Showing 18001 words to 21000 words out of 77288 words

Chapter 7 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

juna kuri da ido.


Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce "Sannunku da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi asibiti".
Ta ce "Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!"
Ya ce "Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya saukar dashi tare da maganinsa ba".
Ta ce "Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru…….."
Cikin matsananciyar damuwa ya ce "Wane abu ne kike gudu Inna?"
Ta ce
"Zaman Mairo da Iyalan Abbas". Daga haka ta yi shiru.


Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata alhamis da daddare suna kwance ta ce "Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba, da na ce Junaidu YA AURE KI".


Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce "Inna ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani na daban ko ya ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin wannan, sai mutunta juna".
Inna ta yi murmushi ta ce "Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu.
Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan, amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa. To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba?
Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun. Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki……."
Cikin gundura da zancen ta ce "Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne".
Inna ta yi murmushi ta ce "Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina hango inda za a alkinta min ke".
Ta ce (kamar ta yi kuka), "Ni dai don Allah Inna ki bari……..".
Ta ce "Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba".
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce "Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?"
Ta ce "Na bari".


Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin alwala, ta zo gittawa ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga kafafun babu karfi, ta zame ta baya sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke hannunta.
Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta kasa yakice al'amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna ya tabbata gaskiya? Uncle Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa'a zata yi a rayuwarta?
A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka fara game mata jiki.
Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin sura, halayya da kyawawan dabi'u.
Ta kasance ma'abociyar karance-karancen littattafan nobels' na Turanci. Littattafan Shakespear, Wole Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata karanta ba. A duk lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al'amarin jaruman littafin da Uncle da ita kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa cikin ranta, "Kaman Uncle Junaidu".
Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma'abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da matsayin da yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne)
Mutum ne da yasan mene ne 'dressing' wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da da zubin halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan ya shigo, sabida kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara'a amma yana da zucciya, abu kadan sai ya bata mishi rai, haka abu kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta taba ce da Nabilah matar duk da Uncle ya aura ta caba.
Nabilah ta ce "Dalili?"
Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na sociology mai banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar da diya mace a shimfida, kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin da zasu yi masu. Tana jan layi-bayan-layi tana fassarawa Nabilah.
Ta kare tana murmushi, ta ce "Edactly Uncle ko?"
Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta nakalci harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce "Ke dai wallahi shegen karance-karancenki sai ya lalataki. Yanzu ina ke ina littafin 'yan jami'a? Tukunna ma ina kika samo shi?"
Ta yi dariya cikin nishadi ta ce "A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi staff-room na ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke".
Nabilah ta ce "To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce".
Maryam ta ce "Da Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology. (With first-class honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan".
Nabilah ta ce "Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu da Nasara?"
Ta ce "Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta".
Nabilah ta kyabe baki ta ce "Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so".
Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, "Ku gama kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….".
Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu.


To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a ranta "Shin ko dai Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu? Neman tabbacin hakan abu ne mai matukar wahala a kwawalwarta".
Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta ya soma bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa, babu Inna babu alamarta.
Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta ce, "Inna kina ciki ne?"
Shiru babu amsa, ta ce "Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba".
Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata da abinta cikin kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda karfen guga ya makale ya yage. Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita. Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama, maganar motsi kuwa babu shi a tare da su.
Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu, kafarta babu takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama'ar kauye, ma'abota hadin kai da taimakon junansu, nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure Allah Sarki!!
Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama hancin suka rike, daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su.
Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta. Innan da ta rage mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda kanta yake ba.
***




























F
arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an kai ta makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta kuka kamar ranta zai fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, "Wannan ba shi ne karshen rayuwarki ba Mairo. 'Ya'ya nawa ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya rasu, lokacin haihuwata uwata ta rasu, amma gani nan da nawa 'ya'yan goma sha uku. Ina yi miki ta'aziyya Allah Ya jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri".


Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu'a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da uba ba karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya kamar iyayenta? Ina zata je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar da haihuwarsa tai wa iyayensu ba.
Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta dauki loma ta kai bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame hannunta tana sharce wasu dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna addu'a ba.
Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta suturce jikinta ta tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta bude Alkur'ani mai Tsarki ta shiga karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da (du'a'ul mutawaffa) tana addu'ar Ubangiji Ya yi mata masauki da aljannah.
Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta, ta ba wa Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin Gurin-Gawa suka zo suka same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta'aziyyah, sanan Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce amanar da za su sauke.
Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, "Wata kila abin da nake gudu ne dole sai ya faru... Zaman Mairo da iyalan Abbas".
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce "Hakuri za ki yi Mairo, mutuwa riga ce akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure".
Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta tana kuka.
Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin gadon bononta. Ta tattara 'yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo.
Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da 'ya'yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi.
Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa Yakasai ta nan.
Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai.
Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu.
Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce "Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba".
Ta dukar da kai ta ce, "Gurin-Gawa".
Habiba ta kalle ta sosai na 'yan dakikai, nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko'in'kula ta ce
"Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?"
Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce "Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne".
Sai da ta mula ta ce "Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa".
Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar.
Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce "Bude motar ki kwaso kayanki mana ki shiga da su?"
Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce "A'a, mu dai jira Baffan".
Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce "Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne".
A ranta ta ce "Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa".
Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce "Ah! Yau wace rana?"
Ta yi murmushi, ta ce "Ladidi ke nan, kuna lafiya?"
Ta sake kyabe bakin (ga alama al'adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce "Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?"
Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login