa da rayuarki na baya ba,na kyaleki a wajan oncle dinki,amma ba dare ba rana,kullun sai nazo layinku,a duk sanda zaki tafi makaranta ina ganinki,ban taba sallake ko da -da rana daya batare dana zo naduba halin da kike ciki ba,har i zuwa wannn ranar,


Na san tsarai bakiya jin dadin zaman gidan oncle dinki,


Naso tun a wancan lokacin na daukeki "amma ban samu dama ba sai yau,"yaudinma ina da dalilin dayasa na daukeki,amma ko nagaya miki dalilin ba lallaine ki fahimceni ba,saboda ke yarinyace har yanzu,




Jannat "dai tun lokacin da barista ya fara magana tayi shiru,tama rasa me zatace,


Har suka karasa gidan barista "batayi magana ba,fita sukayi suka nufi cikin gidan barista"suna zuwa ya tarar da iyalensa suna jiranshi,dama kuma dabiyarsu ce in har baya gida bazasu kwanta ba,har saiyadawo tukun.


Walida na ganin jannat "ta mike taje ta rungumota"jannat kinzo amma dai yanzukam bazaki tafiba,walida tayi magana,tana kallon Dadinta "insha allah daga yau tare zaku rayu da jannat"har sai sanda allah ya baku mijin aure.


Salle walida tayi kamar wata karamar yarinya , girgiza kai barista yayi,yana dariya,dauketa kuje ku kwanta dan daga yau tare zaku dinga kwana a dakinku,kuma insha allah zanje na nemo mata makaranta "da zata karasa karatunta"tunda wannan shekaran ne zata zana jarabawarta na ,WAIS da NICO .


Gaida momy jannat tayi "walida ta riko hannunta suka haura sama,


Suna zuwa walida tacewa Minal ta bawa jannat gadonta"ta kwanta,inyaso itta ta shimfida katifa,da farko dai kamar Minal tace aa,sai ta tuna labarin jannat "da momynsu ta basu na cewa, jannat yer gatace sosai kafin iyayenta su rasu,kuma a yanzuma tana da dukiya sosai wadda iyayenta suka rasu suka bar mata"
Shiyasa Minal na tunawa da zancen tayi saurin cewa shikenan taxo ta kwata "walida tayi mamakin na tsaurin amincewar Minal,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login