Showing 42001 words to 45000 words out of 77288 words

Chapter 15 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

abubuwan da ta zana ai duk haka suke, zata je neman auren Uncle Junaid ne? Ko haka zata kare da zaman jiran tsammanin warabbuka?
Zata iya ci gaba da zaman jiran ranar da Junaid zai neme ta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya ba ta uzurin da ya hana shi yin hakan har nan gaba da abada. Amma ba zata iya jure bukatar gangar jikinta da zuciyarta ba, kamar kowanne lafiyayyen dan Adam. Idan haka ne tana bukatar aure, domin kare kanta daga ZINA, da sauran ayyukan ALFASHA, cikar mutunci a idon duniya, da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.


Wayarta da ke karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text). Cike da mamakin wanda ya yo mata sako a dai-dai wannan lokacin, karfe biyu na sulusin dare agogonsu na can. Ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna, ba tasan lambar ba, don bakuwa ce. Ga abin da ke rubuce.


'... When life change, and we go our separate ways, U will still be in my heart till my dying days... My world has never meet a person like U……...!
(A yayin da rayuwa ta canza , ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu), za ki cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin ki ba).


Haka ta sa sakon a gaba, tana ta karantawa. Har aka yi kiran assalatu. Don ta tabbatar ba kowa ba ne, Amiru ne, duk da bai sa suna ba. Allah sarki ko YA HUCE ne? Ta fada a fili. Tana so ta ba shi amsa, ba ta san me zata ce masa ba.


Da safe ta ke nunawa Dina, ta karanta, ta yi dan miskilin murmushinnan nata, ta ce.
"Ke kuma kika ce mene?"
Ta zumburi baki. "Ni ko kulasa ma na yi?"
Ta yi dariya, ta na kwaikwayon ‘yar muryar ta tace, "Haba Mairo? Yi hakuri ki dan kula sa. Kinga shi ya yi fushin amma ya sauko, saboda ya gane ba son sa ne ba kya yi ba, kawai ke mai aminta amana da alkawari ce!".
Ta yi dariya har kumatun ya lotsa, Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.. Ta ce "To me zan rubuta?"
"Ki ce kawai ya zo yayi joining dinmu break fast…..".
Ta rubuta ta tura, amsar da ya ba ta ta sata yin murmushi. Domin ya ambato rabin-ranta (uncle Junaidu).


"...A'ah kirawo Junaid….".


"He is far-away...!!"(Amsar Mairo )


"And am not closer too... am far-away either, and I'll not come back...!!! On my way to Detroit Metro…...".


Hankalin Mairo yayi mummunan tashi, da sauri ta jefar da wayar, da gudu ta yi daki ta dauko mukullinta, Dina na kira amma ba ta juyo ba, cikin rishin kuka ta ce.


"Shi ma zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min soyayyarsu. Bana son in samu wannan heart break (karyewar zuciyar) a karo na biyu".


Dina ta ce "Bishi Mairo, shi ne ZABIN ALLAH!!"


Gudu ta ke shararawa akan titin da zai kai ta airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC Terrain. Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke, Wannan ita ce soyayyah! Da gaske Dina ta ke, Amiru shine zabin Allah!! Da gaske Dina ta ke da ta ce ta kama mai sonta, ta rabu da JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA. Ta karbi 'Soyayyah' a hankali zata rikide ta zama 'Kauna'. To gashi soyayyar ma zata tafi ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata…….…


Koda ta iso airport din ko kulle motar ba ta yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta sheka cikin reception tana dube-dube, babu Amiru, babu ko mai kama da AMIRU. Ta karasa terminal bayan ta hankade ma'aikacin da ke kokarin hanata shiga. Dai-dai sanda aka rufe kofar jirgin (Lufthansa), wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dumbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi. Kafin ya dai-daita sosai, a sararin samaniya.


Mairo ta durkushe a nan tana kuka, kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin da ta samu cikin Michigan wanda Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne don ya rusa komai . Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar Uncle Junaidun? Meyasa ita ba ta da sa’a ko kankani a soyayya ???.
Ji ta yi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma, an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. Don haka ta dago idanunta jage-jage da hawaye... don ganin ko wane ne wannan???


Masha Allahu La Kuwwata Illa Billah!
Mu biyo Mairo da Amiru da Junaidunta a littafi na uku. Kafin nan ina sauraron ra'ayoyinku kan jaruman namu, AMIRUN ko JUNAIDUN???
Maman SAFAH da MARWA ce.


07030137870
8/3/21, 12:25 PM - Kawata: 444
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, "Mairo?"
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
"Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
"Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin.
Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen kayan ma'ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka'ida da dokar duk da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka'ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
"Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin 'yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata.......”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
"Wallahi bazan je ofishin 'yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba".
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.


Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara.
"Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?"
Cikin kuka ta ce
"Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba".
Ya ce "To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?"


Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya kuta ya ce
"Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki?
Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi, sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya ba garin ba.
To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike so.
Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA... akan yi UWAR DAKI...? To ba da abokina ba!
Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi.
Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa. Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu ke babu tukin mota. To kin ji".


Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din suit' dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba.


Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina.
"Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?"
Dina ta yi shiru, ya ce "Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta magana ni kadai?"
Ta ce "To me ya faru?"
"Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a'ah?
Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?"
Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce
"Am... Eh, ai sako zata kai wa Amirun".
A fusace ya ce
"Sakon me?"
Ta ce "Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu".
Ya yi dogon tsaki, ji kake 'tsiiittt!' Ya maida kallonshi ga Mairo
"Ba ni wayarki".
Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin.


Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri.
Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce "Kin same shi?"
Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo.
Dina ta sa yatsunta tana share mata, "Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah. Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba".


Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta.


***
A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk 'yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani. Maryam Muhammad Bedi, ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin ko da dar a zuciyarta ba.
Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud's stages of psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga phallic-stage... Anal stage... da 'yan uwansu.
Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!! Habibu da ke cikin 'yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka.
Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace... Malam Muhammad Bedi, zai dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al'umma.


Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan ajinsu don yayi supervising hakan.
Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo.
"Mairo 'yan makaranta......Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu".
Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce.
"Zo zauna, mota zan sake miki".


Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa "Gaya min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai.


Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al'amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi sati daya, me kike so in kawo miki?
Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da sauransu. Ke kuma fa?"
Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, "Ladidi nake son gani".
Ya ce
"Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta".
Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta.
Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman sociology. Habibu na addu'ar Allah Ya sa ba sociology'n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba. Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba.


Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo ga Ladidi. Ita da Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da ya kare, sannan suka nufi wani kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya, ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida.


Duk a kokarinsa na son farantawa 'yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina, ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba.
Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu.
Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba ta damu ba, ta ci gaba da ayyukan gabanta.
Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma an sanar da ita wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta samu Habib ba.
Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba ta shiga. Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba.
A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da labarin Habibu? Sun kasa samunshi a waya.


Baffa ya yi gyaran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login