Showing 60001 words to 63000 words out of 77288 words

Chapter 21 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

ba kya so".
Ta mika mishi hannu, ta ce.
"To ba ni takardun".
Ya yi wuki-wuki da ido, can ya ce.
"Habibun ne ba ya nan, idan ya dawo za mu zauna a ware a kawo miki……..".
Sai hawaye sharr-sharr wasu na korar wasu, domin gani yake Hajiya ta gama tozarta shi, a duk ranar da ya doshi Habibun da wannan zancen. Domin Habibun zai yi zargin abubuwa da dama, ciki kuwa har da tunanin ko Amirun na zarginshi da cin amana ne, ba zai taba kawowa ranshi Hajiya ce ta sa shi ba sabida yadda ta dauke shi kamar dan cikinta, shi ma yake daraajjata kamar mahaifiyarsa.
Hajiya ta kama baki, tana cewa.
"Yanzu sabida ina so na rabaka da abin da zai cuce ka, shi ne za ka sanya ni a gaba kana yi min kuka?"
Ya dago sosai yana dubanta da idanunshi da suka kada suka yi jawur. Muryarshi abin tausayi ya ce.
"Hajiya, Habibun ne zai cuce ni?"
Ta girgiza kai.
"A'ah, ba zai cuce ka ba. Ni uwarka ni ce zan cuce ka. Habibu sai ya je kauye ya biya malamansa. Tashi ka je, na yafewa Habibu da kanwarshi Mairo kai, idan har ba zaka kawo min takardun komi na dukiyarka ba. Kuma zan maka Habibu a kotu sai ya ba ni dukiyar da na!"


Zuciyarshi ta bushe da etsoro da al'ajabi. Ya ce, "Hajiya me ya yi zafi da za ki kai Habibu kotu? Ki kara min alfarmar kwana biyu. Na yi alkawarin zan cika umarninki ko da hakan shi ne aiki na karshe da zan gabatar a rayuwata".
Fitowa ya yi zuciyarshi na suya, ya zaburi mota bai tsaya a ko'ina ba sai a kofar gidan Habibu.
A lokacin Habibu na shirin shiga mota zai fita, shi kuma yana danno hancin motarsa (Camero, 2 door) cikin 'gate' din Habibun. Don haka ya fasa shiga motar ya jirashi har ya karaso ya fito daga motar.ŕ
Ba karamin faduwar gaba ce ta samu Habibun ba ganin irin halin da aminin nashi ke ciki. Suka rankaya suka koma cikin gidan. Dina ba ta nan, ta je Malaysia ita da yara, duba jikin mahaifinta da ba shi da lafiya.
Habibu ya isa ga firij, ya dauko mishi gwangwanin 'coke' ya bincire hancin ya mika mishi ba tare da sun gaisa ba. Ya karba ya yi kurba daya, amma ya kasa wucewa a makoshinsa. Dole ya furzar da na bakinshi idanunshi sun kara kadawa sun hargitse.
Habibu ya zauna a gefenshi, ya ce
"Be a man, plz! idan kana raye ba abin da ba zaka gani ba".
Ya rausayar da kai cikin amincewa da kalaman Habibun. Ya ce
"Alfarmarka nake nema, sai dai bana son ka tambaye ni dalilina, na yin hakan".
"Ba zan tambaye ka ba Amiru. Fada min komi tsaurinta".
"So nake na janye komi nawa daga cikin 'Habib Bank!!".


Habibu ya yi shiru, domin Amiru ke da kaso 60% wanda hakan ke nufin durkushewar bankin da ya faro da nasara cikin shekaru biyu kacal da kafuwarshi, wanda ke nufin shi kadai (Habibun) ba zai iya 'running' bankin ba.
Ya tabbatar makiya sun shigo cikin al'amarinsu, amma bai ga laèèifin Amirun ba, wanda da gani kasan tursasa zuciyarshi yakeyi, wajen furta kalaminshi.
Ya ce "Idan don wannan ne, ai babu damuwa Amiru. Idan har hakan zai samar maka kwanciyar hankali, ka ba ni kwana goma, insha Allahu komai naka zai dawo hannunka. Sai dai ina so ka samu lauya, wani daban, ba Dina lauyar bankinmu ba".
Ya ce
"Ni ba ni da wani lauya".
Habibu ya ce
"Dole sai ka nemo".
Ya juyar da kai yana kwararar da hawaye, ya ce
"Daga yau ba zan kara neman kudi ba, tunda su din fitina ne. Ta yadda har wasu suke ganin su din (kudi) sun fi mutumci da amana, Ya Allah Ka tsiyata ni……….."
A gaggauce Habibu ya toshe masa baki.
"Kana hauka ne?
Kada 'frustration' (bacin rai) ya sanyaka fita daga imaninka. Ka je ka samo lauya, mu yi abin da zai kwantar maka da hankali".
"Ni na ce da kai hakan kwanciyar hankalina ne?"
"Ba ka ce ba, don haka abar kazar cikin gashinta ba sai an fiffigeta ba".
Cikin satin Habibu, tare da taimakon Barrister Dalha wani abokin aikin Dina daya daga cikin lauyoyin 'CBN' da Barrister Mujahid lauyan 'starling' sun hattama komi na dukiyar Amiru, ta koma hannunshi da sunanshi da sanya hannunshi.
Ya kwashi takardu cikin 'briefcase' ya yi sallama a dakin Hajiya. Kallo daya ta yi mishi ta ga yadda ya zabge, ya yi zuru-zuru sai karan hancin da idandanun kadai, amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, da dai ta kyale Habibu da kanwarshi su yi galaba a kanta. Tunda sanda ta ke nakudar abinta bayan rainonshi cikin mahaifarta, har wata tara da dawainiyarshi zuwa girmanshi, ai ba su zo sun tayata ba.
Don haka ta kudure sun daina cin arzikin Amiru, kowa ya ci gashin kansa.
Ya zauna a kujerar da ke fuskantarta, kwakwalwarshi na juyawa. Ya mika mata 'briefcase' ba tare da ya iya hada ido da ita ba.


Ta bude ta zaro takardun ciki ta sanya 'medicated glass' dinta tana dubawa daya bayan daya. Ita kanta ta razana da ganin abin da Amirun ya mallaka a 'yan kananan shekarunshi.
Bayan ta gamsu da ingancinsu, ta maida su inda suke tana murmushi, ta ce.
"To ko kai fa?
Ba ga shi ba yanzu sai yasan zafin nema ba ya tashi daga cima-zaune? Yanzu wane kasuwanci zaka soma da wadannan din?"
Ya kalle ta kawai bai yi magana ba. Ta dauka bai ji ba ne, don haka ta sake maimaitawa.
Ya ce ba tareda ya dubeta ba,
"Sadakar da su zan yi".
"Au fushi ka yi, sabida ina yi maka gata Amiru?"
Ya ce
"Ya ya za a yi na yi fushi da ke Hajiya? Ina juya su, kin ce in kawo miki. Na kawo miki kuma ki ce me zan yi da su?
Ban iya wani kasuwanci ba, bayan wanda nakeyi, ni ma'aikaci ne. Aikin banki shi ne wanda na iya tsawon shekaru goma.
A yau kin ce na barshi, don kada Habibu ya samu dan wani abu a jikina, wanda bai taka kara ya karya ba. Bayan kin san duniyar cudarni in cudeka ce, kuma shi ma ba matsiyaci ba ne, yana da rufin asirinshi wanda da kadan ne bai kai nawa ba.
Haba Hajiya! Shekarata nawa da Habibu bai cuce nin ba sai yanzu da muka zama daya?"
Hajiya ta ce
"Rabi (half) kuka zama ba daya ba, sallamamme, bawan mace. Tunda ba ka so ka yi zuciya har kana cewa sadakarwa zaka yi, ni ina so, zan yi maka sadakar, amma ba duk ba. Ranar da tsiya ta isheka ka waiwaye su, nima ina da 'account' din da zan adana maka su su hayayyafa ba Habibu ne kadai ya iya juya sisi ya koma kwabo ba".


Duk abin nan da ake Daddy bai sani ba, don shi ba mazauni ba ne, sannan ko da wasa Hajiya ba ta yi gigin sanar da shi abin da ta yi ba, don tasan bazai goyi bayanta ba. Sai su Khalisa da Nina wadda ke aure a Lagos sune 'yan abi yarima a sha kida, duk suka yi ta tsalle.
Nina ta ce
"Mun gama da wannan, saura 'yar kauyen Gurin-Gawa, don Allah Hajiyarmu ki yi mana waje-road da ita".
Hajiya ta ce
"Ku barni da su, duk na ishe su, ko ba ta yi waje ba, ai ta yi zaman boranci idan na aura mishi wadda zata cika min gida da 'ya'ya".
*****÷
8/6/21, 5:15 PM - Kawata: F
An debi watanni biyu kwarara, Hajiya na tarairayar danta don dai ta wanke dattin ta dake idanunshi, tana kuma nuna kulawarta akan Mairo, wadda ita kuma ba ta san tana yi ba, karatunta kawai ta sa a gaba.
An yi bikin su Sabah tun shekarar da ta gabata, bayan sun kare karatunsu. Don haka yanzu sassan Hajiya babu kowa, daga ita sai 'yan aiki. Watakila hakan ne ya sa ta kwallafa ranta ga son ganin 'ya'yan Amirun, tunda sauran jikokinta iyayensu maza ba za su ba ta ba.


Yau da ya shigo gaishe ta da safe, cikin sakin fuska ta amsa. Bayan sun gaisa ta janyo wata dirkekiyar jarka irin wadda ake zuwa da zam-zam daga Saudiyyah din nan, cike ta ke taf da ruwan rubutu bakikirin da shi ta girgiza ta tsiyayo a kofi ta mika mishi.
"Ungo shanye ka ba ni kofin".
Ya ce
"Na mene ne Hajiya?"
"Maganin sammu da tsarin jiki ne, ko ba zaka sha ba? Idan ka shanye shi duk wani makaru da ke jikinka zai karye, don haka shanye ka ba ni kofin".
Bai yi musu ba ya karba ya soma sha a kyankyame, don kam shi Amiru tun fil'azal mutum ne mai kyankyami matuka, ko (spring water) ba kowanne ya ke sha ba.
Tun yana kyankyami har ya zamo masa jiki. Don ka'ida ne kullum ta Allah ya zo gaishe ta, sai ta cika kofi ta ba shi tsawon sati biyu suna hakan. Ya ji ya fara jin wasu sauye-sauye a zuciyarshi akan Mairo, sai dai ko kusa bai alakanta hakan da cewa rubutun da Hajiya ta ke daddaka masa ba ne.
Yau da yamma da ya dawo daga ofishin Daddy inda ya koma zuwa yana taya shi da wasu ayyukan, sabida nauyin Habibu da yake ji ya sanya alakarsu yanzu ta ja baya.
Duk da cewa shi Habibun a nashi bangaren, ya maida komi ba komi ba, amma Amirun gani yake Hajiya ta riga ta gama tozarta shi a idon Habibu, ta yadda har abada ba zasu koma kamar da ba.
Ya yi sallama Hajiya da ke harde cikin kushin tana sauraron labaran Al-Jazeera ta amsa mishi. Ya samu kujera mai fuskantarta ya zauna. Ya dan zamo daga cikin kujerar yana gaishe ta.
Ta amsa mishi da sakakkiyar murya, can kuma ta ce.
"Anya Amiru, rayuwa zata yiwu da hakan? Ace mutum ya yi ta zama, ba ya tunanin samun dan kansa, duk tsararrakinka daga masu 'ya'ya uku sai masu hudu amma kai ba abin da ya dame ka, sabida idonka ya rufe da son matarka. Alhalin kuma ba zata iya ba ka sanyin idanu ba, sai dai a cika maka masai da kashi, to wallahi bazan yarda da wannan ba".
Ya dago idanunshi a kankance ya dubeta.
"Hajiya mun isa mu ba wa kanmu abin da Allah bai ba mu ba ne? Sannan ba ki san matsalar nan daga gare ni take, ko daga gare ta ba? Don haka bai kamata ki dau zafi akan al'amarin ba, don Allah Hajiyata".
Ta ja dogon tsaki tsiiit!
"To ku je asibiti mana? Ko haka za mu yi ta zama cikin jiran gawon shanu? Ai gara a banbance, don a san matakin dauka".
Da wannan tunanin na maganganun Hajiya ya kwana, har ya soma jin kamshin gaskiya a cikinsu. A shekarunshi ya ci ace shi ma ya aje masu yi mishi addu'a. Har ya soma zargin Mairo ko tana amfani da 'contraception'. Tunda dama ai tun farko ba sonshi ta ke yi ba.
Ya yi gaggawar kwabar zuciyarshi daga wannan mummunan zargin da ta darsa mishi. Ya yarda da matarsa 100% (Azzannu zambun, wa lau kana hakkun), sai dai rashin damuwarta akan al'amarin ma ai abin dubawa ne, bokonta kawai ta sa a gaba, da son ganin kwalayen ilimi, tare da son hango kololuwar biro da takarda.


Ta murda kofar ta shigo cikin sallama cikin sassalkar doguwar riga baka sid, kirar Dammam, fararen duwarwatsu na ta walwali a jikinta, sannan ni'imtaccen kamshinta na din-din-din ya doki hancinsa.
A kwance yake 'flat' bisa makeken gadonsu ya lumshe ido kamar mai barci. Har ta zauna gefen kafafunshi ta soma ja mishi yatsu bai juyo ba. Haka nan ya samu kanshi da jin haushinta babu gaira babu dalili. Ta yi kiranshi cikin tattausar murya, amma bai bude idonshi ya dubeta ba.
Karewa ma kara runtse idonshi ya yi, tareda janye kafarshi dake ciin hannunta, don ba ya son ganinta, ba ya son kamshin turarenta.
Ta yi wa kanta kyakkyawan matsugunni a kirjinshi, ji ya yi kamar ta dosana masa wuta. Ya yi azamar angijita ya ce
"Leave me alone, please!"
Cikin mamaki ta ke dubanshi, idanuwanshi sun hargitse kamar ba Amirun nata ba. Ta ja gefe ta zauna jikinta yana rawa, don ko kadan bai taba yi mata magana cikin tsawa irin haka ba, sannan ita a rayuwarta ba ta iya tashin hankali ba.
Zuwa can kuma ya mike ya soma shiri, ya dan juyo a kai-kaice ya kalle ta.
"Ki shirya, asibiti za mu".
Ta yi ta maza cikin sanyi ta ce.
"Waye ba lafiya?"
"Idon matambayi ne".
Abin da ya ce da ita ke nan.
Kamar ta ce, 'to ba zani ba', amma kwarjinin Amirun da kimarshi dake cikin idanunta ya hana. Soyayyar da ta ke mishi wata kaddara ce daga Allah da ita kanta bata san adadin ta ba. Ta yadda ba ta iya fushi da duk abin da ya yi mata. To balle ma bai taba yin ba. Idan haka ne ya dace ta yi mishi uzuri, ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba.


Suna tafe a motar amma ba mai ce da dan uwansa uffan, kowanne abin da yake sakawa a zuciyarsa daban ne da na dan uwansa.
Tunanin Mairo shi ne, shin laifin me ta yi wa Amiru haka da zafi, da har ba zai iya budar baki ya fada mata ba don ta gyara?
Shi kansa Amirun ya rasa laifin da ta yi mishi ya ke ganinta bakikkirin da jin zafinta babu gaira babu dalili. Amma ransa na gaya masa rashin haihuwar tane, yazo wani limit na kasa jurewa. Har suka iso babban asibitin Abuja, kalma daya ba ta hada su ba.
Kai tsaye ofishin Dr. Fredrick suka nufa, Amiru ya ce da shi.
"Doctor mun zo ne yau ka duba mana dalilin rashin haihuwarmu, al'amarin ya fara damuna. Sannan Hajiya ta tada hankalinta, idan ba asibitin nan muka zo ba, ba zata barni na zaun lafiya ba".
Sai a sannan ne Mairo ta cira ido ta dube shi. Yanzu ne ta gano dalilin bacin ranshi. Wato sun fara damuwa da rashin haihuwarta, wanda ita ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Dr. Fredrick ya hada su da Gynaec Doctor da za su gani, wato Dr. Ma'u. Bincike iri-iri Dr. Ma'u ta yi amma ba ta gano wata matsala a tare da Amiru ba. Da ta zo kan Mairo, sakamako ya nuna cewa, ita ce bakin mahaifarta yake a tsuke sosai. Idan har tana son haihuwa, dole sai an yi mata aiki, an bude bakin mahaifar.
Ya roki Dr. Fredrick da Dr. Ma'u lokacin da Mairo ta nufi mota cewa su taimake shi su bar wannan sirrin a tsakaninsu, ba ya son Hajiya ta ji.
Dr. Ma'u ta ce da shi.
"Ai ko ba ka ce ba, amana ce tsakanin likita da 'patient' dinsa, insha Allahu ba za a fada mata ba".
Ya yi godiya ya barsu da alkawarin idan sun dai-daita ranar da za a yi mata aikin za su dawo.


Mairo ta shiga cikin tsananin damuwa. Tashin hankali da rudani. Yadda farat daya Ameeru ya sauya mata. Kamar ba shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai kidimata. Kullum daga fada sai hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko Dina ba ta taba tunanin fadawa ba.
Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da shi dashi ya ke amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa surukarta karfar baka, mai wuyar magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake mawa.
Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura mata da nacin maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke soya zuciyarshi.
Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga damar ba ta zata samu ne.
"Amma Shi Ya ce 'tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba.
Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu muke jiranta".
Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida tsakinta.
"Ni fa babu inda zan je".


Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na wannan lokacin ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE... Gaba daya ya soma tunanin bokon da ya barta tana yi ne ya sanya ta raina shi... Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya kawo mishi ita.


Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce ofis wajen Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci.
Habibu ya ce
"Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba?
Idan ke ba kya son 'ya'yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi miki aikin ba?"
Ta fashe da kuka, ta ce
"Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma yanzu ban san me yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara. Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min mahaifa".
Habibu ya ce
"Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin rayuwar kenan, wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba!".


Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma'u ta yi mata aikin.


***















Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin aikin. Babu ciki ba alamarsa.
Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun 'project' dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta nuna kai tsaye suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato 'lecturing' a jami'ar Abuja.
Mairo ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login