Showing 12001 words to 15000 words out of 50838 words

Chapter 5 - Mijin Attajira Book Complete in 2025 By Sakeena Ismail Cameroon--.txt

shirin kiranka sai gana ka kirani , Ibrahim ya sherbawa barista karya,
Ayya babu mas'ala ai ba gashi ni nakira ba, barista yayi magana yana kara sakin wani murmushi"ina maganar mu ta kwana Ibrahim"?.
Wllhy har yanzu bamu ganta ba,jiya ma a bunda yasa bankira ka ba,yini mukayi dani da abokina muna yawon nemanta 'har can adamawa sai da mukaje,bamu dawo ba sai dare,shiyasa ban samu na kiranka ba,yanzune nayi niyar kiranka,na dau waya kenn sai ga kiranka "ya shigo wayata,


Kaji yanda akayi kenn barista"dan allah ka janye maganar kotun nn..insha allah zamu kara nemota,ko allah zaisa a dace....


Haba _haba Ibrahim "ya zakace na janye maganar kotu bayan kuma kafi kowa sanin yau kusan kwana biyar bamusan inda yarinyar" nn take ba,yanzu haka ma bamusan wana hali take ciki ba,sann sai kace na bar zancen kotu.
Taya zan bar maganar kotu bayan kuma a gidanka ta bata,waye sani ma ko kaine ka saceta ban sani ba...
Wllhy_wllhy kaga dai Har sau biyu na rantse maka..?bansan inda jannat"take ba,sedai kuma kasan halin yaran yanzu,kila ma... tsaurayinta" tabi suka gudu bamu sani ba,shiya sa nace ka kwantar da hankalinka"barista mu nemota a hankali...


Kaga dakata Ibrahim"...dama tun_ tuni na lura ba kaunar yarinyar nn kake ba...ban tabbatar hakan ba,sai yau,insha allah sai ka fito da yarinyar nn...barista na gama fadar haka ya kace waya....


Kallon wayan Ibrahim yayi wani gumine yaji yana sassafo mai,tudda sanyin AC dake dakin..


Hajiya maryam na tambayar sa meyake faruwa, bai ma kalle ta ba _ballantana "tasa rai zai amsa mata....da taga ya mata banza ma,ficewarta"tayi daga dakin ta bararshi _shi daya...


Waya _ya dauka ya dannawa a bokinsa" kira,gayamai duk yadda sukayi da barista "yayi..ya kara da cewa shi bai ma san ya zaiyi ba,saboda yace zai kaishi kotu..,


Kwantar masa ta hankali a bokinsa yayi,suka kara tattaunawa,akan maganarsu" shekaran jiya..sai da yaga hankalin Ibrahim ya kwanta kuma ya _yedda da shawaran da ya zomai dashi,sann sukayi sallama..ya kashe wayan,sai a lokacin ya samu ya kwanta,




*India*


Ranar Monday jannat "tafara zuwa school kuma Alhamdulillah komai yana tafiya dai_dai
Kasan cewa tana son yara sosai, shiyasa take ganin su aryan kamar kannenta "gashi kuma yaran nada shiga rai..
Shiyasa a kwanaki kadan da tayi dasu har sun shaku sosai da yaran,tare ma take kwana dasu"?




*Nigeria*


Gidan barista bayan ya gama waya da Ibrahim"fadawa matarsa "duk yanda sukayi da Ibrahim "yayi,mai zatayi in banda dariya,ya kara da cewa koda zai gaya mai inda jannat take sai ya koya mai hankali tukun saboda gobe....


Karfe biyun dare wasu mutane "masu bakaken"Kaya sun rufe fuska.bazama ka iya gano kosu waye su ba, suka shiga gidan barista"sukayiwa mai gadi dukan tsiya suka shiga cikin gidan...



Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment and sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️



By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Jumma'at Mubarak too all Muslim 🕌🥰




Page 27&28




Bismillahi rahmani rahim




______"barista ne tsaye a dakinsa" yana sallan... dare kasancewa ,shi mutunne mai yawan ibada ,sallan dare baya wuce shi,ko da bai da lfy yakan daure ya tashi yayi sallan...yana cikin sallah yaji kamar motsi a falo,sharewa yayi_ yaci gaba da sallan sa,har ya idar da sallah bai kuma jin motsin ba,
Yana cikin lazzumi"yaci gaba da jin motsin,kamar ana hauro mai sama,bai tabbatar ba,sai dayaji ana buga mai kofar daki.
Mikewa yayi _ya matso kusa da bakin kofah yana tambayar waye?"nine ka bude kofah in ba haka ba,kuma mu karye kofar..haka yaji ana fadi,juyowa yayi _ya kalli matarsa"dake zaune akan gado, da yaga dai hankalinta duk a tashe yake sai zare ido take,lumshe mata ido yayi _ya kuma dudesu,alamar kwantar mata da hankali"..ittama lumshe mai idanunta tayi,jin mutann suna maganne yasa shi tsaurin budewa,yana kallon su ,bai gane kosu waye daga cikin su ,dan ko wannesu fuska a rufe tureshi sukayi,suka sakai suka shiga cikin dakin, hankalin barista a matukar tace,yake suwaye su"? barista ya tambaya .
Har ma kana da bakin tambaya su waye mu ? suna karewa dakin kallo, kuyi hakuri,barista ya fada....


Hankalin barista duk a tashe,daurewa kawai yake, saboda kar matarsa fahimci hakan,


Magana suke amma hankalinsa"gaba daya ma baya garesu,shi tsoransa "bai wuce kar su cutar masa da iyali ba..yana cikin tunani suka tureshi suka shiga cikin dakin,basa ganin komai nasu sai idanunsu, shiyasa ma bazaka taba gane kosu waye su ba,nufo hajiya lubabatu sukayi,gadan_gadan .....
Barista ne ya fara rokonsu "don Allah don annabi karku cutar min da iyalena ,barista yayi magana tare da hada hanna yensa biyu a waje daya alamar roko ,dan dakatar da zuwa inda hajiya lubabatu take sukayi,suka juya suna kallon sa,wani dariya ogansu ya sheke dashi "yana kallon barista"...kaga barista "ina yarinyar nn take?" In har bakaso,na tabama iyalae, ka bamu yarinyar nn da kuma ragowar dukiyar dake hannunka"in ba haka ba...bai karasa magana ba yayi hayyar kofar dakin yana wani muskilin murmushi "sai daya je har bakin kofar ya juya a karo na biyu yana karewa barista"kallo,kasan ina zani?"ya tambayi barista, girgiza kai barista yayi,tsawa suka daga mai, kaga malan baki zaka bude kayi magana...
Bawai ka dinga girgiza mana kai ba,sai kace kurma,daker barista ya iya bude makinsa,ba...ba...ban...sa..bansani ba,daker ya iya furta kalman bansani din saboda tashin hankalin da yake ciki,zai iya cewa ma tun da yake bai taba shiga irin tashin hankalin da yake ciki a yau ba,shi tsoransa" ma bai wuce kar a cutar masa da iyalae ba,


Wajan yayanka zamu muga wadda tayi mana,sai mu dauka tunda yaya wasu sunfima yayanka,suna gama magana basu tsaya sunji waca amsa barista zai basu ba,sukayi ficewar su ,




Mikewa barista da hajiya lubabatu sukayi suka fita,basu gansu a waje ba,sai suka nufi dakin yaran nasu_suna zuwa kafin ma su karasa,dakin, suka ganshi a wangale,shiyasa da sukaxo "cusa kansu kawai sukayi suka shiga,
Suna shiga,suka tarar dasu daya_ yana tsaye,daya kuma yana kan gadon Minal, wandonsa a tube dan dagashi sai gajeran wando zaiyi lalata da itta "salati barista yayi ya karasa bakin gadon,in kanayiwa allah da annabi kabar mun yata,ba itta ta muku laifi ba,nine nake ganin nayi muku laifi ba yata ba,ni dinma bansan wana laefi nayi muku....
Barista yayi magana ?"


Ha.ha.ha.ha barista naga alama kana da taurinkai.
In har kana so na bar maka yerka,na tafi ba tare danayi mata komai ba,ka tabbata ka fito da jannat " a duk inda kaje ka boyeta,in bahaka ba,a yanzu kuma a gabanka,zanyi wa yerka fiyade,kafin na tafi daga gidan nn kuma sai ka bamu ragowar dukiyar daka boye,na marigayi Muhammad Ali,in ba haka ba,ina gama yi mata fiyade kasheta zanyi mukara gaba,kaga kai zakayi a tsara bani ba,


Yana gama magana ya mike ya tire rigarsa,ya take daga shi sai single da boss kawai ya rage a jikinsa,kara matsowa kusa da itta yayi _ya fincike rigar baccin take jikinta "ya rage daga itta sai pad,kuka minal ta farayi,walida kuwa sai zare ido take,ai barista na ganin haka baiyi wata_ wata ba,da gudu ya karaso bakin gadon, yajà bargo yana rufewa minal jiki,bai karasa ba,ya mike ya dauki barista da wani gigiceccen mari tare da tureshi gefe,ya bawa dayan umarni daya dauré barista" dauré kafarsa sukayi da bakinsa ,


Haba mai gida yanzu ashe zaka iya bari a lalata rayuwar yerka ,kuma a gabanka kana gani,bayan kuma kana da mafita "...in har kai zaka iya,ganin a cuci yermu toh ni bazan iya ba,


Kaga dakata ni zan gaya muku inda jannat"din take,amma dan allah karku cutar min da yarinyata "pls, hajiya lubabatu tayi magana...
Dan dakatar da a bunda zaiyi yayi yana kallon hajiya lubabatu,alamun yana jinta,fadi ina jinki?"
Wllhy bata kasar nn ya dauke ta ya kaita karatu a India,amma bayan wannan bansan komai ba,


Hahaha shegen barista "dama nasan tsarai kasan inda jannat"take kaki gaya mana kawai saboda tsabar taukin iron naka ,


Gaskiya hajiya kin burgeni,da kika ceci yerki,amma kisani cewa dole sai ya bamu ragowar dukiyarnn ko kuma mu tafi dashi muje mu kasheshi,


In allah ya yarda zai baku amma dan allah karku kashemun miji, hajiya lubabatu,tayi magana jikinta na kerma, kinga dakata hajiya ko dan kinga na kyale yerki ?toh kisani na kyaleta ne dan ra'ayin kammu,dan ke baki isa kice zaki bamu umarni ba,


Maza ki kwashe yayanki kuje ku kwanta "ai da tsauki momynsu walida ta tattara yayanta suka bar dakin suka koma dakin ta,ya rage daga barista "sai su ,bindiga suka fito tashi suka saita mai a kai basuyi wata_ wata ba,saiji kake........




Sakeena ismail Cameroon✍️




Comment and Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️


By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




29&30




Bismillah rahmani rahim




______"ji kake bummm,
Suka harbi saban cilin dakin.wajan da sukayi Harbin har sai da ya bule,
Badan bakin barista a rufe ba,da tuni ya kurma ihuu,yan zu hakan ma sai zare ido yake,kamar ma jari ...dariya ogansu ya kuma shekewa dashi ",ya fara magana,kaga barista na baka nan zuwa gobe,ka kira yarinyar nn ta dawo "ka kuma tabbatar daka ajiye mana ragowar dukiyar nn in ba haka ba,kanka zan hanba a wann karon,kar kaga yanzu nayi harbi a silintar dakin "toh wllhy in har bakayi a bunda muka saka ba,toh wllhy gobe bazaka kwana da ranka a duniya ba,abu na biyu da zan gaya ma kuma shine in har ka sanar da yan sanda "wllhy iyalenka zamu kace,in mungama da iyalenka semuxo kanka kaima, inyaso kuwa bar duniyan a tare,tunda kana sonsu,
Yana gama magana yayiwa dayan alama da hannu,dasu tafi,fita sukayi suka bar gidan....




Mommynsu "walida kuwa suna jin harbin binduga,suka saki kuka"yanzu shikenn yayanta ma sunzama marainiya"ya zasuyi da rayuwarsu"kallon yayanta tayi ta gafa magana,kinga walida ku zauna yanzu_ zan dawo,
Kallonta sukayi,suka fara magana suma haba mommy ina kuma zaki?"mun rasa Dady kina so"kema mu rasaki ne,pls mommy karki tafi,
Kunga walida in allah ya yarda babu a bunda zai sameni,ku kwantar da hankalinku"ku zauna yanzu_zan dawo nace muku aiko,toh mommy suka amsa,


Fita _tayi ta nufi dakinsu walida"tana zuwa taga kofar a bude take,saka kai kawai tayi ta shiga,dube dube tashigayi"amma bataga kowa ba,sai ta shiga kwanceshi "tana gama kwanceshi"ta kalli mai gidanta...mai gida ina suke ?dama bakai suka harba ba, Alhamdulillah nagode allah,karasa kwanceshi tayi, daker barista ya mike,sai zare ido yake "Rishi mommy tayi, suka bar dakin, ta nufi dakinshi dashi,tana zuwa,gefen gadon ta nuna mai ya zauna,ta shiga toilet ,ruwa mai zafi ta hada mai,ta kuma fitowa,ta kamashi har bakin kofar toilet din ta kaishi "kallonsa tayi ta fara magana,ka shiga ka watsa ruwa mai gida kyaji dadin jikinka,geda kai kawai barista yayi dan yanzu bashiga bakin magana, toilet ya shiga ya jà kofar ya rufe,har yagama shiga toilet din hajiya lubabatu bata dena kallon mai gidan nata ba,har saida ya rufe kofa sann ta juya ta koma dakinta dan duba su walida dan ,yana zuwa ya tarar dasu rungume da junansu suna kuka...yanzu shikenn sun kashe Dadynsu?suna cikin haka sukaji karar bude kofah,dan waiwayowa sukeyi ,sukaga ashe ma mommynsu ce,rufo kofa momy tayi _ta karsa cikin dakin,ai suna ganin haka suka mike suka rungumota sam a jikinsu,
Sai kuka,saida sukayi mai isarsu sann suka dena,dagosu momy tayi tana kallonsu ,kunga ku share hawayenku babu a bunda ya samu Dadyn ku yanzu haka ma na barshi yana wanka na taho nn dakin saboda bansan wana hali kuke ciki ba...kunga yanzu a subaha tayi kuje_ kuyi alwala kuzo kuyi sallah kuyiwa allah godiya, toh suka amsa walida ta wuce toilét,shafa kan minal momy tayi,ta fita ta nufi dakin mai gidanta,dan tasan yanzu kam kila yagama wanka.aiko tana zuwa ta sameshi zaune a kan gado yana zaune yayi tagumi,allah ne kadai yasan tunan me yakeyi.
Zama momy tayi kusada itta ta kamo hannunsa "sai a lokacin barista ya dawo daga tunanin daya dafi,


Magana hajiya lubabatu ta farayi,haba alhaji wai tunanin me kakeyine haka har na shigo dakin baka sani ba,dan dagowa barista yayi yana kallon hajiya lubabatu,sai ya fara magana..haba hajiya taya zaki tambayeni meke damuna bayan kuma kinfi kowa sanin halin da nake ciki.


Haba mai gida ka rage damuwa a ranka,


Yanzu abunda zakayi kawai ka kira a bokinka ali Khan"kace mai ya saka jannat a jirgi ta dawo gida,in ya tambayeka lfy kace mai rasuwa akayi mata,shine kakeso tazo tayi musu gaisuwa,ba dadewa zatayi ba,zata koma...
Kaga tana dawowa ka dauketa,da itta da dukiyar duka _ka masu,ai nasan bai wuce wann oncle Ibrahim" dinn ya turasu ba,kaga kana basu itta zasu barmu muyi rayuwarmu"yadda mukeso,babu dakura,


Itta kuma jannat "nasan tunda Ibrahim din kanin mahaifinta nasan bazai cutar da itta ba duk rashin imanin da yake fashi,


Kaga allah ma ya taimaketa,tunda itta macece,tana samun mijin aure sai tayi aurenta"kaga daga lokacin wahalarta "takare zataci gaba da rayuwarta kamar kowa,




Tun lokacin da hajiya lubabatu ta fara magana barista bai tanka mata ba har tagama...




Sai a yanzu daya daga yana nazarin maganarta,


Amma in yace zai amince da shawararta"..ya zaiyi da alkawari daya daukar wa a bokinsa?


In Kuma yace bazai bi shawararta ba kuma iyalansa suna cikin tashin hankali...


Tashi yayi baice mata komai ba, ya wuce masallaci,yana idar da sallah ya dannawa a bokinsa kira...bugu biyu ya dauka,gaisawa sukayi.
Yake tambayarsa ya jannat "dasau aryan yace suna lfy,


Bayan sun gama gaisawane yake sanar da shi komai,kamar yanda hajiya lubabatu ta bashi shawara haka ya fadawa Mr ali Khan"ma..


Yace ya bawa jannat"zaiyi mata bayani.
Kiran jannat "Mr ali yayi _ya bata waya..bayan sungama gaisawa ta barista yake sanar da itta data shirya anjima zataxo Nigeria insha allah...tayi mamakin sosai amma bata nuna hakan ba,dan itta kanta tayi missing dinsu walida sosai,bayan sungama wayane,barista ya karasa gida kwanciya yakeso ya danyi, dukda dai ba Lallaine ya iya bacci ba,amma babu abunda yake da bukata a yanzu daya wuce kwanciya,


*Bayan awa shida*


Jannat "take saukowa daga kan jirgi,dukda ba wani dadewa tayi a India ba amma tayi migun canjawa sosai kamar ba itta,sanye take da bakar abaya daya amshi jikinta"idonta manne da bakin glass,kasan cewa itta din farace sosai shiyasa ba karamin kyau glass din yayi mata ba,
Karasa saukowa tayi tana waige _waige can ta hango su momy da barista haddasu walida,da duk jikinsu yayi sanyi, can ta hangosu"sai ta fara tafita kamar mai tsoron kasa.....




Sakeena ismail Cameroon ✍️




Comment Sharee pls
[8/29/2023, 1:49 PM] Mom Muwadda: 🧝‍♀️MIJIN ATTAJIRA 🧝‍♀️




By


Sakeena ismail Cameroon
(Mom muwadda)




Page 31&32




Bismillah rahmani rahim




_____karasa wajansu tayi gaida barista da mommy tayi tana kallonsu walida murmuchi ta sakar musu, rungume "walida jannat tayi,dama kuma tana da rauni zuciya shiyasa,kawai ta saki kuka bubbuga bayanta jannat ta shigayi,haba aunty walida,ko baki farincikin ganina bane...
Ai barista najin haka yayi saurin amsar maganan,haba jannat "taya zakice batayi farinciki ganinki ba,duk munyi farinciki ganinki,itta dimma farincikin ne ma ya sata kuka, sakin walida jannat "tayi_ taje ta rungumi minal ma,sai da barista yayi magana,sann kowa ya shiga mota suka wuce gida..


Muna zuwa gida wanka nayi sannun naci a binci.nadan kwanta,nikam har na kwanta ina ganin canji wajansu walida sosai dan fara'ar da na saba gani akan fiskokinsu yau babu shi,in na tambayesu kuma cewa suke babu komai...


Sai wajan karfe 4na tashi kasan cewa bana sallah ,,shiyasa dana tashi wanka kawai nayi.


Barista ne zaune shida hajiya lubabatu,a dakinsa "dawowarshi kenan daga masallaci,lokaci ya duba a 'agogon dake daure a tsinsiyar hannunsa"yaga 4hadda yan mintuna,sann ya maida dubansa ga hajiya lubabatu,kinga hajiya kitashi kije ki hada duk a bubuwan da kikasan yana da mahimmanci sosai a wajanki,sann kicewa su walida ma su hada kayansu da sauran a bubuwan da zasu bugata,


Ban fahimci mai kake nufi ba mai gida ?"


Muhada kayanmu muje ina ?"
Kinga hajiya kitashi kije kiyi a bunda na gaya miki
Banason yawan tambaya...zata sakeyin magana,sai ya daga mata tsawa da tunda take da mai gidanta bai taba mata haka ba.....
Fita tayi sai data leka dakinsu walida, ta fada musu sakon mahaifinsu "sann ta wuce nata dakin
Tana zuwa ta nemi gefen gado ta zauna sai kawai ta saki kukan dani kaina bansan kona meye ba...ta jima tanayi sai daga baya ta tsagaita da kukan nata,wayarta_ tajâ tayi kiran wata number ,bugu daya aka dauka,sai ta kuma sakin wani kukan bansan me aka gaya mata a wayan ba,sai kawai gani nayi tayi murmuchi tana share hawayenta" ....toh na kumaji ta amsa,sai ta kashe wayan,ta shiga hada kayanta"dama duk a bubuwan da zatasan yana da mahimmanci sosai a wajanta...zuwa karfe 5 ta gama hada komai nata....




Dakin su walida.
Bayan fitar momy taga dakinsu,suka juya suna kallon _kallo,me momy da Dady suke nufi,da zasuce su hada kayansu ?har suka gama yiwa kansu tambayoyi basu samu amsa ba...
Da sukaga lokaci na kurewa kawai tashi sukayi suka,fara shirya kayansu a cikin akwati.
Tayasu jannat tayi,kasancewa itta dama tunda ta dawo kayanta suke cikin a kwati bata sakasu a wardrobe ba....suna cikin shiryasu ne,momy ta kuma shigowa dakin a karo na biyu... kallonsu tayi tana tambayasu sungama ?suka amsa da eh,umarni tabasu dasu sauko da kayan kasa..saukowa sukayi da kayan,suka sake komawa sama suka tattara sauran kayayyakinsu da suka rage suka sake dawowa falon,zama sukayi suna jiran wana umarni Dady zai kuma basu...ba'a dau lokaci ba sai gasu suma sun sauko da kayayyakinsu "kwashe komai sukayi suka saka a mota,sai wata jakace kadai ta rage wanda barista baisakashi a mota ba,


Dama kuma ya riga daya gayawa mai aikisu,da mai gadi dasu shirya suma tun dazu,shiyasa suna fitowa kudin mota ya bawa kowannesu "ya kara da cewa insha allah in yadawo zai nemesu...
Dama kuma ya rigada yayi musu karya akan cewa zasuyi tafiya amma suna dawowa zai kirasu a waya suma sai su dawo wajan aikinsu..
Sai da su mai gadi suka bar gidan sann barista ya kukkulle ko ina,mota suka shiga suka bar gidan...


Sai da yayi nisa sosai da gidan ya sauke wani a jiyar zuciya,dashi kadai yasani..


Tunani ya shigayi yanzu shikenn ya bar gidan sa har a badan,


Tafiya kusan na awa daya sukayi sann sukaga yayi parking a wani gida ma daidaici mai kyau,


Gidan yana da kyau sosai..irin gidacen turawann ne.amma bai kai wanda suka bari girma ba,


Remod ya dauka ya danna sai kawai sukaga get din gidan ya bude shiga da motar ciki yayi_yayi parking,sai yace su fito ,fitowa sukayi daga cikin motar,sai kallon gidan suke ya burgesu walida sosai,amma banda momynsu walida....
Walida ce ta juya tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login