Showing 66001 words to 69000 words out of 77288 words

Chapter 23 - ABARI YA HUCE Complete 1,2,3,4 Book by Sumayya Abdulkadir Takori .txt

Advertisement

damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka muna da kyakkyawan zaton Zai tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa.
Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce.
"Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da muka rasa auren Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har mu cinye jarrabawarmu.
Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da 'yan uwanshi suka yi, kan halinda yake ciki. Kuma Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti.
Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi gafarar ki sun rasa. Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana.
Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a gabana don na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi mana, yayi mamaki nima nayi mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun soma gani tun a duniya, tunda Amirun na neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko kofar gida Amiru bai kara takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki.
Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya rage ya saketa saida nasa baki tukunna ya hakura.
Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki shikuma ya gaya musu.
Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari ne ga mai juna biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa ki……...bani da Uwa, bani da Uba, sai ke da abinda zaki haifa…."
Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa.
Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce.
"Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye".
Ya ce,
"To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz... Mairona!".
Ta ce
"To ba ni in ci".


Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman kaji ya yi lugub. Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika mata. Ta karba ta soma ci sosai har tana taune harshenta sabida yunwa.


Dina ta shigo rike da kwandon kayan abinci, suka zauna akan kilishi suna ci ita da Habibu. Mairo na kallonsu tana raya abubuwa a ranta, wato ranar da aka kaita gidan Amiru ya takura mata sai ta ci abinci akan idonsa.
Ta kai hannu da sauri ta goge hawayen da suka kara shimfido mata, don ba ta son Yaya Habibu ya gani, ranshi ya baci. Amma ta riga ta san kuka ta dinga yinshi kenan, har karshen rayuwarta. Tunda yanzu itada Amiru sai dai a TUNA BAYA……Yaya zatayi da dimbin soyayyar shi data kankanewa zuciyarta????


















An sallami Mairo ranar wata asabar bayan likitocinta sun tabbatar komi nata ya koma dai-dai. A lokacin cikinta ya cika watanni shidda cif, wanda ya yi dai-dai da cikar Amiru watanni hudu yana jinya.
Suka dawo gidan su Dina, inda a washegari Habibu da Dina suka yi shirin tahowa gida Najeriya. Gidan ya rage daga Mairon sai Hajiya da masu aiki, don Abban Dina bai cika zama ba sai a weekend, kullum yana ofis.
Bata tashi daga inda ta yi sallolin farilla guda biyar, ba tareda ta yiwa Amiru addu'ar neman lafiya daga Ubangiji ba.
Hajiyar Dina na kula da ita yadda ya kamata, ko Innarta iyakacin kulawar da zata yi mata kenan.
Watan Hajiyar Dutsinma biyu tare da su jikinta ya yi kyau ta koma gida.


Kwanaki na mirginawa su zama watanni, har watan Aprilu ya kama, wanda shi ne EDD dinta. Sai dai Mairo ba ta yarda anyi mata ‘scan’ ba. Ranar wata alhamis nakuda ta tashi cikin dare, haihuwa gadan-gadan. Don haka ba da bata lokaci ba Hajiya ta tuka su da kanta suka nufi asibitin da ta ke awo, nan da nan aka karbe ta a (labour ward), nakuda ta tsayin awanni uku cur, kan Hassan ya bullo, kamin likitocin su yi wani yunkuri, shi ma Hussaini ya biyo dan uwansa.
Aka turota dakin hutu, Hajiya na rungume da jariran tana yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, sabida kamar Amiru ya yi kaki ya tofar. Sannan ‘identical twins’ irin wadanda banbacesu zai yi wuya.
Sai dai da alama Hassan kalar Babanshi ne, wato (choculate), yayin da Hussaini ya debo hasken fatar Mairo.
A take Hajiya ta yi waya ta sanar da Habibu, ya yi hamdala ya kuma nemi wayar Alh. Abdurrahman ya sanar da shi, don haka a karshen satin suka dungumo har Hajiyar Amiru dasu Sabah suka iso Malaysia.
Farin ciki a wajen Hajiya Aisha da Alh. Abdurrahman abin ba’a cewa komi. Hajiya har da kukanta na nadama, ga dai ‘ya’ya ba daya ba har biyu Mairo ta Haifa, duk kunyar Mairon ta isheta, ta kama 'yan jikokin ta rungume tana yi musu addu'a, ji take kamar Amirun ne ta rungume a ranar data haifeshi, sai dai dukkaninsu babu mai ra'ayin a yi wani taro sai addu'a da kowa yake yi wa mahaifinsu, wanda har zuwa lokacin ke kwance cikin halin jinya.
Yara sun ci sunan Habib da Amir, babu kuma wanda ya yarda da a sakaya. Ana kiransu da sunansu abinsu.
Bayan su Hajiya sun koma Mairo ta ci gaba da rainon 'yan biyunta cikin koshin lafiya da taimakon (Nanny) Bamaleshiya da Hajiya ta daukar mata.
Kamin watanni hudu sun cika sun yi kiba, sun yi bul kamar 'yan watanni goma sabida samun kulawa da ruwan nono isasshe. A lokacin ne kuma 'addmission' dinta na yin PhD ya fito a 'university of Malaya'.
A satin da zata fara karatu, Yaya Habibu ya zo Malaysia. Yace tayi shiri suje Najeriya ta kaiwa Amiru ‘ya’yan shi ya gansu. Don ya samu sauki har ya soma zuwa ofis. Daddy ya samo mishi aiki a CBN. Don shi Habibun bai yarda su sake yin hadin gwiwar ba kamar yadda Daddy da Amirun suka bukata, yace saboda halin rai. Ya kuma ce da Daddy akwai kudurin da yake dashi a kan bankin nan bada jimawa ba. Amma ba wai don yayi fushi da abinda Hajiya tayi ba.
Mairo bata son wannan tafiyar sai don Yaya Habibu ya matsa mata. Amirun ne bata son gani, don bata son duk wani abu da zai taba zuciyar ta a halin yanzu. Ta riga ta sanyawa zuciyarta YAKANAH (sunan littafin Takori mai zuwa). Ta koya mata dangana, ta koya mata rayuwa ba AMIRU. Karatun ta kawai tasa a gaba, da rainon ‘ya’yan da Allah ya bata.
Lokacin da Daddy ya gayawa Amiru mairo ta haihu har ‘ya’ya biyu, bai nuna wani farin-ciki ba, don yana kullace da Mairo, da bata taba zuwa ta dubashi ba har yayi ciwon sa da jinyarsa ya gama ya gaji ya mike. Bashi da wani sauran buri a rayuwa, tunda ya rasa Mairo.
Sannan Daddy yace babu maganar biko, ba zancen kome, don bai yarda sun gama horuwa ba, Amirun yayi ta zama a gwauro, ko su aura masa mai haihuwa. Ya kuma ce da Amiru in zai mike ya fuskanci sabuwar rayuwa to ya mike, in bazai mike ba, yayi ta kwanciya soyayya ta kassara shi. Don shima yana da nasa laifin. Na kin gaya masa duk abinda ke faruwa saboda tsoro da son Hajiyarsa. Har saida komai ya lalace. Daddy yace
“ita tana son ka ta lalata maka rayuwa?”


A fannin ita Hajiya, zaman Amirun haka babu iyali ya fara damun ta. Tana so tayi zancen biko a maida aure tunda saki daya ne, babu fuska daga Habibu da Daddy. Don haka tasa ido, don ganin hukuncin da suke nufi.
8/9/21, 12:13 PM - Kawata: 33




Saidaifa rayuwar Amiru ta canza sosai. Ya zama babu murmushi babu far’a sai ‘dark-spaces’ kusan koyaushe make a fuskarsa. Sai ayyukan dake gabansa. Ya kudire a ransa idan ba Daddy ne da kansa ya bude baki yace ya maida Mairo ba da bakinsa, to ya hakura da ita har karshen rayuwarsa.
Yamma lis, suka iso filin jirgin saman Abuja. Dina dasu Muhammad sukaje tareda direba filin jirgin suka dauko su. Suna zuwa gida Dina ta karbi yaran tayi musu wanka ta shiryasu da kaya na alfarma. Habibu ya dura su a mota tareda su Muhamnmad da mai rainon su Esta da suka taho da ita daga Malaysia sai Asokoro.
Kasancewar ranar Lahadi ce, Daddy yana gida shida Amiru a karamin falonsa, suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Habibu ya yi sallama rike da mai sunan sa yayinda Muhammad ya biyo bayansa dauke da Amir. Ya saki takardun hannunsa ya bisu da kallo. Ba zaka iya karantar halin da zuciyarshi ke ciki ba.
Suka yiwa kansu mazauni a falon Esta tana waje, Daddy sai murmushi yake yayinda Amiru ya zamo mutummutumi, tsigar jikin shi na tashi cikin kauna da shauki. Ya matso ga Habib dake zaune a cinyar Habibu, ya durkusa a gabansa ya mika mishi hannu, siraran lebbansa dauke da wani irin ni’imtaccen murmushi, da bai taba yi a rayuwarsa ba.
Wata irin kauna ta da da mahaifi ke fizgar zuciyar shi. Amma sai Habib ya noke a kafadar Yaya Habibu wato, bai san shi ba.
Yaji ba dadi, ya koma ga Amir yana karkada mishi ‘ya’yan mukullai, da wayo da dabara ya samu ya yarda ya dauke shi. Ya rungumeshi sosai a kirjinshi yana sunsunar shi. Yana shakar kamshin turaren Mairo (Fahrenheit) daya kama jikin yaron. Ganin dan uwanshi a hannun shi sai shima Habib ya miko hannu, ya hadasu su duka biyun a kirjinsa, sai yaji kamar Mairo ce ya rungume. Amma don mazantaka, bai yarda ya zudda hawayen da suke son bashi kunya ba.
Daddy da Habibu suka bisu da kallo cikin tausayi. Daddy yace “saukar yaushe?” Yace “dazunnan muka iso”.
Dai-dai lokacinda Hajiya ta shigo falon cikin kwalliya ta alfarma. Bakinta ya fadada da far’a da murmushi. Tace
“A’ah! Sababbin masu gidan sun zo, tsofaffi sai su zo su fice…” tana kallon Daddy tana dariya. Ya harareta don yasan dashi take, yace “da tsohuwar zuma ake magani. In dai wadannan ne da ba mazauna ba ai gaki gasu, da sun tafi zaki dawo min ne kina rara-gefe”.
Ba yadda bata yi ba don ta dauke su amma sun like jikin Ubansu. Ta fita ta kawo ‘teddy’ na ‘ya’yan Nina da suka zo hutu sannan suka yarda da ita. Daddy yana son ya tambayi Habibu mai yasa Mairo bata zo ba? Yaga babu dalilin da zai yi masa wannan tambayar sai yayi shiru. Shikuwa Amiru Allah kadai yasan abinda ke cin zuciyar shi. Mairo ta daina son sa……! Mairo bata son ganin sa…..!!

Har goma na dare suna can, yaran suka soma rigima, duk da an basu madara. Uwarsu suke so haikan. Amma Amiru ya kasa bada su. Saida Habibu yayi mishi alkawarin kafin su tafi gobe zai kai mishi su ofis sannan ya dauko su har motar Habibu, bayan Hajiya ta cika su da toshi. Daddy ma ya bada check na kudi masu yawa yace a dinka jamfa, baya son ganin su da daura ‘suit’ irinna Ubansu.


Mairo tayi shirin barci a dakinta dake gidan Yaya Habibu. Ta sanya yaranta a gabanta tana kallon su da fuskar mahaifinsu. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ wanda ya tuna mata da ‘those precious moments’ da suka shude a baya. Tana sunsunar su da kamshin ‘miyaki’ da suka kwaso, wanda ya dawo da so da kaunar mijinta sabo fil a zuciyar ta.
Ta shiga tsakanin su ta rungume kowanne a jikinta. Ta soma sheshshekar kuka a hankali, na tashin tsohon mikin daya jima da samun sauki. Shiyasa bata so zuwa ba, amma Habibu ya takurata. Ta fadi a ranta Amiru ya daina son ta.......! Tunda har bai damu daya ganta ba. A karshe ta hakura ta sanyawa ranta salama. Tunda ance komai yayi farko, to inshallahu yana da karshe WATARANA!


Washegari Habibu ya cika alkawari, ya sake diban Amir da Habib da Esta ya zuba su a mota zai fita da niyyar kaisu office din Amiru suyi sallama kamar yadda yayi alkawari. Yana kokarin tada mota Amiru na sanyo hancin motarsa ‘camero’ cikin get din Habibun. Don haka Habibun ya dakata har ya bude motar ya fito.
Ya karbi ‘ya’yansa ya soma ‘kissing’ kamar bazai bari ba.
Daga can saman bene Mairo ta yaye labulen dakinta don iska ta shigo. Nan ta hango su. Ta kurawa Amir ido. Bayan muguwar ramar da yayi, ya bar lallausar kasumba mara tsari ta cika fuskarshi, abinki da mai yawan gargasa. Sannan ya saya kwayar idon shi cikin ‘dark-spaces’ wanda ya hana mata gano halin da kwayar idanun shi ke ciki.
Karan hancin ya kara fitowa, zirit, kamar karas. Wani irin so na fizgarta. Ta saki labulen a hankali ta koma da baya ta fada a gadonta. Tana mai fidda numfashi da sauri-da-sauri. INAMA ACE…….hannun agogo zai dawo baya???
***
















Washegari suka koma Malaysia. Mairo ta fara karatunta cikin nasara, tana barin yaran a gida wurin mai rainonsu da yake an fara ba su madara. Kafin su cika watanni tara suna gudunsu ko'ina, musamman Alh. Abdurrahman ya bude mata 'account' a nan ‘Kuala-Lampur' duk wata yana sako mata makudan kudi na fita hankali, don lalurorinta da kula da ‘yan jikokinsa.
Bayan kuma ba abin da Ambassada ya rage su da shi, ga na Yaya Habibu. Gaba da baya gata ya lullube Mairo da 'ya'yanta, abin sai godiyar Allah.
Shekaru ukku cif, wadanda suka yi dai-dai da cikarta shekaru talatin a duniya, da kwalin digiri, master, da digiri na kololuwa.


Dr. Maryam Muhammad Bedi, ta tattaro ta dawo gida Najeriya a garin Abuja, zuwa lokacin Habibu ya yi ficce, bankin ‘Habib Bank’ ya samu habaka zuwa 'branches' a dukkan 'thirty six states' da muke da su a gida Najeriya, kamar yadda Amiru Abdurrahman ya yi fata. Yau ga ci gaban ya samu, ba tare da Amiru ba.


A wannan ranar da ake (ten-year anniversary) na cikar bankin shekaru goma da kafuwa, Habibu kuka yake, maimakon ya yi farin ciki.
A yayin da al'ummar taron suka dauka kukan farin ciki yake yi, amma shi kadai yasan dalilin kukansa, wanda bai wuce na alhinin samuwar cigaban shikadai, ba tare da Amiru ba.
A kalaminshi na karshe, bayan ya yiwa mahalarta taron godiya mara iyaka. Ya ce,
"Ya tafi ya bar bankin da kewa, bayan shi ya kirkireshi. Ya bar bankin da babban gibin da har gobe bai cike ba. Na kuma tabbata har abada ba zai cike ba. Sakamakon dumbin ALHERINSA gare ni. A yau na tashi daga mamallakin ‘Habib Bank’, na kyautar da shi ga 'ya'yan AMEERU ABDURRAHMAN GAYA".


Amiru ya daga ido yana kallon shi, extremely puzzled! To haka Alh. Abdurrahman. Ashe wannan shine kudurin da Habibu yace yana dashi kenan akan bankin, ya ki yarda amaida hannun jarin Amiru cikin bankin?
Ya sanya hannu cikin takardu, lauyoyi suka diba, su ma suka rattaba hannu. Sannan ya ce,
“as a servant, zan ci gaba da juya musu dukiyarsu har zuwa girmansu”.
Hajiya ma ta dauko duk takardun dukiyar Amiru dake tare da ita, ta danka mishi. Ya hada dana wajen Habibu ya adana a bankin. A wannan ranar Habibu yayi kuka, kawai sabida tausayin AMEERU. Don gabadaya rayuwarshi ta canza ‘completely’ ta zama ‘no meaning…’ kamar yadda ya fadawa Mairo a baya.


“My life has no meaning......idan ba tareda ke ba”.
***






Habibu ya watsa mata takardun neman aiki, a manyan jami'o'inmu, tun daga Ile-Ife, Ahmadu Bello, Nsukka, Bayero, Lasu da sauransu, ba don neman kudi ba, sai don al'ummar Najeriya su amfana da ilimin da ta wanzar da rayuwarta tana nema, don su amfana.
Ba da jimawa ba jami'o'i har biyar suka dauke ta, ciki kuwa har da jami'ar Abuja, wadanda ta bari a baya. Amma ta zabi BAYERO domin a ganinta al'ummar Kano su ne al'ummarta.
Habibu bai takura mata da zancen aure ba, ko tayin ta koma gidan Amiru. Sai dai shima yana ganin lokacin yayi daya kamata a maidawa Amiru matarsa sabida yadda zawarawa manya-manyan kusoshi ke yi mishi rubdugu, a gida ne ko ofis. Alh. Abdurrahman ya fara tsawatar mata da cewa, ba zata koma Kano ba har sai ta fidda miji ta yi aure.
Sai ta sa musu kuka tana rokonsu, kada su kara yi mata zancen aure, idan ba so suke ita ma CIWON ZUCIYAr ya kamata ba. Me zata yi da wani da namiji ba Amiru ba? Me zata nema a jikin wani namiji bayan Amiru? Amiru yasa ta raina sauran maza, ta yadda har basa burgeta, duk ilminsu da mukamin su kuwa.
Gashi da alama Daddy baya son komen nasu. Tunda koda wasa bai taba furtawa ba. Ya kama Mairo da Habibu ya rungume kamar shi ya haife su, ya jibanci dukkan al’amuransu, amma baya ko son kallon Mairo da sunan matar Amiru. Itama kuma tunda hakane bazata taba nuna tana son komawar ba, koda hakan na nufin ta auri wani ne ba shi ba!
Alh. Abdurrahman ya ce,
"Aure ya zama dole Mairo, domin shi ne cikar kima, mutumci da darajar diya mace. Duka wadannan kwalayen naki aikin banza ne idan babu aure".
Ta yi masa alkawarin su barta ta fara aikinta, a hankali za ta zabi wanda hankalinta ya kwanta da shi. Ya so ya karbe yaran, amma ta roke shi ya bar mata, zuwa wani dan lokaci kalilan, don suna debe mata kewa.


Gida guda suka bata cikin 'new site', suka tare ita da 'ya'yanta da mai rainonsu, mai suna Lami. A lokacin Lawan da Ahmad 'ya'yan Baffa suna karatu a Bayeron, sai suma suka dawo gidan suna zaune a baskwata.
Baffa yana zuwa duba su akai-akai, su ma suna zuwa idan sun sami lokaci. Mairo ta fara 'lecturing' a 'department of sociology' cikin nasara da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login