Showing 24001 words to 27000 words out of 77288 words

Chapter 9 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci ko matsatsi na rayuwa ba".
-mai son ki.


Ta karanta ya fi cikin 'ya'yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba. Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da zuciyarta ba.


To haka washegari, mai 'logo' na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.


"........ Some one misses you!".


Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu, wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.


Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce "Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina a tashe ya ke".
Ya ce "Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don't want to lose AMEERU. (bana so in rasa Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo".
Dina ta kidime "Lafiya? Me ya faru da Amirun?"
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce.
7/29/21, 11:15 PM - Kawata: 666667778888








Ranar Litinin. Tun asuba da Mairo ta tashi ta yi sallah ba ta koma bacci ba, ruwa ta taro a famfo ta yi wanka ta shafa mai, ta sanya uniform dinta ta shirya tsaf ta zauna jiran fitowar Baffa.
Ba shi ya fito ba sai karfe takwas dai-dai na safe. Ya yane labulen dakin su Mairo cikin sallama ya ce "Ya ya kin gama kimtsawa mu tafi?"
Ta ce "Na gama Baffa tun dazu".
Ya sa hannu ya daukar mata katuwar jakar, ita kuma ta dauki karamar suka fito. Ta leka dakin Habiba da Hajara ta yi musu sallama suka amsa duk cikin yanayi daya, wato a yatsine, don ita Habiba ba ta so wannan komawa makarantan na Mairo ba, so ta ke abar musu ita tai ta yi musu bauta, don Ladidi ko za a kashe ta ba zata yi musu bautar da Mairo ta yi musu ba cikin kwanaki ukun da ta yi tare da su ba.
Shi kuwa Baffa Allah-Allah yake ya maida Mairo makaranta don ta huta da kwarzabar su. Idan ya tuno daga wannan zangon Mairo ta gama makaranta hankalinsa tashi ya ke. Ya soma tunanin da ta gama makaranta idan ta samu masoyi zai ganganda ya yi mata aure, idan ma ba ta samu ba ko cikin mutanensa ya nemi wani wanda ya yaba da hankalinsa ya ba shi ita, shi dai ta bar gaban su Habiba, sai hankalinshi ya kwanta.
Ya bude boot ya zuba kayan, ita ma ta sanya jakar hannunta. Ya bude kofar wajen mai zaman banza ta shiga ta zauna, sannan ya zagaya shi ma ya shiga ya tayar da motar suka mika kan titi.
Karfe goma dai-dai suna cikin Minjibir, duk wasu shige da fice na dawowar dalibi Mairo da Baffanta sun kammala cikin dan lokaci. Suka yi sallama da Baffan ya kada kan motarshi ya tafi, ita kuma ta nufi ajinsu.


Tun daga nesa ta hango Uncle yana rubutu akan allo, wani irin dadi da farin ciki suka ziyarci zuciyarta. Ji ta yi tamkar Baba da Innanta ne suka dawo.
Daga can mazauninsu Nabilah ta hango ta, ta kuwa sheko da gudu ta rungume ta, ba tare da la'akari da cewa akwai malami a cikin ajinsu ba. Ya dakatar da rubutun ya juyo, juyowar da ta ke nufin al'amura da dama a gare su a wannan ranar.
Mairo ba ta iya ta hada ido da Uncle ba saboda matsanancin kwarjinin da ya yi mata a yau, shi kuma kokari yake ya kalli cikin kwayar idanunta cike da tuhuma da tarin laifuffukanta gareshi. Ya mannawa Nabilah harara ba shiri ta koma cikin nutsuwarta, kai tsaye Mairo ta wuce wurin zamansu shi kuma ya cigaba da bada darasi cikin wani sabon kuzari da nishadi gami da wani karfin gwiwa da ya same shi duk a lokaci daya.
Aka fita break amma ita da Nabilah ba su fita ba, sun nutsa hirar bayan rabo. Nabilah ta ce "Yaya Inna? Kusan kullum sai na yi mafarkinku Mairo, tun bayan rasuwar Baba nake jin tausayin Inna, ina gayawa Mamana da Daddy. Dama idan kika yi sati baki dawo makaranta ba zan bi sawunki ko makaranta ta yi min izini ko ba ta yi ba".
Idanun Mairo suka kawo kwallah, ta ce "Innar ma na rasata Nabilah ... Ba ni da kowa a yanzu sai Baffana sai Allah da Ya halicce ni. Na zama marainiya Nabilah, ba uwa ba uba…...."Hawaye suka kece mata, ta dukar da kanta cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka.
Nabilah ma sai ta sa kuka, tana tuna Inna da kirkin da ta yi mata. Sun dauki mintuna suna kuka, kamar wasu kananan yara. Ba su san yaushe Uncle ya shigo ba, har ya tsaya a kansu. Ya sanya hannu ya kwankwasa desk din da suke sunkuye. Duk hirarrakin da suke yi ya ji su, ya rasa inda zai sa kansa da tausayin Mairo. Ba kankanin abu ne ke sanya Junaidu kuka ba, amma a yau ya ce Maryama I cannot control my tears……….."Suka dago ido suka dube shi cikin ido, Mairo da Junaid ke kallon juna, irin kallon da ba su taba yi a rayuwarsu ba. Wani muhimmin al'amari na samun muhalli cikin kwayar idanunsu. Nabilah sai ta bude baki, galala! Tana kallonsu, tana cewa cikin ranta "A yau dai, dole Mairo ta yarda Uncle Junaid yana sonta……..".
Mairo kwana ta yi ba ta yi barci ba, baya ga dacin mutuwar iyayenta da ya dawo mata sabo fil, sai kuma SOYAYYAR Junaid da ke dawainiyya da zuciyarta, amma ta kasa ganewa, sabida kuruciya da wauta. Ga dai zahiri al'amarin ya sauya, amma ta sanya kafa tana takewa da gan-gan.
A ganinta mai Junaid zai ci da 'yar kauye kamarta? Sai dai ta ce zuciyarta na yaudararta, tunda shi din bai furta ba. To ita ma ba zata taba yarda da tunaninta ba.
Shirye-shiryen jarrabawar fita ya kankama. A wannan dan tsukin Uncle ya takura musu matuka da karatu, musamman akan lissafi (mathematics) da Ingilishi (English). Burinsa kawai Mairo ta lashe dukkan takardunta. Ta gama makaranta with flying colours', ta samu gurbi a babbar makaranta, ta yi karatun da zata dogara da kanta cikin kowanne hali. Idan hakan ta faru to shi kam Alhamdu lillahi... Ya sauke nauyin alkawarin da ya daukar wa Malam Bedi, sannan ne yake jin zai fallasa mata soyayyar shi, don haka wannan ba lokaci ne da ya dace ya fallasa asirtacciyar soyayyarsa ga Mairo ba. Ya manta masu iya magana sun ce "A BARI YA HUCE... Shi ke kawo da rabon wani.
Ba ta da abin da zata ce da Uncle Junaidu sai godiya, domin da taimakonshi da kwarin gwiwar da ta ke samu daga gare shi ne ta zana jarrabawar Jamb, Waec da Neco cikin kwanciyar hankali, tamkar ba jarrabawa ta zana ba, sabida yadda komi ya zo mata da sauki. Sai dai kuma wannan gama jarrabawar na nufin al'amura da dama cikin rayuwarta. Rabuwa da UNCLE JUNAIDU? Wani muhimmin al'amari ne da ke cinta a zuci, da zuciyar ba zata iya jurewa ba, da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Ina ma Uncle zai ce yana sonta ya aure ta? Ya rabata da rayuwar maraicin da zata je ta fada a gidan Baffanta?
Hawaye suka ciko idanunta. A karo na farko da zuciyarta ta kawo shawarar ta nemi Uncle ta roke shi ya aureta, ya tserar da ita daga rayuwar kunci da zata je ta fada, ko da ba ya sonta.


Ta shiga neman Uncle cikin makaranta, lungu-lungu, sako-sako, abun kamar wasa ko mai kama da Uncle babu. Tuni dalibai sun soma tafiya, don duk wacce ta fito daga last paper daukar kayanta ta ke ta tafi, bayan anyi sallama da kawaye da abokan arziki. Tana tsaye nan cikin tashin hankali Nabilah ta iskota,
"Ga can Baffanki ya zo daukarki yana ta aike a nemo mishi ke".
Hankalinta ya kara tashi da ta tabbatar a yau zata tafi ne, tafiya ta har abada daga Minjibir, ba tare da ta yi sallama da Uncle ba, wani mutum daga cikin mutane biyu da ke ba ta farin ciki da buri (hope) a cikin rayuwarta.
Tabbas yau ya sauke nauyin alkawarin da ya yiwa mahaifinta. Ta kammala makaranta cike da kyakkyawan zaton samun nasara. Muhimmin al'amarin da ke dawainiya da zuciyarta akan Uncle, ta ke so ta sauke, amma babu Uncle a cikin Minjibir, babu alamarsa.


Sai ta sa fuskarta cikin tafukanta ta soma shesshekar kuka. Nabilah ta rungume ta suka ci gaba da kukan tare, sai dai ita Nabilah ba ta san hakikanin dalilin kukan Mairo ba.
Ita kuka ta ke na kewa da rabuwa da Maironta, yayin da Mairo ke kuka na tausayawa rayuwarta. Ta kullaci Uncle mummunar kullata, (irin kullatar data yiwa Habibu) ta tuhume shi da YAUDARA da wasa da rayuwarta. Ba tasan inda za ta ganshi ba, ta gaya mishi shi kadai zuciya da ruhinta ke so. Ya taimake ta ya aure ta koda BA YA SONTA. Shi kadai ne namijin da ta ke jin zata iya aure a rayuwarta. Shi kadai ne ta ke jin zai kula da rayuwarta a bayan idon Baba da Inna. Shi kadai ne ta ke kalla ta ji shi kamar Yaya Habibu. Yau shekaru dai-dai har shidda dai-dai da rana daya zuciyarta ba ta taba hutawa da kaunarshi ba.
A da kam ba ta gane ba, amma yanzu ta yarda ta amince da mahaukaciyar soyayyar da ta ke yi wa Uncle Junaidu. A yau da ta yanke shawarar fada masa don su tallafi rayuwar juna ta neme shi ta rasa.


*****
K
arfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta litinin suka iso gida, inda direban su Nabilah da ke biye da su don ya ga gidan ya juya da Nabilah, da alkawarin bayan sati zata zo su je da Mairo gidansu, don ba ta taba zuwa ba.
Tun daga soro Mairo ta soma cin karo da kwanuka, da busasshiyar miyar kuka a jiki. Gabanta ya ci gaba da faduwa don ta tabbatar ita da rayuwar farin ciki, sun yi hannun riga ke nan. Ta fado cikin wata sabuwar rayuwa ta MARAICI, wadda Innarta ta ke jiye mata. Ta tabbata Inna tasan rashin kirki na matan Alhaji Abbas shi yasa a lokacin rayuwarta ta ki yarda ta zauna da su. Mai za a yi da hali irin na Hajara da Habiba? Sai Allah Ya kyauta.
Karatu dai an kare shi, yanzu zama ne za a yi na din-din-din. Kowacce waina za a toya? To bari mu bi Mairo da iyayen rikon nata mu gani.
Habiba na daki lokacin da suka shiga, sai Hajara ce a tsakar gida tana tankaden garin tuwo. Baffa ne a gaba rike da jakar mairo, ita kuma ta biyo bayansa rike da wata jakar.
Hajara ta amsa musu sallama fuskarta ba yabo ba fallasa. Bayan haka ba ta kara tofawa ba. Baffa cike da takaici ya ce "Hajara baki ga 'yar taki ba ne, ko sannu da zuwa babu? Ai ba a haka".
Ta cira kai ta jefe shi da harara, "Cewa za ka yi tashi ki yi tsalle 'yar gaban goshina ta dawo, ba sannu da zuwa ba".
Jin cece-kucensu sai Habiba ta leko. Ita kam tayi fara'a ta ce "Ah! 'Yan makaranta an dawo? Lale-lale". Ko ba komai ta samu jakar da zata yi ta yi mata bauta.


A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko'ina kayan Ladidi ne a watse, nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta ga inda zata dosana duwawunta ba a dakin, don haka ta aje jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar.
Ta gabatar da sallar azahar da la'asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur'aninta ta soma tilawa. Ko aya biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma'idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe Alkur'anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta nuna mata tulin wanke-wanke ta ce "Kina ganin aiki ya kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan cikinsu zan kwashe tuwon dare".
Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa "Ki dinga iza min wutar nan, sallah zan yi".
Ta ce "To".
Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce "Cika min randar can da ruwa, ga kuma tsummokaraina ba yawa, ki dauraye min su".
Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce "To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken, ta ce tuwo zata kwashe".
Habiba ta ce "Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki fuska?"
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce "Au, bar min wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama mini".
Suka soma bala'i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu.
Baffa ya shigo yana "Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota ana jiyo ku, asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na matan aure ba".
Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce "Habiba waye zai yi miki wannan wankin?"
Ta yi shiru, ya ce "Da ke nake magana fa".
Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce "Au... to, kana nufin haka zamu aje gansamemiyar budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a katifa?"
Ya ce "Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?"
Cikin rashin gaskiya ta ce "Bai zo ba".
Ya ce "To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi miki, ko ki tura 'ya'yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba. Mairo ba baiwar uwar kowa ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba. Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke Ladidi!"
Ya kwala mata kira, ta fito a razane, "Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in kwashe miki hakora yanzun nan".
Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare.


Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al'amarinta, ya sayo mata matsananciyar kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah, daga su har 'ya'yansu, su suyi mata, 'ya'yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo wuka ta mutu kowa ya huta da bala'in Baffa a kanta.
Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri, sai karan hanci da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata taba ganin mutane marasa imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba.
Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan mutum ba a wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu biyayya ba iyakar iyawarta.


Wata mota kirar Kia-Rio ta yi fakin a kofar gidan Alhaji Abbas, misalin karfe goma dai-dai na safe. Lokacin Alhajin bai kai ga fita kasuwa ba. Nabilah Bebeji, ta fito daga mazaunin direba tana duba agogon hannunta, ta doshi kofar gidan Alhaji Abbas, tana mai addu'ar Allah dai Ya sa Baffan Mairo bai fita ba.
Ta yi sallama a tsakar gidan, Habiba ta amsa yayin da ta bi ta da kallon mamaki. Sanye ta ke da atamfa mai karshen tsada shudiya ta karkata dauri mai ban sha'awa kamar nadin inji, a hannunta 'yar matsakaiciyar jaka ce, samfarin Louis Buittion da takalminta marar tudun dunduniya. In ban da kamshin turaren Rasasi (blue-royale) ba abin da ke tashi a jikinta, ta yane jikinta da gyale kalar atamfarta, daure a hannunta agogo ne shudi samfurin polo.
Jiki na rawa Habiba ta dauko sabuwar tabarma ta shimfida mata, ta tsugunna har kasa ta gaishe ta, ta gaya mata ta zo wajen Mairo ne. A lokacin Mairon tana bayi tana wanka, cikin bakin-ciki karara Habiba ta yi mata nuni da dakin su Mairo kamar ba ita ce mai yi mata fara'ar da ta ke yi mata ba.
Dakin tsaf ya ke, da yake Mairo ba ta wasa da tsaftarsa, sau dubu Ladidi zata bata, sau dubu zata gyara.
Ta samu gefen katifar Mairo ta zauna, ta dauki wani littafi na Mairon da Mairon ta aje, da alama shi ta ke karantawa kamin ta shiga wankan na Dynasties the Ashtons (Condition of marriage), ta ce "Maryama na nan da karance-karancenta".
Dai-dai lokacin da Mairon ta shigo, kanta na yararin ruwa domin wankan sallah ta yi, zata soma sallah. Ta harari Nabilah ta ce, "karfe taran ke nan?"
Ta yi murmushi ta ce "Go-slow ya tare ni,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login