Showing 27001 words to 30000 words out of 77288 words
Chapter 10 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt
amma ai na yi kokari, ke fa da sai yanzu kika yi wanka, ni tun asuba Momi ta tashe ni wai inyi maza in shirya in dauko mata Mairo ta ganta".
Ta yi murmushi, ta ce "Yau dai da yardar Allah zan ga Momi".
Ta ce "kwarai kuwa".
Mairo na shiryawa Nabilah na kallonta cikin yin tazbihi ga Sarkin halitta da Ya kaga halittar Mairo.
"MAIRO MATAR MANYA CE". Nabilah ta ayyana a zuciyarta. Wani irin jiki lukui-lukui kamar mai shiga wankan inji, ga kwantaccen gashi na fulanin usuli, wanda ke kwance lambam akan dogon wuyanta yala-yala da shi kamar ba zai kitsu ba, alhalin ba ta taba shafa masa relader ba koda wasa. Idanuwanta dara-dara, farare kal masu wani irin maiko da sheki (oily-eyes). Kai ita ba ta taba ganin mace mai lafiyayyen kugu da shafaffar mara irin Mairo ba. Kai ka ce idan ta sunkuya karyewa zata yi. Tana sharce kanta ta lura Nabilah kallonta ta ke, ta ce "Ke don Allah wannan kallon fa?"
Ta ce "ke din ce, abun kallon ce Mairo, duk mijin da ya aure ki ya caba, ai ban san haka kike da kyau ba sai yau".
Ta yi murmushi ta ce "Ni kuma ban taba ganin mai kyau irin naki ba Nabilah".
Ta ce "Kayya! Gyara ne kawai Mairo, ina maganar natural beauty ne".
Sai Mairo ta ja bakinta ta tsuke, ba ta kara cewa komai ba.
Ta kammala shiryawa tsaf cikin atamfarta ta ganin sarki (Ghana wad), wani tausayi ya kama Nabilah, mace har mace, sai dai ba kayan ado, da da suttura ya ya za a ga Mairo? A hakan ma Mairo abin a juyo a kalla ce, ina ga ta samu sutturu da kayan gyara? Sai dai duk yadda ta so ta dinga taimakawa Mairon tun a makaranta Mairon ba ta yarda, cike ta ke da wadatar zuci, kuma cikin godiyar Allah.
Mairo ta yi wa Nabilah jagora zuwa dakin Baffa. Ta zube a kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin far'a da cewa, "Lafiya kalau Nabilah, an gama karatu sai aure ko, ko kuwa babbar makaranta za ki wuce kamar kawarki?"
Ta ce "Eh, makaranta zan wuce".
Ya ce "To Allah Ya ba da sa'a".
Sannan ta gaya mishi ta zo ta dauki Mairo su je gidansu, iyayenta su ganta. Ya ce "Babu damuwa, don Allah kada Mairo ta kai dare".
Suka ce "Insha Allah".
Cikin nutsuwa Nabilah ke tuki har suka hau kan titin sakateriyar Audu-Bako, Mairo ta dauka Tarauni suka nufa, sai ta ga Nabilah ta karya akalar motar ta sha round ta hau kan titin state library, ba ta kai karshen titin ba ta yi kwana ta shiga unguwar Ahmadu Bello Way, ta tsaya a harabar gidansu mai lamba dari da biyu (No. 102), suka rufe motar suka karasa cikin gidan.
Tun Mairo na mamakin tangama-tangaman falullukan da suke wucewa har ta daina mamaki, sai tazbihi ga Allah Mai azurta wanda ya so. Ba ta taba shiga gida irin wannan ba ko a mafarkinta. Ba su tsaya a ko'ina ba sai a babban falon Momin Nabilah, wadda ta fito tana tafa hannu tana 'Lale da Mairon Nabilah".
Ta yi murmushi ta zamo daga cikin kujera tana gayas da Momin, kamin ai haka tuni Nabilah da wata dattijuwa wadda da alama mai aiki ce sun cika gaban Mairo da kayan tande-tande da lashe-lashe irin wadanda ba ta taba ci ba a rayuwarta.
Shi ma Daddyn Nabilah ya sauko yana marhaban da Maryam. Ya zauna a cikin su, Mairo duk ta kasa sakewa sabida bakunta da rashin sabo. Saukin kan iyayen Nabilah ya burge ta. Ta tabbatar Nabilah 'yar gata ce ta karshe, ita kadai ce kwallin kwal, a wurin iyayenta. Daddy ya ce da Mairo da zarar takardunsu sun fito ta kawo mishi zai taimaka su samu gurbi a jami'a ita da Nabilah, ta yi godiya sosai.
Karfe biyar na yamma Mairo ta yi haramar tafiya. Akwati guda Momi ta shake mata da kayan shafa da dogayen riguna kala-kala, Nabilah ta maidota gida.
Tana shigowa idanun Hajara da Habiba akan jakar hannunta. Jikin Habiba har rawa yake, ta bi bayan Mairo tana son ta ji ina Mairo ta samo wannan diyar arzikin, har ga shi ta dawo da galleliyar jaka cike taf da kaya.
Har karo suke ita da Hajara wajen shigowa dakin. Habiba ta ce "Bude jakar mu gani, me muka samu?"
Hajara kuma ta ce "Wannan bakauyar ta iya bude irin wannan jakar ne? Gafara nan ki gani".
Ta jawo jakar ta soma kici-kicin budewa. Ta zazzago duk kayan da ke ciki tana al'ajabi. Habiba ta ce "Ina kika samo wannan diyar arzikin kuma?"
Mairo ba ta yi magana ba suka soma kasawa, Habiba ta daga rigar da ta fi kowacce kyau a ciki, ta ce "Wannan zata yi wa Ladidi". Ta sake daga skirt da rigarshi ta ce, "Wannan sai a bar wa Batulu idan ta kara girma zata yi mata dai-dai, ke ki rike wannan din".
Ta tura mata wata 'yar yaloluwar rigar barci suka tattara kashi uku bisa hudu na kayan suka yi waje da sauri har suna tuntube tareda karo da juna kada Baffa ya jiyo su suka gudu dakinsu.
Mairo ta ce, "Allah na tuba, suttura tsumma, mene da zan damu kaina?"
Duk da Baffa ya hana a bata aikin wahala wanda ya fi karfinta ba su fasa ba a bayan idonsa. Mairo na hakuri da su da kokarin kyautata musu su da 'ya'yansu a kullum, amma ta rasa dalilin da yasa mutanen nan suka ki jininta, ko zata wuni tana aikin bauta, shara, wanke-wanke, wanki da wankin bandaki ba zata taba yi musu gwaninta ba, balle kalmar “madallah” ko “an gode” ta gitta a tsakani.
Watanni uku cif da gama makarantar su ta samu labarin fitowar jarrabawarsu, don haka ta soma shirin zuwa gidan su Nabilah don su je makaranta su karbo sakamakonsu.
Baffa da kanshi ya kaita gidan su Nabilah tana yi masa kwatance tana nuna masa hanya har suka iso gidan. Ya sauke ta ya juya da cewa, idan sun dawo Nabilar ta maidota gida.
Amma Allah sarki, sai ta tarar da Nabilah kwance ba ta jin dadi. Ta zauna a gefen gadon da ta ke kwance ta dora hannu akan goshinta, zafi rau! Momi ta shigo da filet a hannunta mai dauke da soyayyar plaintain da dankali da kwai, ta ce "Ungo ba ta Maryam da kanki, watakila zata ci, tunda ni nayi-nayi ta ki karba".
Mairo ta ce "Haba Nabilah, ciwo da rashin cin abinci ai abin ba kyau, ki daure ki ci ko kadan ne don Allah".
Ta karba tana kokarin mikewa, Mairo ta tusa mata filo a bayanta don ta ji dadin jingina. Momi ta fita ta bar su. Tana fita Nabilah ta fashe da kuka mai tsanani. Hankalin Mairo ya tashi, ta ce "Lafiya Nabilah? Wani abu ya faru ne?"
Cikin kuka ta ce, "Me ye bai faru ba? Hajiyar Daddy ce ta zo ta ce ba ta yarda na ci gaba da karatu ba, aure za a yi min da wani cousin dina. Bayan kuma bana sonsa, kuma sati mai zuwa za a daura auren, shi ma bai ce yana sona ba, wai wata Igbo ya zo musu da ita daga can inda yake karatu a Kudu, shi ne ba su amince masa ba, suka ba shi ni. Allah na tuba auren soyayya ma bai tsira ba a wannan zamanin balle auren tushe? Sabida Allah na yi kama da matar tushen iyaye?"
Mairo ta rasa abin da zata ce "Ki ce ba ciwo kike ba, tunanin aure ne. Ni ban ga aibu a nan ba, tunda iyaye ne suka hada, ai ALHERI ne, kuma alherin suke nufin ki da shi. Ki yi biyayya ga iyayenki Nabila za ki ga da kyau a rayuwa.
Soyayya aikin banza ce, don watakila yadda kike son mutum shi ba haka ba ne a zuciyarshi ba. Na gani akan kaina Nabilah. Har yanzu kuma ban ga inda soyayya ta kaini ba, sai kunci a zuci, ruhi da gangar jiki. Nabilah yau zan gaya miki abin da ke raina shekara da shekaru. Wato soyayyar Uncle Junaidu. Na dauka yadda na ke azabtuwa a zuci, da gangar jiki da soyayyarsa, shi ma haka yake sona, ashe ni ban sani ba, Uncle ba haka ba ne a zuciyarshi ba.
A ranar da na yanke shawarar fallasa mishi asirin zuciyata, a ranar ya zame, ya gudu ya barni, ba tare da ya sanar da ni komi a kanshi ba. Wanda ke nufin ba ya bukatar anymore mu'amala da ni. Har yau ni kadai nasan abin da nake ji a zuciyata Nabilah. Hasashenku ke da Innata, bai zamo gaskiya ba, Uncle Junaidu ba SO NA yake yi ba, tausayina ne da taimako".
Nabilah ta yi shiru cikin mamaki, yau Allah Ya nuna mata ranar da Mairo ta bude bakinta da kanta ta fada mata cewar tana son Uncle Junaidu.
Ina ma ace shi ma hakan ne a zuciyarshi? Duk duniya ba ta taba ganin mijin da ya dace da Mairo ba, irin Uncle, wanda yasan zahirinta da badininta, jinin jikinsu ke gauraye guri guda yana circulating. Amma ba zata taba yarda cewa wai Junaidu ba son Mairo yake ba.
Babu wanda zaka bai wa jinin jikinka sai wanda kake matukar so.
Ta dago a hankali ta dubi Mairo ido cikin ido, ta ce "Wallahi Mairo yadda kike son Uncle, shi ma haka yake sonki. Zan yi rantsuwa in dafa Alkur'ani akan hakan. Sai dai ban san dalilinshi na janye kafa a ranar da zaku rabu ba. Zan yi mishi uzuri da wani abu mai muhimmanci a gare shi, amma haka kawai Uncle ba zai ki yi miki sallama ba, sai ko sakamakon wani muhimmin abu da ya faru gare shi.
Rashin haduwarku ya zama rahma ke nan ga mutumcinki da martabarki a idanunsa……."
Ta yi saurin duban Nabilah, tana mai daga gira ta ce, "Yes, gara da Allah bai baki ikon ki furta masa ba, wai ya aure ki koda ba ya sonki. Duk inda yake, Mairo ni na gaya miki ko ba dade ko bajima WATARANA zai neme ki, ki rike wannan a zuciyarki ki ce, ni na gaya miki".
Ta mike ta fada bandaki tana cewa, "Bara na shirya mu tafi, ni har ma na warke da ganinki Mairo".
Ta yi dariya, cikin samun nutsuwa a zuciyarta da kalaman Nabilah, ta ce "Dama ba wani ciwo ke damunki ba, sai shagwaba da gata, da suka taru suka lullube ki".
7/30/21, 1:01 PM - Kawata: B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru shida cur, cikin dalibtaka da al'amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno Kausar suka yi mata addu'a. Suka karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike da alhini ya ke sanar da ita cewa, "Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice) zuwa kasar Russia (Ukhrain). Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar".
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta taba yi ba a rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma faduwa. Ta dubi takardunta, wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya yi mata nisan da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a gareta da ba zata taba mantawa ba. Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi kadai zata ci gaba da so har zuwa karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle, amma shi ba hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin yanzu, daga Baffa sai shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta a duk yadda ta zo mata.....!!!
*** ***
B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye da 'yan uwa ke ta sha'aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai ce zata yi mata magana ta ji. Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don wai fushi ta ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka, Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al'amuran rayuwa. Yau dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata nata Mr. Right din? Tunda Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai, tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma ba da kowa ba, da wanda ruhi, zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta fado mata a rai. Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar Galadanchi ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da 'yan uwanshi musamman Ilham, wai an ce Gaida mai gaisheka...!'
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake cikin watan Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a tsakar dakin. Mairo na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure baki babu ta koma ta kwanta. Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin ta je asibiti ba ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, "Ladidi ki shirya na rakaki asibiti mana, ko magani ne a baki, wannan aman ya tsaya?"
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce "Mu je".
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga ido ta dube su. Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da kwarjini na musamman a fuskar Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a rufe ido don muni da rashin tsafta.
Ta ce "Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?"
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al'adarta, ta ce "Asibiti wai zata kai ni".
"Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?"
Ta sake kyabe bakin ta ce "Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!".
Ta gallowa Mairo harara ta ce "Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai idan ya ci abin da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin zuciyar zai lafa".
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa tabbacin ya dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin abinci ga Hajara da autarta Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce "Yaya dai Mairo, babu wata matsala ince ko?"
Kanta a kasa ta ce "Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne".
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce "Ga shi ayi kudin mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje".
Ta ce "Insha Allahu Baffa".
Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan komi a kanshi ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce "Gaida mahaifiyarsa kamar yadda yake gaida naki". Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce "Galadanchi". Ya bude mata kofa ta shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba ta canji, ta gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar magriba, ba zata iya shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama, ya juyo ya amsa, ta ce "Don Allah Yayana tambaya nake".
Ya ce "Allah Ya sa na sani kanwata".
Ta ce "Gidan su Junaid nake tambaya".
Ya ce "Junaid? Ya ya sunan maigidan?"
"Gaskiya ban sani ba".
"Babba ne ko yaro ne?"
"Babba ne, don zai girme ka".
Ya yi