Showing 72001 words to 75000 words out of 77288 words

Chapter 25 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

haihuwa ba.
Mairo har da hawaye na tausayawa Amina, don ita kanta shaida ce a kan matsananciyar soyayyar da suke yiwa juna. Mairo na so ta tambaye ta AMEERU ba ta so ta bada kanta. Amiru ya yi mata miki mai girma a zuciyarta. Tunda suka rabu bai taba nema ko sau daya ya ganta ba, sai ‘ya’yansa. To akan me ita zata nemeshi?
Ta tabbata duk inda yake yanzu ya dade da shafe ta a babin rayuwarsa. Watakila ma ya kara aure bayan Hanan, ya sallamawa wata wannan gangar jikin da ada ta dauka mallakinta ne ita kadai. Don ta san Dan Abdurrahaman Gaya, ba zai iya kaiwa tsawon wannan lokacin ba tare da aure ba, in ta yi la’kari da halittarsa, na mutum mai tsananin yawan bukata. Sannan Hanan, bata da surar irin matar da yake son aure. Ko kuma watakila ya komawa banasariyar matarshi? Allah masani.


Amina ta ce
“Rayuwa tafe take tare da destiny (kaddara) kala-kala Aunty Mairo, kin manta da brother, kin bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki, kin kara kyau, kin kara kiba, kin kara haiba da kamala. Sabanin shi da a kullum yake kara lalacewa.
Cikin shekaru ukun nan ban kara ganin dariyar Yaya Amiru ba, ki yafewa mai kaunarki wanda ya sadaukar da zuciyarsa ga soyayyarki. Ku tallafi juna, ku baiwa zuciyoyinku abin da suke so.
Hajiyata da ‘yan uwana sun yi kuskure, sun kuma gane kuskuren su, sun yi nadama mai suna nadama amma ku, (keda Amiru), Daddy da Habibu har yau kun ki karbar tuban su, ban san me yasa ba”.
Mairo ta yi murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce,
“Mun karbi tubansu man? Watakila dai iyakar zaman ke nan, babu saura, tunda aka kawo wannan lokacin. Shi ya gaya miki yana son komen? Yana da mace irin Hanan a gefe?”
Mamaki ya kama Amina, ta tabbata Mairo ba ta san tare suka yi waje ita da Hanan ba. Ta ce,
“A kan sakin Hanan aka yi naki, Allah sarki brother! Zurfin cikin shi na bani mamaki. A halin yanzu Hanan tana Porthercourt ‘ya’yanta biyu tare da mijinta Ramadan wani ma’aikacin kwastom”.


Mairo ta yi shiru, kamar an zuke jinin jikinta. Tausayin Amiru ya kama ta, Allah kadai ya san halin da rayuwarshi ke ciki.
Ta tura hannu cikin jakarta ta zaro wasu kananun katina da aka yiwa rubutu da kumfar golden, ta dorawa Amina a cinya.


A kasalance Amina ta dauka, kati ne na gayyatar daurin auren PROF. JUNAID ATIKU GALADANCHI da DR. MARYAM MOHAMMAD BEDI, wanda za a gabatar kwanaki goma sha hudu masu zuwa. Ba ta kai karshen karanta katin bikin ba Amina ta rushe da kuka.
Ashe masu kukan suna da yawa, domin a can falon Baffa ma Hajiya ce ke ta kuka tana rokon Alh. Abbas ya yi wa Amiru uziri, su ne da laifi ba shi ba. Su kuma ba su yi hakan da nufin A BARI YA HUCE...... ba, sai don a bawa Mairo dama ta sarara ta cika burin neman iliminta. Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali


Daddy ya ce.
“Idan da mai laifi to ni ne, don ni na hana Amiru yin wani yunkuri na dawo da iyalinsa har tsawon wannan lokacin. Ina so in koya masa jarumtaka, in nusar da shi cewa;
“kallafa rai a kan abin da ake so, da amanna da cewa samuwar abin nan kadai shi ne samun lafiya da kwanciyar hankali ba shi ne ba”.
Dauriya, hakuri da juriya da tawakkkali sune halayen da ake son namiji ya suffantu dasu. Kuma na gode Allah....... DUK WASU EXPERIMENTS DANA YIWA AMEERU BAI FADI KO DAYA BA..............!!!”


Baffa ya jinjina kai ya ce.
“Nima in son samu ne, na fi son Mairo ta koma wurin mijinta ta tarbiyanci ‘ya’yanta a gabanta. Amma Alh. Junaidu ya zarta duk yadda kuke tunani a wurin mu. Don haka bana cikin wannan magana..... Zabi yana ga Mairo, tunda ita Allah ya baiwa damar zaben mijin da za ta iya zama da shi a halin yanzu. Don haka ku bani kwana biyu zan tuntube ta”.
Habibu bai ce komai ba, don ba shi da ta cewar, bai san me zai ce ba, bayan Allah ya yiwa Mairo zabin alheri, wannan karon ba zai yi shisshigi ba.
***


SUNA tafe cikin jirgi amma Daddy baya cikin nutsuwa. Tausayin gudan ransa ya ishe shi, ko ma me ya faru ya tabbata shi ya jawo mishi. Shekaru uku ba kwana uku ba!!! Ya nesanta Amir da iyalinshi a kan laifin da ba nashi ba. A kan hujjojin sa da basu da karfi.
Don haka suna sauka a jirgi ya bude waya ya kira Amiru yana nishi kamar mai ciwon asthma. Ya ce,
“Ka bar duk abin da kake ka taho, ka wuce Kano ka nemi sasanci da iyalinka in har kana so. Na amince maka Amiru, da sanya albarkata.... saura kwana goma sha hudu a daurawa Mairo aure!!!”


Ga mamakin Daddy sai ya yi murmushi, wanda har sautinsa ya ratso cikin wayar, ya ce.


“Ka kwantar da hankalinka Daddy, na dade da sanyawa zuciyata salama, na yi amanna da cewa idan akwai sauran zama tsakanina da Mairo, to za ta dawo mini ko ba dade ko ba jima”.


****


Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa ne a harabar gidan Dr. Mairo, wanda ke a Area C cikin sabuwar jami’ar Bayero suna wasan kwallon kwando, ya yin da a gefensu Habib da Amir ne tare da wasu sa’o’insu ‘ya’yan makota suke wasan tsaren kekuna, yara masu ban sha’awa. Suna sanye da kayan sanyi masu laushi farare sol, an rubuta I LUV MUMMY, kafafunsu daure cikin farin cambas, sunyi kyau har sun gaji kamar ‘ya’yan South-Western.


Daidai lokacin da motar kirar (Camero, 2 Door) ta yi parking and hankali a gefensu, matukin motar ya duba katin da ke hannunsa ya tabbatar lambar gidan ta yi daidai da wadda ya gani a rubuce. Sai ya kashe ya fito.
Sanye yake da suwaitar ‘Dolce & Gabbana’ mai dogon hannu, da shudin wandon jeans. Ya yin da rigar ta kasance fari da ratshin ja da blue. Ga duk wanda ya san shi, ba zai yi gaggawar gane shi ba, saboda yadda fatar jikinshi ta kara kwanciya, tare da goguwa mai nuni da alamun hutu. Ya jawo bakin PRADA ya saya kwayar idanun shi. Daidai lokacin da idanunshi suka kai ga sanyin idaniyarshi.
Ya dade yana kallon su yana murmushi, har bai san tsayin mintunan da ya bata a tsaye ba, ba tare da yaje gare su ba, don ganin yadda hankalinsu ya raja’a a kan wasansu. Har sai lokacin da Amir ya karawa Habib keken shi ya fadi, ya sanya kuka.
Da sassarfa ya karasa garesu, ya mika hannuwa ya dauki Habib wanda ke ta kuka ya rungume a kirjinshi, ya kuma kama hannun Amir suka doshi kofar gidan. Su Lawan suka gaishe shi suka koma ga kwallon su, Lawan na radawa Ahmed Baban su Amir ne.


Aikin marking takardun dalibai ya kacame mata, ta yi dai-dai da takardu a tsakiyar falon sanye cikin riga da wandon da basu kama jikinta ba, kanta babu kallabi, tufkar gashinta a tsakiyar kanta. Fatar nan ta kara zama fresh ta nuna mace danya sharaf, mai wadatar jini a jika, ta yadda ba za ka yi tunanin ta taba haihuwa ba.
Sassanyan kamshin ‘miyaki’ da ta dade da sani ne ya bakunci hancinta. A razane ta cira kai. Ta sake yin arba, da dan Abdurrahaman Gaya. Rungume da ‘yan biyunshi masu tsananin kama dashi.
Sai dai wannan AMIRUN ya sha banban da wanda ta bari shekaru uku a baya. Ya sirance, ya bar lallausar kasumba ta bata kyawun shi da tsarin shi, duk da haka yana nan a Amirun sa, dan gaye, mai kyau, kuma mai sanyi, wanda idaniya ba za ta taba gajiyawa da kallon shi ba.


Mikewa ta yi tsaye kamar an umarce ta da yin hakan, alama ce ta girmamawa a wajen bature. Ta rasa cikin yanayin da ta tsinci kanta tsakanin rudewa da gigicewa. Sannan wani sanyi ya tsirga a zuciyarta, ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar shi din ne, ba mai kama da shi ba.
Kafin ta yi wani action ya daga dogayen kafafunshi da sassarfa ya isa gareta, ya hada ta ita da yaran ya rungume, jikinshi in ban da kyarma ba abinda yake. Ya kankame ta ita da yaran hawayenshi na sauka a gadon bayansu. Ya ce,
“Mairo kin yi min alkawari........ ba za ki taba barina ba, kin yi min alkawari...... we are meant for each other. Me yasa kika karya?
Kin riga kin sani kowanne numfashina yana fita ne tare da sunanki. Me yasa kika amsawa Uncle Junaidu, kika kasa jirana mu maida auren mu? Kika kasa yi min uziri? Uzurin da zan yiwa Daddy biyayya, kada ya ga rashin juriyata?
Ya ya zamu yi da ’ya’yan da Allah ya bamu bayan fidda rai da samun su? Baki yi sha’awar ki rayu tare da su ba? Ki basu tarbiyya irin taki? Jarrabawa ce Allah ya yi mana, kuma mun cinye ta da ikonsa, yanzu ne ya kamata mu karbi sakamakon mu.
Zan nemi Uncle Junaid in roke shi alfarmar ya bar min ke, ko da hakan na nufin zan durkusa masa akan gwiwoyina, don na fishi bukatarki, ‘ya’yanmu sun fishi bukatarki.
Kalle ni. Am all alone Mairo, leading a shattered life.........!!!


Dukkansu basu ankara da wanzuwar mutum a falon ba, tsayin lokacin da suke rungume da juna suna kuka dukkaninsu, su suna yi ‘ya’yan na yi. Sai jin karar rufe kofa da aka yi a hankali, suka juyo dukkanninsu, babu kowa!
Amma kamshin ‘Irresistible Givenchy’ da Mairo ta ji, ya tabbatar mata da ko wane ne ya shigo, ya kuma fita, ba tare da ya yi wani motsi da zai katse su daga kololuwar duniyar shaukin soyayyar juna da kewar juna da suka fada ciki ba.


Hankalin Mairo ya tashi, ta tabbatar Uncle Junaidu ya ga Amiru, cikin halin da ita kanta ba ta san wanne ne ba. Ta zame da karfi, da gudu ta biyo bayan shi amma sai kurar motarshi da hasken fitilar motar shi ta gani.
Ta rasa ina za ta sa kanta, sai ta kifa kai cikin tafukanta ta soma kuka. La shakka maza biyu take so, ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.


Lallashi na duniya, ban baki na duniya Amiru ya yi amma Mairo ta ki ce da shi komai. Ransa ya fara baci, amma ya danne fushinsa, tunda mai nema.....baya fushi. Ya ce,
“Shi ke nan na tafi Mairo, na ba ki daga yau zuwa gobe ki yi tunani, zan je wajen Baffa daga nan zan wuce inda na yi masauki, sai gobe insha Allahu”.
Ya dauki Amir ya kama hannun Habib za su fita, ta taso da gudu ta rike rigar shi ta baya cikin kuka ta ce,
“Ina za ka kai su?”
Ya harare ta ya ce, “Gidan ubansu, tunda bakya son ubansu to suma bakya son su”.
Ta ce, “Ni na ce hakan?”
Ya yi mata kallon rahma, sannan ya ce, “Za su taya ni kwana ne”.
Ba ta yi magana ba, ta shige daki ta hado musu duk abin da za su bukata cikin karamar jaka ta ba shi. Suka ce, “Mummy bye-bye”. Ita ma ta daga hannun tana yi musu bye-bye din har suka fice daga falon.
Cikin hanzari ta dauki waya ta soma kiran nambar V.C Junaidu, bugu daya ya amsa, babu komi cikin muryarshi sai kulawa ya ce,
“Ya aka yi MARYAMA?”


Ta shafe hawaye ta ce,
“Ka fasa zuwa yin ‘dinner’ din?”
Ya yi murmushi ya runtse idonsa, tsigar jikinsa na wani irin tashi saboda KISHI. Idanunshi na tariyo mishi hoton abin da ya gani, wani image da bai taba ganin mafi muninsa a rayuwarsa ba, cikin sanyin murya ya ce,
“Na zo na tarar kina da bako, don haka na tafi”.
A raunane ta ce,
“Ba bako bane Baban su Amir ne ya zo ganin su”.
A ranshi ya ce,
“Ka ji rainin hankali irin na ‘ya’ya mata....”. Amma a zahiri ya ce,
“Ki saurare ni, idan na gama da Baffa zan kira ki”. Ya kashe layin.


Damuwar duniya ta ishe ta, ta kuma rasa abin yi, ta shiga halin rudani. Wadannan dakarun maza, jaruman soyayya sun sanya ta a kwana. Tana neman Dina, tana neman Nabilah..... don neman shawara, tunda an ce “Aikin mai shawara baya baci”.


Ta kira wayar Nabila, ta ce, “In kina gari zan zo gobe around 11”. Ta ce,
“Ina nan amaryar uncle sai kin zo”.
8/9/21, 9:04 PM - Kawata: 87






Junaid na yin parking a harabar gidan Baffa, shima Amiru na sawo kai, suka yiwa juna kallon-kallo, bayan kowanne ya fito daga motarsa. Kwayar idon Amiru har girgiza take saboda KISHI, akwai wani feeling na kishi iri daya a zuciyar kowannen su, sai dai babu wanda ya bari nashi ya fito fili.
Da sauri Amir da dan uwansa suka balle kofa suka nufi Uncle Junaid suka rungume kafafun shi, ya russuna ya kama kowannen su da hannu daya ya dauke su, suna ta zuba mishi surutu wai Mummy tana kuka, don Abban Abuja ya taho dasu. Ya yi murmushi ya ce,
“Zamu je mu lallashi Mummy ta daina kuka”.


An ce “mai Da, wawa..... sai Amiru ya karaso a hankali, ya mikawa V.C hannu, suka yi musabaha, aka rasa wanda zai fara janye hannunsa. Dai-dai sanda Baffa ya fito, ya yi musu jagora zuwa falon ganawa da bakinsa.
Kallo daya zaka yiwa Alh. Abbas, ka san cewa shima a rikice yake, ya debo gorar ruwa da tambulan cikin firij ya baiwa kowannen su. Aka rasa mai fara sha, aka rasa mai fara magana. Har shi kansa Baffan kuwa, kafin Junaid ya yi gyaran murya cike da tausayin Baban Amir da Habib da ya ke ratsa zuciyarsa. Da ganin wannan ‘giant’ kaga wanda ke fama da dingimemiyar soyayya, wadda ta rasa madafa. Yaran sun baibaye Uncle Junaidu sun kwanta a jikinsa.
Ya ce,
“Baffa na janye niyyata ta auren Maryama! Na hakura har ga Allah na barwa Baban Amir da Habib, ina bayan Maryama ta koma dakin mijinta uban ‘ya’yanta, don samun kwanciyar hankalin kowannen mu.
Ba lallai sai na auri Mairo ba shi ne zan nuna ina kaunar ta, a’a, ni da Mairo mun wuce haka, Yaya ne da kanwarsa, alakarmu hadi ne daga Allah, ba don mu yi aure ba.
Ina son ‘yan biyu su tashi gaban uwa da ubansu......kamar yadda Maryama ta tashi gaban Innarta da Babanta, ta san dadin iyaye, tasan amfanin su. Nikuma ina bukatar addu’arku Baffa, da fatan dorewar zumunci na har abada a tsakanin mu”.


Baffa ya ce,
“Allahu Akbar! Allahu akbar!! Wannan shi ne halin GIRMA, halin ‘yan aljannah!! Da gaske ne kai da Mairo kun fi karfin soyayyah!!! Sai ‘yan uwantaka, mun gode da wannan karamci Junaidu, Allah ya biya maka bukatunka na duniya da lahira, ya kara maka daukaka, ya baka duk abinda kakeso a duniya da lahira......”.


Amiru ya cira kai ya tsura ma Junaid ido ya ce, “In aka yi hakan, ni kuma na so kaina.......”.
Junaidu ya ce,
“Ni kuma ba zan auri Mairo alhalin zuciyarta na ga tsohon mijinta ba”.
Amiru yace
“nayi rantsuwa da Allah! Mairo tayi maka son da ni bata yimin ba, na aure ta ba da son ranta ba, sai a hankali na koya mata soyayyata. Uncle Junaidu kana da matsayi mai girma a gun Mairo, wanda ni bani da shi.....”
Junaid ya rausayar da kai cikin jin wani irin frin ciki a zuciyarsa, koda wannan ya tsira ya tabbata ya isheshi rayuwar duniya, yayi murmushi ya ce,
“Kauna ce tsakanina da Mairo Amiru ba soyayyar aure ba tun daga ranar dana fara ganinta, a halin yanzu jin nauyin junanmu ya fi yawa, wanda da kyar za mu iya sakin jiki da juna mu yi rayuwar aure yadda ya kamata. Ka yarda ko kada ka yarda, kai Mairo take yiwa soyayyar aure....!”


Amiru ya lumshe ido, ya ce,
“Uncle Junaid, bani da bakin da zan gode maka....... bani da abin da zan biyaka wannan alfarmar da ka yi min.....” Uncle ya yi murmushi ya katseshi yace,
“Kana dashi Amiru!.
Mairo ta sha bani labarin soyayyar da kanwarka Amina take yi mata, wannan wadda suka zo mai kama da kai. Ta shaida min cewa maigidanta ya rasu. Ka bani Amina in aura Amiru, don wanzar da dauwamammen zumunci a tsakanin mu”.
Cikin al’ajabi Amiru ya ce,
“Amina is special a gare ni ko a cikin kannena goma sha biyu, lallai Amina is among the luckiest....
Na taba gayawa Habibu zan roke ka ka bar mini Mairo, ni kuma in baka kannena hudu ba lefe ba sadaki. Na fada ne kawai a fatar baki, ashe Mala’iku sun amsa. Uncle Allah ya kara GIRMA!”.


Suka hade hannunsu suka cure kamar ba za su saki ba cike da wata shahararriyar kauna daga Allah, Baffa ya ja su doguwar addu’a suka shafa. Baffa ya ce, su barshi da Mairo, su ci gaba da shirye-shiryen su, yana so zai yi mata ba-zata ne. Suka yi murmushi. ***


Kwana ta yi tana gwada lambar Uncle Junaid ba ta samu ba. Ta shiga damuwa sosai. Tsoron ta kada Allah yasa fushi ya yi saboda ganinta da ya yi tare da tsohon mijinta.
Abu kamar wasa Uncle har kwana uku babu wayarshi babu kafarsa cikin gidanta, don haka ta yi tattaki har office amma ba ta same shi ba. Shima Amiru ko sallama bai zo ya yi mata ba, ya kwashe ‘ya’yansa ya tafi Abuja dasu ba ta kara jin duriyarsu ba.
Da albishir mai dadi ya tari Alh. Abdurrahaman da Hajiya Aisha, ya kuma gaya musu bukatar V.C na auren Amina. Daddy da Hajiya suka yi ta hamdala tare da kara yawaita sadaka. Ko da Amir ya tuntubi Amina ya yi mamakin amincewar ta nan take. Bai san ita tunda ta dora ido a kan Junaidun ba ta kara gane kanta ba.


Ya yiwa gidan Habibu tsinke a daren bakinshi ya kasa rufo, zumudin ya gaza boyuwa. Habibu ya dafa kafadarshi ya ce
“Angon Harrit ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login