Showing 1 words to 3000 words out of 77288 words

Chapter 1 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

: *DANDANO DAGA ABARI YA HUCE*




*MAIRO A GIDAN YAYA HABIBU!!!*
© *Sumayyah Takori*
Litinin babbar rana, ko bature yana tsoronki. Habibu ya yi shirin ofis cikin _suit_ din ma'aikatan bankin _Barclays_ , da jibgegiyar rigar sanyi, hand-socks da leg-socks, yana so zai fita aiki. ga yara sunyi shirin makaranta tsaf, misalin karfe bakwai daidai na safe. amma babu hanya, domin kuwa tashi sukayi suka tarar kankara ta rufe kofar gidan ruf, da tagogi bakidaya.


Dina ma ta fito cikin nata shirin cikin kayanta na lauyoyin banki, tana ta korafi akan 'snow'. Dole Habibu ya fiddo waya ya kira ma'aikatan sare kankara, nan da nan suka zo cikin minti goma, suka bambare kankarar sannan suka samu hanya suka fita.


Mairo ta fito daga dakinta ta yiwa sanyi mugun shiri, baka ganin komai nata sai shacin kayatacciyar fuskarta kai ka ce balarabiyar *Morocco* ce. Tasa yaran a gaba suka fito tana dauke da little Mairo, suka zo bakin hanya suka tsaya tana rike da hannayensu, tsayuwar minti biyar sukayi motar makarantar su ta iso ta sanya su ciki suka tafi, suna daga mata hannu itama tana daga musu. Kasancewar ita bata da karatu a yau sai ta kama hanya cikin nutsuwa ta koma gida.


( _Wannan shine tsarin rayuwar gidan Yaya Habibu a kullum. Duk wayewar gari kowa abinda yake yi kenan)._


Mairo na karantar Zamantakewar Dan adam (Sociology ) a jami'ar Michigan (Michigan State University) tun bayan dawowar ta gidan Yayanta Habibu. A yammacin ranar tana zaune a _study-room_ da farin gilashin karatu a idanunta tana nazarin littafin 'Haralarambus and Holborn ( _Sociology_ , _Themes and Perspectives_ ) domin wani assignment (aikin gida) mai matukar wuya da aka basu akan *hedonism* zasuyi _submitting_ a washegari.
Aunty Dina ta murda kofar ta shigo fuskarta dauke da murmushi, sassanyan kamshin ta na turaren (yves saint laurent) shi ya fara bakuntar hancin Mairo kamar koyaushe, Dina mace ce mai darajja kamshi a jikinta ta dade da sanin wannan. Ta ja kujerar dake fuskantar Mairon ta zauna sannan tace "Mairo dan rakiya nake nema, London zan je gobe ko zan samu ki raka ni?"Mairo ta shiga girgiza kai da sauri "inada aiki mai yawa a makaranta goben, kuma zanyi submitting assignment dina, me zaki je kiyi?"
Ta ce "kallon 'film-fare award' na wannan shekarar, gara in gani _vivid_ fiyeda a talabijin nafi gane komai. Tun wancan satin ake ta sanarwa za'ayi".


Mairo bata san kallon Indian na Aunty Dina ya kai matsayin haka ba, da zata ni ki gari kasa-ya-kasa tun daga birnin Michigan har babban birnin Birtaniya don kawai ta ga GALA! Da sauri tace "sai kin dawo. Ni kam, bazan samu zuwa ba".


Habibu da taya bera bari ya yankowa Dina tiket ta tashi a washegari, gidan ya saura sai su kadai. Tun safe Mairo na makaranta tana fama da ayyukan gaban ta itada kawarta Ir'eesh Tawheedah 'yar asalin kasar Somalia. Bata dawo gida ba sai yamma lis, ta tarar tuni Yaya Habibu ya riga ta dawowa. Zaune suke a falon shi shida yaran suna aikin makaranta yana nuna musu. Mairo tayi sallama ta shigo suka yi tsalle suka daneta suna yi mata "oyoyo".


Yaya Habibu ya daga ido ya kalle ta yana mamaki cikin ransa wai wannan Mairo ce, MAIRON GURIN-GAWA, MAIRON-HURE! Abu daya ya tuno a wannsn lokacin yayi murmushi (goruba daga kan bishiya a kauyen GURIN-GAWA) ya ce "Mairo 'yan makaranta.... Mairon Dina. ... Mairon Yaya Habibu...!" Ta yi dariya har fararen jerarrun hakoranta suka fito. Kirarin da yake mata kenan idan ya so nishadi. Ta wuce dakinta rungume da jakarta don ta kimtsa.


Bayan tayi sallar magriba tayi wanka ta canza kayan jikinta ta fito falon ta zauna tare dasu. Zuwa can Yaya Habibu ya fito daga dakinsa cikin shiri, sai kamshi yake. Ga dukkan alamu cikin sauri yake. Ya dube tayace "maza a shirya dinner, amma _African-Dish_ . Inada babban bako anjima kadan. Babban abokina Amiru zai sauka yanzunnan daga Washington D.C zan je filin jirgi na dauko shi". Yadda yake maganar cikin rawar jiki kadai zaka fahimci wannan bakon mai muhimmanci ne da matsayi na musamman a gareshi. Ba tun yau ba Mairo na jin sunan Amiru a bakin Yaya Habibu da Dina. Zata iya cewa rana bata fitowa ta fadi wani cikinsu bai ambaci Amiru ba.


Ta amsa da ladabi "toh, sai kun iso".


Yana fita ta mike ta nufi kicin, Lynder na goge-goge ta bata hanya ta wuce, ta bude _deep-freezer_ tana tunanin me zata dafa musu? Daga bisani zuciyarta ta tsaya akan tuwon shinkafa miyar danyar kubewa tunda dai suna da Okora (danyar kubewar gwangwani).


Nan da nan ta dora sanwa, tayi amfani da _dried fish_ da _mushroom curry_ cikin miyar, duk kicin din sai ya dau kamshi. Sunada zobo, don haka ta tafasa shi ta tace, ta markada abarba ta hade da zobon da fulebo din abarba ta juye a _jug_ ta sanya a firji don ya yi dan sanyi ba tareda ta sanya sukari ba.
Ba tun yau ba ta san Yaya Habibu da son Danwanke, kai shi duk wani abinci ma na Africa to ya bi bayan dan wake. Don haka nan da nan ta jika kanwa ta kwaba ta jejjefa cikin tafashashshen ruwan zafi, cikin dan lokaci ta kammala komai.
******


Ta kashe wayar ba tareda ta baiwa Nabilah amsa ba. Jikinta a sanyaye matuka, maganganun Nabilah kullum irin na Anty Dina ne, ko maiyasa? Alhalin basu san juna ba, basu taba ganin juna ba ko a hoto, balle tace sun hada baki ne suna _sharing idea_ don su kalubalanceta! Dai-dai lokacin taji shigowar Yaya Habibu da bakonsa. Da alama ba su biyu bane don tana jin muryoyin maza daban daban. Ta sake kudundunewa a cikin bargonta sama-sama take jiyo tashin muryarsu anata turanci kamar tashin duniya. Kira ya shigo wayarta, daga kwance ta mika hannu ta amsa a kasalance.
Dina ce.


Tace "yaya kuke Mairo? _Hope_ ba matsala, ina nan tahowa gobe insha Allah, mai zan sayo miki?"
Mairo ta ce "munyi kewarki ne kawai Anty, duk gidan ba dadi da baki. Bana bukatar komai sai dawowar ki lafiya". "Nima haka Mairo, ji na nake kamar nayi shekara ban ganku ba. Me ya samu wayar Habib ne? Na kasa kama shi".
Tace "yana falo, yayi baki ne".
"Su waye?"
Mairo ta ce "Na dai ji yace Amiru ne"
Dina tace "wow! Amiru yau a gidanmu? Maza kaiwa Habib wayar inason magana da shi".
Ta mike rike da wayar ta fita, shaf ta manta ko kanta bata rufe ba tsabar yadda Dina ta matsu tayi magana da mijin nata, a haka ta isa falon. Ta karasa kusa da Habibu ta mika masa wayar. Juyowar nan da zatayi sai idonta cikin na Amiru, wanda ke zaune gefen Habib cikin _Italian Suit_ bakake wul, ya sassautama wuyanshi ruwan tokar _tie_ dake jikinshi. Suka samu kansu cikin matsananciyar faduwar gaba a lokaci guda. Ga ita Mairo, kwarjini ne da kyawun Amirun ya haifar mata da faduwar gaban. Amma ga AMIRUN, bazan iya cewa ba!


Habibu yace "Amiru *meet my beloved sister MAIRO* , da nake baka labari...".
Yana mai kokarin saita lumsassun idanunsa akan Habibun, don kawar dasu daga nacewar da sukayi akan Mairon yace "itace Mairon??? Mairo zo mu gaisa....". Amiru dai Hausa yayi, amma wani _accent_ ne da Mairo bata taba jin mai gardinsa cikin kunnuwanta ba. Kamar yadda bata taba ganin mutum mai kyau da kwarjininsa ba, ilhamomin dake tare da shi bata taba haduwa da mai irin su ba! Wannan shine AMIRUN Yaya HABIBUN???

( _The beginning of everything_ kenan)
*****


Mairo data koma daki kwanciya tayi rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima kamar Amiru, kace baka sonsa ai ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta daidai tayi, don bata iya karya ko yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san bata kyauta ba. Saidai a ganinta gara hakan, da dai tayi irin auren da zuciyarta ta raya mata akansa.


Dina tayi sallama ta shigo tana fadin "tashi, abincin da kike gudu ne na biyo ki da shi. In dai Amiru ya dade da barin gidannan. Ta tashi ta zauna sosai ta karbi farantin ta soma ci. Dina na kallonta, can kuma tace "Mairo me kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita a yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?".
Ta cira kai daga cin abincin tamkar wadda aka katse wa gudun jini a cikin jikinta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta tace.
"Yana magana ne kan wai yana so na, so kuma na aure, yana burin na zama uwar iyalinsa. Nikuma na gaya masa kai tsaye cewa "bana son sa!".
Dina tayi murmushi, daga jin kalaman Mairo da yanayin maganarta kasan kuruciya na dawainiya da ita. Cikin sanyin murya tace "sabida me ba kya son nashi Mairo? Gashi kyakkyawa son kowa kin wanda bai samu ba, gashi da dimbin ilmi kamar Yaya Habibun da kike cewa yana burge ki. Yanada matarshi baturiya zallah amma ya tsallakota yazo yace ke Mairo yana son ki. Zai iya rabuwa da ita saboda ya aureki. Gashi da kirki ga addini, ke kuwa Mairo me kike nema a da namiji da ya wuce wannan?"


Sai Mairo tasa kuka, ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, ta shiga kuka mai tsuma zuciya.


"Na kasa mance *Uncle Junaidu* ne Anty Dina! Na kasa mance dimbin alherin da yayimin a rayuwa. Shine tsanin duk wani matsayi da matakin dana ke kai a yau. Idan na auri wani ba shi ba na ci amanar sa.......!"


Dina ta katseta "akwai hanyoyi da yawa da zaka sakawa mutum Alherin da yayi maka ba dole sai ta hanyar aure ba. Misali shine ki dinga bin shi da kyakkyawar addu'a ba tareda shi din ya sani ba. Wannan addu'ar Ubangiji yayi alkawarin karbar ta Mairo. Kada ki yi mamaki zuwa yanzu shi Junaidun ya samu wadda yake so ya aura ya manta da ke.
Ni na kasa gane kan wannan soyayya da kike yiwa Junaid maras dalili. Kin ce bai taba cewa yana son ki ba! Kince ba kuyi alkawarin aure ba! Kince ya san gidan Baffa amma bai nemeki ba! To Mairo gaya min wace hujja gareki da zata tabbatar da cewa yana son ki?
Bakisan akwai masu taimako sabida Allah ba? Ba don a aure su ko a saka musu da soyayya ba? Haba Mairo, kiyi tunani mana, kiyi amfani da hankalinki, ki so mai son ki a zahiri da badini. Kiyi aure saboda Allah da raya sunnar Ma'aiki amma ba don abinda zuciyarki ta afu a kai ba.


Ina tabbatar miki Amiru in kin nutsu, kin bude zuciyarki a hankali zaki so shi wallahi har ma fiyeda son da kike ma Junaid. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yiwa Junaid, ko baki aure shi ba Allah ya shaida! Yayi alkawarin sanya masoyan gaskiya da suka mutu ba tareda sun auri juna ba a gidan aljannah. Ina tunanin Junaid yayi abin nan ne da hausawa ke cewa ABARI YA HUCE SHI KE KAWO DA RABON WANI!"


Ta dubi Dina da sauri har tsakiyar idanunta tace.
"Idan hakane Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana so na, furtawa ne baiyi ba kamar yadda _Inna ta_ da Nabilah ke cewa???"


Gyada kai Dina ta yi. "EH, yana son ki, amma ya bari YA HUCE! Don kuwa a zahiri babu wata mu'amala ta mutunci da tausayi tsakanin mace da namiji sai 'SOYAYYAH'. In ma mutuncin ne da farko, to daga baya rikidewa yake ya koma soyayya. ...


Ke dinnan Mairo har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yimawa ba soyayya ba. Amirun shi kike so da gaske; na gani a kwayar idon ki, na gani a gangar jikinki. Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aureki ne don ya tallafi rayuwarki a wancan lokacin da kike neman matallafi ido rufe, amma ba don kinsan hakikanin me aure ya kunsa ba.


Mairo kinaso ki ramawa Junaid halaccin da yayi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba, ya sanki, kin san shi, a tunanin ki wannan shine karshen soyayya, to ba shi bane! Soyayyar aure daban take, Allah ke hada ta, kuma bata fassaruwa.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shine tsakaninki da Junaid ba soyayyar aure ba! Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne to sai muyi shirin tafiya Kano, unguwar Galadanchi gidansu Uncle Junaidu, mu nemeshi mu kai kudin aure... mu gaya masa yadda kike son shi, har kina duban tsakiyar idanun masu son ki da aure na hakika kina gaya musu ba kya son su. ......sabida kawai kada ki ci amanar soyayyar shi da ya baki a makaranta. ......" .
Ala dole ta murmusa, ta san _zambo_ ne Dina take mata. Duka wannan bata lokacin da yawan bakin da Dina ta share tana bayani, ba duka abinda tace ne Mairo ta yarda dasu ba.


Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga AMEERU! Sabida shi ta sani, shine mai irin tsarin rayuwar su. Bata san komsi game da rayuwarta ta baya ba, batasan wanene Uncle Junaid a rayuwarta ba. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro yake bata balle na Amirun da ta ji suna cewa yana _World Bank_ karewar _Barclays_ . A karkashin inuwarsa rayuwar Habibu ta ginu bakidayanta. Shi ya maida Yaya Habibu ko me yake a yanzu.


Ta yarda ta hakura da Uncle Junaidu sabida hujjoji kwarara da kowa yake gaya mata. Hatta Nabilah tace da ita "lokaci yayi da zata manta da Uncle Junaidu tayi aure". Ta dubi irin auren da ita tayi, amma daga baya ya zame mata ALHERI. Don yanzu ba abinda take so a duniya sama da Ismael kuma shima hakan har ga albarkar haihuwa.


Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta bayan fitar Dina. Ta ja bargo har kanta ta kudunduna. Bacci take so ta yi amma ya ki zuwa. Al’amuran na neman tarwatsa mata kwakwalwa tareda wargaza mata tunani bakidaya. Tana so ta yarda da Dina, halaccin dake zuciyarta na karyata Dina. Amma abubuwan da ta zano ai duk haka suke; zata je neman auren Uncle Junaidu ne??? Ko kuwa haka zata kare a zaman jiran *tsammanin warabbuka* ???


Zata iya cigaba da zaman jiran ranar da uncle Junaid zai nemeta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya bata uzurin da ya hana shi yin hakan a lokacin da ya dace daga nan har gaban abada! Amma bazata iya jure bukatar gangar jiki da zuciyarta ba irin na kowanne lafiyayyen dan Adam. In hakane aure ya zama dole a gareta domin kare kanta daga _zina_ , da sauran ayyukan alfasha, cikar mutunci a idon duniya da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.


Wayarta dake karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text ). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a daidai wannan lokacin karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna. Bata san lambar ba don kuwa bakuwa ce, ga abinda ke rubuce;


".......... _When life changes, and we go our separate ways, you will still be in my heart till my dying days...... my world has never meet a person like you!"_

(A yayin da rayuwa ta canza ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu) zaki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).


Haka ta sa sakon a gaba tana ta karantawa har akayi kiran Assalatu. Don ta tabbata ba kowa bane; Amiru ne. Duk da bai saka suna ba ko wata alama mai nuna shi din ne. Allah sarki! Har YA HUCE ne? Tana so ta bashi amsa bata san me zata ce masa ba.


Da safe take nunawa Dina a kitchen, ta karanta tayi dan miskilin murmushin nan nata. Tace "ke kuma kika ce me?"
Ta zumburi baki "ni ko kula sa ma na yi?"
Dina tayi dariya tana kwaikwayon muryar ta tace "Haba Mairo! Yi hakuri ki dan kula sa. Kin ga shi yayi fushin amma ya sauko, sabida ya fahimci Mairo ba sonsa bane bata yi, kawai ita din mai *amana* da *rikon alkawari* ce".
Tayi murmushi har kumatunta ya lotsa. Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami. Tace.
"To me zan rubuta???"
"Ki ce kawai yazo yayi _joining_ dinmu _breakfast_ ".
Mairo ta rubuta ta tura. Amsar da ya bata ta sa ta yin murmushi, domin ya ambato rabin ranta.
"A'ah kirawo JUNAID......"
" He's far away....!_ " (Amsar Mairo).


"And I'm not closer too.... I'm far away either, and I will not come back. On my way to Detroit-Metro".


Hankalinta yayi mummunan tashi. Saboda ita ne Amiru zai bar kasar da haihuwarsa ne kawai ba'ayi cikinta ba? Da sauri ta jefar da wayar. Da gudu tayi daki ta dauko mukullinta. Dina na kira amma bata juyo ba take fadin.


"Shima zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Banaso in samu wannan _heartbreak_ (karyewar zuciyar) a karo na biyu".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login