Showing 45001 words to 48000 words out of 77288 words

Chapter 16 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

murya ya ce
"Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja wajenshi ban san halin da suke ciki ba".
Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya kasance ciwon Amirun yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al'amuran rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban ikon Allah.
Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba.


Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce
"Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi".
Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce "Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai ko? Tun ranar da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba".
Dina ta shirga karya
"Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba".
Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo ta wutsiyar idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu'azzam Kanti, ke kwararowa. (Alkawari bayan rai). Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta, da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani bakon al'amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba zata ce mene ne ko na mene ne ba.


Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta yaye labulen dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature yin harkokin gabansa ba.
Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma duk lullube suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani wajen rage azabtaccen sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba.
Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat da bakin wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk bakake wul. Sakonnin suka soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da sabbin sakonni guda goma sha biyar.
Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta kasa samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh inda ita kuma ta ke sanar da ita cewa akwai test' karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin. Sai na wani dan ajinsu Henry baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta ba.
Ta yi mishi ta'aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta, kasancewar an yi shi ne cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin rubutun a gurguje.


"Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu kansu cikin gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a banza.
Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci ko matsatsi na rayuwa ba".
-mai son ki.


Ta karanta ya fi cikin 'ya'yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba. Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da zuciyarta ba.


To haka washegari, mai 'logo' na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.


"........ Some one misses you!".


Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu, wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.


Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce "Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina a tashe ya ke".
Ya ce "Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don't want to lose AMEERU. (bana so in rasa Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo".
Dina ta kidime "Lafiya? Me ya faru da Amirun?"
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce.
8/3/21, 9:03 PM - Kawata: B
Cikin dauriya ta ce "Habib, me ya faru da shi? Ka gayamin don Allah. Sai dai na taho ni kadai, Mairo jarrabawa zata fara zanawa, wadda idan ba ta yi ba, sai ta maimaita shekarar".
Da budaddiyar murya ya ce.
"Karatun ma, ai ina jin ta barshi kenan. AURE zan yi mata".


Dina ta kyafkyafta 'yan idanunta ta sato kallon Mairo, cike da fargabar Allah Ya sa ba ta jiyo abin da Yayanta ya ce ba. Ta ga hankalinta ba ya kanta, ya tafi ga lallashin Little Mairo ta ci abincin da ta ke ba ta da dan kankanin cokali. Ta godewa Allah da abin da ya darsu a ranta (mutuwar Amiru) ba shi ne ba. Ta kawo gwauron numfashi ta ce "Kano za mu taho ko Abuja?"
Ya ce
"Ku biyo jirgin Abuja, idan kun sauka ki kirani zan zo na dauke ku".


Don haka a daren yau bakidayansa Dina ba ta samu isasshen barci ba. Tausayin Mairo ya cika mata zuciya. Irin yadda ta ke wahala akan karatun nan, ta kwallafa rai a kansa, kullum cikin ‘solving assignments' ace ya tashi a banza! Shekaru biyu cur! Sai dai kwarin gwiwar da ta ke da shi, shi ne Habibu ba zai kai 'yar uwarsa inda za ta tozarta ko ta wulakanta ba. Duk son da ta ke yi mata ta tabbata bai yi rabin-rabin wanda shi yake yi mata ba. Sannan akan Amiru ba abinda bazai iya ba.
Da safe karfe takwas ta yi shirin fita don yi musu booking din tickets na jirgin ‘Lufthansa’ wanda zai tashi karfe goma na daren ranar. Sannan ta dawo, ta cimma Mairo ta fito daga wanka tana shafa akan stool ta ce (tana mai kawas da kai) "ki hada kayanki masu dan yawa, gida Najeriya zamu tafi, ban san kuma ranar da zamu dawo ba".
Tana mai kawas da idanunta daga gare ta, don ba zata iya fada mata abin da Habibun ya gaya mata ba.
Cikin mamaki Mairo ta ce
"Me ya faru? Irin wannan tafiya haka unexpected?"
Dina ta ce
"Bai fada min ba, amma dai ya ce lallai mu tafi".
Kamar ta yi kuka, ta ce "Ina da 'test' yau, kuma jibi za mu fara jarrabawa, kuma Yaya Habibu ya sani, yaya yake so in yi?"
Dina ta ce
"Hakuri za ki yi, haka Allah Ya shirya miki. Wani hanin ga Allah baiwa ne".
***








J
irginsu ya sauka a Abuja karfe biyar na asubahi. Ban da kunci da kumburi ba abin da Mairo ta ke yi. Dina sai lallabata ta ke tana ba ta hakuri. Idan takaicin ya yi takaici, sai ta kai hankici ta tsane hakwayen da ke 'racing' a fararen kundukukinta.
Idan Dina ta ce "Ki yi wa Allah Mairo ki yi hakuri..."
Sai ta ce
"Haba Aunty Dina? Shekaru biyu ina wahala, in fadi, in tashi amma ace sun tashi a banza?"


Wani farin dattijo, dan kimanin shekaru sittin da biyar, wanda alamun jin dadi, tsantsar ilimi da gogewar rayuwa ya boye shekarun nashi. Sanye cikin kaftan na wata irin farar sassalkar shadda da akalla ta baiwa naira dubu dari baya, yana da tsagin biyu-biyu a gefen fuskarsa na Fulanin Gaya. Biye da shi escort ne har guda biyu cikin bakaken suit wadanda harsashi na kowacce irin bindiga ba ya huda su, sun maka 'dark-spaces' fuskokinsu kamar hadari, sabanin dattijon wanda kyakkyawar fuskarsa ke yalwace da ni'imtaccen murmushi wanda da alama tabbatacce ne akan fuskarsa cikin kowanne yanayi.
Abin nufi, cikin halin bakin ciki da farin ciki, kwanciyar hankali da tashin hankali, wannan sassanyan murmushin ba ya gushewa daga fuskarsa. A takaice dai na halitta ne, watau 'nature', shi ne a gaba wajen tarbar su Habibu a baya.
Don haka kwarjininshi da haibarshi ya sanya dole Mairo ta daina kukan da ta ke, ta tsugunna har kasa ta gaida shi. Ya dora hannun damanshi a kanta ya ce
"Barka da zuwa Maryamu. Godiya ga Allah da Ya sauke ku lafiya".
Yaya Habibun kuwa ko arzikin kallo bai samu ba, sai matarshi ke binshi da kallon mamakin muguwar zabgewar da ya yi cikin kwanaki biyar kacal.


Mairo ta sha mamakin ganin 'chebrolit' yau a gida Najeriya. Motar da ko a America, sai wanda ya ci ya tada kai. Ba wannan ne kadai ya razanata ba, sai tangamemen 'gate' irin wanda ake kira 'Mahdi ka-ture' da aka wangame musu a lokacin da motarsu ta sawo kai cikin unguwar Asokoro. Ta hango wani irin ‘American billa’ mai kama da jirgin ruwa.
Ita dai Mairo ido ne nata, sai kuma ta cilla kafa duk inda ta ga an cilla. Tana cewa a ranta, watakila Yaya Habibu siyar da mu zai yi. Dama ni kudin nan nasa ai ban yarda da su ba. Sai dai kuma babu dar ko tsoro ko yaya cikin kalbinta, wadda ke cike taf da takaicin rabota da karatunta da aka yi babu gaira babu dalili.


A kofar wani kayataccen falo mai kofar gilashi Yaya Habibu, dattijon da sauran mutanen da ke take mishi baya suka tsaya. Su kuma aka sa wata mace wadda ga dukkan alamu mai aiki ce, ta yi musu jagora cikin gidan. Ta nuna musu dakin da za su sauka, sannan ta sanar da su cewa, matar gidan tana asibiti, idan sun kimtsa su danna 'bell' za a shigo musu da abinci. Dina ce ta amsa, amma Mairo ta zama hoto.
Dina ce ta fara yin wanka, sannan Mairo. Suka dauro alwala suka bada faralin sallar subhi da ta riske su a jirgi. Suka shirya tsaf, Mairo cikin 'swiss lace' ruwan madara da yarfin kananan duwatsu, riga da 'wrapper zani', ta yi 'simple' nadin kallabi a kanta. Dina cikin atamfar 'super' shudiya ita ma riga da zani da yalwataccen mayafi. A tsaitsaye suka ci abincin sabida kiran Yaya Habibu cikin wayar Dina cewa, su fito za su wuce asibiti.
A babban asibitin koyarwa na Abuja, ita Mairo ta sha wajen matar gidan suka zo da ta ji an ce tana asibiti, sai raba ido ta ke cike da son ganin wace ce mamallakiyar wannan 'bungalow' din. Wanda aka yi amfani da hikima, ilmi da tunani wajen sarrafa shi. Kai ita a iya yawonta cikin U.S ba ta taba ganin irin wannan ginin ba, wanda ta fahimci cewa gidan wannan farin dattijon ne, da ya je tarbo su filin jirgi.
Dattijon ne a gaba, sai 'escort' dinshi, sannan Habibu da Dina biye da shi, Mairo ce karshen shiga dakin, wanda ya kasance 'amenity'. Sabida cikowar da dakin ya yi da kyawawan mata masu kama daya, kuma masu kananan shekaru akalla daga mai talatin sai mai kasa da haka, sai kuma 'yammata tsararrakinta, wadanda ga dukkan alamu ko auren fari ba su yi ba, ta rasa inda tasan fuskarsu kamar ta sansu a wani wuri. Daga can gefe wata dattijuwa ce kyakkyawa cikin kyakkyawar suttura zaune bisa darduma, ta yi nisa cikin sujjadarta ba ta san me ake a dakin ba.
Cikowar da dakin ya yi, shi yasa Mairo ba ta yi nasarar hango 'patient' din ba, wanda ke ta kelayo aman jini, har da guda-guda. Daya daga cikin matan ta rike shi tana kuka, sauran ma duk sharar hawaye suke yi da gefen mayafansu, wanda ke nuni da cewa kauna ce mai tsanani tsakaninsu da dan uwansu.
Da sauri dattijon ya karasa gaban gadon ya tallafe shi cikin kirjinsa. Ya danna wani abu, da gudu likitoci biyar suka shigo. Nan suka yi umarnin kowa ya fita.
Mairo dama tana bakin kofa, don haka ita ce ta farkon fita. Dattijiyar ma tana sallarta ko dagowa ba ta yi ba, su ma likitocin ba su ce ta fita ba. Daga likitocin sai dattijon sai Habibu, wanda idanunshi suka kada suka yi jajur, zaka iya hango tsabar tashin hankalin da ke kwance cikinsu. Don ma yana dauriya ne, amma da fashewa zai yi da kuka.
Cikin gaggawa kowannensu ke ba shi taimakon da zai iya. Masu jona abin janyo numfashi na yi, masu auna bugun zuciya na yi, da ya ja wata doguwar ajiyar zuciya su dukka suka kalli juna suka girgiza kai, sannan suka ci gaba da aikinsu cikin kwarewa da sanin makamar aiki.
Kafin su cire 'odygen' din su yi wa Habibu da dattijon alamar su biyo su ofishinsu. Fitarsu ke da wuya leburori suka shiga dakin suka soma tsaftace wajen. Har zuwa wannan lokacin dattijuwar nan ba ta daina sallah ba. Ba ta daina kai goshinta gaban mahaliccinta ba, domin ta yi imanin Shi kadai ne zai tashi kafadar danta, amma ba wadannan tarkacen nasaran ba.


A can ofishin Dr. Fredrick Engles (consultant) na bangaren zuciya, bayani yake musu dalla-dalla na bugun zuciyar ba-zata da 'patient' dinsu ya samu, wanda ya yi mugun yi wa zuciyarshi illa farat daya.
Ciwon zuciya na lokaci daya ya yi mishi mugun kaye, wanda idan ba a yi gaggawar magance mishi damuwarshi ba, daga yanzu zuwa kowanne lokaci komai zai iya faruwa. Ya kare da tambayarsu, shin ko sun san hakikanin abin da ke damun mara lafiyan? Domin su sunyi-sunyi ya fada musu, amma ya ki cewa komai.
A nan ne dattijon ya soma yi wa babban likitan bayanin duk abin da Amirun ya fada mishi ranar da ya dawo, kafin ciwon ya ci karfinshi. Wato kanwar Habibu yake so, ita kuma ta ce ba zata aure shi ba.
Habibu kuma ya dubi likitan ya ce
"Ni kuma na yi alkawarin zan aurawa Amiru Mairo, ko da a gobe ne, idan hakan shi ne zai zamo FANSA ga lafiyarshi. Ko da kuwa ace wannan shi ne abu na KARSHE da zan gabatar a rayuwata".
Dattijon ya ce, "A'a Habibu, ba za a yi haka ba, a bi-ta a hankali, domin dai da na kowa ne, ban yarda a tursasata bisa abin da ba ta so ba".
Dr. Fredrick ya ce
"Yanzu ina yarinyar?"
Habibu ya ce "Tana waje, sun zo tun dazu. Sai dai ba tasan abin da ke faruwa ba. Da kyar ma idan tasan Amirun ne kwance a gadon asibiti".
Likitan ya ce "A kirawo ta".


Habibu ya fita, jim kadan suka shigo tare da Mairo, duk da ranta a bace yake, amma ba zaka karanci hakan a fuskarta ba. Ta nemi kujera gefen Habibu ta zauna, kanta a sunkuye, Dr. Fredrick ya yiwa su Habibu alamar su fita, yana mai ci gaba da rubuce-rubucensa cikin 'file'. Ofishin ya rage daga shi sai Mairo, har zuwa lokacin bai gama rubutun da yake yi ba. Daga bisani ya dago, ta karkashin farin gilashinsa yake kare mata kallo. Cikin ranshi ya ce, Dole maza su kwanta ciwo.


Ya yi gyaran murya, sannan ya yi murmushi, ya ce "Maryam".
Ta dago a hankali ta dube shi cikin fararen idanunta ba tare da ta ce dashi komai ba.
Ya mike zuwa dan karamin firij da ke gefenshi ya fiddo gorar ruwan (Faro) ya bincire murfin ya sha, ya maida robar. Maimakon ya koma mazauninshi, sai ya ja kujerar da ke fuskantarta ya zauna. Ya sake yin murmushi kafin ya sake kiran sunanta. Wannan karon kam ta amsa, ta ce
"Na'am".


Ya ce "Sunana Dr. Fredrick, ni ne likitan da ke kula da lafiyar iyalin ABDURRAHMAN GAYA. Ina so ki ba mu hadin kai mu ceto rai, wanda ke cikin halin ha'u'la'i akan soyayyarki. Shin za mu samu wannan taimakon Mairo?"
Cikin murya mai sanyi ta ce
"Ni Doctor?"
Ya ce "Ke fa Maryam".
"Ta ya ya zan taimaka?"
"Ta hanyar tayamu jinya, har sai ya samu lafiyarshi, domin a halin yanzu ba ya bukatar komai Maryam, sai soyayyarki, sannan ne mu ma za mu samu namu aikin ya yi kyau. Mai zai hana ki yarda ki auri mai sonki Maryam? Har ya ke neman rasa kyakkyawar rayuwarshi a dalilinki?"
Cike da matsanancin mamaki ta ce "wai wanene?"
Yayi murmushi ya ce
"Taso mu je".


Dr. Fredrick ne a gaba, Mairo na biye da shi. Ya tura kofar dakin dazu ya shiga, ita ma ta sa kai. Dakin babu kowa, sai mara lafiyan, wanda ke barci sadidan. Sai dai fa da ganin irin barcin da yake yi kasan ba na Allah da Annabi ba ne, na karfin allurai ne.
Ba karamin bugawa zuciyarta ta yi ba (kamar wancan lokacin da ta fara ganinsa) a lokacin da ta sake yin arba, da dan Abdurrahman Gaya. Sai dai fa wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login