Showing 51001 words to 54000 words out of 77288 words

Chapter 18 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

fuska sosai, ya ce
"Lafiya kike kallona? Ko na yi kama da tsohon saurayinki ne mai sunan aljanu? Haka kawai yarinya kin zama kurma, in dai ni ne to mu zuba, shege ka fasa".
Ya kuta, ya sake cewa
"Halan Dina ko gayar da mutane ba ta koya miki ba?"
Ta dauke kai ba ta ba shi amsa ba, sannan ta yunkura ta mike ta fada bandaki ta yi wanka tare da wanke baki ta fito. Yana tsaye jikin sif dinta yana amsa waya, ga dukkan alamu da Harrit yake wayar, wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare ta. Ta yi saurin komawa bandakin don ta dauka ya fita ta aje tawul din ta maida kayan jikinta. Ta sake fitowa wannan karon ya gama wayar yana sanyata a aljihun wandonshi.
Ya bi-ta da wani irin kallo kasa-kasa ya girgiza kai, ya fita yana cewa
"Abinci za mu ci, ko yau ma ba za a ci da ni ba?"
Ko ta tafas ba ta ce masa ba, don ta lura neman baki yake yi da ita.
Ta shirya cikin shadda 'orange' babbar riga 'senegalese', ba ta yin kwalliya rankacau don haka kullum fatarta ta ke danya shar (fresh). Ba kankanuwar yunwa ta ke ji ba, don haka ta nufo falon ta cimmashi a 'dinning area' na falon. Kallo daya ya yi mata ya dauke kanshi, zuciyarshi na bugawa. Wannan yarinya kamar Juliet ta ke.


Ta ja kujera mai fuskantarshi ta zauna, sannan ta fara bude ma'adanan abincin, sinasir ne da waina, sai hadaddiyar miyar agushi wadda ta ji naman rago, a gefe farfesun hanta da Koda ne sai Shawarmah da snacks dangin su meat-pie, samosa, spring rolls da sauransu.
Cikin sassanyar murya ta ce "Can I serve you?"
Hakika ya ji wannan muryar har cikin kokon ransa. Bai iya ya amsa ba, illa kai da ya gyada mata, don haka ta fara da hada mishi ruwan 'lipton' mai zafi da ganyen 'Hemorrhoid tea', sannan ta zuba mishi Sinasir din da farfesun a faranti daban-daban.
Ya yi mata wani sassanyan kallo ba tare da ta sani ba, sannan ya soma ci. Ta hada 'lipton' ta sha, amma ta yi-tayi ta ci abinci a gabansa ta kasa. Ta mike ta ce
"Zan shiga wajen Hajiya".
Ya ce
"A'a, sai kin ci abinci na gani tukunna".
Ta koma ta zauna, ta dauki sinasir guda daya, ta sanya a faranti ta soma ci cike da kunya. Ya tura mata farfesun gabanshi ya ce, "Cinye shi".
Ba musu ta karba don ba zata iya yin jayayya da shi ba. Sai da ya tabbatar ta cinye, sannan shi ma ya mike yana cewa
"Mu je na rakaki wurin Hajiyar".


Tare suka jera har gidan Hajiya. Tana sallar walha sanda suka shiga a karamin falonta. Sai da ta idar ta shafa addu'o'inta sannan ta juyo gare su, cikin matsananciyar kauna ta mikawa Mairo hannu
"Zo dawo nan kusa da ni diyata".
Sai ga su Sabah su ma sun fito, suka gaida Yayansu wanda ya maida hankali ga amsa kiran da ke shigowa cikin wayarshi.
Daga karshe ma fita ya yi ya barsu, bayan ya fadawa Hajiya zai je ya raka bakinshi airport. Su Amina kamar su hadiye Mairo. Nan ta wuni sur tare da su.
Bai dawo ba sai bayan la'asar, lokacin da ya shigo tana kicin ita da su Sabah suna hada abincin dare. Hajiya na falo ta ce
"Sai yanzu?"
Ya ce
"Wallahi kuwa, ai bakin nawa ne suna da yawa, kuma jirage daban-daban za su shiga, amma dai alhamdulillah duk sun tafi sai fatan Allah Ya sauke su lafiya".
Hajiya ta kwalawa Mairo kira, ta fito ba tare da ta iya hada ido da Amirun ba. Wanda ya bita da kallo kamar bai santa ba. Ta russuna gaban Hajiya cike da girmamawa, Hajiya ta ce, "Shi miji idan ya dawo yana bukatar kulawar matar sa, ta hanyar yi mishi sannu da zuwa, da ba shi abu mai dan sanyi ya sha kafin a gabatar mishi da abinci. Don haka bi shi ku tafi, su Amina za su shigo muku da abincin idan an karasa".
Cikin jin nauyi ta ce
"to Hajiya".
Shi abin ma dariya ya ba shi, wai wannan katuwar ake koyawa kula da miji, Hajiya ba ta san yaran zamani da wayonsu ake haifarsu ba, balle Mairo rainon Dina, kula da miji sai dai ta koyawa wasu, sai dai in ba ta sa kanta ba.
A 'bedroom' dinta ya cimmata, tana kokarin sauya kayan jikinta. Duk dauriyarshi da jarumtakarshi ya kasa sarrafa kanshi, don haka ya yi hanzarin komawa da baya ya ja mata kofar. Ta yi saurin juyowa amma ba ta ga kowa ba, sai karar rufe kofa.
Ta ci gaba da abin da ta ke yi kamin ta jiyo sallamar Amina da Rayyah a falo. Ta fita suka aje abincin a 'dinning. Suka yi 'yar hira ba su jima ba suka fita. Ba ta san dakin da ya shiga ba, ko ta sani ma ba zata shiga ba, don haka ta zauna nan falon tana jiran shi sai zuba kamshi ta ke.
Zamanta da wajen mintuna ashirin sannan ya fito, da alama wanka ya fito. Wannan karon cikin shigar kananan kaya, farar shirt din (Tommy Hilfiger) da bakin wando Tokyo. Sai ‘miyaki’ ke tashi. Mairo ta daga kai a hankali tana kallonshi. Wani irin abu na tsirgawa cikin jikinta yana tada tsigogin jikinta. Kallo daya ya yi mata ya karanto halin da zuciyarta da ma gangar jikinta ke ciki.
Ya murmusa ya daga gira ta kara rikicewa, a ranshi ya ce "munafuka! Idan dai wannan Amirun ne yarinya, to kwalelenki har sai kin so shi, kin kaunace shi don Allah, tunda kiri-kiri kin fada mishi cewa ba kya sonshi, akwai wanda kike so, don haka wannan jikin ma da kike wa marmari ba zaki same shi ba".
Abincin da Mairo ba ta iya ta ci ba ke nan, sabida gani ta ke kamar Amirun yana karanto zuciyarta. To da gaske hakan ne, tunda yake shi din ba yaro ba ne. Ya fita ilmi da hankali nesa ba kusa ba. A kwayar idanunta ya gama gane ta tsaf.
Yana kallonta sai caccaka cokali ta ke cikin abinci ta kasa kai ko loma guda. Shi kuwa cin abincinshi yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana kallonta a kaikaice. Wani zubin ya yi murmushi, wani zubin ya girgiza kai. Wannan karon bai takurata da lallai sai ta ci ba, don ya tabbata ba zata ci din ba. Dan Abdurrahman Gaya, kadai ta ke so a jikinta.
Kararrawar kofar shigowarsu ta yi kara, wannan ne ya ceci Mairo daga kaifafan idon Amiru. Da azamarta ta mike ta nufi kofar ta bude. Ta sha mamakin ganin Daddy da kansa. Cike da girmamawa ta ba shi hanya ya wuce.
Sai da ya zauna a 'seater' ta zube a kasa tana gayas da shi. Ya ce
"Yaya bakunta Maryamu?"
Ta ce
"Alhamdu lillah".
"Babu wata matsala ince ko?"
Ta ce
"Babu Daddy".


Amiru ya baro kujerarshi ya iso inda Daddyn ya ke ya zauna a gefensa suka soma hirarsu. Ta mike ta je kicin ta kawo mishi ruwan (Eva) mai sanyi da lemun 'shany' sannan ta gabatar mishi da abinci.
A nan ne ya yi murmushi, ya ce
"Lemun kadai zan sha Maryamu, na Hajiyarku yana can yana jirana, kada inci a wajenki inje in kasa cin nata".
Ta yi murmushi ta ce
"To Daddy babu komai".
Ta koma daki ta barsu don su gana.


Yau ma irin kwanciyar jiya suka maimaita, wato shi yana bisa kilishi ita tan kan gado. To haka kwanakin da suka biyo baya. Idan ka gansu a gaban Hajiya da Daddy. ko su Amina, ba zaka taba zaton cewa zaman 'yan Marina suke ba. Kowanne na ji da miskilancinsa ya kasa kwantar da kai ga dan uwanshi. Ga ita Mairo, a ganinta shi ne namiji, shi ya kamata ya nuna mata kulawa irin ta kowadanne ma'aurata amma ba ita ba. Sannan ba haka Dina ta gaya mata ana yiwa amare a renakun su na farko a gidan aure ba. Ba haka kuma ta ga Yaya Habibu yana yiwa Dinan ba. Amiru yace yana son ta baka da zuci, amma bayan aurensu ta ga ba haka ba. Wannan al’amari yana sanya ta cikin wani irin tunani mai zurfi da wuyar fassarawa. Har ta kasa jin dadin rayuwar gabadaya.
Shi kuma Amirun, a nashi bangaren, ya riga ya saba samun tarairaya ta karshe daga banasariyar matarshi, kamar ta goya shi. Bai san cewa matar Bahaushe da matar bature akwai wasu manya-manyan banbance-banbance ba. Hakika mu Allah Ya ba mu wannan darajar ta kamun kai da alkunya, wanda ya zamo kowanne irin namiji, duk kyau, aji, mukaminsa da iliminsa dole ya lallame mu idan har yana son ganin yadda ya ke so.
Yau juma'a ta tashi da kewar Dina kwarai a ranta, ba abin da ta ke so irin ta ji muryarta. Ya dawo daga sallar juma'a shi da Daddy daga babban masallacin Abuja kamar yadda suka saba kowanne sati idan suna nan. Ta rasa yadda zata yi ta roke shi ya ba ta aron waya. Dabara ta fado mata don haka ta nemo biro da 'yar takarda ta rubuta mishi, ta soke a jikin kofar dakin da ta tabbata shi ne nasa.
Ya zo shiga dakin don sauya manyan kayan da ke jikinsa ya cimma sakonta. Ya yi murmushi ya sumbaci takardar ya share ta bai ce mata komai ba.
Sai da daddare sun yi shirin kwanciya, bayan ya jefa filonshi ya mike. Ta zuba tagumi a gefen gado abin duniya ya dame ta, idan jurinta miskilanci ta gamu da wanda ya fi ta miskilanci. Ta juyo kadan, ga dukkan alamu barci mai nauyi ya tafi da shi. Cikin sanda kamar barauniya ta iso gabanshi don ta dauki daya daga cikin wayoyinshi sai caraf! Ya damke hannunta tareda wayar ya kuma bude lumsassun idanunshi sannu a hankali a kanta.
Kunya ta duniya Mairo ta gama jinta. Ashe ba a yi komai ba sai sanda ya fizgota ta fada gaba daya a jikinshi. Ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, fargaba da wani bakon tsoro da ya ziyarce ta duk a lokaci guda.
Jikinta ya soma rawa kamar mazari, amma hakan bai sa ya cikata daga sassaukan rikon da ya yi mata ba. Duk yadda ya so da su hada ido cikin dan sauran hasken fitilar baccin dake dakin amma Mairo ta ki. Runtse idon ta shiga yi da karfi. Wani sabon Son mijinta AMIRU da kaunarsa ne farat daya suke tsirgawa a zuciyarta. Wadanda bazata iya tantance tun tsahon wane lokaci hakan ya soma ginuwa a zuciyarta ba. Yana danne wancan feeling din mai karfi da dukkan tasirin sa, wanda zuciyarta ta dade tana kallon Amiru dasu. Tareda gina mafarkanta da shi a kansa.
Ya dago fuskarta daga kirjinsa, a wannan lokacin ya yi nasarar hango cikin kwayar idanunta, cikin murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya ce
"Sata ko Mairo?"
Ta ce
"A'a, ina so in kira Anti Dina ne, kuma na fada maka ai ba ka ba ni ba".
Ya ce
"Ni ban kai kararki wajen Anti Dinan ba, sai ke za ki kai karata?"
Kamshin 'mouth fresh' dinshi na fizgarta, yana sanya mata rashin kuzari ta ce,
"Me ka yi min da zan kai kararka, kuma nima me na yi maka da zaka kai karata?"
Ya ce,
"Kin yi min laifuffuka da yawa Mairo, wadanda idan na fadawa Anti Dina sai ta zane ki wallahi".
"Dame-dame ne laifuffukan nawa?"
"Ai ba ki ma sansu ba?"
"Da na sani bazan tambaye ka ba".
"To sunkuyo nan na fada miki".


"Kinga na farko ba kya gaishe ni da safe, sannan ba kya zuwa dakina taya ni kwana, sai dai ni na biyo ki dakinki. Sannan idan na biyo ki ba kya hada makwanci da ni, sai ki bar ni a kasa ki dare gadonki. Haka Dinan ta fada miki tana yi wa Habibu? Ko ba ki ga har kaya ita ta ke saka mishi ba? Amma ke bana jin ko inda nake wanka kin sani a gidan nan ko don har yanzu ba kya sona?"
Taji zafi a ranta da kalamansa. Da zai taimake ta da ya daina zancen rashin so a tsakaninsu. Ta ce
"Maganar ina sonka ko bana sonka, tunda mun riga mun kasance cikin inuwar AURE, to bata taso ba, bare kuma ni wallahi ban taba jin kiyayyarka a raina ba. Ko wancan lokacin da na fada, na fada ne kawai don ban amince da irin son da zuciyata ta ke yi maka ba".
Ya lumshe ido a hankali, tare da sake yi mata muhalli cikin ni'imtaccen kirjinshi mai cike da gargasa.
Yace “wane iri ne shi wancan son?” Ta dan rufe ido kafin tace “irin na shirme!”.
“Wane irin so ne irin na shirme?”
Amiru ya tambaya cikin mamaki.
Mutsu-mutsun kwacewa ta hau yi, ko zai kashe ta bazata iya yi masa wannan bayanin ba.
Sako riko ta yayi da karfin da yafi na dazu, ya juyo ta sannan ya sa hannu ya dago habarta. Yana iya ganin kyallin dake cikin idanunta wadanda ke cike taf! Da soyayyar data mamaye su. Soyayya mai cike da kauna mara algus or material attachement. Zaiyi rantsuwa bai taba ganin wannan yanayin cikin kwayar idanunta ba, wani yanayi da yake matukar jira, yake kuma da yakinin zai iya cigaba da jiran zuwansa cikin idanun Mairo har nan gaba da shekaru goma kafin ya yarda ya hada shimfida da ita.
"To yanzu fa? Mairo! Mairo yanzun kina sona?"
Amiru ya tambaya, da wata murya tamkar ba tashi ba.
Sai ta yi murmushi, irin wanda bai taba gani bisa siraran labbanta ba.


Wannan kadai ya tabbatar mishi da cewa, ya gama mallakar soyayyar Mairon, saura da me? A take shi ma ya soma mallaka mata ta shi. Cikin wani irin salo mai ban mamaki da Mairo ba ta taba tunanin akwai irin wannan soyayyar a duniya ba. Koda a duniyar karance-karancen novels dinta kuwa.
Su Hajiya Mairo, tun ana dauriya, ana cijewa, cikin bin shawarwarin uwardakin ta Dina, har lissafin ya soma kwace mata......aka kai ga gejin kiran Anti Dinah, Baffa, da Yaya Habibu su zo su kawo taimako. Yau har Ladidi da Nabilah sun sha kira don tana ganin karshen rayuwarta yazo! Shi kanshi Amirun ya rasa control din kansa, ta yadda har zai yi tunanin cewa Mairon virgin ce, ba kamar matarshi ba. Tunda yake a rayuwarsa bai san akwai Hurul-eeni tun a duniya ba. Bai san aure iri-iri ne kuma suna ya tara ba. Don haka bai farga da aika-aikar da ya yi ba, sai da ya duba ya ga Mairon ta sume mishi.
Ba ita ta dawo hayyacinta ba sai da sanyin ruwan 'ragolis' ya ratsa kwanyarta, da sauran sassan jikinta. Ya rungume ta sosai, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, cikin shauki ya ce
"Mairo kar ki gudu ki barni! Mairo ki ci gaba da zama da ni ko ba kya sona, ni ina sonki da dukkan ruhi na! Ki rike naki son ko bazaki bani ba! Zan zamo ‘impotent' a duk ranar da kika guje ni, ko kika juya min baya...!"


***










MAIRO A GIDAN AURENTA!




Zuwa yanzu, wato watanni biyu a gaba, Mairo an zama manyan mata, an iya komai na kula da miji. Ta iya daukewa mijinta lalurar da mata hudu ba zasu iya dauke masa ba. Soyayya, kauna da shakuwa ke kara kamari tsakaninta da mijinta. Ga kauna da kulawa da ta ke samu daga surukanta kamar su suka tsugunna suka haife ta.
Cikin wannan dan tsukin Amirun ba ya samun zama sosai, sabida shirye-shiryen bude bankinsu da suke yi shi da Habibu. Shi Habibun ke tafiyar musu da komi ta can, shi kuma yake tafiyar da komi ta nan.
Gaba daya ya mance da wata Harrit da ya sanya lambarta a (divert call), sannan a ka'idarshi bai daukar wayar da bai san lambar ba. Al'amuran gabanshi kadai sun ishe shi, sannan Mairon shi kadai ya sanya a gaba, a yadda yake ji cikin ransa, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.


A wannan daren na ranar talata shiri yake don tashi zuwa Washington a washegari, domin mika takardar yin retire daga aiki a World Bank, a gefe guda kuma ga Mairo ta dira shagwaba ita dai sai ya tafi da ita ta ga Yaya Habibu da Dina.
Ya kamo hannunta ya ce
"rigimarki yawa gare ta Mairo, na fada miki Washington za ni ba Michigan ba. Kuma ba dadewa zan yi ba, karkari na yi sati biyu. Ina duba yiwuwar komawarki makaranta, idan komi ya dai-daita gidan Habibun zan barki ki zauna gaba daya".
Ai da jin haka ta yi tsalle ta dane shi cikin nuna farin cikinta a fili. Inda shi kuma ya juyo ta gareshi ya bi ta da deep-kisses tsakiyar bakinta, wuyanta, da idanunta; mai nuni da cewa, lallai zai yi kewarta.
Ita da Sabah suka yi mishi rakiya filin jirgi a asubahin washegari. A gaban Sabah ya rungume ta yana fada mata wasu irin kalamai masu rikirkita kwakwalwa cikin kunnuwanta. Sabah sai ta sa mayafinta ta kare fuskarta tana murmushi. A zuciyarta kuwa addu'a ta ke, Allah Ya ba ta miji irin Yayanta.
Yana sauka a Washington ya tarar tuni Raymond da Franklyn suna jiran isowarshi, don haka suka zubo jakarshi a bayan mota suka nufo cikin gari.
Kai tsaye gidanshi suka nufa suna tafe suna yi mishi bayanin muhimman abubuwan da suka gabatar (in his absence), ci gaban da aka samu da shortcomings din duk da ya biyo baya. Suna sanyo hancin motarsu a farfajiyar gidan ya ga bakuwar mota kirar (Ferrari 458) kusa da ta Harrit.
Bai kawo komi a ranshi ba, don ya yi zaton baki ne Harrit din ta yi kasancewarta ma'abociyar hulda da jama'a, don haka ya yi amfani da mukullinshi ya bude kofar. Su Raymond suna daga waje suna magana. Ya ratsa falon babu kowa, ita ba musulma ba, balle ya yi mata sallama don haka kai tsaye ya sanya kai 'bed-room' dinsu. Idanunshi kuwa suka yi kyakkyawan gani.
Harrit ce kwance tare da wani bature dan uwanta haihuwar uwarsu-ubansu cikin halin turmi da tabarya.
Ya tsaya kawai yana kallon tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarshi ba, wanda a take ya tabbatar ba komi ba ne, hakkin iyaye ne da son zuciya suka jawo mishi (al'ummar musulmi irin Amiru sai a yi hattara, kafiri har gobe kafiri ne, duk soyayyarsa gareka kuwa, kuma babu soyayya ta hakika tsakaninshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login