Showing 48001 words to 51000 words out of 77288 words

Chapter 17 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

Amirun ya sha ban-ban da wanda ta gani satittikan da suka gabata, ma'abocin kuzari da koshin lafiya, hadi da wasu nasibobi da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. Wannan Amirun ya rame fiye da tunaninta, sannan ga dukkan alamu ba karamin jin jiki yake yi ba.
Ta tsaya jikin gadon kawai ba ta ce komai ba, sai dai zaka iya karantar karyewar da zuciyarta ta yi, hadi da tausayi tsantsa, da shi ma ya bayyana bisa kyakkyawar fuskarta. Tambaya ta ke cikin ranta, ita kuwa wace ce da Amiru zai kwanta ciwo a dalilinta?


Kamar an ce da shi bude idonka, a hankali ya ke bude idonshi a kanta. To ita ma din kallonshi ta ke, sai ya dauka ko mafarki ne da gizon da ta ke mishi dare da rana, don haka ya dauke kanshi daga kanta, don bai gasgata idanunshi ba. Ya mayar da su kan Dr. Fredrick, wanda ke ta murmushi.
Shi kam al'ummar Hausa suna ba shi mamaki akan soyayya, shi wallahi har duniya ta nade, bai ga macen da zata kwantar da shi a gadon asibiti ba. Balle mutun irin Amiru, dan gata gaba da baya, wanda duk irin macen da yake so a duniya zai iya aura. Ganin abinnasu yake kamar irin a fina-finan India. Ya kama hannun Amirun yana murmushi, ya ce
"Kana da bakuwa fa? Wadda tayo tattaki tun daga U.S domin ta duba jikin ka!"


Bai juya ya kara kallon Mairon ba, wadda ganinta ya kara haifar mishi da faduwar gaba. Kirjinshi in banda bugawa ba abin da yakeyi. Zuwa yanzu ya yarda ita din ce, ba gizo idanun shi ke mishi ba. Likita ya kama hannun Mairo ya dora mishi kan kirjinshi, dai-dai santar zuciyarshi. Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa fat-fat-fat! Amma don karfin hali bai fasa magana ba cikin nishi.
"Ba wajena ta zo ba, ta biyo bayan Yayanta ne".
Mace mai rauni da saurin karaya, sai ta soma kuka.
Tun fil'azal Mairo mace ce mai tausayi, abin kuka bai da wuya a gurinta, bare an ce a dalilinta ne Amir ya kamu da ciwon zuciya. Wato wannan ne dalilin Habibu na yanke mata karatunta, Allah sarki Yaya Habibu, a da har ta kullace shi tayi fushi dashi mai tsanani. Ban da abinsu ita wace ce? Da kasancewarta tare da shi zai sa ya samu sauki?
Likita ya daga mata gira, ya rausayar da kai, ta gane yana lallaminta ne ta rarrashi Amiru. Ta janye hannunta daga kirjinshi, cikin sassanyar murya ta ce
"Ni na fada maka cewa ba wajenka na zo ba?"
Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude ba. Dr. Fredrick ya zame ya fita, don ya lura Amirun ba zai iya yi mata magana ba idan yana kallonsu.
Ya sake bude ido a hankali ya dubeta, da wani irin sassanyan kallo. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, sabida wasu irin allurai da ta ji suna bin jinin jikinta. Hawayenta na diga a kasa dis-dis.
Ya tara hannu ya taro hawayen, ya ce "Wannan hawayen kuma na mene ne? Ni da kika ce ba kya so na? Ban yi kuka ba, sai ke?"
Muryarshi bata fita sosai, ba don tana kusa da shi sosai ba, da ba zata ji shi ba.


"How dare you want to me to believe you (ta yaya kike so in yarda da ke cewa) kin zo sabida ni ne? Bayan kin fada min ga wanda kike so, ni ba kya so na? Na hakura na tafi, don me Habibu zai takuraki ki biyo ni?
To me kika zo ki yi min? Kin zo ne ki kara min ciwon, ko kin zo karasar da ni zuwa kushewata ne?"
Ta dago sosai ta dube shi, ya yi saurin kauda kai, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanunta a wannan lokacin ba, wadanda suke kamar 'magnet' cikin nashi idanun, suke kuma sanyaya mishi zuciya, tare da karya karfin zuciyar duk da yake rikewa da jarumtar zucin duk da yake takama da ita. Har yake ganin zai iya jayayya da ita, ga shi tun ba a je ko'ina ba, ta fara karya lagon zuciyarshi.
Ta ce a sanyaye
"Har airport na bika, dai-dai lokacin da jirginku ya tashi. Ban ce lallai ka yarda da ni ba, amma Allah shaidata ne!"
Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa, ya tattara iya sautin da ya rage mishi a makoshi ya ce
"Mairo!"
Ta dakata, hannunta jikin marikin kofar, amma ba ta juyo ba. Ya yi tari kuful-kuful! sau uku, kamin ya ce "Fushi kika yi? Za ki sake tafiya ki barni? Ciwon sonki ya karasa ni?
Ki yi hakuri idan na fadi wani abu wanda ya bata miki rai, zafin sonki ne ya kawo hakan. Dawo ki zauna tare da ni, ina jin wani sanyi cikin zuciyata, a dalilin tsayawarki tare da ni.
Ki yi wa Allah, kada ki sake barina, har zuwa karshen rayuwarmu. My life has no meaning…... Idan na rasa soyayyarki. I’m impotent….idan ba tare dake ba!


Bana son Habibu ya takuraki ki aure ni, soyayyarki na ke nema, ba da tursasawar wani ba".
Wannan lokacin ba ta ce komi ba. Ta rasa abin da zata ce, ta kasa tantance shin abin da ta ke ji game da Amirun cikin zuciyarta da illahirin gangar jikinta a halin yanzu, soyayya ce ko kauna ce? Idan kauna da soyayyar ne baki daya, to shi kuma Uncle Junaidu fa? Shi kuma me ta ke masa idan ba so da kauna ba?
Idan haka ne ke nan MAZA BIYU ta ke so ko yaya ne? Soyayya guda daya ce, wadda a halin yanzu ba ta san ko ta waye ba, don haka ba zata ce ba. Amma data tuna halin da Amirun ke ciki, yana bukatar lallashi da kauna daga gareta a daidai wannan lokacin kamar yadda likitanshi yace, sai ta dawo kujerar da ke fuskartarshi ta zauna kanta a kasa. Kamun kai da kunyar Mairon, su ne manyan al'amuran yarinyar da suke kara masa kaunarta.
Ya tabbatar ba zata taba bude baki ta ce, tana sonshi ba, sai dai idan su kwana a hakan, wannan din ma ba karamin burge shi ya yi ba. Domin duk yarinyar da zata budi baki gatsar ta ce da namijin da bai zamo mijinta ba, ina sonka. To wallahi ba matar aure ba ce.


Inda Allah Ya ceceta daga kaifafan idanun Amirun, shi ne shigowar Yaya Habibu, Dr. Fredrick da dattijon da a yanzu ta gane shi ne Alh. Abdurrahman Gaya. Mahaifin Amiru.
Cikin murmushin jin dadin ganin dan nashi cikin yanayin da ya bashi mamaki, zaune sosai bisa gadon ya zuro kafafunshi kasa. Fuskarshi cike da walwala da yalwataccen murmushi ya karaso gare su, shima Amirun murmushin yake yi.
"A'ah sauki ya samu, lallai, kai Mairo ta iya jinya!".
Amiru ya harare ta, ya ce
"Ni ba wani jinyata da ta yi, sai kuka ta ke yi mini. Kai Yaya Habibu mai yasa ka takurata ta zo? Me ya hada ciwona da zuwan Mairo Nigeria? Alhalin karatu take yi? Da ka kyale ta ai zan samu sauki ne a hankali cikin yardar Allah".
Habibu ya harare shi ya ce
"Kwarai fa, shi yasa na ga kamin ta zo ana ta janyo maka numfashi".
Duk suka yi dariya ban da shi Amirun. Da kalaman Habibu suka jefa shi a tunanin anya ya cika namiji? Anya shigowar Mairo rayuwarsa bata maida shi mace ba?
Dr. Fredrick ya ce
"Ya ci abinci Mairo?"
Ta girgiza kai, sannan ta dubi kular abincin da ke kan lokar jikin gadon, ta dauko ta bude, farfesun kaza ne da ya ji kayan kamshi, a daya kular 'chips' ne da soyayyen kwai. Tana son ta tambaye shi wanne zai ci a ciki, amma kunya ta hana ta, don haka ta zuba kowanne kadan cikin faranti daban-daban ta mika mishi.


Dai-dai sanda ya debo shanyayyun idanunshi ya dora a kanta, sannan ya mika hannu ya karba. A hankali ta ce
"Ba zaka wanke baki ba?"
Cikin kankanuwar murya shima ya ce
"Kin bani abin wanke bakin na ce ba zan wanke ba?"
Ta ce
"Ai ban san inda ya ke ba".
Alh. Abdurrahman da kansa ya bude lokar ya fiddo sabbin burushi da makilin ya mika mata, ta bude ta shafa jikin burushin, Yaya Habibu ya mika mata roba. Tana zuba mishi ruwan robar 'swan' yana wankewa har ya gama, sannan ya soma cin abincin. Shi kanshi likitan ya yi mamakin yawan abincin da Amiru ya ci, wanda tunda aka kawo shi sai yau ya ci, “lallai so ba dama”. (Ya ce a zuciyarshi) sai ruwa ake kara masa mai dauke da sinadaran abincin maras lafiya.
Hajiyar Amiru ta shigo, bakinta ya kasa rufo, ganin Amirunta na cin abinci, alamun sauki sun bayyana sosai a gare shi.
Ta ce
"Kai masha'Allah, har abinci ake ci? Lallai sauki ya samu (don ita ba ta san musabbabin ciwon Amirun ba)".
Ta kalli Mairo da fuska ma'abociyar walwala, ta ce
"Ina muka samo 'yar kyakkyawar budurwa?"
Mairo ta dukar da kai, Alhajin ya ce,
"Kanwar Habibu ce, kuma surukarki insha Allahu".
Murmushinta ya fadada sosai zuwa dariya, ta ce
"Da gaske?"
Ta juya ta kalli Habibu
"Na ce da gaske ne Habibu?"
Ya yi murmushi ya ce
"Idan Allah Ya yarda".
Kunya a wajen Mairo, kamar ta nutse cikin kasa. Hajiya A’isha ta kamo hannunta ta rike cikin nata cike da matsananciyar kauna da kulawa.
Ana haka Dina da wasu daga cikin kannen Amiru suka shigo, don haka dakin ya yi albarka, ba masaka tsinke, wanda ke nuni da lallai Amiru dan dangi ne. Kowa na fadin albarkacin bakinshi. Akan yanayin jikin Amirun. Ba su bar asibitin ba sai dare, aka barshi da Habibu wanda shi yake kwana da shi.
***
8/5/21, 3:11 PM - Kawata: D


Awashegarin daurin aure, wato lahadi, tun safe motocin daukar amarya zuwa garin Gaya suka iso. Dina ta shirya amarya cikin fararen liffaya na Larabawan Mouritania, ta fesheta da turarukan 'gibenchy' su Habiba da Hajara suka sanyata a tsakiya, Dina na gidan gaba suka nufi garin Gaya.
Anyi musu tarba ta GIRMA, a gidan sarkin Gaya na lokacin, wanda ya kasance kaka ga Amiru, tunda kuwa shi ya haifi Alhaji Abdurrahman, dangin Mairo sun tabbatar Mairo ta yi aure da dan dangi, wanda ake so, ake kauna kwarai, ake kuma son abin da yake so, sannan aka san mutumcin dan Adam.
Kwanansu uku ana shagalin biki irin nasu na masarautar Gaya, kuma fulanin usli. Mai martaba Sarki Abdulkarim Sarkin Gaya III ya yi wa amarya kyautar bajimai uku da sabuwar mota.
Washegari suka nufo Abuja inda aka shiryawa amarya gidanta cikin gidan surukanta, bangare guda, wanda dama tun sanda za a gina gidan an gina shi ne musamman sabida Amirun.
Duk da dai gidan ba ya bukatar komi, wannan bai hana Habibu da Alh. Abbas yi wa Mairon su gata ba. Dakuna uku manya-manya aka ba su suka shakewa Mairo da dukiya.
Sai dai fa ba wai rambatsau ba, a'ah, komi ya dace da muhallinshi. Cikin tsari mai burgewa da ban sha'awa, sannan sun kawota da gararta (trailer) guda. Lokacin da suka shigo wajen Hajiya Aisha aka fara kai Mairo, inda dukkan dangin ango suke tare da Hajiyar a babban falonta.
Duk kannen Amiru guda goma sha biyu na ciki da na waje sun hallara, suka karbi amaryarsu cikin mutuntawa da kamala. Daga nan sai sassan Daddy wanda ya dade yana yi musu addu'a ta neman dacewa a duniya da lahira.
Daga nan aka taho da amarya bangarenta banda kuka da shessheka ba abin da ta ke yi. Ta kama Dina ta rike tamau, ta rantse ba zata tafi ta barta ba, sai dai su koma tare.
Dina na dariya ta ce
"Ina kika taba jin anyi haka Mairo? Ai auren ke nan, YAKIN MATA…… Ko ba ki ganin nima namu gidan na baro na ke zaune da Yayan ki, a inda ba ni da kowa? Ke kuwa fa? Ga ki ga su Hajiya, ga su Amina, ko su kadai sun isheki debe kewa. Duk lokacin da kike son zuwa Kano za ki je".
Cikin kuka ta ce
"Yanzu Aunty Dina ni da ku shi ke nan? Ni da su Little Mairo shi ke nan? Sannan ba zan koma makaranta ba?"
Dina ta ce
"Idan na ce za ki koma makaranta, ko ba zaki koma ba na yi karya, sabida a halin yanzu ba mu da iko da ke, sai abin da mijinki ya hukunta a gare ki. Yara kuwa na yi miki alkawarin da zarar sun samu hutu zan kawo miki su. Ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki Amiru is a nice person".
Sabah ta yi murmushi, ta ce
"Sai ma kin zauna da shi for a little while..."
Dina ta ce
"To kinji ba, kannenshi ma sun shaida".


Wayarta ta hau ruri ta yi murmushi
"Ni ma nawa tsohon angon kirana yake yi in mishi tausar gajiyar da kujuba-kujubar aurenki ya sanya shi. Don haka amarya sai ince, asubah ta gari".
Tana ji tana gani Dina ta fice, ji ta ke kamar ta dora hannuwa aka ta ce "Wayyo Allah". Ko ta sami sa'idah.
Ya rage daga ita sai su Amina, don su Hafsat kannen Dina duk sun tafi tun dazun. Nabilah dama ba ta taho Abuja ba, daga Gaya suka nufi gida ita da Isma'il.
Suna so ta yarda su yi hira, amma amaryar tasu ta ki sakin jikinta. Ganin abin ta ke kamar a mafarki, wai yau ita ce a gidan wani mijin ba Uncle Junaidu ba.
Ta yi saurin yin istigfari da wannan mummunan tunanin ta amince, ta yarda da kaddararta. Ta amince haka Allah Ya rubuta musu dukkaninsu. Zata koyawa zuciyarta juriya da karbar rayuwa a duk yadda ta zo mata.
Hajiya ta yi kiran wayar Amina, ta ce duk abin da suke yi su bari su taho gida haka dare ya yi. Dukkansu suka mike suna yi mata sai da safe Hajiya na kiransu. Ta rike mayafin Sabah tana kuka sosai har ta karyawa Sabah zuciya, ta ce su tafi zata taho.
Ta koma ta zauna ta ce "Haba Antinmu? Ya ya kike abu kamar karamar yarinya ne? Amare yanzu ba sa kuka, sakin jiki suke a sha soyayya. Kuma ni kinga idan ban tafi ba zan yi laifi wurin Hajiyarmu, don haka ki yi hakuri na tafi na yi miki alkawarin gobe da safe zan dawo idan Allah Ya kaimu".
Haka ta kalallameta da dadin baki ta samu ta gudu. Ya rage sai Mairo kadai cikin katafaren gidanta, daga ita sai halinta. Ji ta ke kamar an kawo ta kabarinta. Don haka ta ce bari kawai ta yi ibada ko ta samu sanyin zuciyarta.
Ta mike a hankali, ba tare da ta ajiye nadin laffayar da ke jikinta ba. Ta nufi kofar da jikinta ya ba ta bandaki ne, ba don ta saba da ire-iren wadannan wuraren ba, da hakika ta tsaya kauyanci. Komi na bandakin wanda ya kasance (Jacuzzi) kalar ruwan hoda ne, watau 'pink' kamar yadda makeken bed room din shi ma ruwan hodar ne da ratsin fari.
Ta dauro cikakkiyar alwala ta fito. Ba tare da ta tsaya neman darduma ba ta nemi wani gefe a can wani korido na dakin ta tada ikama. Sallolin neman biyan bukatar duniya da na lahira da neman dacewa a rayuwar aurenta ne ta ke yi. Cikin sujudunta tana mai yi wa Babanta da Innarta addu'ar samun rahma da gafarar Ubangiji.
Cikin tahiyarta ta ji alamun ana taba kofa, kafin cikin nutsuwa ta ji an murda kofar an shigo. Angon ya bayyana a dakin cikin fararen kayan barci.
Dai-dai lokacin da ta yi sallah ta mike ta kara tada sallah, ya aje kwali da tambulan din da ke hannunshi, shi ma ya shiga ya dauro alwalar ya cimmata suka ci gaba da sallar tare. Agogon bango ya buga karfe biyu dai-dai na sulusin dare lokacin da kowane mai rai yake neman hutu, amma ga wadannan ma'auratan abin ba haka yake ba.
Sun fada wata duniyar tunani ta daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba. Abin nufi, kowanne da tunanin da ke cin ranshi. Ba auren sha'awa ya yi ba, auren so da kauna ya yi. Don haka babu sha'awar Mairo ko yaya a tare da shi a daren yau.
Ya dauko kwalin 'fresh milk’ na madarar 'oldenburger' da ya shigo da shi ya tsiyaya a kofin ya mika mata. Ba tare da ta tashi daga inda ta yi sallar ba, ta mika hannu ta amsa. Ya sauko daga gefen gadon ya yi zaman rakuma a gabanta. Ya dauki dukkan hannuwanta ya rike cikin nashi. Wannan ya haifar da tashin tsigogin jikinta duka a lokaci daya.
Ta samu kanta cikin matsananciyar sha’awar mijinta Amiru, wanda sassanyan kamshinsa na turaren 'Miyaki' ke kara dagula mata al'amura, dama yaya lafiyar kura, balle an tsokaneta, amma ga shi Amirun, abin ba haka yake ba.


Zuciyarshi ta kasa amincewa Mairo na sonshi, a ganinshi Habibu ne ya takurata ta aure shi, don haka akan me zai sallama mata soyayyarshi? Yana son ya koyar da ita sonshi da kaunarshi, ba wai sha'awarshi ba kamar yadda ya karanto karara cikin fararen kwayar idanunta.
Haka suka yi ta zama dungur-gur bisa kafet har aka yi kiran assalatu, kowanne na ji da miskilanci. An rasa wanda zai fara keta billensa, ya kwantar da kai ga dan uwansa. Ya rausayar da kai, ya ce
"Mu je mu sake alwala".
Ba musu ta mike domin dama ta tsauwala da wannan zaman na babu gaira babu dalili.
Don haka koda suka idar da sallar Mairo gefen gado ta koma ta takure. Shi kuma ya ja filo ya jefa bisa kilishi ya kwanta. Ta leka ta hango idonshi a rufe ta dauka barci ne ya dauke shi, don haka ta mike ta warware laffayarta, yadda zata ji dadin yin barci, ta nade a gado ta ja bargo ta rufa. Wani irin fitinannen barci na fizgarta, hakan yasa ba da dadewa ba sarkin barayin ya yi awon gaba da ita.


Mairo ba ita ta farka ba sai wajejen karfe goma na safe. Shi ma din sakamakon feshin ruwan da ta ji akan fuskarta ne. Ta juya a hankali saitin da feshin ruwan ya ke, Amiru ne ke taje sumarshi. Ya yi shiri cikin bakaken 'suit' masu ban sha'awa.
Ta zuba mishi ido kurr kamar mayya, har yawun bakinta na tsinkewa, sakamakon wata matsananciyar sha'awarshi da ta kara saukar mata. Wannan mutum kamar Romeo ya ke, kamar an ce da shi 'juya' ya juyo suka yi ido hudu da ita, ya daure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login